Showing 9001 words to 12000 words out of 43918 words

Chapter 4 - Bani Da Gata Book 1 Hausa Novel Complete

Ladingo   

11 Dec 2024

379

sammaci daga gidan megari wai su Salamatu sunyi karan Adamcy. Hashim ya ce" Wlh ba inda zaka mahaukatan banza mahaukatan wofi" Adamcy ya mik'e tsaye ya ce"No sai munje bari na kirawo yarinyar". Adamcy ya fad'a yana shiga cikin gida.
Zaune suke a parlon Ma'azzara tana kusan Ummee a zaune kanta sadde a k'asa tana tunanin uncle ko yana ina? Yau bata ganshi ba....!! Sai kawai taji sallamar sa da sauri ta d'ago kanta karaf suka hada idanu, Ma'azzara gabanta ya fadi da karfi saboda wani irin mugun kyau da uncle yayi, yana sanye da shadda maroon coulor karamin dinki, yayi masa masifar kyau sai baza kamshi yake. Sam tayi nisa cikin tunani da kallonsa taji ya mata yar tsawa "Ke wai lafiyarki kina da cutar kallo" firgigit..!! Ma'azzara tayi cikin kunya ta sadda kanta cikin sanyin muryata mai dadin sauraro, tace" Uncle ina kwana" Adamcy ya ce lafiya"ya dauke kansa, ya karasa kusan Hauwa'u ya zauna ya riko hannunta ya ce" Kanwata ya jikin da fatan kin tashi lafiya ya twis dinmu?" Hauwa'u tayi murmushi ta kai masa dukan wasa, tace" Wai Hussaina bazata tashi ba tazo tayi breakfast ne?" Adamcy yay murmushi ya ce" Au bata fito ba ai yanzu bazata fito ba , da sauran lokaci" ya idar da maganar yana sakin Hauwa'u ya mik'e ya koma kusan Ummee, ya zauna ya kwantar da kansa kafadarta. Ummee tayi murmushi ta shafi sumar kansa mai tarin yawa da santsi sai sheki take tace" Bature ka fiye sangarta kai fa ka girma , ka kalli yar amanarka na kallonka" Adamcy ya ce" Yo duk ma nawa nake Ummee zamu gidan megari yan uwan yarinyar sunyi qaranmu" Ummee ta ce" Alhmdllh ai hakan yafi tashi harni za'a tafi....." Adamcy ya katse mata hamzari ya ce" Haba ai kibarni dasu Ummee ki zauna jama'a suna zuwar miki gaisuwa abin ya zama biyu idan ba rashin imani ba ace an musu rasuwa jiya , amma har yau su sami kwarin guiwar yin qara gidan megari" Ummee ta ce" Tashi kuje na yarda da yarona kar ka barmasu yarinyar" Adamcy ya mik'e yana yamutsa fuska ya kalli gefen Ma'azzara kanta a k'asa tana wasa da yatsotin hannunta, hawaye suna shatata saman fuskarta. Adamcy ya karaso gabanta ya sunkuya ya kamo hannunta da sauri ta d'ago kanta hawaye na kwaranya saman fuskarta.
Adamcy ya sanya hannunsa saman fuskarta yana share mata hawayan, yace" Ke ni banaso mutum mai yawan kuka, dan sunyi qara shine yana nufin zan badaki ne ai suna rayan ta bani Amanarki insha Allahu nine zan rik'e ki bisa amana Oya tashi muje mu dawo". Ya karasa maganar yana mik'ar da ita tsaye. Ma'azzara ta damke hannunsa gama kanta k'asa sadda ta ce" Uncle ina Anty?" Adamcy ya yamutsa fuska bai ce mata komai ba, dan baya son yawan surutu. Ummee ta ce"Tana bacci Ma'azzara kuje ku dawo kafin kuzo ta tashi" Kai Ma'azzara ta gyada. Saratu kanwar ummee ta ce" Muje tare wlh mutananan basuda tunani"
Hauwa'u ma ta mik'e ta ce" 'Dan uwana ina zuwa" Adamcy yana rik'e da hannun Ma'azzara ya ce"No Jiddah bazaki iya ba ki zauna ya fad'a yana ficewa, Saratu tabi bayansa.

Suna fita kasancewa ba nisa kusa ne a k'afa suka tafi yana rik'e da hannun Ma'azzara jama'ar da suka santa sai mamaki suke , ina ta san bature su hudu suka tafi, da Hashim da Saratu sai kuma shi uban gaiyar da Ma'azzara.
Suna dab da karya kwanar gidan megari Ma'azzara tayi tozali da 'Dan malle, ihu Ma'azzara ta saki jikinta yana rawa ta rukumkume Adamcy ta fashe da kuka tana cewa" Uncle shine wlh shine ka boyeni karya cutar dani , sanadinsa na rasa gaishina na". Adamcy ya riketa yana cewa" Ke ki nutsu shi wa? Gani ina tare dake babu abinda zai sameki " ya fadi ya janyeta daga jikinsa ya kalli b'angaran da Ma'azzara ta nuna masa. Ai 'Dan malle yana ganin yadda Ma'azzara ta rikice da wanda take tare dasu kafin ma su juyo suga waye wayam ya gudu. Adamcy ya waiga baiga komai ba yaja tsaki, ya ce "Wai kinada hankali ma kuwa?" Hashim ya ce" Adam muje sai kayi hakuri harda maraici yake damunta" Saratu ta ce" Baiwar Allah duk a rikice take" Adamcy bai dai yi magana ba ya kama hannunta suka tafi.

Kofar gidan megari cike take da jama'a yan kallon shari'a, Salamatu da Haliru da wasu mata biyu yan uwansu suna zaune.
Haka su Adamcy suka iso da sallama. Cikin girmamawa megari ya tarbe su, ganin dan Hajiya Sumaiyya ne wato Ummee bayan sun gama gaisawa Hashim ya ce" Malam Hamisu gamu mune bayin Allah nan suke qara" megari Hamisu ya gyara zamansa, ya kalli Adamcy wanda ko a jikinsa yana zaune Ma'azzara kusansa zaune ya kurama Ma'azzara idanu yayi gyaran murya ya ce" Allah Sarki Ma'azzara haka kika dawo abin tausayi da kin addabi yan gari da rashin kunya da daukar magana kullum sai an kawo karanki, amma tunda su Sa'ad da Sa'adatu suka kwanta dama, sanadin gobara, ba fada ba'a sake kawo k'aran ki ba, tallar maganin zafin ki kikeyi keda gaishina, Allah ya jiqan Sa'ad da Sa'adatu da gaishana...." Adamcy ya katse masa hamzari ya ce" Yallabai mu ba wannan dogon tarihin ya kawo mu ba shari'a mukazo". Megari Hamisu ya ce" To Alhmdllh ke Salamatu kince yarinya diyar yayanki ce kuma muma munsan da haka" Salamatu ta ce" Yauwa megari shiyasa na kawosu a kwatar mana 'yarmu" Megari ya kalli Adamcy ya ce" To kai yaro ya akayi Ma'azzara tazo gidanku ita da kakarta har ta rasu kuka rik'e ta a gidnaku?" Adamcy ya saki murmushi ya kurama megari idanu ya ce" Yauwa naji dadin tambayar, yanzun nan zan fad'a muku". Tas Adamcy ya kwashe komai tun daga bigeta a mota har zuwa yadda a kayi kakarta ta bashi amanarta. Ya karasa maganar da cewa" Dan haka babu wanda ya isa ya mashi yarinyar daga gareni" Megari ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Tabbas kai ka cika dan halak kaida matarka dan yakin rabi natane, dan haka nima na goyi bayan ka rike amanar da aka baka wanda yan uwan ubanata suka kasa rik'ewa, dan haka ni babu wata shari'a da zan muku, ku tashi kuje a gaishe min da hajiya Sumaiyya". Ma'azzara wani irin farin ciki ya lulubeta ta kalli Adamcy tana murna ta ce" Unclena" Kallonta yayi ya sakar mata murmushi, ya kama hannunta ya mikar da ita duk dan yaba su Salamatu haushi. Ai kuwa Salamatu ta ciki tayi fam ta mike tana masifa ta ce"Wlh bazamu yarda ba ai wannan son kaine, dan sunada kudi shine za'a basu gaskiya, muda 'yarmu" Haliru yace" Ke muje insha Allahu sai mu kwatota kekuma shegiya munafuka mai manyan idanu zaki ci gidanku bakisan halin masu kudi bane, yanzu haka sunada manufar yin hakan". Ma'azzara duk ta tsorata da yadda Salamatu da Haliru suke mata masifa ta rike Adamcy tana hawaye tana girgiza kai. Adamcy a harzuke ya saki Ma'azzara yayi kan Haliru Hashim ya rikeshi" Megari ya ce "Adamu karka biye masu zafin talauci yake damunsu kuje ku tafi". Adamcy ya ciza lips dinsa ya fara tafiya ko waiwaye ba yayi.

Saratu da Hashim suna biye dashi, Ma'azzara tayi gudu ta isko Adamcy tana biye dashi ta kirasa" Uncle" ya kalli gefanta ya bata hannunsa da sauri ta dora bak'ak'en zara-zaran hannunta saman nashi, ya damke suna tafiya.
Har suka isa gida bai sake magana ba itama bata sake ba.
Saratu da Hashim suna masu dariya yadda za'ayi reno da miskilanci.

Suna zuwa Adamcy ya fad'ama Ummee yadda sukayi a gidan megari Ummee taji dadi sosai yadda megari ya basu hadin kai, duk tasan megarin kansa na rawa. Duk maganar da su ke Ma'azzara bata d'ago kaiba Adamcy ya kalli Ma'azzara tana kusanasa a zaune tana rik'e da hannunsa tana wasa da zoben hannunsa d'aya gold d'aya azurfa sanye cikin zara-zaran yatsotsin hannusa sai wasa take, su Ummee su na masu dariya. Hauwa'u ta ce" Adamuna yar taka alamar zatayi rigima, Ma'azzara ke baki san kin zama budurwa ba?" Shiru Ma'azzara tayi batayi magana ba. Adamcy ya dauke kallons daga kan Ma'azzara ya yamutsa fuska ya ce" To ki sakar mun hannu zan fita ko zoben kike so?". Ma'azzara ta saki hannun Adamcy kanta a sadde ta girgiza kai. Baki ya tab'e ya mik'e ya ce Ummee na tafi na fito da Bebeta tayi breakfast lokacin abuncita yayi" ya fad'a yana saka hannunsa cikin aljihu wando, ya fice cikin takunsa na isassun maza matasa.

Ummee tayi dariya tana kallon Ma'azzara da ta hada kai da guiwa ta ce" Ma'azzara uncle ne?" Kai Ma'azzara ta girgiza ta d'ago cikin sanyinta tace" Ummee zan shiga bayan makewayi" Ummee ta ce tashi kije Adiya tana ciki zata nuna miki yadda zakiyi komai". Da sauri Ma'azzara ta mik'e ta nufi bedroom tana tafe cikin nutsuwarta su Ummee suka bita da kallon tausayi.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
😂Bangaran su Salamatu ita da Haliru Suna zuwa gida suka fara masifa yan uwa suka hadu ana gulma Salamatu da Haliru sai masifa suke da yake gidan na su tsangaya d'aya ce. Salamatu ce tsaye gaban garken awaki, taci uwar d'amara tana k'ok'arin kwance tinkiya dama uwar tinkiya d'aya ce akuya d'aya sai yan awakai uku. Haliru ya ce"Yauwa Salame kiyi maza a saidota zasuci kaniyarsu, duke zamuyi maganin iya shege, mu za'a gwadama kudi wai megari harda mana gorin talauci, ai ko a banza, nasan uwar garkenan za tayi cinquante mille cf wato dubu ashirin da kusan bakwai, kin ga kuwa ai mun tasa". Salamatu ta kwance tinkiyar ta ce" barsu hegu ji suke su kadai sukeda kudi yo Allah na tuba, shi megarin gidansa akwai uwar garkene?" Haliru ya ce"Ina fa sai uwar gulma da take cinsa". Ya fad'a yana kama tinkiyar ya kofa domin tafiya karar siyar da dabobi.

Salamatu ta ce" Wlh karka dade damu suke zancan a gwada mana iskanci". Haliru dai cikin farin ciki ya tafi dan sun dauki alwashin raba Ma'azzara da gidan hutu. Salamatu aikin gida ta shiga kafin Haliru ya dawo.

Hussaina ce d'auro da towel tana tsaye gaban dressing mirror tana shafa mai ta kunnna wakar bonbino tanajin wakar anutse, tana motsa jikinta tana kwaikwayon wakar, dan tana msifar son wakarsa, bata jima da tashi ba sai wanka kawai da tayi. Adamcy ne ya shigo ganin Hussaina bata gansa ba ya saki murmushi hannunsa d'aya a aljihu d'ayan saman fuskarsa yana shafa kwantaccen sajan fuskarshi. yayi dam a hankali ya nufi gunta yadda bazata ganshi ba, yana sakin murmushi sonta da kaunarta na bin duk wata 'kofa da gab'a ta jikinsa sai da ya zo dab da inda zata ganshi ya duk'e yana tafiya a sunkuye. Yasin nagaji😫..............✍🏻
*Real Ladingo ce😅*


*Na kudi Ne kan farashi Nera 200 kacal +22796515805/ +22792589446*



Daga✍🏻 ummu Fareesa yar mutan Niger ina alfahari da k'asata ta gado💋❤️❤️❤️

*💖BANI DA GATA💖*





*MALLAKIN*
👇🏻
```Real Ladingo Sweet Baby💋```



*Bismillahir Rahamanir Rahim*


*Chapter 6*

..... A duk'e Adamcy ya karasa har gun da Hussaina take tsaye gaban dressing mirror tana kwaliya. Hannunsa ya zura a hankali k'asan cinyoyinta ya shafo santala-santalan cinyoyinta ya zura hannunsa gabanta yana shafa pant dinta, yana lumshe manyan idanunsa. A mugun tsorace!! Hussaina ta saki ihu!! Jikinta yana b'ari. Adamcy ya saki sansanyan murmushi cikin sansanyar muryashi mai amon dadi ya ce" Mrs Adamcy nine fa mon bebeta" ya fad'a yana kara zura hannunsa gabanta yana shafawa, ya fizgota ta fado kansa saman kirjinsa ya rungumeta still hannunsa yana k'asanta yana shafawa, ya had'e face dinsu yana hura mata numfashinsa kamshin bakinsa na shiga kofofin hancinta da bakinta.

Hussaina ta janyo numfashi da karfin gaske ta k'ank'ame jikinta, a shagwab'e tace"mon trésor ka bari mana kar kasa na 'bata kwalliyata kaji my Adamcy." Ta fad'a tana fito da harshenta waje tana lasar dogon karan hancinsa zuwa kumatunsa, tana tsotsar habarsa Adamcy ya zaro hannunsa daga k'asanta ya dora hannunsa duka biyu saman cinyoyinta, ya mik'e da ita tsaye cak yana wani irin sansanyan murmushi yana zagayawa da ita tsakiyar d'akin.

Hussaina kuwa tunda taga Adamcyn ta yan tsokanar ne akansa ta sauke ajiyar zuciya tana maida numfashi tana zumburo baki ta sakalo hannunta wuyansa ta kura masa idanunta tana sakin dariya harda kyakyatawa tana cewa"Wayyo mon trésor Adamcy nah ka kusa kasheni , wlh naji tsoro fa, ni saukeni." Adamcy bai saurari Hussaina ba sai da ya gaji da juyi da ita ya sauketa, ya karasa mata kwaliyar ya shiryata tsaf cikin riga da zani na atamfa bak'a mai ratsin fari tayi kyau sosai.
Itama suka shiga bathroom ta temaka masa yayi wanka ta shirya tsaf cikin kananu kaya riga da wando yayi kyau sosai, nan suka baje a parlo suna hira tana manne jikinsa ya bata labarin duk abinda ya faru game da Ma'azzara da dangin babanta, sai da Hussaina tayi kuka daket Adamcy ya lallasheta da mata alkawalin bazai tab'a basu ita ba zai rik'e Ma'azzara da amana tunda hakan ne farin cikinta, sai lokacin ta saki jikinta suna hira duniya.

Bangaran Ma'azzara kuwa tana shiga ciki ta fada saman katifa tana juyi ta dora tafin hannunta saman fuskarta tana shakar kamshin uncle dinta, tana lumshe idanunta tana tuno lokacin da yace mata ko kina son zoben ne na baki? Sai ta dan saki murmushi tana gyada kanta, a hankali cikin sanyin muryata ta furta" Eh uncle ina so kazo ka bani uncle karka barni ka kasance da 'yar amanar ka kai da aunty me kirki." Ta karasa maganar tana juyi saman katifa tana sakin murmushi bata ganin komai sai uncle dinta.

Adiya ce ta shigo tana waya ta zauna gefen katifar da Ma'azzara take, Ma'azzara ta kura mata idanu tana murmushi saboda tsantsar kamar Adiya take da Uncle dinta, sai taga kamar shine.
Adiya kuwa bata san abinda Ma'azzara take ba hirata take da Uncle dinta Sufiyanu da yake France karatu ta shagala tana zuba masa sangarta.
Ma'azzara ta matso kusanta ta kwantar da kanta cinyar Adiya ta rik'e hannunta guda ta lumshe idanunta ba jimawa barci ya d'auketa. Adiya kuwa iyayan surutu har taba Sufiyan labarin Ma'azzara yayanta Adamcy an bashi amana wata yarinya bak'a kyakyawa son kowa, haka tayi tayi ta surutunta har ta gama ta janye Ma'azzara ta fito waje tana ba Ummee labarin uncle Sufiyan.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Bangaran Haliru yana siyar da uwar tinkiya ya wari iya kasonsa ya boye ya shiga gari, bai tashi komawa gida ba sai kusan magarib ya nufo gida da sauran kudin yana cicin magani ta yanda baza ka tab'a ganewa ba yayi cuta.
Salamatu tana tsakar gida ita da Harirah suna shirya yanda zasu d'aura mata aure batare da saninta ba ko iyayan rukonta ba, Haririh kuwa dama irin wannan matan ne makwadaita ta bugi cikin Salamatu ne taji kome dan ta sami yan canji ,dan tasan idan ta kai wannan gulmar gidansu Adamcy zata sami kudi. Haliru ne ya shige da sallama yana yatsina fuska, Salamatu ta Washe baki tana amsa sallamar tace" Haliru kasuwa tayi kyau ko? Nasan kudin ya isa muyi sabgar biki har da kayan d'akin amarya?" Haliru ya iso gaban Salamatu yana wani yamutsa fuska ya zaro kudin jaka ashirin da takwas yabata, ya cire jaka shida dan jika talatin da hudu aka saida tinkiyar.

Salamatu ta amsa ta kirga kudin tayi guda tace uwar garke tayi goshi Haliru sannu da k'ok'ari yanzu mu fara shirye-shiryan bikin shegiya bak'ar daga wannan masakin d'an naka mai farfadiya zamu aura mata, ko wanki kashi ta masa idan farfadiyar tashi ta motsa ai mun 'karu da ita."


Haliru ya had'e face yace"Salamatu bana son cin mutumci fa ai Allah ya dora masa ba mutum ba har zaki fara masa gori, wlh zance ma bana so". Salamatu tayi dariya ta ce"Yi hakuri na bari muyi abinda yake gaban mu shegun mutana nan ba zamu bari su tafi da Ma'azzara ko ina ba....." Kiran magariba ne da ake ya katse musu hura tasu Haliru yayi alwalla ya nufi masallaci, Salamatu tace da Harirah "Wai ke baki tafiya gidanki kiyi sallah ne anya kuwa ba da biyu kikazo nan gidan ba kuwa?" Ai Harirah najin haka ta mik'e tayi mata sallama ta fita ta nufi gida tayi sallah daga can ta tafi gidan su Adamcy kai gulma.

******

Da Misalin 8:30 pm gabaki d'aya sun hallara a parlour an shimfida leda saman carpet an jera kulolun abunci, Hussaina tana kusan Ummee zaune Adamcy na 'barinta ummee na hagun Ma'azzara tana kusan Hauwa'u sai susune kai take, Adiya na kusanta Hashim kanin Ummee ne shi da Saratu duk ba garin suke ba sunzo wajan rasuwa ne.

Hussaina tayi serving din kowa aka fara cin abunci cikin nutsuwa Adamcy kuwa yaki ci coffee kawai yake kurba ya jingina kanshi da kafadar Ummee. Ummee ta kai masa duka tace" Bature wai meyasa baka son cin abunci ne? Kai komai na Fawwad bature ka dauka, Adamu ina fad'a maka rink'a cin abunci da dare, ko da kadan ne dan Allah." Fuska ya dan yamutsa ya shafi cikinsa a hankali cikin sanyin muryasa mai dadin sauraro ya fara magana kamar baya so yace" Ummee dan Allah karki saka yaronki yayi tumbi , ko ya zama kato mana haba ni wlh ko Hussainata bana son tanacin abuncin dare Allah kuwa my ummeena." Ya karasa maganar yana kallon Hussaina wacce take yagar cinyar kaza tana korawa da fruit din kankana.
Ya kalli Ma'azzara wacce ko loma d'aya bata yiba ta dai d'auka amma ta kasa kaiwa bakinta, had'e face yace"Ke me kike jira ne da bazaki ci abunci ba?" Ma'azzara a tsorace ta d'ago da kanta tace"Uncle bana son duk wani abunda baka so nima na koshi bazan ciba." Ta idar da maganar tana sakin kuka.

Adamcy ya zaro idanu yana kallon ikon Allah, Hussaina ta kalli Ma'azzara tana murmushi tace"Babymu 'yar amana kiyi hkr kici karki biya uncle dinki fa, wlh yunwa zata illataka a banza yi shiru kici abunci maza." Adamcy ya ce"Ke bana son shagwab'ar banza ta yaya zaki zauna baki ci abunci ba maza ci ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login