Showing 111001 words to 114000 words out of 148918 words
Nihad ta dauko wani bottle water dake daya side din gadon ta mika mata, Husnah ta amsa ta koma ta zauna tana sauke numfashi a hankali, ita fa dama kwana biyu duk samarin nata basa Kano gaba daya a takure take dama, daga karshe dai Husnah ta kwanta ta kulle ido duk da ba bacci tayi ba, Wajen karfe sha biyu da rabi Nihad ta mike daga kwancen da take ta nufi kofa ta sa makulli sannan ta ciro, Da mamaki Husnah ta mike zaune tana kallonta tace "Me yasa zaki kulle mu har da cire makulli Nihad?" Nihad tace "Saboda duk dare haka nake yi dama" Husnah bata kuma cewa komai ba ta kyabe baki ta koma ta kwanta, Nihad ta saka makullin cikin pillow ta kwanta kai. Washegari da sassafe bayan sun yi sallan asuba sun koma bacci kiran Umma ya tashe su, Bayan Husnah ta daga jin muryar Umma tace "Auu Umma ce, ina kwana?" Umma tace "Lafiya lau Husnah baki yi saving number na har yanzu ba ko?" Husnah tace "Yanzu xan yi Umma, ya gida?" Umma tace "Alhamdulillah, ina Nihad din?" Husnah ta mika ma Nihad waya ta koma ta kwanta, Bayan Nihad ta gaidata, Umma tace "Ya, kin gano sunan iyayen nasa kuwa Nihad?" Nihad tace "Aa Umma, dama sai yau" Umma tace "Kin ji irin shiriritar taki ko? Ke da tun jiya nace kisan yanda kika yi ya gaya maki amma sbda shashanci baki yi ba? Ko dai kin fi son kiyi ta zama da dreban nan ne Nihad?" Da sauri Nihad tace "A'a Umma, in sha Allahu yau xan gaya maki" Umma tace "Toh kar ki bari Husnah ta bar gidan nan sai kin gano kin sanar min ta wayarta tukunna" Nihad tace "Toh Umma" Umma tace "A handsfree wayar yake ne naji maganata na dawo min?" Nihad tace "Aa" Umma tayi kasa da murya tace "To dai ki xama me rike sirrinki a ciki, ciki da kike gani ba don tuwo kadai aka yi sa ba, ko da mun gana waya kawarki ta tambayeki me muka ce kice mata ba komai kawai daddawa da kuka nace xan bada a kawo maki, don ba komai ake sanar ma k'awa ba, wa ya sani ko da hadin bakinsu aka saki video dinki a duniya" Nihad tace "Aa Umma ba haka bane gaskiya" Umma tace "Toh shikenan, ina sauraronki zuwa anjima" Nihad tace "Toh" Daga haka ta katse wayar, Husnah na kallonta tace "Wai me ya faru?" Nihad tace "Aa ba komai, abubuwan da zata kawo min ne take tambayata" Husnah tace "Ohk" Komawa tayi ta kwanta, Nihad ta mike ta dau Hijab dinta ta daura kan kayan baccinta ta nufi kofa Husnah ta bi ta da kallo har ta fita, Nihad na murda kofar dakin Khalil taji an sa makulli, ta fi minti daya tsaye bakin kofar, can ta juya ta tafi parlor ta zauna, tana fitowa da minti biyar sai ga Husnah ma ta fito ta zauna parlon, jan Nihad ta dinga yi da hira, daga karshe wajen karfe tara Khalil ya fito daga dakinsa, babu warce ya kalla a cikinsu ya fita daga gidan, Husnah na ji ya fita da mota ta kalli Nihad tace "Lallai ke me hakuri ce da har kika kai warhaka da mutumin nan a gidan nan, Dubi fa yanda ya wani zo ya wuce mu ko gaisuwa babu, kai kana talaka da kai kayi ta yin abu isa isa?" Nihad ta kyabe baki tace "Ke ma kika lura da mutum ya zo ya wuce ta nan, ai ni ban ga kowa ba" Husnah ta kyalkyale da dariya tace "Ahh lallai kam" Nihad tace "Tashe mu je ko irish ne mu soya da kwai, ni dai na fara jin yunwa" Husnah ta mike suka wuce kitchen din, har kusan la'asar Khalil bai dawo gidan ba, kiran Umma uku duk sai Nihad tace mata ai bai dawo ba, kiran karshe da Umma tayi mata da ta kara sanar mata har sannan bai dawo ba, Umma tace "To kar ki yarda ki bari Husnah ta bar gidan, don tana tafiya babu ta inda xa mu yi communicate" Nihad ta kalli Husnah da ita dama bata ga alamar xata tafi ba tace "Toh Umma" Labari har da na kauyensu Khalil sai da Nihad ta ba Husnah dake ta kyalkyalewa da dariya har da faduwa kasa, tace "Kice ke kika ga asalin dreba ganin idonki?" Nihad tace "Hmm... I wish xaki ga kauyen nan Husnah, wllh with millons baxa ki yarda kiyi minti sha biyar a garin nan ba, it's hell on earth" Husnah dai sai dariya take, sai ga Naf ta kira Husnah, Nihad da wayar ke kusa da ita tayi saurin dagawa ta kai kunne, Naf na jin muryar Nihad tace "Amma Husnah munafuka ce shine bata gaya mana ba tayi tafiyarta ita kadai" Nihad tace "Wallahi nima ban ji dadin da baku zo gaba daya ba, gashi throughout today I wasn't lonely, muna ta hira da Husnah" Husnah ta fixge wayar tace "Toh ai naga xaku fita ne shi yasa bance maku mu taho ba Naf, amma meye a ciki next time idan xan zo ai sai mu taho gaba daya, ba wani tashin hankali bane" Naf tace "No but like seriously kinsan indai kince mana wajen Nihad xa ki babu abinda xai hanamu binki, kuma banji dadin abinda kika mana ba, yanzu ma kawai xa mu iya tahowa da zully tunda babu abinda muke" Husnah ta dinga cewa Hello hello, daga haka ta katse wayar tace "Ji shegen network din ya dauke" Hirar da take ma Nihad ta ci gaba da yi mata, Nihad tace "Kinga lokaci na wucewa me xa mu ci da daddare Husnah?" Husnah tace "Ni yanzu xan fita in amso wani sako na, ko indomie ce ma ci da daddaren, Hijabi kawai xan sa in je in dawo" Nihad na kallonta tace "Kar fa ki ki dawowa Husnah" Husnah ta zaro ido tace "Me xai hanani dawowa kuwa, cabb ai kamar na dawo kinsan yanda nayi kewar ki kuwa, to a nan ma xan bar wayata, amma kar ki cire min a flight mode har in dawo" Nihad tace "Toh" daga haka Husnah ta sa hijab ta dau handbag dinta ta bar gidan, ko da ta dawo bayan kusan awa daya Nihad ta dinga kallon hannunta ganin ba leda tace "Ina sakon?" Husnah ta ja tsaki tace "Wai ashe sai gobe, shine suka bari naje nayi asaran kudin motata na dawo" Daga haka ta shiga dakin Nihad. Sai after Magrib Khalil ya dawo gidan, Husnah da fitowarta daga wanka kenan ta dauki mai zata shafa ta rike ha6a tace "Dama haka yake yi ya fita tun safe sai dare kamar me siye da siyarwa a kasuwa" Nihad ta kyabe baki tace "Ohk ya dawo ne" Dariya kawai Husnah tayi bayan ta gama shafa cream dinta tace "Ke baxa ki yi wankan bane" Nihad ta mike tace "Zan yi" Daga haka ta shiga bandaki, mikewa Husnah tayi da sauri ta bude kofar dakin tana leka parlor, ba kowa parlon sai leda da ta gani a ajiye na eatry, ta dawo daki ta dau handbag dinta sannan ta fice tana waige waige kamar munafuka ta shiga kitchen ta bude handbag dinta ta dau allura me cike da wani liquid a ciki ta bude murfin syringe din, ta dawo parlor har tana tuntube ta tafi gun ledan ta bude ta ciro drink din kwali da ta gani ta tsira masa alluran ta sama ta juye duk content din ciki sannan ta mayar da shi ledan hannunta na rawa, sbda rudewa maimakon ta koma daki sai ta shige kitchen, ta fi second talatin a kitchen din kafin ta leko parlon a hankali still taga ba kowa da sauri ta wuce dakin Nihad ta kulle kofa ta zura doguwar rigarta ta dau wayarta ta kwanta saman gado tana danne danne tana ɗan murmushi.....
*Few mutanen da suka sameni jiya for discount wai basu da halin dari biyar, bayan message dina na jiya, sorry i didn't acknowledge u guys yesterday, after all ni din ce dai zan yi loose still😏, don haka na amince nayi discount daga yanzu xuwa gobe in sha Allah*
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via👇🏻
07087865788
Assalamu alaikum manyan mata!!
For your Egyptian Abaya's, mad gowns, laces and handbags and all sort of jewelries... Give me the privilege to be ur plug plss, and u will never regret it🥰
Ping me on WhatsApp to view our catalogue 👇🏻
https://wa.me/c/2349090591769
Nihad ta fito daga wanka bayan ta gama shafe shafenta ta zauna tana tunanin abinda xata sa yau ta kwanta don dama kayan baccin biyu ne kawai ya rage mata kuma duk ta sa su bata wanke ba, ita tunda take ma ta ta6a wanki a rayuwarta banda pant da bra, Husnah tayi mika tana kallonta tace "Ke kuma tunanin me kike haka?" Nihad ta kalleta a sanyaye tace "Toh kayan baccin nawa duka duka biyu ya rage fa a gidan nan gashi nan kuma duk na sanyesu ba a wanke ba" Husnah ta mike zaune tace "Toh ke garin yaya kika zo da kayan bacci kala biyu kawai?" Nihad tace "Ko ba can kauyensu na rabar ba, da tsummokara fa mutanen kauyen ke yawo wallahi" Dariya Husnah tayi tace "Toh kawai ki saka undies dinki sai ki saka hijabi ki kwanta" Nihad tace "Kin ta6a ganin na kwanta haka?" Husnah tace "Yanzu ma dai ina kayan wanki naki yake?" Nihad ta nuna mata inda ta ajiye su har da hijab kala biyu, Husnah ta mike tace "Nasan ko tsutsa xa su yi a nan ba wanke su xa kiyi ba bari in wanke maki su in samu ladanki" Daga haka ta kwashi kayan ta shige bandaki, Nihad ta mike ta dau Hijab dinta kawai ta saka don dama akwai sanyi sanyi garin alamar hadari, tana ta zaune tana game da wayar Husnah, sai ga Husnah ta fito rike da bucket tace "Can waje zan je in shanyasu ko?" Nihad tace "Ehh ta baya xa ki ga wajen da xakiyi shanyan" Daga sama har kasa Nihad ke kallonta don wani skimpy night wear ne a jikinta, gashi ko bra bata saka ba, Mikewa Nihad tayi tace "Bari kawai in shanya" Husnah tace "Ka ji ki, Aa wllh gwara in cike ladana, da me ya hanaki wankewa balle ki shanya, kawai ni bari in je inyi shanyana" Daga haka ta nufi kofa, Nihad ta kwashe gwangwanin maltina da suka sha da bottle wata ta bi bayanta, Yana zaune parlor hannunsa rike da remote, ga ledan abincin nasa har sannan bai ta6a ba, Husnah sai satan kallon ledan take har sai da ta buge da kujera ta kusa faduwa, da ido ya bi ta, ta nufi kofa da sauri, Nihad dake kallonta har ta fita ita kuma tayi hanyar kitchen taje tayi disposing thrash din hannunta a dustbin sannan ta fito parlo, ta koma kamar xata shiga daki sai kuma ta tsaya bayan 2 seater dake side din tana kallonsa, shi dai idonsa na kan tv, ta yanda xata fara masa tambayar da Umma tace tayi masa kawai take tunani, Ganin bata da alamar barin wajen can dai ya daga kansa ya kalleta yace "Lafiya?" ta jefa masa wani kallo tace "To banda ina son inyi maka tambaya ance maka xan tsaya nan ne" Ya ɗan yi shiru sai kuma yace "Wa za ki yi ma tambaya?" A takaice tace "Kai" Yace "Ohk, ni za ki yi ma tambaya kenan" Hararansa ta dinga yi wato har wani feeling kanshi yake zata masa tambaya, ya kafeta da ido yace "Yi tambayar ki" Babu yabo babu fallasa tace "Dama baka gaya min sunan gwaggwonka ba a can garin, har da babanka ma duk baka gaya min sunansa ba" Ita kanta tasan she sounds stupid, sai kuma ta fara sosa kai, kallonta kawai yake ba ko kiftawa, can yace "Tun a garin baki tambayeni ba sai yanxu da daddare?" A takaice tace "Ehh saboda sai yanxu na tuna" Yana gyada kai yace "Ohk!! To wa ya aikoki ki tambayeni sunan su?" Ta wara ido kamar munafuka tace "Aa fa, ba wanda ya aikoni yace in tambayeka nice kawai na tambayeka ina son sani" Yana kallon kwayar idonta yace "NIHAD" ta kara buda ido a ɗan rikice tace "Na'am" Yace "Sunanta kenan" Lokaci daya ta hade rai tace "Ban gane Nihad ba, sunanta ne sunana?" Yace "Ehh" Ta dinga masa wani mugun kallo, can tace "Toh don baka da kunya sai ka wani kira sunana gatsau wai Nihad, sunan nawa ka raina haka? waye ma ya gaya maka sunana? Aminu me gadi ko???" Khalil bai kuma ce mata komai ba ya bude ledan dake ajiye gabansa ya ciro drink din, dai dai nan Husnah ta shigo parlon ganin lemon a hannunsa wani farin ciki ya mamayeta tana kallon Nihad tace "Ke an fara yayyafi fa, kije ki rufe windows ko" Khalil ya ajiye kwalin lemun hannunsa ya mike ya shiga kitchen xai dauko glass cup, wajen lemon Nihad ta nufa da gudu, Husnah da ke kokarin shiga daki tana ta murmushi ita kadai kamar ance ta juya taga Nihad ta kinkimo lemun ta taho da gudu xata shige daki, cike da zafin nama Husnah ta fixge lemon daga hannunta tace "Meye haka sai kace mayunwaciya Nihad, bai siyo ya baki ba sbda rashin hankali kin wani dauko masa abinda kika fi karfi, me xa ki yi da abin hannunsa, bayan kudin ma kinsan na wanene ya ke ci, a'a wllh kin bani mamaki" Bata jira cewar Nihad ba ta koma da sauri sauri ta ajiye masa lemon ta bar wajen sai gashi ya fito kitchen, tuni Husnah ta figi hannun Nihad ta shige daki da ita ta kulle kofar tace "Wallahi kin bani kunya, me xa kiyi da lemonsa ke da ko ni kika ce in kawo maki carton din lemon can tsaf xan siyo in kawo maki, balle Umma ma kina gaya mata xata bayar a kawo maki har gida? Me ya kai ki? Ke fa har yanxu yarinta na damunki wllh, banda yarinta meye kike abu haka babu class, yanzu na gano dalilin da yasa yayi mugun raina ki" Nihad dai bata ce komai ba, Husnah ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, dai dai nan aka fara ruwan sama kamar da bakin kwarya, Husnah ta zaro ido tace "Lahh ga ruwan ya sauko, ki kulle windows din dakunan ni kuma bari inje in kulle na parlor" Daga haka ta fice da sauri zuwa parlor, Nihad ta bi ta da kallo sai kuma ta bi bayanta, farin ciki bai kara lullube Husnah ba sai da tagansa rike da lemon a glass yana sha, ta kasa daina murmushi ta tafi ta kulle windown parlon ta shiga ma kitchen ma ta kulle sannan ta fito tana kallonsa tace "Sai da safe" Bata damu da ta ji ya amsa ba ta nufi daki tana jijjige inda ya kamata a jikinta, Tana kallon Nihad dake bakin kofa tace "Wai duk kika ga na fito sai ki biyoni" Nihad tace "Aa ni kitchen xan tafi ne" Husnah bata ce mata komai ba ta shige daki, Nihad ta shiga kitchen ita kanta tasan babu abinda xata yi a kitchen din bayan ta gama zagaye zagayenta ta fito ta nufi dakinta, da ido khalil ya bi ta har ta shiga dakin, makulli ta saka ta zare makullin, Husnah dake kwance tana danna waya tace "Kamar da wasa fa sai ga ruwa ko ba komai garin yayi sanyi naturally ayi bacci me dadi" Nihad dai bata ce komai n a ta hau saman gado daga daya side din ta jawo pillon ta jefa makulli a ciki Husnah dai na ta kallonta da gefen ido, Husnah ta mike zaune tana kallonta tace "I want to take malt but gaskiya baxan iya shanye daya ba, idan na rage maki xa ki sha ai ko?" Nihad ta girgiza kai tace "Aa na koshi" a hankali Husnah tace "Toh shikenan, bari in bari kawai kar ayi asaran sa" Nihad tace "Ki sha ki rage ki ajiye mana" Husnah tace "Aa ni kinsan bana son almubazzaranci ke kuma dama kin iya walakanta abinci, da dai kuna da fridge ne sai in je in ajiye sauran amma idan aka bar shi haka ai lalacewa xai yi, ba fa wai da yawa xan rage ba ni nasan gejin cika na, kadan zan rage wllh" Nihad tace "Wa yace maki malt na lalacewa??" Husnah tace "Ke dai tunda baxa ki sha sauran ba shikenan sai in hakura in kwanta da craving dina" Nihad tace "Ni wallahi ban ta6a jin inda malt ya lalace ba sai a bakin ki, ki sha kawai ki rage yayi ta lalacewan mana" Husnah bata kuma cewa komai ba ta kwanta, bayan kusan 10 mins ta mike zaune tana kallon agogo dake nuna karfe goma da rabi ta jawo malt daya kawai ta bude ta fara sha, kallon Nihad tayi ganin kamar ta fara bacci ta tasheta, Nihad ta bude ido a hankali Husnah tace "Wai kin daina alwala ne idan xaki kwanta?" Nihad na lullumshe ido tace "Zan yi" Husnah tace "Aa tashi kije kiyi gaskiya kafin bacci me nauyi ya dauke ki" Sai da ta tashi Nihad kusan sau uku sannan Nihad ta tashi da kyar duk da tunda ta xo gidan nan bata ta6a alwala idan xata kwanta ba amma dabi'arta ce yin hakan tun bayan da taje tayi wani hutu wajen Aunty Jamila na sati uku, Aunty Jamila bata ta6a barin ta kwanta bata yi alwala ba, kuma bayan ta dawo gida kawai training din ya zama jikinta, in dai xata kwanta sai tayi alwala wani lkcn Umma tayi ta mata fada idan taga tayi tace so take sanyi ya shiga jikinta, Nihad na shiga bandakin Husnah ta jawo jakarta da sauri ta bude wani abun maye ta zuba kusan quarter a cikin ɗan malt din ta rage sannan tayi saurin mayar da shi cikin jaka ta ajiye jakar, har ta dauko pillown Nihad xata cire makulli sai kuma ta fasa ta mayar da