Showing 27001 words to 30000 words out of 43918 words

Chapter 10 - Bani Da Gata Book 1 Hausa Novel Complete

Ladingo   

11 Dec 2024

382

Naimey, inda ta auri me kuɗin gaske, shekarata biyu da aure Fawwad shima yay aure auran soyayya me zafin gaske shida ummee, sai dai ba a gari suke ba suna can kauyan Agadez Audarass, wanda duk faɗin Agadez ba wanda bai san da suba wajan kudi a kauyen Agadez, ummee macace buzuwa kyakyawa ajin ƙarshe a kyau, gasu da kudi suma ga kyau ita da Fawwad biyu ce ta hadu. Saida suka shekara biyu da aure Allah ya bata ciki, bayan wata tara ta haifo yan biyu kyawawa masu kama da Fawwad sak, turawa sak mace da namiji faɗin murna wajan Muhammed da lallah tamkar ba jikoki ba, liyafa suka haɗa ta musamman, gidansu ummee ma haka abin yake hajja Nini mahaifiyar ummee a can Audarass ta tara jama'a anci an sha.
Bayan shekaru biyar da haihuwar su Adam da Hauwa'u aka saka su A school ta ƴaƴan wane da wane, lokacin shekarun Hassana da Hussaina ƴaƴan Rukaiyya biyu a duniya, kanwar baban su Adamcy, wanda mahaifinsu Mustapah mukutar ya ɗora masu san duniya.

Tin Adamcy na yaro zaka san cewar ba karamin miskili bane na bugawa a jarida, sai de akwai maida hankali wajan karatun islamiyya da boko, saida suka shekara goma cif aka haifi Adiya kanwarsu, me shegen ɓacin tsiya da sangarta, shiyasa Adamcy baya yinta, Jiddah ce kawarsa baya da aboki bare a bokiya, tare suke karatunsu, ajininsu ɗaya ba a taɓa banbanta masu kome ba, sai bayan gama secondry school ɗin su ne yay aboki Farouq to shine abokin sa har yanzu dan tare suka je Naimey suka shiga University wanda a lokacin ne soyayya me karfi ta kullu tsakanin Hussaina da Admcy amma sun maida hankali kan katatunsu ,dan lokacin tana secondry bata gama ba, akayi rashin sa'a Hassanar hussaina duk duniya ba wanda take so bayan Adamcy, sai de ta boye hakan ganin ba ita ake so ba asali ma ita karatu ne gabanta ba kamar Hussaina ba wacce tace tana gama secondry bazata ci gaba ba...

Bayan Adamcy ya gama karatunsa wanda ya karanci fannin Bank da kuma business ya sake tafiya Canada yay shekara ɗaya ya dawo lokacin ya bijiru da maganar auran Hussaina ɗingi sunyi na'am da auran zumunci zai ƙaru Muhammed kakansu yafi kowa murna, duk sunaga Adamcy yayi zafin cewa zaiyi aure, sai de kashhh kana naka Allah na nashi ana gobe ɗaurin aurensu Adamcy da Hauwa'u dan rana ɗaya aka saka auransu, sunce ɗaya bazai aure yabar faya ba, Allah yasa tanada masoyinta..
Fawwad yana fitowa daga wajan aiki sai murna yake gobe zai aurar da yaransa yan biyu, babbar mota tabi kansa yana cikin ƙaramar motarsa yana driving, ai faɗar tashin hankali a garin Agadez ba a cewa kome mutuwar ta girgiza jama'a Admacy kusan hauka yayi dan kwanan sa uku baisan inda kansa yake ba, haka ummee ma lallah da Muhammed sun shiga tashin hankali mafi muni, dole aka ɗaga auran sai da kome ya lafa akayi sadakar arba'in su Hussaina tunda suka zo gun mutuwa basu koma ba sai bayan an ɗaura auran dan ba ayi biki ba Adamcy yace baya buƙata, haka Jiddah ma gidanta kawai aka kaita, haka dai akayi abu ba dadi abin tausayi sun zama marayu sai kakanin su masu sonsu...
Bayan sun koma Naimey Adamcy ya tare a tamfatsetsan gidansa da Fawwad ya gina masa a Plateau suka tare da Hussaina wanda daket ta samu ya sake har ya fara fita aiki lokacin ana tsakiyar gina masa companyn sa ga aikin bank da yake, masha Allahu a sannu a sannu suke zuba soyayya mai tsayawa a zuciya kasancewar Hussaina macace mai nutsuwa da tarbiya da hakuri sona son juna kamar zasu ci juna ɗanye koda yaushe basa gajiya da junasu sai de idan baya gida kawai. Hassana sai bayan mutuwar da wata uku tazo daga Egipt tayi gaisuwa dan suna cikin karatu sosai, ba damar tahowa sai da suka sami hutu watan ta ɗaya ta koma.
Adamcy yana ba Hussaina kulawa sosai duk wata uku sai sunzo duba ummee dasu lallah. Da haka har suka shekara da aure lokacin an gama gina kamfanin Adamcy an kama aiki tuburan kuma lokacin Muhammed da matarsa suka koma Naimey da zama kusan jikokinsu, lokacin ne Hussaina take fama da laulayi dan dai ba sosai ba a kwai lokacin da dole ya zauna ya hakura da fita yay jinyar bebensa, har Allah ya bata ɗan sauƙi ita ce take matsa masa da ya fita ana fa buƙatarsa a wajan aiki, kiyawa yay sai ɗa ya roki lallah tazo tana wuni tikun ya fara fita, cikin ya shiga wata uku ne Nini ta rasu mahaifiyar Ummee shine suka shigo jirgi suka zo Agadez daga nan suka shiga mota suka nufo Audarass wanda suna shigowa suka ci karo da Ma'azzara...

Wannan shine cikaken tarihin su Adamcy,

*Wacece Ma'azzara*

Sa'ad Sahabi Nazir ould shine cikeken sunan mahaifin Ma'azzara, Sahabi Nazir ould baƙin buzu ne, kyawawa sosai sai de Allah bai masu arziki ba, amma yana ƙoƙarin ya farantama iyalinsa, matansa biyu uwar gida karima sai amarya Agaishina, yaran Sahabi hudu rak a duniya Kabiru wanda ake cema haliru, sai Salamatu sai Fauziyya wacce ta fita daban dan ba ruwanta yarinyar sune ƴaƴan karima, sai Sa'ad auta shine ɗan Agaishina, karima baƙin kishine da ita na masifa, Agaishina tana shan wuya hannunta ga salamatu da shegen baƙin jinin tsiya tin tana karama saboda baƙin halinta irin na uwarta, haka dai tafiyar tayi tafiya har yaran suka girma sukayi aure inda Fauziyya tayi aure a tahoua salamatu kuwa saboda tusar tsiya daket ta sami malam musa ya kwasa.. Bayan auransu da kusan shekaru biyar tikun Sa'ad shima ya sami Sa'adatu ƴar makwabtan su ce suma masu fita neman abinda zasuci ne babanta ya rasu sai mamanta suka kulla soyayya mai tsanani bayan auransu da sati uku mahaifiyar Sa'a ta rasu ta shiga tashin hankali Agaishina ita take kwantar mata da hankali ta kuma riƙeta kamar ƴarta, karima an sami abin habaici da gori amma Agaishina ko kallo bata isheta ba sabgar gabanta take. Bayan shekara ɗaya da auran su Sa'a ta sami ciki murna wajan Sa'ad ba a magana da Agaishina da Sahabi.
Akwana a tashi Allah ya sauketa lafiya ta sami ɗiyarta zankaɗeɗiya kyakywa baƙa mai farin jini abin ba cewa kome Ranar suna taci sunan *Ma'azzara* Ma'azzara ta taso cikin gata da kulawa Sa'ad na ƙoƙarin bata tarbiya sosai, saboda tin daga kanta Sa'a bata kuma haihuwa ba da ta sami ciki sai ya zube. Ma'azzara kyakywace ajin karshe mai diri da surah, ta taso da sangarta akwaita tsokana da faɗa kusan kullum sai an kai iyayanta gidan megari ƙara, karima tayi ta masu gori Sa'a tayi ta mata nasiya tana gaya mata lillar abinda take idan suka mutu wuya zata sha ta bari, da irin wannan nasihar ta mahaifiyarta yasa ta rage rashin ji ta maida hankalinta da karatun islamiyya da boko...

Kwatsam ana cikin haka Sahabi ya kwanta dama, Sa'ad ya shiga tashin hankali shi da Agaishana dan abun kansu zai ƙare.
abinda ya idar da hargitsa gidan baki ɗaya dan bayan Arba'in suka ce ayi rabon gado ɗaki ɗaya suka basu Sa'ad ya ce Agaishana ta zauna shi zai nemi haya da matarsa da ƴarsa, Agaishina taki taje ta siyar da raƙuminta ɗaya da ya rage ta sami dan filinta tasa aka gina mata ɗaki ɗaya da soron kofa guda tace abata Ma'azzara aka bata suke zaune abinsu, idan ba school ko islamiyya tare suke zuwa tallar maganin zafi kuma suna samun kudi sosai suna rufawa kansu a siri har ma dasu Sa'a...

Kwatsam watarana aka aiko surikin Fauziyya ya rasu Sa'ad da karima da Sa'a sune suka tafi Tahoua gun gaisuwa salamatu tace bazata ba kuɗin mota tsada ita matar malam ce ta kira a waya tayi gaisuwa. Haliru kuwa cewa yayi baya da kudi.
Kwanan su uku suka juyo zasu dawo wanda aka cika su da abin arziki anan ne mai afkuwa ta afku Bus ɗin da suka shigo tayi hatsari kusan mutum goma suka rasu ciki harda Sa'a da Sa'ad da Karima dan ko shurawa basu yiba.
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!!
Wannan mutuwar ta girgiza jama'a Ma'azzara kusan haukacewa tayi Agaishana kuwa ba a cewa kome sai godiyar Allah, salamatu tayi sanyi ta rinƙa saka Ma'azzara ajiki wai tausayinta take yanzu amma kafin ake arbain har ta manta har an koma ƴar gidan jiya, sai kyama da tsamgwama daket Agaishina ta daure akayi arbain suka ɗauki duk wani abu mai ɗan kyau zasu bar gidan su koma can gidan ta, Salamatu da Haliru suka hana suka ce kayan ɗan uwansu ne gaisha tace iya ko da ta haifesa fa nan Ma'azzara tace a barsu da Allah su tafi haka ko suka bar gidan suka koma can gidansu na da...

Ma'azzara yanzu tayi sanyi bata hayaniya sai afkin kuka tana faɗin bata da gata Agaishana tace tana da gata itace gatanta da kuma Allah.
Cikin wannan yanayin ne Adamcy ya rinƙa zauwa mafarkinta ko da yaushe ta kwanta shine take gani suna wani irin gurin shaƙatawa, yana yawan rungumeta da shan bakinta da faɗa mata kalaman soyayya masu taushi kullum burinta Allah ya gwada mata uncle ɗinta namfarki ya sha bakinta taji dadi.
Ana cikin hakane ciwo ya kwantar da Agaishina zama daket tashi daket Ma'azzara itace ke komai na gida ta dafa maganin zafi taje ta sedo da kudin take masu abunci suci har maganin ya kare nan ta shiga tashin hankali ta rinƙa zuwa gidansu lailah kawarta tana amso abunci yau da gobe sai Allah, iyayen lailah suka ce ta rabu da ita ba kunya ubanta yace da Ma'azzara ta rabu da lailah dole ta fasa zuwa ta shiga neman aiktau, tana wanke-wanke ana bata abunci da ɗan kudi tana sayama Agaishina magani, a gidansu ɗan malle tunda ya ganta ya haɗa mta miyau yasha ɗana mata tarko Allah ya kubutar da ita sai ranar ne da ciwon Agaishana yay tsanani, Ma'azzara ta fito neman wanda zai temaka masu kar Agaishana ta mutu, shine fa da ya ganta ya bita har ya samu nasarar kamata sai de kafin ya kai ga cinma burinsa Allah ya temake ta baɗa masa ƙasa idanu ta gudu daidai lokacin Allah ya kawo mata gatanta wato Adamcy da Hussiana wanda suka canza rayuwarta daga rashin gata zuwa gata sai, de bamu san meye zai sake saka Ma'azzara wani rashin gatan ba ko akasin hakan, hummm kude ku biyo ni tare da alkalamin Ladingo yanzu labari zai fara na *bani da gata*

Wannan ne cikaken tarihin su

*Na kudi Ne kan farashi Nera 200 kacal +22792589446/ +22796515805*


*💃🏻Daga Alƙalamin Real ladingo Sweet baby* uwa ga Fareesatu😘

*💖BANI DA GATA💖*




*MALLAKIN*
👇🏻
*Real ladingo Sweet Baby*💋
Yar mutan Niger🤙🏻



*Bismillahir Rahamanir Rahim*



*Chapter 12*


...Yanzu kam cikin Hussaina ya girma sosai haihuwa ko yau ko gobe, duk wani abu da ake buƙata na haihuwa Adamcy ya tanada domin fariya ce kawai bayayi wajan siyan kayan beby, ita kanta Hussaina har ƙorafi take yayi yawa amman baya jinta ko kaɗan dan shi zai iya kashe ko nawane akan Hussaina da babynta.


zaune suke a porlour da yake weekend ne Adamcy na kallon labaran yamma a tashar *CNN* Hussaina ce ta dafa Adamcy ta miƙe, shima miƙewa yayi ya bita yasan bata da lafiya duk kwana kinan yana lura da ita bata da lafiya, amman kara da kawaici na Hussaina bazata faɗa ba sai dai shi ya fahimta hakan yana bashi mamaki, har upstair's ya bita yayin da ita kuma taje ta haye bed ɗin tana maida numfashin wahala, domin nakuda takeyi ranga2 saukar tautausan hannunshi taji a tsakiyar gadon bayanta yayin da kamshin turaransa mai sanya zuciya nutsuwa ya daki hancinta, ƙara tamke idanunta tayi tana jin wani sassauci, sannu a hankali ta buɗe magic oil eyes ɗinta ta zuba masa cikin yanayin wahaltuwa, tace"Mn trèsor" ta faɗi tana ciza baki ta damƙe hannunsa sosai.
Adamcy ya zuba mata lumsassun eyes ɗinsa daya zama identity ɗinsa na sanyi da kuma nutsuwa, yasa yace "bebeta sorry little one ne ko?".
ita dai ji takeyi cikin yana murɗamata, sakinta yay wordrobe ɗinta ya nufa wa'ash abaya mai ƙaramin mayafi ya ɗakko mata janyo silifas ɗin ƙofar bethroom ɗin yayi da sauri har yana ɗan tuntuɓe tsugunnawa yayi ya sanya mata sannan ya sanya hannuwansa da iya ƙarfinsa ya sungumeta, sai bakin parking lot Ma'azzara tana ganin haka itama ta miƙe ta bisu a guje tana kiran "Uncle Aunty Hussy haihuwa zatayi ko"? Adamcy ba sautareta ba. Hankalinsa a tashe, bayan wata mota mai kyau ya buɗe ya kwantar da set ɗin duka yayi ya kuma kunna Air Condition ɗin daidai yadda bazai cutar da itaba ko bebyn duk cikin sauri yake gudanar da komi, haka ya koma yana ƙoƙarin zama Ma'azzara ta iso da sauri ganin bazai tsaya sauraranta ba yasa ta sanya wani kuka mai matuƙar firgita mai saurara, da sauri ya dakata yace "Shiru Oyo shigo muje" bata wani yi wata wata ba tabuɗe bayan inda Aunty Hussyn take tashige kan Aunty Hussyn ta dauka ta ɗora a kanta tana shafa fuskarta, Adamcy a guje yabar gidan masu aiki na masu Addu'ar sauka.lafiya. Ma'azzara ko motsi kadan ta kara fuskarta jikin Hussy, ta hau mata magana tana cewa "Sannu Aunty insha Allah zaki haihu lafiya sannu Aunty da sauri Adamcy ya bugi sitiyarin motar yace"shatop kin cikawa mutane kunne da surutu." Ita kam Hussaina zuwa yanzu bata fahimtar komi.

Haka Adamcy yake driving ,cikin tashin hankali har suka isa Hospital, Suna zuwa aka amsheta cikkn gaggawa aka nufi rroom labour da iya, freind ɗin Adamcy ne Faruq ya iso da sauri yasa a ka amshi Hussaina da gaggawa.
Hankalin Adamcy duk ya tashi se goge zufa yafi a kirga amman daya goge sai ta ƙara tsatsafowa tamkar shike naku dar, Ma'azzara tana liƙe dashi tana shara kwalla, Adamcy ya kama hannunta suka zauna ai kuwa ta ɓarke masa da kuka ta faɗa jikinsa ta cusa kanta kirjinsa tana shasheƙar kuka.
Adamcy bai mata magana ba sai hannunsa da ya zagaye bayanta yana buga bayanta cikin sigar lallashi, jin bazata kyaleba yace"Ke bana son damamuwa Addu'a zamu mata Oya yi shiru maza haɗiye kukan ki." Shiru Ma'azzara tayi tana sauke ajiyar zuciya, ta ɗago tana goge hawayen fuskarta, ta janye jikinta daga na Adamcy saboda wani irin yanayi da takeji, ga wani fitinanan kamshinsa.
Ta sanyan tattausan hannunta saman fuskarshi tana goge masa zufa tana hura masa isakar bakinta, tace"Uncle kayi hakuri zata sauka lfy , uncle ina toilet na ɗauro alwalla nayi nafila na roki Allah ya sauke min Hussy na lfy?" ta faɗa ta kura masa idanunta masu matuƙar haske, hawaye na kwaranya a kan fuskarta.
Adamcy ma ita yake kallo ya miƙe ya kama hannunta ya nufi toilet da ita, suna zuwa ya buɗe ya sakata ya tsaya a kofar ya mata nunu da idanu, da sauri ta shige ta rufo kofar, shiko ya tsaya nesa da ita ya fara kai komo, phone ɗinsa ya zaro ya kira number Baffa kakansu, bugo biyu ya ɗaga yake sheda masa suzo hospital shida lallah Hussy na kan guiwa.
Bai jira me zaice ba ya kashe ya kira Rukaiyya mamar Hussaina ya faɗa mata itama nan a rikice ta shirya ko alhaji bata faɗama ba ta kamo hanya.
Ma'azzara na fitowa Adamcy ya kama hannunta ya kaita Office ɗin Farouq nan ta fara sallah.

*BAYAN AWA UKU*

Su mamah da inna lallah duk suna hospital ɗin sunyi cirko-cirko, sai Addu'a suke.
Tunda Hussy ta fara nakudar bata wani lafa ba nakuda take kamar an jona drip, sosai ta galaɓaita dan nurse ɗin dake kanta harta fara tunanin ko bazata iya haihuwar bane? cikin haka taji Hussainar ta saki wani salati da wani irin nishi inda da sauri ta dawo daga tunanin datake ta daina ɗan mamatsa mata cikin daidai nan kuma kukan bebyn ya kartaɗe room ɗin inda ta ida zaroshi aka fita da uwa ciki ɗan lokaci aka gyara mejego da beby masha Allah nurse ɗin ta faɗa dan ganin kyaun beby har tafi iyayanta kyau kamar baturiya.
Tsaf aka naɗota a towel aka fito da ita nurse ɗin da doctor Farouq suka jera inda Adamcy na ganinsu ya taso da sauri,! suma murmushi ne bisa fuskarsu suka miƙa mashi bebyn tana tsokanar shi, ya amsa cikin farin ciki abu ga sarkin kyauta wani haɗaɗɗan ring ne a hannunsa mai matuƙar kyau da tsada dan wani yawan shaƙatawar da sukaje Egipt ya siyeshi ko a lokacin Hussy ce ta yaba dashi shiyasa ya saya, sai walkiya yake yi domin zallar gold ne zareshi yayi yadda yake jin farin ciki bazai iya barin nurse ɗin haka ba dan haka ya miƙa mata yace"Ga tukuice amman bayawa ki jira babban." ya faɗa yana beƙa mata.
Zaro ido nurse Huzaiyya tayi dan tasan zubon nada tsada tace"Ni!"kai ya ɗaga mata dan ya matsu yaje yaga Hussyn amsa tayi hannunta na rawa cike da zumuɗi tana mashi godiya. Adamcy nan ya ma baby Addu'a haɗe da kiran sallah a kunnenta.
Baffa suka iso tare da mamah da lallah suna murna Baffa norènzo ya dirkama Adamcy duka a baya yace" mara kunyar banza bani ɗiyata to na gani."0 Adamcy ya bushe da dariya ya bashi ɗiyar nan suka fara mata Addu'a da mamkin zallar kamarta da Baffan ita sak baturiya ta fito. Ma'azzara cikin murna ta mashe ɗiyar ta matsa gefe tana sunsuna wa ta hana kowa.
Adamci yace da nurse ta kaishi gun matarsa kafin wannan dattijawan su cika ɗakin, gaba ta shiga ya bita a baya har suka isa, inda Ma'azzara ta dinga binsu cikin sauri tana rungume da babyn se murmushi take saki Lallah ce ta mashe babyn, dole Ma'azara ta shiga hannunta goma tana zaro idanu.

Adamcy na shiga ya rungume Hussy yana manna mata kiss ta ko ina yana sunsunata yana zuba mata godiya babu iyaka, Hussaina kuwa kumya ta cikata.
Ma'azzara ce shigo amman bata so tayi magana ya mata tsawa zuwa yanzu tsoron sa takeyi,dan baya mata sauƙi ga barazanar maidata gurin su Salamatu da yake yi in tayi mashi lefi, ita kuma batasan maganar komawar.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login