Showing 42001 words to 43918 words out of 43918 words
ta buge nasa hannun, wata uwar tusa ta sake mai shegen masifar wari tare da galla masa harara, aharzuƙe tace "To mazari, sarkin azarbabi, harwani bakin yaba kaya kake dashi, inace nannan kwanakin baya, kadinga zugani kan cewar kada na yarda na bar musu Ma'azzara, yanzu kuma shine da alkhairi ya isoni, kake neman shigewa jikina muci tare ko, to ƙwalelenka."
Hannu Halliru ya sanya ind a ya toshe hancinsa, sosai warin tusan kesawa yana jin ɗaci amaƙoshinsa, kwantar da murya yayi cikin son lallaɓata yace.
"Haba Salamatu mufa ƴan uwan junane, kuma kin manta tun kwanaki muka shirya muka kuma daina faɗa, inkin bani ae ba raguwa zakiyi ba Salamatu, kuma kin manta da cewar ma ita matan ɗazu da sunan Hajiya ta ƙiraki? Hajiya Salamatu fa tace, kika sani ma ko shirye shiryen kaiki Makka suke!." Halliru yafaɗi haka cikin son Koɗa Salamatun.
Aikuwa ta famfu don lokaci guda taji kanta yaƙara girma, take ta washe baki, nan fa taciro shadda kala biyu da takalmi kala ɗaya ta basa, take ya cika da matsanancin murna, haka ma taɗauki shadda kala ɗaya da takalma kala biyu tabawa Malam Musa dake tsaye yana jinsu tun ɗazun, dubu bibbiyu tabawa kowannensu,ita kuma tasa sauran aƙasan bujenta, nan sukayi mata godiya.
*Naimey*
Yau tsawon sati ɗaya da kwna 2 da faruwar al'amarin, Ma'azzara ta kame kanta bata yarda ta nuna wata damuwarta tana ƙoƙarin cire uncle Adamcy a ranta, sau biyu rak suka hadu, amman bata yarda ta nuna masa wani abubu gaishe sa kawai take, ta saki ranta suna hira da Hussy tana ma ummu wasa. Hakan yasa Hussy watsar da duk wani kokwanto, Hassana kusan kullum se tazo amman bata samun ganin Adamcy ko Ma'azzara dan ta maida hankalinta karatu, bata dawowo sai kusan 5 pm.
Yau ta kama Weekend ne Adamcy yana gida amman yana ɓangaransa can suka wuni suna sheƙe ayarsu da Hussy unmu Saudat kuwa na gun Ma'azzara, wacce yau se kuka take ta rasa dalilinsa.
Tunda Adamcy ya fita bayan sun gama more rayuwar su da Husst, yafita gidan bashi yadawo ba sai bayan sallan isha.
Hussaina ce zaune tayi jigum inda take karanta text message ɗin da ƴar uwarta Hassana taturo mata, wanda gama wayarsu da ita kenan, ahankali take karanta text message ɗin, inda aka rubuta saƙo kamar haka.
_Ni ƴar uwarki ce Hussaina, bazan faɗa miki maganar da take bahaka ba, babban kuskuren dakikayi arayuwa shine bawa tsintacciyar mage dama, nafaɗa miki amma kinƙi amincewa, kan cewar lallai yarinyar nan da Adamsy son juna suke, shikenan to amma inaso kibani haɗin kai don mujarraba, idan muka gwadasu kikaga saɓanin abun dana faɗa miki, nayarda kada ki gaskata tunani na._
Shiru Hussaina tayi, har acikin ranta gani take cewa shirme kawai Hassanan nata ke faɗi, waima bayan tace Ma'azzara ne keson Adamsy, yanzu ta dawo tamace wai Admsyn nata ma nason Ma'azzara, murmushi kawai Hussaina tayi, tabbas tasan idan tabiyewa bahagon tunani irin na Hassana, to fa tabbas zata kwan aciki, amma kodan ta ƙaryata tunanin Hassanan zata amince su jarraba, tasan dai babu wani abu tsakanin Ma'azzara da Adamsy, sam baima yiwuwa ace wai Adamsy da Ma'azzara son juna suke, tasa aranta cewa shirmene kawai irin na Hassana.
Tayi nisa acikin tunaninta,saiji tayi ya kwanta abayanta, murmushi tayi tare da juyowa ta fuskancesa.
Idanunsa ɗaya ya kashe mata, ahankali yace. "Kin manta dani ko?."
Lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa ta shafa, tare da shigewa cikin jikinsa, fuskarta ya ɗago inda ya haɗe bakinsu waje ɗaya, ahankali yake bata professional kissing.
Ma'azzara kuwa tana idar da sallan isha, miƙewa tsaye tayi, ɗan madaidaicin fridge ɗin dake cikin ɗakin ta buɗe, goran yoghurt ta ciro, inda tasha kaɗan ta maida sauran, komawa kan gado tayi ta kwanta tare da duƙunƙunewa waje ɗaya, ahankali hawaye ke tsiyaya daga cikin idanunta, kasancewar tayi kuka sosai, hakan yasa tana kwanciya bacci ya ɗauketa, wanda ke cike da mafarkin Uncle ɗinta, mafarki masu daɗi tayi dangane dashi, wanda sune suka gusar da damuwar zuciyarta.
Washegari, Saturday.
Tun 7 yabar gidan domin suna da meeting da wani babban kamfani da zasuyi.
Kasancewar yau weekend yasan ya koda tatashi bata fito ba, sai wajen 8 sannan ta sauƙo, Nan ta iske Aunty Hussaina zaune a falo, tana bawa Ummu Saudat nono, cikin girmamawa tagaishe da Auntyn nata, tare da zama akusa da ita, nan ta karɓi Ummu Saudat ɗin, tanayi mata wasa, duban tsab Hussaina tayiwa Ma'azzaran, take taji wani abu ya ɗarsu aranta, saurin kawar da tunanin da ke ranta tayi, ahankali taƙira sunan Ma'azzaran.
Ɗago kai Ma'azzara tayi ta dubeta, murmushi tayi tare da cewa "Na'am Aunty."
Cikin kulawa Hussaina tace "Meyasame ki naga idanunki sun kunbura, kuka kikayi ne?."
Da sauri Ma'azzara tayi ƙasa da kanta, cikin sanyin murya tace.
"A'a Aunty kawai dai ƙwaro ne ya shiga idona."
Murmushi Hussaina tayi tare da cewa, "Allah ya sauwaƙe."
Tashi tsaye tayi tare da duban Ma'azzaran tace. "Gacan kayan break ɗinki nan a dinning, ki kulamin da Ummu Saudat, ni zanje gida bazan jimaba zan dawo."
"To" Kawai Ma'azzara tace, tare da ƙarasawa gaban dinning ɗin, still tanayiwa Ummu Saudat wasa.
Sama sama Hussaina tayi kwalliya inda tayafa mayafi ajikinta, sallama tayiwa Ma'azzara sannan tafice daga gidan.
Tana fita tasamu Hassana acikin mota, tana shiga cikin motar tace.
"Gaskiya ni gabana faɗuwa yake Hassana, akan menen zaki tursasani zargin mijina da kuma yarinyar da take matsayin amana awajenmu?."
Murmushi Hassana tayi tare da cewa.
"Zaki gaskata maganata nanda wasu mintuna." Key tayiwa motar inda suka gangara can gefen hanya, duban Hussainan tayi tare da cewa "Ƙirasa."
Cikin faɗuwar gaba Hussaina ta danmawa Adamsy ƙira, bugu uku ya ɗauka.
Cikin fargaba ta kwantar da murya tare da cewa.
"Mon trésor ya meeting ɗin dae?"
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
"Lafiya lau mun ma gama ae, kuntafi ne?."
Ɗan jim tayi tare da cewa "Eh, amma na ɗanyi mantuwa please ko zaka koma gida ka ɗaukomin, ina gida saika kawomin please mon trésor!."
Shiru Adamsy yayi tare da cewa.
"Mantuwa kuma? hope ba Ummu Saudat kika manta ba."
Ɗan murmushi tayi tare da cewa "No ba ita bace ita nabarta wajen Ma'azzara, kasan yau saturday ba school."
"Su biyu kaɗai kika bari agidan?."
Mamakin tambayan da yayi matane yasanya ta cewa. "Eh amma ai akwai Hadiza me aiki a ɓangaranta, hakan baiyi bane?."
"A'a" ya faɗa ataƙaice tare da cewa "Sai nazo." ƙitt ya kashe wayan, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da dafe kansa, dama yana buƙatar komawa gida, domin zuciyarsa cike take da son bawa ƴar amanarsa haƙuri akan abun dayayi mata tsawon kwana 8 dole zai lallaɓata ta yanda zata goge tunaninsa daga mine ɗinta.
Hussaina na aje wayar ta dubi Hassana cikin damuwa tace.
"Nafaɗa masa, amma Hassana...."
Da sauri Hassana ta katseta tahanyar cewa. "Shiiii! Kedai ki zuba ido kisha mamaki."
After 25 minute.
Ma'azzara ce zaune akan kujera, gefe kuwa Ummu Saudat ne keta wasa, shiru Ma'azzara tayi tare da lumshe idanunta, sosai take jin matsanancin kewar Uncle ɗinnata, amma kuma idan tatuna da abun da yayi mata kwanaki, sai taji ranta duk ba daɗi.
Cikin takusan mai ɗauke da nutsuwa ya ƙaraso cikin falon, tsayawa yayi tare da cusa duka hannuwansa acikin aljihun wandonsa, inda ya zubawa Ma'azzaran kyawawan idanunsa, wani irin matsanancin tausayin su ne ya rufesa, aƙalla ya ɗauki sama da mintuna 6 yana kallon kyakkyawar fuskarta, ahankali yaƙara so har inda take, zama yayi akusa da ita, batare data saniba dan sosai tayi nisa cikin duniyar tunani.
Ahankali cikin silent voice ɗinsa yaƙira sunanta.
"Ma'azzara!."
Jin sautin muryarsa acikin kunnuwanta, ya sanya ta buɗe idanunta ahankali, tarwal ta sauƙe ganinta akansa, azabure ta tashi tsaye tana me mamakin ganinsa, tuni kuma tsawan daya yi mata kwanaki 8 da suka wuce ya sanya ta ƙarasa miƙewa da sauri, taku ɗaya zuwa biyu tayi ya riƙo lallausan hannunta tare da jawota jikinsa, tuni tataho luuu tafaɗa cikin faffaɗan ƙirjinsa, hannuwansa ya sanya duka biyu ya rungumeta ajikinsa, ae kuwa take tasaki kukan shagwaɓa, idanunsa ya lumshe tare da ɗaura kansa adaidai gefen wuyanta, bakinsa yakai saitin kunnenta ahankali yace.
"Am so sorry Ma'azzara! am really sorry, kwanaki nayi miki faɗa sosai ko, kiyi haƙuri kinji, bazan ƙara ba!!." Cikin matsanancin sanyi ya ƙare maganar.
Jin abun daya faɗa yasa Ma'azzara tasake shigewa cikin jikinsa, still kuka take mai tsuma zuciya, sake tausasa murya yayi inda yace.
"Kiyi haƙuri Ma'azzara, nasan kinajin ciwo sosai, amma girman ciwonki ko kwatankwacin nawa bai kai ba, bansan tayayane zan fahimatar da keba, bansan mezance ba amma kiyi haƙuri, haka tamu ƙaddaran take, natabbatar Faruk zai zamo garkuwa agareki, haka kuma zai baki farin ciki, shi yaka mata kiso, zuciyata tana barazanar tarwatsewa bisa wani dalili na daban, mu ɗau ƙaddaranmu aduk yanda tazo mana shine abu mafi kyau, ki daina kukan nan kinji!!." ya faɗi maganar yana me ɗan bubbuga bayanta.
Ahankali sautin kukan nata ke raguwa, cikin matsanancin bugun zuciyarta daya tsananta tace.
"Uncle yazanyi? nafaɗa ma kaine acikin mafarkina, haka kuma kaine azahirina, Ina Ina Ina......" Muryarta ne ya sarƙe sakamakon kukan daya zo mata.
lumshe idanunsa yayi tare da ɗago fuskarta ya haɗe goshinsu waje ɗaya, har takai ga numfashinsu na gauraya dana juna.
Rab rab rab haka sukaji tafi natashi acikin falon, da sauri ya sauƙe Ma'azzara dake jikinsa, a matuƙar razane su dukansu suka juya, idanu Ma'azzara tazaro cike da matsanancin tsoro, don kuwa Hassana ce ke tafin, yayinda Hussaina kuwa ke tsaye jikin ƙofa, lokaci guda ta fashe da wani irin razanannen kuka mai ɗauke da tsananin tashin hankali, tace"Na rantse da girman Allah se ka zaɓa ayau ko ni ko Wannan tsintacciyar magen a yanzu ɗinan, ashe Namiji ba ɗan goyo bane ba?" Ma'azzara cikin wani mugun tashin gankali da bazai musaltuba tace"Aunty Wlh ba..." Bata ƙarasa ba! Hussy ta ƙaraso wanketa da gigitattun maruka guda uku wandan suka ɗaukema Ma'azzara jinta da kuma ganinta. Cikin ƙaraji tace"Adamu dakai!! Nake zaɓi ɗaya ni da ita a yanzu nan...?" ta faɗa jikinta na ɓari, dede lokacin Ummu ta fashe da kuka tana harba ƙafafunta. Ma'azzara da ko ganin kirki batayi ta miƙe tana tangadi ta nufin gun Ummu zata ɗauketa, Hussy ta fizgota ta hankaɗata ta faɗi ƙasa, saman carpet ta saki wani irin kuka tana cewa"Kai cona ni Ma'azzara banyiwa kaina adalciba na butulcema Aunty ga inda rayuwa ta kaini yau inaji ina gani dole zan rabu da ita ga ummu, ya Allah ka ɗauki raina a yanzu." ta faɗa tana wani irin kuka.
Wani irin faɗuwar gaba ne ya ziyarci Adamcy cikin matsanancin mamaki yake kallonsu, sosai zuciyarsa ke tsalle tana bugawa Ko a famarki bai taɓa zaton irin wannan kaddara zata hau kan saba.
```(Tofa readers, mekuke ganin zaifaru a next page? wanda se Lallai kun biya zaku sani, don yanzu aka fara wasan, shin wai ko kunsan ma cewa Hussaina nada matsanancin zafin kishi? hmmmm kubiya naira 200 kacal kusha karatu, don kuwa wanda bai karanta ba ansha dashi, yanzun aka soma wasan, sannan yanzu wasan ya ɗauko zafi, kada kubari wannan badaƙalar ta wuce ku, don kuwa akwai rigima, zazzafan ƙauna, haɗi da zallan makirci, kudai kubiyoni, ni Ladingo ƴar mutan Niger Uwa ga Fareesatu, don ni kaɗaice zai iya warware muku komai, babban abun tambayan ma shine wazai auri Ma'azzara Adamcy ne ko Fariuq? hahhhhh akwai chakwakiya fa, da wata irin mahaukaciyar soyayya wacce, abin ba'a cewa kome, amma dai sai kun biya zakusha karatu Real Masoya ina jiranku se kunzo gobe zamu fara kafta wasan fa🤣⛹🏻♀️⛹🏻♀️⛹🏻♀️.)```
*Real Ladingo ce*
*Sweet Baby💋*