Showing 33001 words to 36000 words out of 43918 words

Chapter 12 - Bani Da Gata Book 1 Hausa Novel Complete

Ladingo   

11 Dec 2024

386

shagwaɓarki mai sani na zauce , kema kiban zumar ki nasha , yauma na karo maki baby kalli fa yaranan yanda sukayi girma.sosai..." Ai kuwa ta gantsara masa cizo a ƴar yatsa yasa ya dakata da maganar, ya ɗan saki kara cikin kunnenta yace "Ayshhhh Hussy an cinye maki hannun bebenki." ya faɗa yana ƙamƙame Ma'azzara.
Ma'azzara ta ɗago tana kwakwaɓe fuska tana yarfa hannunta tace" wayyo Noor Qalbina sorry bazan sake ba muga hannun." ta faɗa tana narai-narai da ido, ta kama hannun ta fito da harshenta tana lasa, ta shiga hura masa iskar bakinta. Adamcy ya saki murmushi ya ƙara manneta jikinsa yana kissing ɗin wuyanta zuwa kirjinta, ya dawo ya mata raɗa a kunneta, yace"Kul ki soma min asara hawayenki banji zafi ba." yaɗa yana dora bakinsa fatar wuyanta yana tsotsa, tana kyalkyala dariya. Bakinsa ya maida cikin kunnenta yana gaya mata maganganu masu dadi, ita ko ta wani narke ajikin sa tana zuba mashi shagwaba, ta saƙala hannuwanta a wuyan sa tana sakin murmushi mai ɗauke da ma'anoni na jin daɗin rayuwa iri-iri... Dai-dai lokacin da Ma'azzara ta shiga wannan tunanin mafarkin tamkar a zahirin gaske abun yake faruwa, se murmushi take tana ƙoƙarin miƙewa ta isa gun Adamcy ta rungumeshi dan ta fice a haiyacin ta...

Farouk ne ya dawo da ita haiyacinta, ta hanyar damƙe hannunta ganin zata tashi.
Firgigit!! tai ta dawo hankalin ta nan take taji kunya, ga wani irin feelings da takeji. Sake kai cup ɗin tea ɗin yay bakinta, kanta ta sadda taki kurba tana girgiza kai, ga kwalla ta dan taru a idanunta. Farouq yace" pls my chouchou sha mana." Hussy tai murmushi tace" Amanatu amshi mana ki ƙarasa pls." ta faɗa tana kama hannun Adamcy tace"mn trèsor imata magana mana." Ma'azzara cikin sanyin murya tace" zansha anty Hussy." ta faɗa tana buɗe bakinta Farouq yana bata tea ɗin. Adamcy ya zuba mata eyes ɗinsa yana kallanta, cikin sa'a kuwa ta ɗago zata kalleshi karaf idanunsu ya saƙe da juna. Adamcy yay mata tambaya da ido mine ne ke damuta?
Kunya taji saboda idanusa masu ɗauke da wani irin sirri wanda idai mace zata kalle shi sai taji wani iri, sai tayi sauri ta sadda kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannu ta, cikin sanyi muryar ta mai dadin sauraro tace "Uncle ba komai."
Yace,"gud to amshi tea ɗin kisha."
Nan ta maida hankalin ta wajan Farouk yana bata tana sha har ta shanye. Hussaina ta taso ta kawo mata Ummu ta amshe ta ta ƙura ma Ummu ido saboda tsantsar kamar da take da Adamcy, shi kuma daman Admacy kamar shi ɗaya da kakan shi na wajan uba.
Nan dai suka ci gaba da firasu suna wasa da dariya, Farouk ya sake dubata bata da wata matsala nan ya ɓallo magugunan ya bata tasha tana ma ummu wasa ta matseta gam jikinta.
Ba'a jimaba ta fara jin bacci tana gyangyaɗi Ummu tana jikinta, tana gyangyaɗin har ta jingina da kafadar Farouk ɗin, sai suka yi kyau sosai tana rungume da yariyar shi kuma ya ɗan tallabota jikinsa. Adamcy ya kalle su ya girgiza kai ya miƙe yana cewa "mon bebe Hussy nah kalli mutana bacci soke." ya faɗa yana isa gun Ma'azzara wacce take jikin kafadar Farouq tana bacci, amman ta manne ummu jikinta gam. Hussaina tai murmushi. Adamcy ya rankwafa ya sanya lallausan hannayansa zai ɗauke ummu daga jikin Ma'azzara hannunsa na gugar jikinta, tayi rab da hannunsa saboda tini bacci ya fara fizgarta ta rungume hannushi a kirjinta gam da Ummu ta haɗa ta rungume tana turo baki gaba. Adamcy wani irin zarrrrr yarrrrr yaji, ya fara ƙokarin janye hannunsa ta riƙe gam. Faruk da Hussaina suka sanya dariya suka ce "kaga yar gidan Uncle."
Shi ko Adamcy idanunsa ya zuba mata kawai sai yaji tausayin ta ya kamashi, ga hannushi data rungume a kirjinta yana taba nonuwanta, da sauri ya kara saka hannunsa sosai jikinta ya samu ya ɗauke ummu cak, yana sakin murmushi ya dora ummu a kafadarsa, hannunsa ɗaya kuma sai ya sanya ya kama Ma'azzara, ya janyeta daga jikin Farouk ɗin ya kwantar da ita saman gadan ya gyara mata matashi ya rufa mata bargo, ya juya ya komo wajan Hussaina ya
zauna yana ma Ummu wasa.

Hussaina tace "yanzu Dr
Farouk mine ne matsalar tata?"

Farouk ya yayi sansanyan murmushi yace "babu wata matsala sai wannan dai wanda na faɗin maku, to ita ce matsalar , dan haka dan Allah dan Annabi ayi ƙoƙari a bani auren ta nan kusa ina so."
Murmushi Hussaina tayi ta ɗan kwanto da kanta jikin Adamcy, ta leki fuskarshi tana dariya ta shafi kyakyawan sajan fuskar sa wanda ya ƙawatu a saman fuskar sa tace" mon trésor kaji abinda yace ko?"
Adamcy ya dago da lumsassun idanunsa ya mata kur da ido yana sakin gutun murmushi, sai ya mata nuni da girasa yace" eh naji abinda Farouk ɗin yace bebeta zamu yi mgn ba yanzu ba." ya idar da maganar yana mata hirar ido.
Hussaina tai murmushi ta jingina jikinsa sosai, dan tana gane duk maganar da yake mata da gira ko da ido, sai tayi murmushi taja habar shi kaɗan. Ummu ce tasa kuka, sai yace"kin gani kin takura ma ƴata koh kin takura mata har ta fara kuka to amshi kibata tasha."
Nan Hussaina ta sunne kai jikin Adamcy, takai bakinta dede setin kunnesa tace"Bebena kunyar Dr nake , kaga suruki na zai zama." ta faɗa tana amsar Ummu tana girgizata tana jin kunyar Faruk sai taja mayafinta ta rufe Ummu ta ciro nono a mayafi nan ta fara shayar da ita, tako wawura tana tsotsa sosai.

Adamcy ya saki murmushi ya dora hannunsa saman fuskar Hussy ya shafa, yace"Yauwa matar Adamcy ki shayar min da yarinya sosai , ilove u." ya faɗa yana rankwafawa ya sakar mata kiss a kumatu. Farouq ya miƙe yana cewa"Gaskiya kuna bala'in burge ni shiyasa nake son My heart nasan zan sami kulawarta sosai."ya fada yana dariya yay wajan kofar fita. Adamcy ya ɗago da kansa ya kalli Farouq yace "Ok to muje na gan ka."
Farouk ya juyo yaba Adamcy hannu Adamcy ya kama hannushi suka fita.

Office ɗin Farouq ɗin suka je. Bayan sun zauna ne Farouk yace "ka dai ji duk irin bayanan dana maka wannan shine mafita."
Adamcy yayi sassanyar ajiyar zuciya ya lumshe manyan idanusa, ya bude su tarr akan Farouq yana kal kaɗa ƙafa yana jinjina kai, tamkar baya son yayi magana cikin sanyi maganar sa da amon muryasa me daɗin gaske, da nuna isar sa yace "Ok abokina naji babu damuwa insha Allahu zanyi magana da Ummee idan mu koma gida kasan gobe Hussaina take zubar da ruwa insha Allahu cikin satin nan Ummee zata koma gida sbd Adiya , to insha Allahu za'ayi magana baka da matsala , zamu rankaya mu tafi can tare wajan ɗangi ubanta inya so sai ka biyo mu sai ayi magana , amma fa ba yanzu ba se ta gama jarabawa zan dai ba ummee sako cewar ta sami miji , amma aure kam se ta gama secondary school zan dai baka ita kamu insha Allahu kaine mijinta , wannan ai ba wani abu bane da izinin Allah komi zaiyi dai-dai." ya faɗa yana zuba ma Farouq lumsassun idanunsa.
Faruk cikin farin ciki da jin dadi ya mike ya rungume Adamcy yace "nagode abokina hakika kai aboki na gari ne babu kamar ka bazan manta da kai ba cikin rayuwata ba , amma abokina gama secondary ɗinta da saura fa , kuma tana da larura ta ciwon ciki."
Adamcy ya riƙeshi yana bubuga bayan shi yace"babu komai ka daure kayi hakuri kamar gobe ne insha Allahu , kai de ka nemi so daga gareta ya kasance kafin lokacin babu wani ɗa namiji da take so da kauna bayan kai , amman zan baka amana Ma'azzara amana amana idan kaci amanar ta Allah yaci taka , ka kasance da ita kamata riƙon fiye da wanda nake mata bayan auran ku , marainiya ce gaba da baya bata da uwa bata da uba nine uwarta nine ubanta , bayan na aura maka ita kuma kai ne uwarta kaine ubanta se ni ubanta ni da Hussaina dan haka duk ranar da na aura maka ita , amanarta ta dawo hannunka bawai ina nufin na baka amana gaba ɗaya ba ne na sakar maka ita sai yanda kayi da ita ba , A'a zuwa lokaci-lokaci zan ɗinga sa maka ido duk abinda zai kasance zanyi tsaye tsayin daka na kwatar ma Ma'azzara yacin ta , akan yarinyar nan babu abinda bazan yi ba dan haka mutukar kasan bazaka rike amana ba maganar nan abarta kawai🙅🏻‍♀️."
Da sauri Farouq ya rike bakin shi ya ɗaura hannusa saman bakin shi yana girgiza kai yace "ai kafi karfin haka wlh ka wuce haka insha Allahu komi zai tafi dai-dai da izinin Allah , na yarda na ɗau maka Alkawari ruwa da iska zan rike Ma'azzara amana insha Allahu." ya faɗa yana murmushi.
Adamcy ma murmushi yayi ya buga bayan shi yace "baka da matsala komi zaiyi dai-dai na gode"nan dai suka ɗan taɓa hira kafin suka rankaya suka fito waje. Bayan sun fito suka koma can Ma'azzara tana dai baccin ta.

Hussaina tace,"to yanzu ya za'ayi idan ta tashi za'a sallame mu koko sai ta kara kwana?"
Farouq yace "eh to da sansa mu ne abarta har zuwa gobe a ga karfin jikin nata."
Hussaina tace"to babu komi bari naje gida na dawo Ummee ma tace tana zauwa , nasan ita zata kwana ."
Adamcy ya amshi Ummu ya kama hannun Hussaina suka ma Farouq sallama cewar zasu tafi su dawo, Adamcy yace "amana ka kular mani da ɗiyata kafin naje na dawo."
Farouq yayi murmushi yace "baka da matsala" nan suka fito. Farouq ya raka su farfajiyar asibitin har gun mota, suka shiga mota shi kuma yana tsaye har Adamcy yaja motar cikin nutsuwa suka bar cikin asibitin. Kanin Farouq ya dawo cikin ya duba yaga Ma'azzara tana baccin ta hankali kwance rabin jikinta cinyoyinta duk awaje, sai ya gyara mata kwanciya ya kara lulubeta ya fita zaiyi wani aiki ya janyo kofar sai ya kiro nurse ɗaya ta zauna da ita har yake dawowa.

************** ****** **************

Ma'azzara se washe gari aka salameta, taji sauƙi sosai ta sami kulawa wajan Farouq da ummee da uwayan riƙon ta. Washe garin salamota, ta koma school kuma ranar Hussaina ta zubar da ruwa, tasha kitso da kunshi tayi masifar kyau tasa a kama Ma'azzara ma, kasancewar ta ɗanyi hasken fata kaɗan baƙinta ya washe ba laifi har wani sheƙi take, kunshi ya fito sosai aka mata kitso yari yari a dogon baƙin gashinta masu kyau ta fito sosai.
Da misalin karfe 9:00 pm Zaune suke kan dining kowa nacin abinda yake so.
Ma'azzara sanye da riga da siket yan kanti farare sunyi mata kyau sosai, jelar kitsonta ya zubo har gadon bayanta, saura sun zubo gaba. Adamcy wainar da akayi ta sakada yace a masa farfesun hanji ya haɗa, ita ce yake ɗan ci dan baya cin abunci da dare. Ummee ma ita ce take ci, Hussy kuwa da Ma'azzara tuwon shinkafa da miyar ganye taji busassan kifi da jan nama, kowa se kai komo yake da hannunsa. Ummee tace " Wlh naji dadin wainar sosai wlh Allah yayi albarka dai." Ma'azzara tace"Ummee ai da nan kike kullum sai na miki kinci." ta faɗa tana kallon Hussy, Hussy ta harareta tace" Karya yaushe kika iya waina wannan dai kinsa aikin Hadiza ne da granny..." Sallamar granny ce ita da ɗan tsohon ta, ya katse masu hira sunzo ma Ummee sallama dan jirgin 6 zata shiga gobe. Ummee ta miƙe cikin girmama ta tarbe so Ma'azzara ma ta miƙe da gudunta ta rungume granny tana dariya. Tsoho yace" duk ta shafeki da miya ko?" Dariya Ma'azzara tayi tace" kaji haushi bakai na tara ba dai." ta faɗa tana sakin granny jin ummu da take kwance cikin ɗan gadanta ta tsala ihu, taje da gudu ta ɗauketa tana jijigawa ta nufi kitchen ta wanke hannunta. Adamcy ya rungume tsohon yana jijigashi.
Ummee ta kai masa duka tace"sake shi maza." Hussy tayi dariya ta taso tana cewa"Anzo kwadayi ko to babu rabon ku." nan suka gaisa ta nufi kitchen.
Karo Suka ci da Ma'azzara tana fitowa tana ma Ummu wasa. Tayi dariya ta wuce tace" har kin koshi ko?" Ma'azzara tace"Eh Aunty" ta wuce ta nufi bedroom ɗinta. Bayan sun gama gaisawa Aka shiga hira wasa da dariya. Farouq ne yazo da tsaraba niki-niki da ta ummee da ta yan uwan Ma'azzara za'a kai masu. Adamcy yace" Ah lallai abu nayi ne har da su sako." Ummee tace " Masha Allah Farouq Allah ya tabbatar da alkhairi insha Allahu wannan sakon da kaina zan kaishi har Audarass , daga na huta a Agadez zanje lallai akwaita Halliru da Salamatu..." ko me ta tuna se tayi diff. tayi murmushi. Granny tace"Au ashe in Allah yayi da likita bokan turai za'ayi Allah ya sanya alheri." gaba ɗayansu suka amsa da "Ameen. Hussy tana manne jikin ummee tace"Suruki kaje ka kirawo ɗiyar ka mana nasan dai yana son gaisawa da ita." Adamcy ya zabga mata harara yace"Zauna karki kirawota ɗin." ya faɗa yana murmushi. Ummee tace " abun kunya bazaku kirata kenan?" Hussy ta langwaɓe kai tace"Allah ummee shi zaice ni na koshi dayawa." Adamcy ya mata nuni da ido anjima ba barci. Kai ta sunne tana murmushi dan itama a matse take da mijinta, kusan wata biyu. Tsoho yace"Tab kai Farouq tashi ka shiga da kanka ka kirawo ta ku gaisa ɗin tinda haka ake a maraya surukan banza." Adamcy ya miƙe yana murmushi ya harari Hussy ya nufi saman. Ma'azzara kuwa tana zuwa ta zauna ta tisa ummu gaba tana mata wasa se halba ƙafa take tana bata lips ɗinta tana tsotsa, idan ta janye se ta tsala kuka dole ta maida mata tana dariya. Yanzu ma tana tsotsar lips ɗinta taji ya fara zugi ta janye tako fasa kuka, Ma'azzara tace" Allah bazan baki ba zafi labɓana suke zo na girgiza ki, ni bari na goyaki na canza pad." ta faɗa tana saka ummu bayanta ta goyata ta taɓa siket ɗunta taji lema zumburo baki tayi tana cewa"Tab ya akayi ya pad ɗina ta jiƙe haka har ya taɓa kayana , Baby ki kwanta naje nayi wanka da sauri na canza kaya." ta faɗa tana ƙoƙarin sauke ummu taba kofar shigowa baya. Adamcy ya tura kofar ya shigo da sallama. Ma'azzara ta saki ɗan ihu tana cewa "Uncle wlh ni ba ƙazama bace ummu ce take kuka." murmushu ya saki ya zura hanunsa cikin aljihu yana takunsa na isa yace " Ok kawo ummu ɗin..." sauran maganar ta maƙale masa sbd karaf Adamcy idanunsa suka sauka kan farin siket ɗinta da ya ɓaci da jini, da sauri ya rumtse idanunsa ya bude su ya daka mata tsawa!!... Ma'azzara ta gigice ta saki kuka ummu na ƙoƙarin fadowa daga bayanta. Adamcy yay zafin nama yay kanta a guje... 💃🏻Taku ce har kullum Real Ladingo🤝🏻😍🤣🙊```Insha Allahu sauran page 2 na rufe free page.```




*Karku manta BANI DA GATA Ya koma na kudi 200N ga me buƙata A tuntuɓi wannan lambobin 👉🏻+22792589446/ +22796515805/ Se naji ku Real masoya🥰🤝🏻🤣*

  *💖BANI DA GATA💖*

*MALLAKIN*
👇🏻
*Real ladingo Sweet Baby*💋
Yar mutan Niger🤙🏻


*TO MASOYAN BANI DA GATA DANGANE DA KORAFE ƘORAFEN KU, CEWAR BANI DA GATA  A RAGE MASA KUDI DAGA 300N, TI NA AMSA NA SAUKE 100N NA MAI DISHI 200N DAN HAKA DUK ME BUƘATAR BANI DA GATA ME CIKE DA ABUBUWA WNADA BA SAI NA FAƊA BA, TO  HANYA BUƊE TAKE FARASHI ME SAUƘI AKAN NERA 200 KACAL DUK ME BUƘATA ZATA IYA TUNTUBANA TA WANNAN LAMBOBIN 👉🏻+22792589444/ +22796515805*

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


*Free page*

*👉🏻14*

Amatuƙar hanzarce Adamcy ya usa gaban Ma'azzara, tana ƙoƙarin zubewa ƙasa ita da Ummu, ya taro su su duka suka faɗa jikinsa,  luuuu haka Ma'azzara tayi tare da lumshe idanunta, wani iri taji a jikinta sakamakon haɗuwar jikinsu waje ɗaya, gefe guda kuwa tuni daddaɗan ƙamshin turarensa ya cika hancinta,  cikin takai cin yanda ta lafe a jikinsa ya tureta tare da ɗaura Ummu Saudat akan wuyansa yana ɗan buga bayanta da hannunsa.
Kwaɓe fuska tayi tare da karyar da wuyanta gefe, ɗan ƙaramin bakinta taɗan turo cikin sangarta tace.
"Am sorry Uncle."
Yana me girgiza Ummu Saudat ajikinsa ya ɗan kalleta tare da watsa mata harara, cikin yanayin haɗe fuska haɗi da tsare gida yace.
"Zaki tafi ki wanke ƙazantar dake jikinki ne ko kuwa zaki tsaya ki kafeni da mayun idanuwanki?." yaƙare maganar babu wasa akan fuskarsa.
Sake turo bakinta gaba tayi, cikin yanayin sanyi tare da tsananin shagwaɓa wanda yinsa ya zame mata jiki ta juya ta nufi hanyar toilet, har takai kusan ƙofar ɗakin ta tsinkayo muryarsa inda yace.
"Idan kin fito Farouq yana jiranki awaje."
Yana gama faɗin haka ya juya yafice daga cikin ɗakin.  Itakuma batare da ta juyo ba ta shige cikin bathroom,  ganin jinin ya ɓatata sosai ya sanya ta cire kayan jikinta, ruwa me ɗan ɗumi ta haɗawa kanta tare dayin wanka, towel ta ɗaura ajikinta kana tafito daga cikin toilet ɗin, shirya kanta tayi cikin wata pink ɗin doguwar riga irin bubu gown ɗinnan, sosai rigar wacce taji adon white stones ta yiwa jikinta kyau,  wani ɗan madaidaicin mayafin rigar ta ɗauka tare da yane kanta dashi, wanda ya sauƙo zuwa shoulder ɗinta,  wani pink flat shoe ta sanya aƙafafunta, turarenta mai sauƙin ƙamshi ta sanya, cikin yanayin ta na sanyi ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice,  a hankali take sauƙowa daga kan step ɗin.

Ƙamshin sassanyar turarenta ne ya ratsa hancinsu, hakan yasa su waigawa zuwa ga inda ƙamshin ke fitowa, idanunsu ne duka suka sauƙa akanta,  ahankali take ci gaba da sauƙowa daga kan step ɗin,  idanunta ne suka sauƙa akansu su duka biyun, da ɗan sauri ta ɗauke kanta daga kallon Uncle ɗin nata ta sauƙe ganinta akan Farouq, ɗan murmushine ya bayyana akan black beauty face ɗinta, shima Adamsy saurin ɗauke kansa daga gareta yayi tare da ɗan taɓe bakinsa, duk da cewa shigar tayi matuƙar yi mata kyau,  ahankali tagama sauƙowa daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login