Showing 66001 words to 69000 words out of 148918 words

Chapter 23 - Nihaad Book 1 Hausa Novel Complete

ta fashe da kuka tace "Wayyo Abba me yasa xaka min haka" Ita da dai drivern nan ai gwara ko almajiri ne Abba ya nemo mata su xauna gida daya, ta ci kukanta me isarta bacci ya dauketa a haka. Washegari har kusan karfe goma bata fito ba ga wani mugun yunwa da take ji, tashi tayi da kyar daga karshe ta shiga bandaki tayi wanka ta fito, daya daga akwatunanta dake dakin ta bude ta fiddo wata doguwar rigarta ta saka, xaunawa gefen gado tayi feeling so sad and dejected, daga karshe ta mike ta nufi kofa tana tafiya a hankali ta bude kofar ta fito parlor, babu kowa parlon sai take away din abinci da ta gani a tsakar parlon, ta saci kallon ko ina na parlon sannan ta karasa inda abincin yake tana ta6e baki ta bude take away din tana kallon abincin ciki, jollof rice ne sai sheki yake da katon kaza, ko rabi kuma bai ci ba, kazar ma bai wani ci ba ya bari, ta bude ledan dake wajen taga drinks ne sai chocolates me yawa, vibration din waya taji saman kujera ta kalla da sauri amma bata ga wayar ba, wanda hakan yasa ta gane wayar na karkashen throw pillow dake saman kujeran, har xata kai hannu ta daga pillow din ta ji an kulle kofar kitchen, sosai gabanta ya fadi ta juyo da sauri suka yi ido hudu da shi ya fito daga kitchen din rike da cup din shayi, sai a sannan ya ji vibration din wayarsa ya karaso da sauri, wanda tun kan ma ya karaso Nihad tayi hanyar dakinta tana harararsa, ya ajiye cup din hannunsa ya bi ta da kallo har ta shige dakin, xaunawa yayi saman kujera yana kallon throw pillow din kamar me son gano ko ta ta6a ko bata ta6a ba, da sauri ya dau wayar kafin ya katse ya daga ganin Abba ne, gaishesa yayi da ladabi Abba ya amsa yace "Anjima da yamma ka daukota ku zo gida ina son magana da ku" Khalil yace "Toh in sha Allah" Abba yace "Ai motar na can gidan ko?" Khalil yace "Ehh yana nan" Abba yace "Ina sauraronku xuwa nan da bayan la'asar" Khalil yace "In sha Allah" Daga haka Abba ya katse wayar, ajiye wayarsa yayi ya jinginar da kansa da kujera, this spoilt his mood the more, Allah ya sani he can't endure staying under the same roof with this Brat, he wish this never happened, he detest the sight of her, da yasan this is how things will end babu abinda xai kawosa gidansu, da baxai fara ba, yanxu ta yanda ma xai ce ta shirya su je gida shine babban aiki a wajensa, ko magana baya son yana hadasa da ita, mikewa yayi ya dau wayarsa ya zura a aljihu ya fice daga parlon xuwa compound don ya fi zama comfortable xama a nan, abinda Nihad bata sani ba shine shi ya ma fita shiga damuwa kawai dakewa yake yi, kuma bata ki jininsa ba yanda shi ya ki jininta. Ganin yunwa na neman mata illa ta kara fitowa parlor, this time around hanyar kitchen ta nufa tana bin ko ina da kallo, ga kayan abinci amma babu kayan miya, gashi ita ba gwanar cin indomie ba ce, babu yanda ta iya haka ta dafa indomien ta fito ta wuce dakinta, tana ajiye indomien ta fashe da kuka sosai cike da tausayin rayuwarta, why did this happen to her, waye yayi mata haka yayi ruining happiness dinta all of a sudden, tasan duk rashin jin ta ko da singlet bata xama comfortable zama a inda ba gidansu bane, ko su Husnah da take bi she is very cautious of her self and her body, kuka take yi sosai wishing duk wannan abun bai faru da ita ba, indomien da bata ci ba kenan daga karshe, kawai ta tashi tayi alwala tayi sallahn azahar ta kwanta gefen gado hawaye na sauka idonta. Ana la'asar Khalil ya shigo parlor ya zauna yayi dialing number Abba, Abba na dagawa ya gaishesa sannan yayi kasa da murya yace "Abba tace ita baxata ba" Abba yace "Ohk, ba ta waya" Khalil yace "Toh" Mikewa yayi ya nufi hanyar dakin da take ciki, yanda kasan yana kallonta jikin kofar haka ya hade rai yana kallon kofar, sai kuma yayi Knocking kofar, Nihad da ke kwance har sannan ta mike zaune tana kallon kofar, sai da ya sake Kwankwasawa ta mike xaune ta wani hade rai, sai kuma ta tashi ta tafi gun kofar ta bude cike da tsiwa tana harararsa tace "Lafiya kake kwankwasa min kofa Malam? Ko da bashi ne?" Mika mata wayar hannunsa yayi ba tare da ya kalli fuskarta ba, ta kalli wayar da kamar baxata amsa ba sai kuma tayi tunanin kila Umma ce, fixge wayar tayi daga hannunsa tana kallon Number sai taga number Abbanta ne, sosai gabanta ya fadi, tayi karfin halin kai wayar kunne, cikin sanyin murya tayi sallama, Zaro ido tayi tana sauraron abinda Abba ke ce mata with strictness, can ta kalli Khalil da ya koma can gefe ya jingina da bango ya rungume hannunsa, Abba bai bar ma Nihad space din cewa komai ba ya katse wayarsa daga karshe, ta fashe da wani matsanancin kuka tana kallo Khalil tace "Allah ya isa, ban yafe maka ba wllh, yaushe kace min mu je can gida nace Aa?? Wallahi ni baxan ta6a yafe maka ba" Sai kuma ta durkushe wajen tana kuka sosai ta kalli wayarsa dake hannunta tayi wurgi da shi ta mike ta shige cikin daki ta fada kan gado tana rera kuka, ya dau wayar tasa ya bar wajen. Bayan Nihad ta ci kukanta ta koshi ta mike ta dau hijab din da tayi sallah ta saka sannan ta fito daga dakin, compound ta fito ta gansa xaune driver seat ya bar motar a bude alamar dai ita yake jira, fuskarta a murtuke ta bude back seat ta shiga ta xauna, ya sauka daga motar ya tafi ya bude gate..... Har suka kusa gida Nihad bata daina hawayen da take ba a motar, Horn khalil yayi mai gadi ya leko ganinsa ya daga masa hannu yana washe hakora ya bude gate din, Khalil na parking ya kashe motar ya sauka ya tafi gun Aminu, tuni Nihad ta shige cikin gida, Aminu yayi kasa da murya yana zazzare ido yace "Wani labari muke ji haka mutumina??" Khalil yace "Na me fa?" Kafin Aminu yace komai, Khalil yace "Bari in shiga in fito yanxu" Aminu yace "Toh ina nan ina jiranka" Juyawa khalil yayi ya nufi entrance din gidan, Khalil na tsaye balcony yayi dialing number Abba ya sanar masa sun iso, Abba ya masa izinin shigowa har parlonsa, babu kowa main parlor, Khalil yayi sallama bangaren Abba, Abba ya amsa sannan ya shiga ciki, kansa a kasa ya zauna nan saman Carpet ya kara gaida Abba, Abba ya amsa ganin Nihad bata shigo ba yace "Tana ina?" Khalil yace "Ta riga ni shigowa" Nihad kuwa tana shiga gidan dama direct bangaren Umma ta tafi, Abba ya mike ya fita, a side din Umma ya ga Amina yace "Ina Nihad?" Amina tace "Tana dakin Umma" Yace "Ki shiga ki kira min ita" Amina ta juya ta koma ciki, Abba ya koma parlonsa, bayan wasu yan mintuna sai ga Nihad ta shigo parlon Abbanta kanta a kasa, sallama tayi da muryarta da har ya fara dashewa saboda kuka, bata yarda ta daga kai ba balle ta kalli Abbanta, ta nemi waje daga opposite din inda khalil ya zauna ta zauna, Cikin rawar murya tace "Abba ina yini" Abba bai amsa ba, bai kuma kalleta ba, dai dai nan Umma ta shigo parlon da sallama, kallonta kawai Abba yake, Khalil ya gaisheta ta amsa ta zauna fuskarta dauke da damuwa tana kallon Abba, Abba dai ya kalli Khalil yace "Nagode da wannan alfarma da ka min na auren yarinyar nan Ibrahim, Allah Ubangiji ya baka aljanna" Khalil yayi kasa da kai a hankali yace "Ameen" Abba yace "Ina kuma fatan Allah Ubangiji ya baka hakuri da juriyar zama da ita.... In dai da akwai wani abu kar kayi kasa a gwiwan kirana ka sanar min koma menene shi" Nihad ta fashe da matsanancin kuka tana kallon Abba tace "Abba wallahi bana sonsa kuma baxan ta6a sonsa ba, na tsanesa na tsanesa, ni baxan ta6a xama da shi a gida daya ba, wallahi i hate him...." Mikewa Abba yayi lokaci daya ya sauke mata mari me lafiya a fuskarta, ihu ta fasa ta dafe kuncinta, Umma ta bude baki tana kallon Abba, sai kuma tace "Haba Alhaji, Haba Alhaji...." Dakatar da ita Abba yayi a fusace yace "Bana son jin komai daga gareki, ki tashi ma ki fita" Umma ta ja bakinta tayi shiru, cike da bacin rai Abba na kallon Nihad yace "U think i brought u here to ask for ur opinion? Is that what u think?" Abba ya girgiza kai cike da takaici yace "You are nothing but a disappointment to me Nihad, i regret having u as a child...." Kuka kawai Nihad take tana jin kamar a mafarki wai ita Abba ya mara kuma yake gaya mata wannan maganganun, wanda ko fada bai ta6a mata ba tunda aka haifeta, Strictly Abba ya ci gaba yace "Kuma in har ba so kike inyi disowning dinki ba baki da miji da ya wuce Ibrahim, kuma dolenki kiyi masa biyayya ki bisa, idan ko ba haka ba ki nemi wani uban ba ni ba, sannan idan ba shi ya dauko ki ya kawo ki gidan nan ba bana son in ga kafarki a nan ko da kuwa xa ayi shekara ne bai kawo ki ba, ki sa a ranki baki da wani a yanxu banda shi, shine gatanki, shine komai naki, samun kwanciyar hankalin ki a rayuwa ki bi sa, ko mu da muka haifeki yanxu bamu da iko da ke sama da shi" Kuka kawai Nihad take xuciyarta na mata xafi, ita fa she still can't believe Abbanta ne ke gaya mata wa ennan maganganun, Abba na kallon Khalil da ya sunkuyar da kansa yace "Kai kuma Ibrahim ina me baka umarni in har Nihad xata kawo maka iskanci ko raini ka zaneta, ni na baka wannan umarnin ba wani ba" Khalil dai bai dago kansa ba, Abba yace "Shikenan kiran dama, xa ku iya tafiya" Da kyar khalil ya iya dago kai yace "Nagode Abba, Allah ya kara girma" Abba yace "Ameen" mikewa yayi yana kallon Umma yace "Sai anjima" Umma ta dinga harararsa, shi dai ya nufi kofa, ganin Nihad ta ki tashi sai kuka take kamar ranta xai fita Abba ya daka mata tsawa yace "Tashi ki bar min gidana, useless girl" Tashi tayi da sauri tana kuka sosai ta nufi kofar ita ma, sai kuma ta juyo cikin rawar murya tace "Abba makaranta na fa?" Abba yace "Sai abinda mijin ki yace, don shi ke da iko dake yanxu, don in xai dau shawarata ma babu ke babu makaranta har abada, maza bi sa ku bar min gidana" Khalil dake jin Abba ya fita daga parlon ta bi bayansa tana kuka sosai, shi dai ko kallonta bai yi ba ya fita xuwa gun mota, Aminu sai wage ido yake yana jiran fitowar Khalil, yana ganinsa ya fito kuma ya shige mota, Nihad ta bude bayan motar ta shiga ta hade kanta da gwiwa tana shessheka tana jin kamar numfashinta zai dauke, Khalil na isa gate Aminu yace "Ina ta jiranka" Khalil yace "Xan zo da daddare" Aminu ya washe hakora yace "Toh toh sai ka zo" Da gefen ido ya dinga lekan Nihad dake bayan mota, khalil ya ja motar suka bar gidan. Sai kusan karfe shidda suka isa gida, Khalil na parking ya sauka ya tafi ya kulle gate sannan ya dawo ya kashe motar, har sannan Nihad bata dago kanta da ta kife a bayan motar tana kuka ba, tana jin ya kashe motar ta bude side dinta ta sauka, gaba daya ta jike hijab dinta da hawaye har a sannan kuma ba daina kukan tayi ba, ta fara tafiya towards the building of the house, ji tayi ko ina na juya mata a ido, Rufe motar khalil yayi da sauri ya nufeta ganin abinda take, amma kafin ya isa inda take tuni ta kai kasa, ba karamin faduwa tayi a wajen ba, ya zura makullin hannunsa cikin aljihu da sauri ya durkusa gabanta ya dagota amma tuni tayi pass out, daukarta yayi ya nufi cikin gidan da ita.

_kiyi subscription ki karanta hankalinki kwance. Nima kuma sai in samu kwarin gwiwan dinga yi maku double update_

I am soo grateful for the patronage, Allah ya saka maku da Alkhairi ya biya maku duk wata buƙatar ku ta Alkhairi, Allah ya kara ma iyayenku lafiya.




*Nihaad* is 500 via Fcmb Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence via👇🏻
07087865788


A hankali Nihad ta bude idonta tana bin inda take kwance da kallo, a daki take saman gado, ta mike xaune da kyar tana jin ko ina na jikinta na mata ciwo ga wani sanyi da ke shigarta duk da fankan dakin a kashe yake, ta kalli agogon dakin taga karfe biyu dai dai, window ta kalla ganin duhu yasa ta fahimci biyu na dare ne, hade kai tayi da gwiwa bayan tayi recalling duk abubuwan da suka faru, she couldn't stop tears from rolling down her eyes, ta dinga shessheka a hankali, tunawa da tayi bata yi sallan magrib ba balle Isha'i ya sa ta dago kanta tana goge idonta da ya kumbura, tayi kokarin sauka daga saman gadon amma taji baxata iya ba, ko ina ciwo take ji yake mata a jikinta, hakan ya sa ta koma ta kwanta a hankali, Hijab dinta dake gefenta ta jawo ta lullube da shi ta takure waje daya sbda sanyin da take ji sosai, amma bai taimaka mata da komai ba sai rawan dari take, bayan kusan minti talatin ta ji an bude kofar dakin, ita dai tana takure inda take ta rufe har kanta da Hijab, tsaye yayi bakin kofar dakin yana kallonta, dama ya zo dubawa ne ya ga ko ta tashi or she is still unconscious cause he isn't as bad as she is, he have human conscience in him unlike her, har xai juya ya fita sae kuma ya karasa cikin dakin ganin kamar she is shivering, ya isa kusa da gadon yana kallonta xai cire Hijab din da ta rufe fuskarta da shi, ta riko hijab din a fusace cike da tsiwa tace "Baka da hankali ne?? Uban meye xaka shigo min daki cikin daren nan?" Sake Hijab din yayi ya juya ya fice daga dakin ta bi sa da harara sai kuma ta ja tsaki ta koma ta kwanta jikinta na rawan sanyi sosai. Har aka yi asuba Nihad ta kasa motsawa daga exact spot din da take a kan gadon tun cikin dare, she is so sick and weak, tayi yunkurin tashi ya fi a kirga amma kamar an danneta saman gadon take ji, duk da babu wani abun da ta ci tun jiya amma haka ta dinga jin amai yana damunta kamar xai taho mata, ga ciwon kai me tsanani da ya addabeta, wajen karfe takwas taji aman ya taho mata, bata san sanda wani strength ya xo mata ba ta sauka daga kan gadon tana layi ta bude kofar bandaki, nan ta durkusa ta dinga kakarin amai amma ba abinda ya fito, Khalil na kwance parlor yana jin ta amma ko motsawa bai yi ba daga saman kujeran da yake, a nan tsakar dakin Nihad ta kwanta tana maida numfashi hawaye me xafi na sauka idonta, tana nan a haka har kusan karfe sha daya na safe, zuwa lkcn kuma xaxxabin ya ci karfinta, Duk yanda ya so fita harkarta a gidan kasawa yayi, cause he wasn't raised to be mean, ya kuma san bata ci abinci ba throughout jiya don shi ya fito da indomie da ta bari a daki bata ta6a ba, karfe sha biyu saura ya mike yayi hanyar dakin after soothing himself to do so, kwata kwata ba don ranshi ya so ba ko don tayi deserving ba yayi hakan kawai dai shi din me tausayi ne, yana bude kofar dakin ya ganta nan tsakiyar dakin a kwance, ya fi minti daya tsaye bakin kofar yana kallonta kafin ya karasa cikin bedroom din, ya duka a gabanta ya cire hijab din da ta rufe fuskarta da shi, ta bude idonta da yayi jajir amma babu strength din rashin kunya ko tsiwa, bai kai hannu jikinta ba but yana jin hucin zafi a jikinta, ya mike ya fita daga dakin ya dau wayarsa, bayan ya gama kiran da xai yi ya shiga kitchen, ruwan gora ya juye a kettle ya daura saman gas, bayan ruwan yayi xafi ya hada shayi a cup ya fito, dakin ya koma ya ajiye mata shayin, amma ya kasa ce mata ta tashi ta sha, har cikin ransa bai son ko magana ya hada shi da wannan yarinyar, kawai daga karshe ya fice daga dakin ba tare da ya ce mata komai ba, bayan kusan awa daya ya fita kofar gida ya shigo da wani likita, wani asibiti dake home service ya kira suka turo masa likitan, bayan sun gaisa ya kai sa har dakinta, likitan ya ajiye abubuwan da ya taho da su yana kallon Nihad, Khalil ya juya ya basu waje yayi zamansa a parlor, bayan likitan ya dubata ya tilastata ta dan sha shayi, sai da yayi yakin kusan minti sha biyar kafin ya samu da kyar yayi mata allurai, ya kuma bata magunguna ta sha, da tace masa sanyi take ji ya dauko wani zanin gado da ya gani a leda ya bude sannan ya bata ta rufa da shi, yace "Allah ya sauwake, Anjima da daddare xa a dawo yi maki allura" Ita dai bata ce komai ba don bacci taji yana hauro mata har ya fita daga dakin, yayi ma khalil sallama sannan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login