Showing 117001 words to 120000 words out of 148918 words

Chapter 40 - Nihaad Book 1 Hausa Novel Complete

sai kowa ya dauke kai, har ya kusa shanye shayin sannan ya ajiye cup din taga ya fara hada allura, tana ta kallon ikon Allah, taga ya sauke trousers dinsa, zaro ido tayi ta kauda kai da sauri ta rufe fuskarta da tafin hannunta, bayan few seconds ta juyo a hankali, empy syringe ta gani, ta mike da sauri tace "Me yasa zaka ma kanka allura?" Bai ko kalleta ba ya bude maganin ya sha da sauran shayin da ya rage sannan ya koma ya kwanta ya lumshe ido ta dinga kallonsa da mamaki, har bayan kusan minti goma bata ga ya bude idon ba sai ma taga kamar bacci yake, juyawa tayi ta fita daga dakin ta koma parlor ta zauna, ko minti sha biyar bata yi a parlon ba taji ana kwankwasa gate, ta tashi da sauri ta koma daki, bacci taga yana yi heavily, ta dau makullin gidan ta fita zuwa gate ta bude, Amina ta gani a tsaye sanye da uniform din islamiyya don ranan lahadi ce, Amina na mika mata waya tace "Ina kwana, wai gashi Umma xata maki magana" Nihad ta amshi wayar sai ga kiran Umma dagawa tayi ta kai kunne daga daya bangaren Umma tace "Kin isa gidan Amina?" A hankali Nihad tace "Umma ina kwana?" Umma tace "Ya haka Nihad, tun jiya ina ta jiranki shiru, Nayi ta kiran Husnah kuma bata daga wayar, ko ta bar gidan ne?" Nihad tace "Ehh ta tafi Umma" Umma tace "Amma ba sai da nace maki kar ki bari ta bar gidan ba sai mun gama magana da ke?" Nihad tace "Nima tashi nayi naga bata gidan" Umma tace "Toh Allah ya kyauta, kin tambayesan kuwa?" Nihad tace "Ehh Umma, yace min sunan Mamarsa Nihad" Umma tace "Amma dai ke shashasha ce wawuya, sai kika yi shiru kika kyalesa da yace maki haka?" Nihad tace "Wallahi haka yace min" Tsaki Umma tayi tace "Baki da wayo ko kadan wallahi, kuma banga alamar za kiyi wayon nan ba, ai shkkn sai kiyi ta zama da dreban, ni sai anjima, haba sai kace ba mace ba ki rasa yanda xa ki bi da shi har ya gaya maki sunan iyayensa, ni gata nake maki, gatan da uwarki ko mutuwa xaki yi baxata ta6a maki ba" Cikin sanyin murya Nihad tace "Toh xan kara tambayarsa Umma kiyi hakuri" Umma tace "Ni sai anjima da Allah" daga haka ta katse wayar cike da bacin rai, Amina ta karba tace "Kin gama?" Nihad bata ce mata komai ba, Amina tace "Sai anjima" Daga haka ta shiga adaidaita da xai kai ta islamiyya don kudin drop Umma ta bata, a hankali Nihad ta juya ta koma cikin gidan. Umma ce zaune gaban wani Rantamemen mutumi ita da Hajiya Turai, Umma na girgiza kai tace "Wallahi Malam ba a samo sunan iyayen nasa ba, kasan yarinyar shashasha ce ga ta kuma er fari, ba wayo" Mutumin dake kallonsu da jajayen tulla tullan idonsa yace "To ai tun farko nace maki xa a iya aiki da sunan nasa kadai kuma aiki zai ci kamar yankan wuka, kawai ku dai in ji dumuss" Umma ta gyara zama tace "Toh madallah malam, kuma ai kai ma kasan kudi ba matsala bace" Yana muxurai yace "Ya kika ce sunan nasa?" Umma tace "Ibrahim" Girgiza kafa ya dinga yi, bayan kusan minti daya ya kalleta da gefen ido yana murmushi yace "Yana nan wani me kyau, dogo sangameme sannan shi ba baki ba, yana kuma da faffadan kirji" Umma tace "Haka yake wallahi malam, duk yanda ka fada wllh haka ne" ya kyalkyale da wani dariya Yace "Toh ai jefaffe ne tun asali, Jifa kuwa ba na wasa ba aka yi masa, ga shi nan naga jifa iri iri a kansa, a jefe yake..." Su Umma dai suka yi shiru suna kallonsa, ya langwabar da kai kamar me nazari sae kuma ya gyada kai yace "Gashi nan an nuna min, ashe ma ruwa biyu ne, ko ta ɓangaren uwa ko na uba" Umma tace "Ba shakka, hakan take malam, ai buzu ne, uwarsa wai er Nijar ce" Yayi wani dariya yana jijjiga kai, Umma tace "Toh amma daga ina aka masa asirin Malam?" Mutumin yayi wani shu'umin murmushi yace "Ɗan wani kauye ne kika ce?" Umma ta girgiza kai tace "Aa, shi dai maigidana ne yasan sunan kauyen nasu tunda har can yaje aka daura auren amma ni ban sani ba gaskiya" Yace "Toh daga kauyen nasu aka jefesa, wato ana masa bakin ciki da ɗan abun da yake samu" Yana gyada kai yace "Shi din me kwazon nema ne tun da ya taso, yana kuma da farin jini, dalilin da yasa ake jifansa kenan.... Sihiri me karfi aka yi masa gashi nan na gani" Umma tace "Ikon Allah, kuma gashi an ga ya fito birni nema dole kuma ya dinga samu sosai" Mutumin yace "Kwarai kuwa, sannan kamar yanda nace maki Allah yayi sa da farin jini da cikar kamala, duk wanda ya ra6a sai ya so shi so na gaske, zai kuma iya damka masa amanar dukiyarsa sbda yarda" Umma ta wani hade rai tace "Toh ni sai6 yanzu so nake ayi masa yanda sisin me gidana baxai sake shiga hannunsa ba don Ubansa, kasa masa mugun tsanarsa wanda xai ji baya son ganinsa baya son mu'amala da shi har abada" Hajiya Turai dake kallonta tace "Idan aka yi haka ke kuma ai sai ya iya cewa sai ya sakar masa er sa" Shiru Umma tayi tana nazari, can wayar Umma ya fara ring ta bude jaka da sauri ta fiddo ganin me kiranta tace "Minti biyu Malam" Daga haka ta mike ta fita can tsakar gida ta daga wayar ta kai kunne tace "Malam barkanmu da safiya" Ta kara da cewa "Eh ba a dai samo sunan ba amma nan da awa daya za mu karaso in sha Allah, don Allah ka jira mu Malam kaga dai daga waje me nisa za mu zo" Hajiya Turai na kallon Mutumin dake gabanta tace "Kana ji malam? so muke shi Alhajin ya fita tsabgar daga shi dreban har yar tasa, sannan maganan gini da yace zai ma yar a Zaria a rushe zancen kwata kwata, malam gaba daya a sa yaji bai son su gaba daya, bai kuma son ganinsu, ita yar dama kawai ya sallama ma duniya ita, sannan abu na karshe ka saka ma shi dreban jin son zai koma inda ya fito wato kauyensu, ka sa zaman birnin ya gagaresa, idan ya so su koma can inda ya fito su ci gaba da zama shi da ita yarinyar" Umma ta shigo ta zauna, Hajiya Turai ta kalleta tace "Duk na gama gaya masa abinda zai yi" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shikenan" Dariya mutumin yayi sosai yace "Kudi... Aikinku aiki ne babba, kuma aiki dole sai da kudi, kinga kafin mu daura aiki a kansa dole za mu warware kadan daga abubuwan da aka masa sannan aikin mu xai samu shiga, ba a hada aiki da aiki ai, sai wancan aikin nasu ya lalata min nawa, wato ya ki barin nawa yayi wani tasiri, ko kuma nawa ya rage tasirin nasu, haka abun yake, yanzu dai nine xan rage tasirin na kansa sannan in dora nawa" Umma tace "Tohh mu dai koma yaya za ayi kawai mu ga mun ci nasara malam, sannan ya dai ci ace an saba yanzu Malam, abu dai shekara da shekaru ana tare ana harka, wannan karan a dubemu karba tsula mana kudi" Hajiya Turai tace "Ai kuwa dai malam, ayi mana sassauci gaskiya" Yana ta6e baki na wasu yan sakwanni sai kuma yace "Kawai ki dire dubu dari da hamsin idan aikinki ya ci ki cika dubu hamsin" Umma ta bude jakarta ta ciro zoben gwal ta ajiye masa tace "Gashi nan wannan dubu dari da tamanin ce, ka rike ka fara min aiki" Ya amsa yace "An gama" tace "Toh malam zuwa nan da yaushe za a fara aikin sannan za a fara ganin tasirin aikin?" Yace "Yanzu zan afka jeji in fara aikinku babu bata lokaci, gaba daya a yau xan yi duk abinda xan yi, zuwa gobe kuma aiki zai fara ci kamar yankan wuka" Umma na Murmushi tace "Toh mun gode Malam, Allah ya saka maka da alkhairi, aikin ka ai mun san ba wasa, mu yanzu za mu tafi sai na kira ka" Daga haka suka masa sallama suka kama hanyar wani kauyen daban. Nihad na ta zaune parlor har kusan sha biyu, can ta mike ta nufi dakin da yake kwance, a hankali ta murda kofar dakin tana kallonsa saman gado ta gansa yana bacci, ta rufo dakin sannan ta shiga dayan dakin tayi wanka ta dauro alwala ta shirya ta fito, sai da ta fara zagayawa ta kwaso kayan da Husnah ta wanke mata ta kai su daki ta linke daga nan ta dawo parlor ta shiga kitchen, kallon kitchen din kawai take, akwai kayan miya da komai a gidan kawai nama ne babu tunda babu fridge, ta fito ta tafi dakinsa, ta bude kofar trying to make no sound, gun Atm card dinsa ta tafi ta dauka da makullin mota da na gida sannan ta fito, cikin mintin da bai wuce talatin ba ta fita taje ta siyo frozen chicken guda biyu da few spices sannan ta dawo gida, ta sake daura alwala tayi sallah bayan ta idar ta koma kitchen din, sai kusan karfe biyu ta fito daga kitchen bayan ta gama duk abinda take, gaba daya ta gaji likis uwa wace tayi girkin mutane goma, ta fada kan kujera, har ta mance rabon da tayi girki don ko da wasa Umma bata sa ta wai saboda hayaki da warin gas, duk sanda taje gidan Aunty Jamila ne take girki don dama Aunty Jamila chef ce, tana gwada mata abubuwa da yawa na girke girke, saving grace din Nihad kenan da har Allah ya taimaketa ta iya girkin, tana ta zaune parlon sai kuma ta mike ta tafi dakinsa ta bude tana kallonsa, bata ga alamar yayi sallah ba, ta karasa ciki ta tsaya side din gadon ta bubbuga pillown da yake a kai tace "Baka yi sallah ba" Ya bude ido da kyar ya kalleta yace "Ina ruwanki?" Kyabe baki tayi tace "Toh don ma ka samu ina tashin ka?" Ta wani juya ido ta juya xata fita ya bi ta da kallo, sai kuma yace "Ina son ruwan zafi" Ta jefa masa wani kallo tace "Toh meye zaka gaya min? Ko house help dinka ce ni?" Daga haka ta fice daga dakin, lumshe ido yayi yana son tashi amma ba shi da enough strength din yin hakan, bayan kusan minti ashirin har wani baccin ya kara daukesa ta shigo dakin rike da kettle din ruwan zafi, ya bude ido da sauri jin sound din bude kofar, bandaki ta shiga ta dauraye bucket ta juye masa ruwan zafin a ciki tana fitowa kuma ta fita daga dakin ba tare da ta kallesa ba, ya yunkura ya mike zaune sannan ya sauka daga saman gadon ya shiga bandakin. Ko da ya fito yaga abinci ajiye a dakin, ya gama shiryawa yayi sallahn zuhur, yana ta zaune saman darduma yana kallon warmers din abincin, can ya jawo karamin warmer din ya bude aroma din miyan ya doki hancinsa, ya bude dayan ya ga shinkafa ce, kawai zuciyarsa ya basa ai aiko mata da abincin aka yi ya kulle ya matsar daga kusa da shi. Har aka yi la'asar Nihad bata sake shigowa dakin ba, zuwa lkcn he is feeling much better, fitowa daga daki yayi ya ganta kwance kan 2 seater tana bacci, ya karasa cikin parlon, a hankali ya kai hannu ya buga kujeran, ta bude ido da sauri zata kwala ihu ta gansa, don duk tunaninta aljanin daren ne ita ma ya zo mata, Ya dauke idonsa daga kallonta yace "Sallah" Tace "Ina ruwanka?" Bai ce komai ba ya juya ya koma daki, karamar wayarsa ya dauka ya zauna gefen gado yaga miss calls din Nadeeyah har hudu sai kuma miss calls din Abba biyu, sannan message na debit din dubu ashirin da biyar bayan debit din drugs da ta siyo masa da safe, yana ta kallon debit din sai kuma ya mike ya fita daga dakin tana zaune kan kujera yana kallonta yace "Me kika min da dubu ashirin da biyar?" Ta kyabe baki tace "Toh kaza naje na siya na dubu goma nayi girki don ni baxan dinga cin abinci lami ba, bayan nasan Abbana na baka har da kuɗin nama, dubu biyar kuma na siyo spices, dubu goma kuma na zuba mai a mota, idan ma kudin account din ne suka kare ai sai ka kirasa kace sun kare" Kallonta ya dinga yi, ta ɗan kallesa ta gefen ido, sai kuma ta turo baki ta mike ta wuce dakinta ya bi ta da kallo, komawa cikin dakin yayi ya kara bude abincin da tace tayi yana kallo, har cikin ransa bai yarda ita tayi girkin ba duk da bai ci ba, can dai ya dau spoon yayi tasting stew din, nan ya kara tabbatar ma kansa ba ita tayi ba, duk da yunwan da yake ji bai ci abincin ba. Da magrib bayan ya fito daga masallaci ya ga almajirai biyu ya tsayar da su sannan ya shiga cikin gidan ya fito da abincin ya juye masu ya koma kitchen ya wanke warmers din ya fito, daki ya shiga ya dauko makullin mota da atm card dinsa ya bar gidan, tana jin ya fita ta fito balcony da sauri ko gama goge jikinta bata yi ba don wanka take taji ya kunna mota ta kwara ruwa kawai ta daura tawul ta fito da gudu, Hijab dinta da ta fizgo ta saka a kan tawul din, duk a tsorace take da gidan tun da taga gari ya fara duhu dama hankalinta ya tashi, can saman dakalin da yake zama ta tafi ta zauna hawaye cike idonta, ta fi awa daya wajen zaune ga uban sauro dake ta cizonta har da guntun gyangyadinta, sai bayan isha ya shigo gidan, bayan yayi parking ya tafi ya kulle gate ya dawo yana kallonta amma bai ce mata komai ba, juyawa yayi ya shiga cikin gidan ta bi bayansa da sauri cikin kuka tace "Ni wallahi kar ka sake fita ka barni ni kadai cikin gidan nan da daddare, don baka ga abinda ya faru da Husnah bane har ta bar gidan shi yasa zaka wani tafi ka bar ni kadai kuma ka tafi da makulli" Ya juya ya kalleta yace "Wacece Husnah?" Ta hade rai tace "Kawata da ta zo gidan nan ta kwana mana" Yace "Ohhh ta tafi ne?" Nihad tace "Aljanun dare ne fa suka zaneta fuskarta duk ya kumbura shine ta gudu" Yace "Au haba?" Ta wani daure fuska tana kallonsa, yace "Toh Allah ya sa kar su dawo kanki tunda ita ta gudu" Yana fadin haka yayi hanyar dakinsa ta bi sa da gudu ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me yasa zaka ce min haka? Me nayi masu ni za su dawo kaina?" Yana shiga dakinsa ita ma ta shige tana kallonsa tana maida numfashi hawaye cike idonta, duk a mugun tsorace take, yace "Malama kwanciya xan yi ki tafi dakinki sai da safe" Ta wani gwalo ido tana kallonsa, sai kuma kawai ta nufi can karshen gadon dakin ta zauna, ya tsaya yana kallonta sai kuma yace "Ohk, sai in bar maki dakin in koma wancan" Bata san sanda ta fashe da kuka ba tace "Don girman Allah kar ka barni ni kadai wallahi tsoro nake ji kuma baxan iya kwana a dakin ni kadai ba" Sai kuma ta hade kai da gwiwa tana rera kuka, bai kuma ce mata komai ba ya kulle kofar ya karasa cikin dakin. A hankali ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito ta tada sallan isha, yana kwance daya side din gadon waya kare kunnensa, duk da can kasa kasa yake magana amma lkci daya ta gane da warce yake wayar, ta ja tsaki ta mike ta dauke darduman ta linke ta ajiye ta nufi saman gadon ta fizge duvet da ke kai ta dau pillow daya ta shimfida duvet din a kasa sannan ta ajiye pillon ta kwanta, tana ta juye juye kan duvet din can ta kara jan wani tsaki ta tashi ta tafi ta kashe wutan dakin ta dawo ta kwanta, shi dai bai daina wayar da yake ba kuma duk maitarta baxata ce ta ji abinda yake cewa a wayar ba, for almost one hour bai gama wayar ba, ya mike sabida iska da aka fara alamar hadari, kunna wutan dakin yayi Nihad da tayi lamo a kasa tana jin iskan ita ma ta mike zaune da sauri ta bi sa da kallo sai kuma ta tashi ta bisa parlon, ya juya ya kalleta, sai kuma yace "Zan kwanta yanzu kinsan nace maki bani da lafiya, za mu yi magana gobe" Daga haka ya katse wayar yace "Lafiya kike bi na?" Kin cewa komai tayi tana kallonsa, haka kawai tayi masa rashin kunya ya ki yarda ta kwana a dakinsa, shi sa ma taki ce masa komai juyawa yayi ya tafi ya kulle duk windows din gidan, duk inda ya nufa sai ta bi sa har dakinta sai da ya shiga ya kulle windows sannan ya fito tana biye da shi suka koma dakin nasa, kulle nasa windows din yayi ya kashe wutan dakin ya kwanta daya side din, ba a wani dau lokaci ba aka fara yayyafi, Nihad dai duk a tsorace take a kasa da take kwance, can ta mike zaune a hankali tana kallon saman gadon, sai kuma ta turo baki ta mike ta dauke pillown da duvet ta koma saman gadon ta kwanta, yana jin ta bai ce komai ba sai ma juya mata baya da yayi ya rufe ido, Nihad na jin sauwkan ruwa ta mirgina a hankali ta koma bayansa tayi lamo, ta dade a hka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login