Showing 3001 words to 6000 words out of 43918 words
kuka ta shige jikinsa Adamsy duk ya rude ya kalli gefen da Ma'azzara take karaf idanunsu suka sark'e da juna, yaga ta kura masa idanu hawaye ya wanke mata fuska, ya ce" Mayya kurwata tafi karfinki kuma ta Husaina ma da kika kama sai kin sakata." Ma'azzara ta sadda kanta tana wasa da yatsotsin hannunta, jini na fita.
Adamsy ya dauki Husaina cak ya dorata saman kujera ya duk'a a gabanta ya ce"Kanwata yi shiru fadi me kike so ayi ina sauraranki Oya fad'amun...?" Husaina ta ce"Kirawo Dr a duba lafiyarta a tsiada dan jinin da yake fita a hannunta kafin na fadama abinda nake so." Ta fad'a a shagwab'e tana dora kanta kirjinsa.
Adamsy ya shafi kanta ya d'agota ya manna mata kiss saman lips dinta, ya lashe mata hawayen fuskarta ya janyeta jikinsa ya mik'e ya ce" Ok mon Bebeta an gama." Ya fad'a yana juyawa ya nufi kofa yaje kirawo Dr.
Ba daɗewa suka dawo dakin tare da likita, ya dubata ya maida mata drip d'in yana mata faɗan ta natsu karta ƙara cirewa ita ko saurararsa ma bata yi saboda hankalinta na can kan Adamsy ta ƙura masa idanu kir sai kallonsa take kamar zata cinyesa, likata yayi mata allura ya fice.
Shi ko Adamsy bai ma san tanayi ba, dan yana can rungume da Husaina a jikinsa yana lallashinta yana faɗa ma daɗaɗan kalamai masu daɗi da sanyaya zuciya, yana ci gaba da lallashinta ya kira Ummeensa a waya ya miƙa mata, tana kuka ta karɓa ta manna akunnenta ta shiga zayyanewa Ummee duk abinda ke faruwa, gashi tana so a taimakawa yarinyar kuma taji tana kuka tana kiran Agaishana bata da lafiya, amma Adamsy yana so ya ƙiya, tana kuka ta ƙarasa faɗa mata komai, daga can Ummeen tace taba Adamsy wayar, yana kallonta ya karɓa ya manna a kunnensa, ya ɗan saurara yana jin abinda Ummeen take faɗa masa, ɗan kallon Husaina yayi kafin yace "Dama ai tunda tanaso Insha Allahu zanyi k'ok'ari iya ƙarfina Ummee zan taimaka mata." Tana jin haka ta janye jikinta da murna ta koma gurin Ma'azzara ta zauna a bakin gadon ta riƙe hannunta tana kallonta cike da tausayinta tace "A wane gari kike?" Tana kallonta a hankali cikin sanyin muryarta tace "Nan... Cikin Audaraas nake..." Nan ta yi mata kwantaccen komai ta faɗa mata har inda take, gyaɗa kai Husaina tayi tana ƙara jin tausayinta tace "Insha Allahu zamu je gidanku a taikamawa Agaishanki kinji.?" Tana murmushi ta gyaɗa mata kai cike da farin ciki ta lumshe idonta tana jin daɗi a ranta.
Sun jima a haka tana riƙe da hannunta, har drip d'in ya kare Adamsy yaje ya kirawo likita yazo ya cire mata ya kara dubata sosai, yace bata da wata matsala, ya basu sallama, Husaina ta tallabota ta taimaka mata ta tashi tana riƙe da ita ta sauko daga gadon suka fice daga d'akin Adamsy na biye dasu a baya yana taɓe bakinsa yana ji aransa, dan dai babu yanda zaiyi da Husaina ne dan baya son ɓacin ranta, amma da babu abinda zai kaisa taimakawa wannan abar mai wari har ya sake ɗaukarta a motarsa ya kaita gidansu.
Direct inda yayi parking motarsa suka nufa ya buɗewa Husaina ta shigar da ita baya ta zauna ta rufe mata ƙofa sannan ta shiga gaba kusa da Adamsy ta zauna ta ɗauke kai tana kallon titi ya tada motar suka fara tafiya, ganin tayi shiru tai banza dashi tama ɗauke kanta daga garesa yasa yayi murmushi ya kamo hannunta ya riƙe a nasa yana murzawa a hankali cikin taushin murya ya fara lallaɓarta "Haba Mon Bebeta kiyi hak'uri mana, insha Allahu nayi miki alƙawarin tunda har kina son yarinyar zanyi k'ok'arin taimaka musu, ki kwantar min da hankalinki pls, kin san a kanki zan iya yin komai? So pls ki saki fuskarki bana son ganinta a haka..." Ya faɗa yana shafa kumatunta, tana jin daɗi ta juyo tana kallonsa tana ƙara damƙe hannunsa sosai a nata ta sumbaci kumatunsa tana murmushi tace "Nagode Mon trèsor, Allah ya barmu tare." Yana ci gaba da tuki da hannu ɗaya, ya ɗago hannunta ya kai bakinsa ya sumbata yana ƙara jin sonta sosai a ransa da zuciyarsa.
Haka Ma'azzara tai ta kwatanta musu hanya har suka kai gidansu.
Gidane dan madedeci ginin k'asa da ko soron kofa babu. Parking Adamsy yayi ya kalli Husaina tana rike da hannunsa guda, murmushi dauke kan fuskarta Adamsy ya ce"Oya sai ki fita ku shiga" ya fadi yana tab'e baki da mamakin ta yadda mutum yake rayuwa anan.
Husaina ta saki hannunsa ta bude motar ta fito, ta budewa Ma'azzara ta ce"Fito meye sunanki?" Ma'azzara cikin sanyi maganarta ta ce"Ma'azzara" Husaina ta ce"Wow nice name" Baki Adamsy ya tab'e.
Ma'azzara tana fitowa Husaina ta kama hannunta suka nufi cikin dan k'aramin gidan, ba tare da kyankyamin komi ba.
Adamsy ya rakasu da idanunsa masu ruwan zaiba ya dauki wayarsa yana latsawa yayi dailing din wata number bugo d'aya aka dauka.
Adamsy ya ce"Salut cava?" Faruq yayi dariya ya ce CV très bien wai kai dan wulakanci shine ka bar Naimey kun tafi Agadez ko ka kirani kace hajiya Nini ta rasu ai da munzo tare kowa a motarsa zaizo." Adamsy ya saki siririn murmushi saida dimples dinsa suka loba fararan
hakoransa suka baiyana, cikin daddadar muryasa ya ce" Afuwan my Umaruru wlh a jirgi muka zo duk dan musa mu sutura amma ina Ummee ta ce an binneta tun yau da safe, naga kiranka yau Husaina rigima ta keji". Nan dai ya bashi labarin duk abinda da ya faru Faruq ya masa fadan kar yayi hakan dan wulakanci ba halinsa bane, ya temaka mata Allah zai bashi lada.
Suna shiga Ma'azzara ta nufo d'akin sa gudu tana shiga dakin ta iske Gaishina ba yadda take Ma'azzara ta fashe da kuka ta fada samanta.
Husaina ta shigo dakin hankalinta a tashe.
Ta ce"Ma'azzara kibar kuka tashi kamata muje hospital" Husaina ba tare da kyankyami ba ta kama gaishana tana fitar da numfashi daket Ma'azzara ta kamata tana kuka Husaina ta ce"Ma'azzara saketa zan rik'eta dauki kayan da zaki canza gobe da safe ki saka hijabi ki cire mayafin." Ma'azzara jikinta na rawa ta nufi gurin gari yayi zafinta ta ciro riga da zani na bakin yadisu na bugaje mai.kyau duk yasha ruwa a wanke fes sai kamshi yake ta daukarma gaishana ma ta cire mayafin, ta saka hijabi ta linke mayafin ta nasa cikin ledar kayansu ta iso gurin Husaina.
Husaina ta ce"yauwa to kamata mu tafi." Ma'azzara ta kama sharan kafadar gaishana Husaina share suka fito.
Adamsy yana hangosu ya kashe wayar da suke da Faruk Babban aminsa ya fito ya bude musu motar suka shigar Gaishina, wacce take a halin jigatuwa dan Adamsy yayi mugun tsorata da ganin tsohuwar sai sannu ya ke mata.
Ma'azzara ta shiga kusanta ta zauna Adamsy ya rufo mota ya kama hannun Husaina ya shigar da ita gaba ya rufo ya zagaya ya shiga ya tashi motar ya dauki hanyar hospital din da suka fito.
Husaina ta kwantar da kanta kirjin Adamsy yana driving da hannu daya dayan yana shafa kanta da fuskarta, Husaina ta ce" Adamsyna" Ya shafi fuskarta ya ce"Na'am Husaianta yi hakuri zan temaka musu hakika suna neman temako." Shiru Husaina tayi ta lafe jikinsa.
Ma'azzara ma tana rungume da Gaishina sai wani irin nishi take da huci.
Suna zuwa hospital likitoci suka amshi gaishana aka fara bata teamakon gagawa domin ceto ranta dan tana mawuyacin hali.
Husaina ta rungume Ma'azzara tana kuka tana lallashinta. Adamsy sai hararan Ma'azzara yake dan gani yake ta amshe masa matarsa.
Kusan 2 hours sukayi kafin likintan ya fito.
Lokacin Ma'azzara tayi bacci jikin Husaina.
Adamsy ya tari likitan ya ce"Dr yaya mai jikin?" Dr ya ce Alhmdllh da sauki amma gaskiya ciwon ya cita sosai dan kodarta d'ayar har ta fara zagwanyewa, dan wlh dole gobe sai an mata operation amma dole Agadez zaku kaita ayi k'ok'ari goben ." Adamsy ya ce"Allah ya kaimu insha Allah babu damuwa a bata duk kulawar da ya dace goben da zaran anyi sallah Asubah zan zo na tafi da ita." Dr ya amsa da "babu damuwa ku shiga ku ganta"Adamsy bai yi magana ba ya daga kansa ya dawo gurin Husaina ya ce"Bebeta ya za'ayi tayi bacci tashi muje gida na dan huta". Husaina ta tashi Ma'azzara firgigita ta farka.
Husiana ta kama hannunta suka nufi room din da gaishina take Adamsy na biye dasu.
Suna shiga suka ga an mata Karin ruwa harda abun Karin numfashi a jikinta.
Ma'azzara ta isa kusanta ta dora kanta saman kirjinta ta rufe idanunta.
Tausayinta ya cika Husaina tazo ta kama Ma'azzara ta temaka mata ta hau saman gadon, ta ce"kanwata ki kwanta ki huta zamu je gida da safe zamu zo insha Allah kinji". Ma'azzara ta gyada kanta bata bude idanuba.
Husaina ta gyara mata kwanciyarta ta juyo gurin Adamsy ta kama hannunsa ta ce"Yayana Muje na maka tausa kayi bacci". Murmushi Adamsy ya saki ya kara damke hannunta suka fito ta janyo masu kofar.
Tun a cikin motar Husaina take dannawa Adamsy jikinsa tana masa sannu murmushi kawai yake sakar mata har suka iso kofar gidan.
Rumfa ce katuwa a kofar gidan saboda yan amsar gaisuwa.
Gidan dan madedeci ne ya hadu ta ko ina tamkar ba a kauye ba, Lokacin da suka shiga duk jama'ar gidan sunyi bacci sai Ummee kadai a parlor tana jiransu.
Suna shigowa wata kyakyawar dattijuwa yar kimanin 45 year farar buzuwa mai kyan gaske wacce kallo daya zaka mata kasan akwai masu gidan rana.
Ummee ta tarbesu ta rungume Husaina Adamsy ya rungume Ummee ya shagwab'e ya ce"Ummee ni baki tawa sai ta yarki" Ummee ta kai masa dukan wasa ta ce"To yanzu abar gaishe-gaishe sai da safe kuje kuyi wanka ku huta na shirya maku komai". Ta fad'a tana sakinsu ta shige bedroom.
Adamsy ganin Ummee ta shige ya dauki Husaina cak suka nufi part din da suke sauka idan sunzo.
Suna zuwa wanka sukayi saka saka kayan bacci suka kwanta manne da junsu Husaina ta dan ma Adamsy tausa har tayi bacci kafin itama baccin ya dauketa tana manne jikin mijinta Asuba ta gari.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Washe gari bayan sunyi sallah Asubah Adamsy ya lallaba Husaina ta koma bacci, dan bayaso tasha wuya ta ce zata bishi Agadez dan so yake ya isa da wuri da zaran an gama operation ya dawo Audarass bayan ya nemi mai kula da tsohuwar.
Adamsy ya fad'ama Ummee komi ta bashi goyan baya barin ma da taji gaishana ce dan tasan tsohuwar sosai, duk zauwar da zatayi kauyan sukan gaisa kayan breakfast Ummee ta hada masa ya taho dasu.
Adamsy lokacin da yaje hospital Ma'azzara tayi wanka ta canza kaya tayi tsaf da ita bayan tayi sallah ra saka kakarta gaba tana mata hira, dan kasa kunna panpon tayi sai da ta kirawo.likita ya kunna mata.
Adamsy ya bawa Ma'azzara kayan breakfast ta ko amsa ta shige karkashin gado taci iya cinta, dan ya ce gaishana bazata ci komai ba bai wani saki fuskar saba ya dai ce mata ya mai jiki ya zauna kusan gaisha yana mata Sannu amma ina bata san inda take ba tana dai numfashin.
Ma'azzara kuwa bayan ta ci abun da taci ta fito taje ta wanko hannunta ta tsare Adamsy kur da idanu baima san tana yiba a shagwab'e ta ce" Uncle ni ce yar lelanka har goyani kake yi kana mun waka mai dadi da hira mai dadi , har wannan abun da naga kama Anty jiya nima kana mun wai bakajin tsamin bakin mutum wlh ni sai naji kamar zanyi amai...."Manyan idanunsa ya zaro ya mike ransa a bace ya ce"Ke wai uban waye...." maganar sa ce ta tsaya saboda kofar da aka turo Dr tane Adamsy ya juyo ya kallesa Dr ya ce"Yallabai an gama shirya tafiyar" Adamsy ya ce"Ok muje ko" wasu nurse suka shigo da gadon marasa lafiya suka ajiye suka dauki gaishana sai lokacin ta bude idanu tana tari ta kalli Adamsy, shima da sauri ya iso yana mata sannu.
Hannunta ta bashi da sauri Adamsy ya kama ya rike.
Gaishina ta jimke hannunsa, bakinta ta bude tana magana ba'a ji Ma'azzara ta matso ta ce"Gaishnata an sallame mu gida zamu kinji sauki gobe sai ki fadamun maganin zafi na tafi tallah...." Adamsy ya ce"Ke bamuson shirme" gaishina ta ce" Dan Allah ga Amana zan baka ka rik'eta amana bata da kowa bata da gata sai ni sai Allah ina yarinyar jiya ku taru ku rike Amana...." Cak bakinta ya tsaya tana shakuwa tana fadin wani abu amma ba'a jinta, Adamsy cikin tsawa ya cema Dr "Dallah malam ku duba lafiyarta kafin mu wuce Agadez". Adamsy bakinsa ya tsaya cak ganin gaishina bata motsi idanunta a bude tar.
Wata irin zufa yaji ta keto masa.
Nurse suka maidata kan gadon Dr ya fara dubata Ma'azzara ta matso kusan Adamsy ta kamo hannunsa ta ce" Uncle kaga yadda take ko jiyama haka tayi, dan Allah a mata magani itace gatana bani da gata sai ita." Adamsy ya kasa magana jikinsa sai rawa yake gabansa na faduwa.
Muryar Dr ya tsinto yana cewa" Allahu akbar kabiran kullun nafsin za'ikatul maut" Adamsy ya ce"Dr pls karaka cemun ta mutu, dan Allah ni ina zankai Amana, taya daga ganina baki sani ba ki bani amanar mutum, ya zanyi Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun" Ma'azzara ta saki hannuna Adamsy tana ja baya ta kece da kuka ta ce"Karya kuke bata mutuba wlh idan kuka kashe mun gaishana wlh sai kunyi nadama a rayuwarku" ta fada tana kuka ta nufi gun gawar Adamsy ya karaso gurin gawar Ma'azzara ta taba jikin gaishana ba inda yake motsi Adamsy ya beka hannunsa ya shafema gaishana idanu.
Ma'azzara ganin da gaske gaishana ta mutu ta kurma wani gigitaccan ihu tayi luuuuuu zata fadi Adamsy ya tareta ta fado jikinsa sumammiya, Idanu Adamsy ya zaro ya ce"Ya Allah wannan lamari ya kenan"...................✍🏻
*Real Ladingo ce*😅
*Karku manta ya koma na kudi kan fara shi me sauƙi sbd masoya nera 200 kacal +22792589446/+22796515805*
Ummu Fareesa💋
*💖BANI DA GATA💖*
*MALLAKAR*
👇🏻
Yar mutan Niger🤙🏻
*Bismillahir Rahamanir Rahim*
*Chapter 3*
....Adamsy hankalinsa a tashe ya nufo kofar fita, yana rungume da Ma'azzara ganin bata motsi, duk ma ya rikice saboda bai saba shiga irin wannan tashin hankalin ba.
Har ya kai kofar zai fita likitan ya ce"yallabai maidota na temakon gagawa" Adamsy bai juyoba ya tsaya ya ce" Dr muje wani room din saboda inaso a bata kulawa mai kyau ta samu hutu kayi mata alluran bacci wqnsa akalla zata kai lokacin da za'a binne kakarta bata farfado ba, idan san samune ta wuni Rana bacci bayan ba nutsu zan dawo ga amanar Allah". Ya karasa maganar yana ficewa yana mai cike da tarin damuwa fuskarsa ta nuna hakan karara dan baisa ya zaiyi da amanar yarinyar ba.
Adamsy yana fita likitan yabi bayansa tare da nurse guda.
Wani room da ba kowa likitan ya nunama Adamsy ya shiga ya kwantar da ita saman karamin gadon ya gyara mata kwanciyarta ya juya ya fice.
Likinta ya dukufa ceton ran Ma'azzara cikin 30 minutes Ma'azzara ta dawo haiyacinta ta kurma wani uban ihu tana kiran uncle da gaishana, tana fizge-fizge daket likitan ya riketa dama nurse ta hada alluran ta ba Dr ya tsura mata ko minti biyar ba taiba bacci ya dauketa tana kiran uncle da gaishana.
Adamsy yana fita ya nufi motarsa inda ya faka ya shiga ya kira Ummee yana fad'a mata, hankali a tashe ta ce zata turo masa mutum biyu su raho da gawar zata tura a kira Salamatu kanwar gaishina ta fad'ama sauran dangisu su zo a hadu a zauna ayi zaman makokin ana gidan su ummeen tunda Bature da Hassana nason temakonsu itama tana so.
Adamsy ya hana ta fad'ama Husaina dan ka hankalinta ya tashi baya kusa bare ya lallabata.
Haka kuwa akayi Ummee ta turo masa agali da gumar akayi komai aka gama aka basu gawar suka nufi gida, lokacin Ummee har tasa an kirawo yan tsarekun yan uwan su Ma'azzara wanda basu damu da rayuwarsu ba amma harda kukan munafurci kafin ma a iso da gawar, Hussaina kuwa tana can tana barcinta cikin nutsuwa dan ummee bata so ta tajima har sai na binne gaishina.
Ba'adau wani dogon lokaci ba adamcy suka k'araso da gawar gaishina aka shirya gawar aka tafi da ita gidanta na gaskiya.
Usaina ba ita ta tashi ba sai bayan da aka kai gashina yenuwan nasu ma sun soma tafiya , dama su mutuwar bawani damunsu tayi ba dan koh muazzara basu tambaya ba sunsha koke kokensu na karya da nuna tsantsar damuwar .
Daki Adamcy ya wuce dan dubo usaina ya tadda ba kowa a dakin karan ruwan dake fito a setin toilet ya tabbatar mai da usaina na ciki,Zama yayi bakin gado yana jiran fitowarta yashiga kololuwar tunanin Muazzara shi Yanzu ya zeyi da amarta da akabashi Yanzu matarnan tamishi adalci data hadashi da amarna mutum tayaya ze rike amarta bayan ko kadan bason yarinyar yake ba jininshi kwata kwata be hadu da yarinyar ba abunda yakuma samai tsanar yarinyar haukar datake mai tana kiranshi da uncle shi sam besan yazeyi ba ,
Yayi nisa cikin tunaninshi Hussaina ta fito daga wankan datake zaune saman gado ta ganshi yayi jugum kallo daya za'amai asan hankalinshi baya kusa dashi ita sam batasan ma da shigowarshi ba
Murmushi tayi ta k'arasa kusa dashi ta dafo kafadan tace" Mon trèsor meya faru yaushe ka shigo ne, k'okarin seta kanshi yayi da boye damuwarsa ya janyota jikinshi ta zauna kan cinyarshi yace "Ma babe shigowa kenan ,tashi muje na shirya ki Chak yadauke ya dire gaban mirrow yashiga shafa mata mai tare da shiryata cikin salon so da kaunar junaa...
Ta cikin mirror din ta kalleshi tace" Mon trèsor ya jikin Gashinan yaushe za'a mata aikin ne matar nan ba karamin tausayinta nakeji ba kaga irin halin datake ciki da jiya bamu taimaka ba bansan halin da zata shigaba zuwa yau kilama ta iya rasa ranta,
Hankalinshi ne yakuma tashi yasan Husaina batasan da mutuwar gashina ba taya ze Sanar mata da gashina ta mutu yasan halin Husaina da rikicewa akan abunda bekai yakawo ba bare kuma wannan da suka shiga ranta daga haduwar farko.
Maganar Husaina takoma da Adamcy daga duniyar Nazarin daya shiga ,
*💖BANI DA GATA💖*
*MALLAKAR*