Showing 30001 words to 33000 words out of 51618 words
Chapter 11 - Gudun Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
jiya har yanzu yana taso masa
"suis désolé(am sorry),zan fito yanzu naci zan shirya" boyayyar ajiyar zuciya ta saki tana juyawa
"Ka shirya gaba daya don zaka kaini gidan dezatou,conducteur na(driver)baya nan"
"d'accord(okay)" ya amsa mata yana dubanta har ta fice daga falon. Ajiyar zuciya ya sauke me qarfi yana komawa ya zauna saman kujerar falon,jiya kwana yayi zuciyarsa na gaya masa ya bar sultana da su bibi suyi duk yadda sukaga dama,tunda hakannan suka tsarama rayuwarta,bashi kuma da wani mataimaki a cikinsu din da yake gani sune dukkan wani jigo kuma ginshiqi na rayuwarsu gaba daya.
Idan yayi kamar yayi na'am da hakan kuma sai zuciyarsa ta tuna masa da NAFESSA,anya idan yayi hakan ya kyauta?,ya kumayi adalci?,hannunka yana rubewa ne ka yanke ka yar?.
"Kada ka sake saka hannu kace zaka daketa,diya macace ita" Maganar aba kenan da suka zauna da shi bayan ya dawo gida a daren jiya
"Zata daina,wani abun akwai quruciya a ciki,amma da sannu zata daina,tsanani baya tarbiyya mainassara" Kalaman aba ya sake dawo masa.
Kadan yadan daki hannun kujerar da yake kai sannan ya miqe yana komawa bedroom dinsa.
Yaja lokaci a falo yana tariyar abinda ya farun jiya,don haka a yanzun adan gaggauce ya shirya cikin wata shadda gezner da aka yiwa dinkin zamani,ya zauna masa das a jikinsa ya kuma yi masa kyau,duk da cewa shi din ba ma'abocin sanyasu bane. Sassanyan turarensa na ko yaushe ke tashi a jikinsa,ya tsaya gaban madubi ya gyara sumarsa me santsi da baqi ya kuma gyara gashin fuskarsa. Fuskar ta fita sosai,ta bayyanar da zallar kyawu irin na buzun asali.
Yana tafe yana daura agogon hannunsa tare da duba lokacin da ya kashe. Dab da zai gifa sassan bibi wanda tun jiya bai sake komawa ta can ba,daidai lokacin da sultana ke fitowa hannunta dauke da sabuwar game dinta tana nufo harabar gidan,da alama tana neman me saita mata ne.
Kallonta yayi sama da qasa da wani bahagon kallo. Vest ce a jikinta me siririn hannu da iyakacinta gwiwa,sai wando ta ciki wanda bai qarasa sauka idon sawunta ba. Kanta a bude babu koda hula bare ayi batun mayafi,sai sassalkan gashinta dake reto har dokin wuyanta wanda yake daure cikin siririn ribbon. Tsaiwa tayo cak qirjinta yana bugawa. Duk tsaurin idanunka idan ya saka maka lion eyes dinnan nasa sai ya cire maka duk wani qwarin gwiwa taka. Taku biyu tayi baya saita juya da sassarfa tana komawa ciki.
Qwafa yaja zuciyarsa na sake zafafa akan zafin jiya. Duk wani abu da za'a hanata ita kuma shi takeyi. A age dinta sam bai kamata tana fitowa koda veranda dinsu a haka ba bare ta kawo farfajiyar gidan. Ga security zaratan qatti dake kai kawo a wajen.
Da wannan qarin takaicin ya jefa qafansa falon ama din nasa. Ya sameta tayi nisa a breakfast dinta don har ta kusa kammalawa. Kujera yaja ya zauna,daya daga cikin masu aikinta data fara tattara abinda aka bata a wajen ta matso da zummar serving nasa sai ya daga mata hannu yana dakatar da ita.
Abu biyu kadai ya buda a ciki,sai ya bari ya soma zuba Black tea,sam bakinsa bakinsu babu wani dandano. Shi kansa yasan damuwa ce qasan ransa,ya sani yana da fushi sosai da zuciya,shi yasa yake yawan kaucewa abinda duk zai bata masa rai.
Duk yadda yake cakalar abincin ama tana ankare da shi,taso kawar da kai tayi banza da lamarinsa amma ta kasa jurewa,wacce jaraba ce ne wai irin haka?,har yanzu jinin nafessa baibar wahalar da rayuwarta ba?,wai sai yaushe?.
Mug din tangaran din hannunta ta ajjiye,banguls din gold guda biyu dake hannunta suna bada sauti
"Inaso ka shirya cikin kwanaki uku ka koma makaranta,bana kuma buqatar zuwanka a nan kusa" ta baiwa maina umarnin kanta tsaye tana kafeshi da kallo. Shima ita yake kallo kafin ya janye dubansa. Wanne irin umarni ne haka na kai tsaye daga wajen ama din?. Kamar tasan tambayar dake Kai kawo a zuciyarsa kenan ta dora da maganarta ba tare data damu da yadda yayi sak da jin maganar tata ba
"Bana son ganin gilmawarka cikin gidan nan maina,ka fita a harkar 'yarsu,haka sukeson ganinta shin kai meye naka?, nafessa dai ko?,duk yadda kakai ga son nafessa ma wanda ya fika sonta ya dauke abarsa,ka rabu da nafessa ma bare sultana?...... abu na qarshe da zan gaya maka shine,nima ban yarda ka sake kai hannunka fuskar 'yarsu ba,diya macace data soma girma,banaso kada na sake ji ko gani" ta qarasa fada tana nunashi da yatsa kafin ta sauke hannun nata ta miqe tana tura kujerarta baya sannan ta fara sauka daga dining area din tana cewa
"Zan shiga mu gaisa da bibi,ka dauki key din farar Ferrari na" daga haka tayi gaba taba qwalawa me aikinta kira kan ta dauko mata hand bag da mahadin shoe dinta.
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
PAGE 18
Dezatou din na daya daga cikin manyan abokan business na ama,sannan kuma qawa a gareta ta hannun damanta. Mansion House ne da ya cancanci wannan sunan,me dauke da manyan katangu da kuma gini na alfarma tsakiyarshi. Gate na biyu suka zarce kai tsaye bana sun samu tsallake gate din farko, already tasan da zuwansun,don haka maina yana tsaida motar tana isowa wajen.
Gwanar fara'a ce da son mutane,don haka fuskarta wasai da fara'a take cewa
"Wai wai,yau maina nake gani hamdee.......da kin gayamin tare kuke ai da na shirya tarbar baqo na musamman" dan murmushi ama tayi,tana jin dadi sosai akan yadda dezatou ke nuna qaunar maina a fili. Tadan kalleshi kadan,tasan cewa kawai ya kawota ne saboda fushinta na jiya.
Har sunyi gaba dezatou ta juyo
"Shigo mana maina,ya zaka tsaya a nan,kaimafa nan din gidanku ne" kansa ya girgiza kawai yana dan sakin fuska kadan
"Zan jira nan cikin mota,akwai wayar da xan amsa"
"Bazai shiga bafa dezatou,rabu dashi" ama ta fada tana yin gaba
"Shikenan,zan turo meena ta kawo maka ruwa" ta fada tana bin bayan ama.
Cikin motar yayi zamansa yana latsa wayarsa,shige shige kawai yakeyi cikin Instagram yana bibiyar pages din da yakeso yake kuma bin labaran da suke dorawa kullum.
Wani dogon tsaki yaja ya sanya tafin hannunsa yana dafe goshinsa kamar wanda goshin nasa ke masa ciwo,sai ya maida kansa ya jinginar ga kujera yana lumshe idanunsa yana jin zafin abinda ya gama karantawa a wani page yanzu yanzu. Labari ne akan fyade da aka yima wata budurwa,sau da dama yakanyi dana sanin daukar wayarsa aduk sanda yaci karo da labari makamancin wannan,ba kalmar da ya tsana ya kuma qi jininta irin kalmar FYADE din.
Knocking din glass din windown qofar da aka fara yi shi ya sanyashi bude lumsassun idanunsa a hankali.
Tana tsaye daga gaban window din,hannunta riqe da wani kyakkyawan vanish tray me kyau sosai samanshi wani irin cups ne qananu da gorar ruwa data lemo,sai wani qaramin tray din dake dauke da wasu nau'ikan snacks.
Farar buzuwa ce tas,doguwa sosai,fuskarta dauke da fara'a,sanye cikin riga da wando jeans,kanta wani siririn dan kwali ne da yafi kama da yadi wanda ta daure gashinta da ya sauko kafadarta ta hagu. Budurwa ce da duka duka ba zata wuce shekaru sha takwas ba. Fuskarta shimfide da murmushi take dubansa. Sai ya dauke kansa sannan yasa hannu ya sauke glass din,a maimakon ya bude mata cikin motar kamar yadda take da buqata
"Yaa maina,ta yaya zan saka maka tray din." Ta tambayeshi tana narke wuya cikin shagwaba. Kanshi ya sake daukewa ransa yana baci. Baisan me ya sanya dabi'ar saka qananun kaya da rashin damuwa da hijab ko babban mayafi ta zame musu al'ada ba. Kaman meenatun a yanxun yana ganin ta wuce munzalin yawo da irin wannan suturar,amma su a wajensu basu ga hakan ba,hasalima dai dai ne.
"Na gode,zaki iya maidawa ciki" ya amsata ba tare da ya waiwayo ba.
Dukka gwiwarta ya kashe mata da Maganarsa,tunda mommy dinta tace mata maina dinne yazo takuma kai masa ruwa da snacks hankalinta ya dauku. Ya jima yana burgeta,ta dade tana qissimashi cikin ranta a matsayin miji,saidai tana mugun shakkarsa,yana kuma yi mata matuqar kwarjini sosai,don koda taje gidansu daga gaisuwa babu abinda yake sake hadasu. To yau din tana ganin ta samu wata babbar dama da ko yaya zatayi wani motsi da zata isar masa da saqon zuciyarta,sai gashi shi din kuma ya katsi hanzarinta.
A sanyayen ta juya tana komawa cikin gidan,wanda da shigarta da kadawar wayarsa duka ba'a yi minti guda ba. Ama ce,sai ya daga yana saka wayar a kunnensa
"Aliyyu"
"Na'am" ya amsa mata
"Wanne irin shashanci ne wannan?,ya yarinya zata kawo maka ruwa ka maidota bakasha komai ba?,wannan ba maida alkhairi baya bane?"
"Afwan" ya fada a gajarce
"Gatanan dawowa,koda ruwan kasha ladan kyautata makan da tayi"
"In sha Allah" ya sake amsawa ama din sannan ta kashe wayar.
Iska ya furzar daga bakinsa yana kallon wani guri na daban. Ta cikin madubi yaga tahowarta,don haka kafin ta iso ya bude side din da yake,abinda ya yiwa meena din dadi sosai ta saki murmushi sanda ta iso tana miqa masa ruwan.
Hannu ya sanya ya dauki gora daya yana cewa
"Na gode" sai ya maida qafafunsa cikin motar yaja murfin ya rufe a hankali. Dan saroro tayi kafin kuma ta juya a hankali tana sake komawa cikin gidan,ranta duka a jagule babu dadi, wato kisan mummuqe yayi mata ruwa ne ya dauka kuma yayi godiya,ya yiwa amansa abinda takeso ba wani qorafi kuma da zata kai.
Sun dan jima suna waya da sultan kafin ama ya iskoshi. Tare suka fito da hajja dezatou din da meena dinma kanta. Tanayi tana satar kallon maina din har suka gama sallama,sai ta matso saitin window dinsa cikin siriryar murya take magana bayan ta miqa masa ledar turaruka
"Yaa maina.....ka gaida gida mun gode sosai da ziyara"
"Au yama gaida gida shi daya meena abun 'yar haka ne?" Ama ta fada tana kallonta cikin dariya. Dariyar tayi itama tana dan sunne kai
"Kiyi haquri ama,ki gaida gida kema mun gode"
"Banaso,sai dana roqa" ta fadi cikin dariyar tsokana maina yana tayar da mota.
Shuru ne ya fara biyo baya cikin motar kafin ama tayi magana
"Kaga meena ko?,yarinya nutsatsiya me hankali,kullum daga makaranta sai gida" ama din ta fadi
"Uhmmm" mainan ya amsa mata
"Ba ruwanta ba surutu ko hayaniya ko rawar kai,shekararnan zata gama karatunta,hajiya dezatou so takeyi ta bada aurenta ko kudinta a kawo idan yaso saita dora karatunta"
"Uhmmm" maina din ya sake fadi
"sanda zataci rabin karatun sai ayi auren,kafin takai ga haihuwa ma qila ta kammala karatunta"
"Hrmmmm" ya kuma fadi idanunsa suna kan titi. Wani kallon takaici ama ta bishi da shi
"Hala kam kurmantaka ta sameka maina?" Ta jefa masa tambayar cikin hasala. Kadan ya waiwayo ya dubeta sannan ya maida dubansa ga titi
"Me ya faru ama?"
"Ya ina baka labari kaman me ciwon baki?,daga hmmm sai hrmmm?" Dariya taso qwace masa amma ya daure,ya fuskanci inda ama din ta dosa tsaf,saidai kuma shi sam baiga macen data dace ya aureta ba kaf fadin niger da maqotanta,a yanzun dai bai gani ba,shi ko kusa ko alama meena batayi masa ba,baiga wani abu tattare da ita na musamman ba,shi da yakeson macen da ilimin addini suka ratsata ainun,ilimin boko dinma ya samu mazauni a wajenta,macen da shigarta ta banbanta da shigar matan qasar nijer ma gaba daya,shidai a yanzu cikin qasarsu baiga matar aurensa ba,kaf cikin matan da yake gani baiga wadda ta taba burgeshi koda kuwa sau daya ba
"Kiyi haquri ama,ai labari kike bani,bazaiyiwu kuma na katseki ba"
"Kaji dashi dai......ni meenatu banga ta dace da kowa ba saikai,ita nake maka sha'awa,saboda haka ka maida hankalinka,zaka saka rana ka koma ku sake ganin juna kai da ita"
"Allah yayi zabi mafi alkhairi" kawai yace da aman. Babu wani zafafawa,shi yasan halin ama,a yanzun rigima kawai takeji,shi yasa ya lallabata aka bar maganar a haka. Yanzun banda rigimar ama shi daketa kiciniyar ganin ya zama cikakken likita kuma soja wa yake ta wannan batun?,baijin yanzun zai kalli ma wata diya mace,har sai ya kammala cika mafarkinsa da tun yana yaro qanqani yakeyi.
Suna parking harabar gidan suka taka zuwa haraba ta biyu qasan rumfar da aka tanada saboda hutawa ya hanga cike da matasan yara,koda ya duba still dai sultana ce gang leader. Agogon hannunsa ya kalla ranshi yana baci,dai dai lokacin da ya dace ace tana islamiyya amma ta tara mutane ana buga game ana ihu.
Dole ya dauke kansa ya kuma taushi zuciyarsa yayi wucewarsa ciki,amma na ankare da shi,hakan kuma da yayin ya kwantar mata da hankali,ko banza tasan aliyyu din me biyayya ne.
Ta gabansu ta wuce,kusan hada baki sukayi suka gaidata. Wani abu guda daya dake bawa kowa mamaki cikin gidan. Yadda sultana din ke ganin girman ama ainun cikin gidan,tana cikin jerin sahun mutum ukun da ko meye sukayi mata bata iya maida musu martani.
Ita dinma kadaran kadaham ta amsa musu tana wucewa ciki.
******** To cikin kwanakin ukun da ama tace masa a cikinsun ya shirya ya koma makarantar. Abinda ya sake baiwa sultana dama tayi wata irin sakewa,komai nata gaba gadi take yinsa,koda bibi ta soma fada yanzu zata saki kuka,kukan da yake mugun raunata bibi din.
Hankalinta kwance ta baje kolinta,koda akayi hutu ma,dogon hutun da yakan dauki dalibai a qalla wata uku tafiya tayi yawan hutu abinta cikin dangi da 'yan uwa da suke abun arziqi tasu tazo daya. Abinda ya sake taka muhimmiyar rawa wajen koyon abubuwa da yawa a tattare da ita,saboda kusan duk gidan da taje din gida ne da yaran gidan basusan wani abu waishi takura matsi ko sanya takunkumi ba
(Kira a nan a gareku iyaye,bawai yara sunyi hutu ba a dauki kuma dabi'ar zuwa hutu gidajen 'yan uwa,a kula da inda yaro zayaje,a tabbatar inda zaije din saidai ya koyo wasu zababbun kyawawan halaye bawai ya sake bankada ko azama cikin nashi dabi'un da akeson rabashi da su ba).
Duk da maina din ya zare hannu da jiki da yawa daga cikin sha'aninnikanta amma hakan bai sanya a boye ya zare hannu daga kanta ba,a duk sanda yazo gida hutu yana biye da komai nata,abun da yake sake bata masa rai na rashin ci gaba akan dabi'unta saima koma baya da ake sake samu. Tuni a islamiyya dukka yaran gidan da suke aji daya sukayi gaba suka barta. Don su najma da lamira yanzun haka suna ajin sauka,watanni kadan zasuyi khatama. Ko a boko dinma don kawai tsarin makaranta ne na 'ya'yan masu dashi,abinda ya tseratar da ita kawai kenan,amma a matakin karatun dake cikin kanta duka duka bai wuce ace a sannan tana primary ba.
Abun yana daga masa hankali ta yadda kowa ya gaza hango abinda shidin yake hangowa,ko kuma yace me ruwa da tsaki da kuma damar sakata ko hanata suka gaza gano hakan. Ba abbansa kadai ba,hatta oncle bashar da oncle umar din suma duk sammakal. Wata irin soyayya ce gaba daya ta uwarta da kakanta wato dan uwansu suka aza mata,wani irin gata da ko quda basuso ya cutata mata.
Ama dinsa ce kadai yake hangen tana hangen abinda yake hange din,zuciyarsa ta jima tana gaya masa zata iya tallafa masa wajen taro sultana. Yana shakkar tararta da maganar,amma ranar da abun ya cishi tura dole ya isketa da batun.
Wani babban album ne a hannunta amma saita rufeshi tana kallonsa
"Maina,ka cireni daga wannan