Showing 39001 words to 42000 words out of 43918 words
take kuma idanun nata suka ciko da ƙwalla, sake maida idanunsa yayi ya lumshe a hankali yace.
"Waya taɓaki kike ƙoƙarin yi mini kuka?"
Ɗan ƙaramin bakinta ta turo gaba, batare da tace komai ba. Hussaina ne tayi murmushi tare da cewa.
"Ae amana fushi take da kai, kwana biyu kenan bakwa haɗuwa"
Murmushin daya bayyana zallan kyawunsa yayi tare da duban Ma'azzaran, sai a lokacin ta ɗauke ido daga kallonsa, miƙewa tayi tsaye tare da cewa "Bara naje na cire uniform." ta faɗa tana amsar ummu hannun Hassana ta haye sama tana mata wasa.
Harta haura sama Hassana bata ɗauke idanunta akan taba. Adamcy ya miƙe jin ana kiran sallah la'asar. Cikin wani irin tunani Hassana tace.
"Hussaina wace wannan?"
Murmushi Hussaina tayi cikin rashin damuwa tace
"Amanar muce nida Adamsy na"
Idanu Hassana ta juya tare da cewa "Amana kamar ya?"
Babu ɓata lokaci Hussaina ta zayyane mata gaba ɗaya abunda ya faru, da yanda riƙon Ma'azzara yadawo wajen su.
Gyara zama Hassana tayi tare da duban Hussaina cikin matsanancin ɓacin rai tace.
"Hussaina baki da hankali, bakuma ki da tunani, tayaya zaki ɗauko wannan ƙatuwar yarinyar ki aje acikin gidanki?"
Murmushi Hussaina tayi cikin halin ko in kula tace "akwai aibu ayin hakan ne ? Mu'azzara yarinyace babu abun da ta sani, sannan marainiyace, idan ma wani tunanin kikeyi dan Allah Kibari"
Tsuka Hassana tayi cikin takaicin abun dake damunta tace.
"Ko kinsan Yarinyar nan son mijinki take?"
Murmushi Hussy tayi tare da duban ƴar uwartata, cikin nuna mata batasan me takeyi ba tace.
"Dama nasan tunanin da zakiyi kenan dan Allah Hassana karki kawomin tarzoma acikin gidana sam wannan maganan naki ba gaskiya bace"
Murmushi takaici Hassana tayi cikin ƙufula ta miƙe tsaye, duban tsab tayiwa Hussaina, cikin son jaddada mata maganan tace "Nafaɗamiki Yarinyarnan son Adamcy take ko ki yarda ko kada kiyarda wannan badamuwata bace, amma kisa ido zakiyi kallo" tana gama faɗan haka ta ɗauki jakarta tafice daga cikin falon, da kallo kawai Hussaina ta bita tabbas tasan halinsu ya banbanta dana Hassana, domin ita Hassana akwai jinkai ga kuma zafin zuciya, miƙewa itama tayi ta wuce ɗakinta, sam koda wasa batasa zancen Hassanan akanta ba.
Mu'azzara kuwa na shiga ɗaki tayi wanka, wani riga marar nauyi tasa, tama ummu wanka ta shiryata tsaf, kai tsaye ta nufi parlo don samawa cikinta abunda zataci.
Adamsy ne zaune akan dinning area sanye yake da wando 3 quater jeans, wa ta farar singlet ya sanya, goran ruwane a hanunsa yana sha da kaɗan kaɗan, gaba ɗaya hankalinsa naga wayarsa,
Cak Ma'azzara ta tsaya tana kallonsa, tana jijiga Ummu, sosai yayi mata kyau hakanan taji shauƙin zuwa garesa ya kamata, nan take taji wani matsanancin feelings ya rufeta, a hankali ta shiga takawa zuwa garesa, tabbas tasa aranta cewa tana zuwa garesa zatayi hugging ɗinsa.
Cikin nutsuwa Hussaina ke takunta tana ƙoƙarin sauƙowa daga sama taku uku kacal yarage taƙaraso zuwa kan step ɗin da zai bayyanar mata komai dake cikin parlon.
Hakama saura taku uku kacal Mu'azzara taƙarasa ga Adamsy don cika burinta na rungume Adamcy ta haɗa da Ummu Saudat dake manne a kirjinta....
(Tofa readers Hussaina zata gaskata maganar Hassana koya? Ya zataji a yanzu idan takama Ma'azzara tayi hugging din Adamsy a bayan idanunta? Lallai akwai chakwakiya)
*Karku manta littafin nan na kudine kan farashi me sauƙi 200N Kacal👌🏻*
```Ni taku har kullum ```
👇🏻
*Real Ladingo😅*
*Sweet Baby💋*
*💖BANI DA GATA💖*
*MALLAKIN*
*Real ladingo Sweet Baby*💋
Yar mutan Niger🤙🏻
*WANNAN BOOK NA KUƊI NE KAN FARASHI ME SAUƘI NERA 200 KACAL, GA DUK ME BUƘATA ZAKU TUNTUƁENI TA WANNAN LAMBOBIN 👉🏻+22792589444/ +22796515805*
*Bismillahir Rahamanir Rahim*
*Daga yau Na rufe Pagen kyauta😅*
*Last Free page*
*👉🏻15*
Ahankali take tafiya harta ƙarasa kusa da inda yake.
Jin alamun mutum akusa dashi ya sanya shi ɗago da kansa a hankali, ya watsa mata kyawawan idanunsa, wani irin yarrr haka taji ajikinta, take duk wani tunanin dake kanta ya goge, wani irin abu take ji acikin jikinta wanda har batajin zata iya jurewa, hakan yasa kawai tayi ƙasa da kanta, take ƙwalla suka cika idanunta.
Girgiza kai Adamsy yayi kasancewar yasan bazai wuce shirmenta bane ya motsa, sai dai ganin tayi ƙasa da kai, ya sanya a hankali yace.
"Ma'azzara!."
Wani irin sauti nadaban taji muryarsa ya bada acikin kunnenta hakan yasa ta rumtse idanunta.
"Wani abu na damunki ne?." ya tambaya yana me ɗan kallonta, wani irin kuka ne ya ƙwace mata, take ta tafi da gudu tana riƙe da Ummu ta faɗa cikin jikinsa, Adamcy ya janye Ummu dan kar ta jimata, ganin bata haiyacinta, ya kwantar da ita kusan sa. Ma'azzara ta hannuwanta duka ta sanya ta rungumesa, yayin da ta ɓoye fuskarta acikin faffaɗan ƙirjinsa, sosai take kuka mai sauti, tana ƙara shigewa cikin jikinsa.
Kyawawan fararen idanunsa ya lumshe ahankali ya fesar da wani irin numfashi, cikin sanyin jiki, haɗi da yanayin daya ji kansa aciki, sakamakon rungumar da tayi masa ,ya sanya hannunsa yaɗan jayeta daga jikinsa, duban kyakkyawar fuskarta wanda gaba ɗaya ta ɓaci da hawaye yayi, ahankali cikin cool voice ɗinsa yace.
"Waya taɓaki? ko wani abu naki nayi miki ciwo ne? uhmmmm faɗamin kinji Amana." Yaƙare maganar cikin yanayin sanyi, harma da ɗan lumshe idanunsa.
Kasa rage sautin kukan nata tayi, sannan batajin bakinta zai iya kaiwa ga motsi, har ta faɗa masa sirrin zuciyarta.
Ganin taƙicewa komaine ya sanya Adamsy, kamo hannunta, kujeran dake gefe ya jawo zuwa kusa dashi, akan kujeran ya zaunar da ita, cikin tsananin nuna mata kulawa yace.
"Kidaina kukan nan haka, kin daisan banason yawan sakalci da sangarta ko, ki kalleni ki faɗamin meke damunki?."
Sam Ma'azzara ta kasa tsaida kukanta, domin ayanda takejin zuciyarta kukan ne kaɗai mafita, tana me tir da irin wannan zuciyar tata da addabeta akan uncle.
Ganin taƙi daina kukanne kana taƙi yin bayani, ya sanya Adamsy daka mata tsawa cikin faɗa yace.
"Ba tambayarki nakeyi bane? Meyasa bakya jin magana ne ke? Zakimin shirune ko sai na makeki yanzu anan!."
Jin tsawa da faɗansa yasa Ma'azzara shiga yanayin tsoro, amma hakan da yayi sai ya ƙara jefata acikin shauƙin yin kuka, hakan yasa ta ɗan ja baya da tashi tayi akan kujeran, da gudu ta juya inda take sake sakin sabon kuka ta nufi stairs don komawa ɗaki, gaba ɗaya sautin kukanta ya cika falon, sam ko lura da Hussaina dake tsaye tun ɗazu akan stairs ɗin tana kallo da jinsu batayi ba, gaba ɗaya idanunta sun cika da hawaye ko kallon gabanta sosai bata yi.
Jikin Hussaina ne yayi sanyi, da sauri takai hannu dan kamo Ma'zzara amma ina tuni Ma'azzara tayi mata nisa, don har takai ɗakinta.
Har ta gama haurawa steps din bai ɗauƙe idanunsa daga kanta ba, har saida ya daina ganinta, hannuwansa ya sanya inda ya rufe fuskarsa, sam bayason kukan Ma'azzara ko kaɗan, yana jin kukan nata har acikin zuciyarsa.
Abinci yake da niyar ci, amma hakanan yaji gaba ɗaya abincin yafita daga ran shi, ko yunwar ma yaji ya daina jinta, daman baici na rana ba, miƙewa yayi daga zaunen da yake, da sauri ya ɗauki ummu Saudat ya rungumeta ya nufi bedroom ɗinsa yana shiga ya rufo ƙofar, da kallon mamaki Hussaina ta bisa, ta fahimci cewa sam baima ganta ba, ahankali ta gama sauƙowa daga kan step ɗin, kaitsaye ɗakinta dake ƙasa ta nufa.
Adamsy na shiga cikin ɗakin ya faɗa kan gado, ya dora ummu kirjinsa, a hankali ya lumshe idanunsa, yana mejin wasu irin abubuwa na yawo ajikinsa, karon farko kenan da yaji wani abu ajikinsa, sakamon rungumarsa da Ma'azzara tayi, sannan hakanan yaji zuciyarsa tayi masa zafi sosai da ganin hawayenta, wani irin haushin kansa ne duk yabi ya lulluɓesa sakamakon tunawa da irin yanda ya ɗaga mata murya, har yanzun sautin kukanta ne ke yawo acikin kunnensa, rumtse idanunsa yayi da ƙarfi, sakamakon tunawa da yayi cewar itaɗin Amana ce agaresa, sam kome tayi bata cancanci tsawa irin wanda yayi mata ba, wani irin yarrr haka yaji ajikinsa sakamakon tunawa da yanda ta shige cikin jikinsa da yayi, wani irin ɗumi na musamman yaji ajikinsa, da sauri ya kawar da wannan tunanin daga mine ɗinsa, tashi zaune yayi, ahankali yaji zuciyarsa na tsananta bugawa, yayin da yake jin ƙirjinsa yayi masa nauyi kamar zai faɗo, lumshe idanunsa yayi tare da sanya hannu ya dafe daidai saitin zuciyarsa, ko kaɗan baya fatan abun da zai tarwatsa rayuwa da jin daɗinsa, baya son gaskata tunaninsa, sosai yake jin tsoron sabuwar ƙaddaran dake shirin zuwar masa batare daya shiryawa hakan ba, tabbas idan abunda yakeji azuciyarsa ya zamanto gaskiya baisan ya zaiyi da rayuwarsa ba, menene matsayinsa kenan? Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da sanya tafukan hannuwansa ya dafe kansa, tabbas yasan SO yakuma san alamominsa, saidai kuma yana jin tsoron Soyayyar Ma'azzara da ta jima tanacin ƙasan zuciyarsa batare daya sani ba, saidai kuma wani lokaci yakan ji cewa ba soyayya bace, kawai tausayinta yake ji domin itaɗin ta kasance Amana ne agareshi.
Duban agogo yayi yaga ƙarfe 6 hadda rabi, hakan yasa shi kwantar da ummu wacce take ta halba ƙafafunta tana zullo harshe waje, ya shiga toilet ya ɗauro alwala, yana fitowa daga cikin toilet ɗin Hussaina na shigowa, sosai tayi kyau cikin shigar doguwar rigan dake jikinta, dubanta yayi tare da ɗan sakar mata murmushi, itama murmushin tayi masa, ahankali tashiga takowa zuwa garesa, saida ta kawo daf dashi kafun ta tsaya, shagwaɓe fuska tayi tare dayi masa kallon tsantsar so, akasalance tace "Mon trésor masallaci zakajene?."
Kansa ya gyaɗa mata alamar "Eh." murmushi tayi tare da jinjina kanta, so take tayi masa magana akan abun da yayiwa Ma'azzara sam baidace ba, amma kuma wani abu da zuciyarta ke faɗa mata yasanya ta yin shiru, so take tagaskata tunaninta akansa, saboda haka zata ƙyaleshi kawai, matsowa kusa da ita yayi inda ya manna mata kiss akan goshinta, Ummu ta ɗauko, tana kissing ɗinta Adamcy ya kama hannunta suka fice daga cikin ɗakin, suna zuwa falo ya saketa, inda ya fice daga gidan gaba ɗaya, itama ɗakinta ta koma danyin nata sallah'n.
Ma'azzara kuwa koda ta koma ɗakinta, kuka ta cigaba dayi mai tsananin taɓa zuciya, tayi kuka sosai har saida taji kanta nayi mata ciwo, lokaci ɗaya idanunta sukayi luhu luhu dasu, sosai takejin wani irin azababben kewa na game gaba ɗaya ilahirin jikinta, shiga jikinsa da tayi yasa ta shaƙo daddaɗan ƙamshinsa, wanda ako da yaushe ke ƙara hura mata wutar so da sha'awarsa, sosai tsawan da yayi mata ya taɓa zuciyarta, hakan yasa taƙara narkewa tare da jin cewa tarasa madafa, taso ace ya fahimceta amma me yasa yakasa fahimtar ta, tayi alkawali daga yau zata kama kanta, ko mafarkin ma da tanada damar hanashi zuwara mata da tayi, tayi alkawalin ko zata rasa ranta bazata ci Amanar Aunty Hussy ba, ko maza sun ƙara wlh bazata taɓa yarda Hussy taga son mijinta a idanunta ba, ko shi kansa daga yau bazai sake gani ba, sosai yunwa ke ƙwaƙulan cikinta amma hakanan taji abincin ma yafita aranta, jin anata ƙiraye ƙirayen sallan Magriba ne ya sanyata tashi ta ɗauro alwala, koda tayi sallan magriba bata tashi akan sallayan ba nan tazauna tanajiran aƙira sallan isha tayi....
************** ******** **************
Bayan sati ɗaya
Garin Audarass
Acan garin na Audarass kuwa yau Ummee ta kawo masu ziyara, bayan ta kwashi hutun kwana goma A garin na Agade, ta isa lafiya, inda ta shirya da kanta tanufi gidan Salamatu don isar da saƙon da Farouq ya bata.
Tun daga zauren gidan taketa kwaɗa sallama amman babu wanda ya amsata saima hayaniya da masifan da takeji na tashi acikin gidan, tun daga cikin zauren taji wani irin ƙara irin na tusa marar daɗin ji, tuni ma kafun taƙarasa shigowa gidan masifaffen warin na tusa ya ziyartota, da sauri ta sanya mayafinta ta toshe hancinta, kana ta ƙarasa kutsawa cikin gidan, Salamatu ta hango atsakiyar gidan ita da wata mata sai dakuwa suke, yayinda Halliru da kuma Malam Musa ke ta ƙoƙarin rabasu amma sun kasa, tuni zanin Salamatu ya faɗi ƙasa, babu abun da kake hangowa sai wani macaccen buje wanda yaci uban datti,😹 saboda tsabar dattin dayake dashi har baka iya tantance wani kala gareshi, uwa uba jikinsa kota ina jurwaye ne, ba abun dake tashi ajikin bujen sai tsamin tsiya.🙊
Cikin ƙarfin hali irin na Salamatu ta kamo kan Kaltume me adashe,wanda da itane suke faɗan, duk dan wai akan tazo kan maganar adashe, don ankwana biyu Salamatun batayi zubi ba, shine tabiyo jin dalili daganan kuma faɗa ta kaure tsakaninsu, kasancewar dukansu masifaffun mata ne kuma sam basuda haƙuri. Cikin ƙarfin hali irin na Salamatu ta kada Kaltume mai adashe, nanfa ta ɗale kan Kaltumen inda ta kamo kan Kaltumen ta nannaɗe cikin bujenta, wani irin ihu haɗi da kururuwan neman taimako Kaltume ta shiga yi, inda take cewa.
"Wayyo Allah Na jama'a kutaimakeni, zata kasheni da wannan fitinannen warin bujen nata, nashiga uku wani irin buje ne wannan?." Tuni maganan Kaltume ya maƙale sakamakon wata ƙatuwar tusa da Salamatu ta sake, wayyo Allah tuni ɗaci yacika maƙoshin Kaltume mai adashe, yayin da warin tusan yakusa zautar da ita, cikin gajiya haɗi da tsananin neman taimako, tace. "Don girman Allah Malam Musa ka ceceni, zata kasheni wayyo Allah na wannan wani irin masifaffen warine mai kama da guba, wallahi wannan warin na buje da tusan yamafi guba illa." Tarine ya sarƙeta don kuwa tuni cikinta harya fara wuntsulawa, sakamakon wari da tsami.
Ummee dake tsaye ne tasaki murmushi, sosai itakam take mamakin ƙarfin hali, da shegen yawan tusosi irin na Salamatu, ba abunma dake bata dariya kaman yanda Kaltume mai adashe ke ihu tana neman agaji, Malam Musa kuwa babu yanda baiyi ba akan Salamatu ta sauka akan Kaltume, amma sam taƙi saima ƙara zauneta take, Halliru kuwa komawa gefe yayi yanata buga dariyarsa, don ya tabbata Kaltume yau saitayi jinyar kusan sati guda, donshi kansa da sukayi faɗa da Salamatu, duk da baiji ɗoyin bujenta ba, amma saida yayi kwana uku cur yana jinyan jikinsa da kuma numfashinsa wanda ya sanja, yazama idan ma ya shaƙi numfashi warin tusosin Salamatu kawai yake shaƙa, saboda yanda tayita buga masa su, hakanan sanadin faɗansa da ita ya daina jin wari da kuma ƙamshi.
Ganin dagaske Salamatu na shirin nakasa Kaltume yasanya Ummee ƙarasowa da sauri, cikin tausasa murya tace "Hajiya Salamatu ayi haƙuri hakanan, nasan zuwa yanzu ta tuba."
Jin baƙuwar murya yasa Salamatu ɗagowa don ganin wake magana, ganin Hajiya Ummee ya sanyata washe baki, lokaci guda ta miƙe tsaye, cikin farincikin ganin Ummin tace.
"Ranki ya daɗe sannunki da zuwa, ae inanan ina koyawa wannan Kaltumen hankali, bansan da zuwanki ba." Taƙare maganar tana me laluban zaninta ta ɗaura.
Kaltume kuwa jin Salamatu ta ɗagata hakan yasa awahalce ta yunƙura zata tashi, wani irin amaine yazo mata take tashiga kwarara aman awajen, tayi matuƙar galabaita.
Tsalle Salamatu tayi ta dire, cikin sabon fitinan daya ciyota tace.
"Kutumar Ubancan! Kaltume ni kike zubawa ƙazanta acikin gida? kan babban bala'i, to wallahi saikin kwashesa tsaf, kokuwa kisa harshenki ki lashesa, idan bahaka ba kuwa mu ɗaura daga inda muka tsaya, dan Uban mutum ae yanzun kam zai san cewa ba tsoronsa nakeji ba!."
Tuni cikin Kaltume ya ɗuri ruwa, cikin matsanancin tsoro, tayi ƙoƙarin maida aman daya kuma taso mata, tayi imani cewa yanzu kam Salamatu na ƙara maida ita cikin bujenta, to wallahi mutuwa zatayi, yanzun ma kaɗan ya hana ta suma, ko yanzun ma bawai ta tsira bane, dole nema sai taje asibitin cikin gari anyi mata wankin ciki, don warin tusan Salamatu kaɗai ya isa ruɓar da hanji.
Ummee ne taja Salamatu suka koma gefe dan sauri take zata koma, ita kuwa Kaltume tuni ta rarrafa ta arce da gudu batare data kwashe aman da tayin ba, kwafa Salamatu tayi tare da cewa.
"Wallahi zankwashe nakuma samiki aleda abiyoki dashi har gida."
Murmushi kawai Ummee tayi tare da gyara zama, nan suka sake sabon gaisuwa da Salamatun harma dasu Malam Musa, da kuma Halliru, babban ledan dake gabanta ta miƙowa Salamatun cikin halinta na nagarta tace.
"Wannan saƙone daga wajen Farouq , wato wanda yake neman auren Ma'azzara, shida kansa yace akawo muku!."
Baki Salamatu ta washe take ta jawo ledan tare da buɗewa, ganin abun dake ciki yasa ta dafe ƙirji, cikin mamaki tace.
"Ƙalu innalillahi duka wannan nawane? kayafa nake gani niƙi niƙi Hajiya, halan ko mai shegen arzikine shiɗin?."
Jin abun da Salamatun ta faɗa yasa Halliru matsowa da sauri, ya ƙaraso wajen yana kiran Ladi matar sa , so yake ya leƙa cikin ledan amma tuni Salamatu ta kulle bakin ledan ta ɗaga ƙasan bujenta ta tura ledan, fuskarta cike da tsananin farin ciki marar misaltuwa tace.
"Wayyo daɗi barni daraina karka kasheni, ashe Ma'azzara zata zamo alkhairi agaremu, kai nagode sosai Hajiya, Allah yaƙara muku arziki dukanku, a'a wannan abu ae yayi daɗi hahahhhhh, lallai wasu zasu mutu da baƙinciki." Taƙare maganar cikin matsanancin shauƙi, har wani karkaɗa ƙafanta take, tana girgiza kai alaman duniya tafara samuwa agareta.
Murmushi Ummee tayi, tare da miƙewa tayi musu sallama, nan fa Salamatu ta rakota Itada da Halliru da Ladi matarsa, suna tambayar lafiyar Ma'azzara da uwayan hidanta, sun duk a gaishe su, har bakin ƙofar gida suka rakata, Salamatu ta dawo sai washe haƙora take, kai kace bushara akai mata da aljanna.
Tana dawowa gida ta baje akan ɗan rumfan dake bakin ƙofar ɗakinta, nanta buɗe ledan tare da zazzage duk wani abu dayake ciki, atamfofine masu kyau sosai guda uku, sai kuma yadin shadda na maza masu kyau suma guda uku, sai kuma takalman maza ƙafa uku, haka na mata ma irin flat shoe ɗinnan suma masu kyau, sai kum kuɗi naira Jaka ashirin ta cefa, guɗa Salamatu tayi saikuma ga tusa mai ƙarfi ta biyo baya, cikin tsananin jin daɗi tace.
"Ayyiririii!! Saini Salamatu, tabbas dama naji ajikina cewa duniya takusa fara damawa dani, ahayye nanaye!." Taƙare maganar tana sake sakin guɗa.
Ganin uban kayan dake gaban Salamatun yasa Halliru sakin murmushi, cikin jin daɗi yace.
"Kai amma kuwa Salamatu mun more suruki, lalle zamu fantama ji wasu yadukan shadda masu uban kyau." Yaƙare maganar yana kai hannunsa daniyar ɗaukan shadda ɗaya ya duba.
Hannu Salamatu ta sanya