Showing 93001 words to 96000 words out of 148918 words
kace idan na gama sanye kayan da na kawo za mu tafi gida, toh gashi yanxu ko kayan da xan canza gobe bani da shi" Yace "Sae ki maimaita na yau" kuka take sosai, ya juya mata baya, ta ci kukanta ta gode Allah sannan ta koma ta kwanta a hankali, bayan kusan awa daya ya kunna torch dinsa ya haska fuskarta ya ga bacci take. Can kusan asuba xafin jikinta ya farkar da shi, kamar jiya tana kusa da shi ta takure waje daya, ya kai hannu jikinta ya ji da xafi....
*Ki biya dari biyar ki karanta hankalinki kwance er uwa*
NIHAAD is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via👇🏻
07087865788....
Yau ma kamar jiya hasken rana ne ya sa Nihad ta farka, da kyar ta mike xaune tana jin duk jikinta na mata ciwo barin kanta da yayi mata nauyi, sosai hankalinta ya tashi ganin khalil baya dakin, ta hade kai da gadon karan da take kai tana kuka a hankali, can dae tayi karfin halin mikewa ganin lokaci na tafiya bata yi sallah ba, ta nufi yar jakar da ta sa brush dinta da Toothpaste ta dauka ta fita daga bukkar. Bayan ta idar da sallah tana xaune saman abun da tayi sallan lkci lkci tana share hawayen dake gangaro mata, rashin ganinsa na kara saka mata damuwa a kan wanda take ciki, shadow da ta gani bakin kofa ya sa ta daga kai da sauri hoping shi ne ya dawo, amma sai ta ga ba shi bane, wata budurwa ce warce xa su yi sa'anni da Nihad din ta shigo dakin, fara ce kal kal don duk hasken Nihad yarinyar ta fi ta, ga ta kyakkyawa ajin karshe, dogon gashinta da aka kitsa gida biyu manya manya har ƙafadunta suke tabowa, ga uban wushiryarta a baki, Nihad ta ganeta don jiya kaya kala biyu ta bata da turare, budurwar na murmushi ta duka gaban Nihad ta ajiye mata kwanon sha dake hannunta tace "Hannu, yau kamar kin makara ko" Nihad ta kirkiri murmushin ita ma tace "An tashi lafiya" Yarinyar tace "Lafiya lau, ga farau farau nan na kawo maki, yanxu xa a dunduma tuwon sae a kawo maki" Sosai gaban Nihad ya fadi jin kalmar tuwo, ita fa bata ta6a sanin akwai wani kalan tuwo bayan fari ba, gwara gwara amala ta san baki ne, to da wannan abun da suke kira tuwo ba gwara a bata amalan ba, ta dai sakar mata wani murmushin karfin halin tace "Toh, nagode" Yarinyar na wasa da gashinta tace "Ni sunana Furera amma ana kirana Fure ke kuma fa?" Nihad ta sauke idonta tace "Sunana Nihad" Yarinyar ta zaro ido tace "Sunan yan birni, ae baxan ma iya kiran sunan ba" Nihad tace "Toh ki kirani Ummi" Fure tace "Yauwa gwara wannan, amma ae xa ku yi sati a nan ko?" Nihad ta kalleta da sauri ta girgiza kai tace "Aa yau xa mu tafi" Yarinyar tace "Gwaggo fa tace min xa ku yi sati" Nihad xata yi magana sai ga Khalil ya shigo bukkar da sallama, lkci daya kamshinsa ya cika Bukkar, Fure ta koma gefe tana d'an Murmushi, tace "Hamma wai ashe yau xa ku tafi?" Yanda take maganar kasan a kunyace take da Khalil, Khalil ya kalleta yace "In ji wa?" Fure ta nuna masa Nihad, yace "Aa xa mu yi sati" Gaban Nihad yayi mugun faduwa ta gwalo ido tana kallon khalil a ranta ta dinga nanata satin da yace, meye kuma sati, ba dai sati daya yake nufi ba, cike da murna fure tace "Yauwa dama haka Gwaggo ta sanar min, ai ko naji dadi sosai, duk xan bi in xaga da Ummi kauyen mu da wanda ke gaba da namu, a kawo maka farau farau din ne ko fura da nono xaka sha, nonon ma sabuwa ce jiya aka tatso" Yace "Toh kawo min fura da nonon" Tace "Toh" daga haka ta fita, Nihad ta marairaice tana kallonsa tace "Amma dai xaka maida ni gida sae kai ka dawo kayi satin a nan?" Ya dauko tabarma ya xauna kai ba tare da ya kalleta ba yace "Ko kuma ni in tafi bayan sati daya in xo in dauke ki ba" Bata san sanda ta fashe da wani matsanancin kuka ba tace "Don girman Allah kar ka min haka ka rufa min asiri..." sai a sannan ya daga kai ya kalleta, ta hade tafin hannunta tana kuka a hankali tace "Don Allah kayi hakuri, wallahi baxan iya ba, kaji har na rantse" Gyara xama yayi yace "Bukka guda Gwaggo xa ta bar maki kiyi rayuwarki ke kadai har bayan sati dayan babu me takura ki" Nihad ta mike da sauri ta nufesa ta durkusa gabansa tana kuka tace "Wallahi xan iya mutuwa idan ka tafi ka bar ni a nan, kar ka tafi ka bar ni" Kallonta kawai khalil yake, dai dai nan Fure ta turo kai cikin Bukkar rike da kwaryan nono da fura, Nihad ta koma gefensa da sauri ta zauna, Fure ta durkusa gabansa ta ajiye fura da nonon tana kallonsa tace "Kana son sukari?" Khalil yace "Kadan" Mikewa tayi ta nufi kofa xata fita, khalil ya bi ta da kallo, Nihad ta kallesa, sannan ta kalli yarinyar har ta fita, Khalil tankwashe kafarsa yana kallon fura da nonon dake cikin kwarya a gabansa, muryar Nihad ya ji kamar daga sama tace "Kanwarka ce?" Ya ɗan kalleta, sai kuma yace "Aa, er makotanmu ce, Baabarta ai ta shigo kun gaisa jiya" Sai ga fure ta shigo rike da sugar a hannunta, durkusawa tayi gaban Khalil tana murmushi ta juye sugar din a kwaryan nonon, ta ɗan kallesa tace "In dama maka?" Ya gyada mata kai yace "Ehh" Nihad dake kallonta ta mike tace "Bar shi xan yi" Fure ta kalleta sai kuma ta mike tace "Toh" Kallonta kawai khalil yake babu yabo babu fallasa ta dawo gabansa ta durkusa ta dau ludayi ta saka cikin kwaryan, Fure ta mike ta fita, Nihad na kiciniyar dama fura da nonon kwaryan ya kife duk suka malale a kasa, da mamaki Khalil da ya koma baya yake kallonta, kana ganinta kasan bata ta6a dama fura da nono ba, ta turo baki ta mike ta bar wajen ta koma can karshen gadon kara ta zauna tana kallon mess din da tayi a kasa, khalil yace "Na kara sati daya a kan satin da nace xa ki yi a nan" da sauri ta mike ta nufosa ta fashe da kuka tace "Wallahi ba da gangan nayi ba, kwa6ewa yayi a hannuna" Ya hade rai yace "Da baki iya ba me yasa baki bar warce ta iya ba tayi" Tana goge hawayen idonta tace "Toh meye xata wani zo tana ma mutane yauki kamar kubewa a nan?" Mikewa khalil yayi yace "Ni dai na gaya maki, ki shirya kwana sha biyu nan gaba a nan" Nihad na kuka ta riko rigarsa da sauri ganin xae fita cikin rawan murya tace "Don Allah kayi hakuri, idan na kara ko kwana daya a kauyen nan yunwa xae iya kashe ni" Ya janye rigarsa daga hannunsa ya fice daga bukkar, Nihad ta sulale kan inda ya tashi tana kuka a hankali. Goge idonta tayi da sauri jin ana sallama, ta kalli matan da suka fara tururuwan xuwa kofar Bukkar da take don gaisheta, da murmushi take amsa masu gaisuwar tasu cike da karfin hali don yunwa ba na wasa ba take ji, tunda take bata ta6a jin irin wannan kalan yunwan da take ji ba, wata mata ta shigo ta kwashe kasar dai dai inda fura da nono ya xuba ta fita da shi, Nihad ta bi ta da kallo, to ko kiwon dabba ake yi ai a tunaninta ba a kiwonsa a ordinary sand balle mutum, ko kaji ma ana shimfida masu kwali.... Nan ko ga kasa kiri kiri a daki kamar a kofar gida, Gwaggo ce ta shigo daga karshe rike da kwanon dumamen tuwo ta ajiye mata tace "Hannu Ummi, an tashi qlau dai ko?" Nihad na Murmushin karfin hali tace "Ina kwana Mama" Gwaggo tace "Lafiya lau, ga tuwo ki ci kafin kiyi wanka, ko dai kina son yajin daddawa a kawo maki da man shanu" Da sauri Nihad tace "Aa nagode xan ci haka" Gwaggo tace "Toh, Don naga jiya ma kamar baki wani ci tuwon ba, wannan na barbada maki me tauraro a kai, xaki ji dadinsa, kinsan ku yan birni baku amfani da manda a girki" Nihad dai sai ka rantse tallan close up take yanda take murmushin karfin hali tana kallon tsohuwar, Gwaggo tace "Ko a damo maki hurar ki hada da tuwon naga faro faron ma baki sha ba" Nihad ta girgiza kai tace "Aa wannan ya isa mama, nagode" Gwaggwo tace "Idan kin gama ci sai ki fito an kai maki ruwan wanka" Nihad tace "Toh" Bayan fitarta da kamar minti sha biyar Nihad ta mike ta fita tsakar gida, haka duk matan gidan dake shirin surfe suka bi ta da kallo, Gwaggwo ta taso tace "Har kin cinye" Nihad tace "Ina son xan yi wanka" Gwaggo ta rakata xuwa bandakin ta bude mata kofar karan tace "Ga ruwan a ciki" Nihad ta saka kai ta shiga ciki, bayan matar ta bar wajen kawai ta fashe da kuka, yau ita ke ganin rayuwa haka, yanzu a haka xata yi wankan?? A daddafe ta watsa ruwa tana rike numfashi sbda uban zarnin da wajen ke yi ta fito da sauri, har ta shiga bukka kallonta matan tsakar gidan suke, ko mai Nihad bata shafa ba ta saka kayanta ta xauna gefen gadon kara jiki a sanyaye tana bin kudajen dake ta shawagi a dakin da kallo, Sai kuma ta hade kai da gwiwa ta fara shesshekar kuka tana jin kamar Ulcer xai iya kamata at anytime. Har rana bata ga Khalil ba, aka kawo mata gwaza da mai da gishiri, da farko tayi xaton doya ce amma bayan warce ta kawo mata ta fita, ta dauka tana kare masa kallo kafin ta 6are ta kai baki a hankali, da sauri ta fito da shi tana yamutse fuska, a haka ta matsar da kwanon a inda kwanon tuwo da faro faro suke tayi tagumi, cike da tausayin kanta. Kusan karfe hudu saura Gwaggo ta leko bukkar tace "Ke baki fitowa shan iska Ummi, ai da xafi dakin..." Nihad ta girgiza kai a hankali tana mata murmushin karfin hali, alamar bata son ta fitowa, Gwaggo ta kyaleta ta tafi ta ci gaba da abinda take, duk motsin da xata ji sai ta leka ko Khalil ne amma sai taga ba shi bane, a haka har ta fita taje tayi alwala ta dawo tayi la'asar, xuwa lkcn jikinta rawa yake saboda yunwa, she is very very hungry, amma babu abinda xata iya ci cikin abubuwan da aka kawo mata, kukan ma ta gaji da yin sa yanxu ta daina, tana idar da sallah ta kwanta saman gadon karan tana juye juye, daga karshe ta mike ta sauko kasa jikinta na rawa ta bude farau faron dake kulle ta dauka, runtse ido tayi cike da karfin hali ta kai bakinta kan kwanon ta rike breathing dinta sannan ta hau kwankwada, ajiye kwanon tayi da sauri bayan ta kwankwadi kusan rabi, saboda wani amai da taji ya taho mata, ta mike da gudu ta fita daga dakin, gwaggo da matan tsakar gidan dake surfe suka taso da sauri suna tambayarta lafiya, nan ta dinga kwararar masu aman abinda ta sha kamar xata shide, Gwaggo da duk ta rude tace "Subhanallahi, me ya sameki, gashi baya nan" Wata mata ta kawo ruwa da sauri suka ba Nihad dake maida numfashi, amsan ruwan tayi da kyar ta wanke bakinta duk jikinta na rawa, Gwaggo da hankalinta yayi mugun tashi ta kawo mata kujerar tsugunno tace "Hannu, zauna nan, zauna" Nihad ta xauna a hankali kan kujeran tana maida numfashi, Gwaggwo tace "Me ya sameki kike hararwa haka?" Da kyar tace "Bani da lafiya ne dama" Matan gidan suka dinga yi mata sannu, ganin yanda jikinta ke rawa Gwaggo ta maida ta cikin Bukkar tana mata sannu ba adadi, wata yarinya da ta aika ta dubo mata Khalil a waje ta dawo ta shigo Bukkar tace "Gwaggo bamu gansa ba" Gwaggo tace "Toh bari a mata jike jike tasha ko xaxxabin xai sauka" Daga haka Gwaggo ta fita, kuka Nihad take a hankali tana juye juye tana jin kamar kanta xai fashe don ciwo, bayan wani lokaci sai ga gwaggwo da kwano ta ajiye kasa ta dago Nihad tace "Ga nan jike jiken sassaken itatuwa na maki, tashi ki sha, ba daci ba bauri, ba hamami" Nihad ta mike tana rawan sanyi Gwaggwo ta dauko kwanon ta kai mata baki tace "Ungo sha" Cike da karfin hali Nihad dake ta kallon cikin kwanon ta kurbi ruwan ciki, Gwaggo tace "Kara sha" Nihad ta runtse ido ta kara kurba ta hadiye tsikar jikinta na tashi, dacin ruwan kuwa ba a cewa komai, Gwaggo tace "Yauwa, to koma ki kwanta yanxun nan xaki fara xufa, su ararrabi ne da sabara da tazargade, ga su nan dai" Nihad ta koma ta kwanta Gwaggwo na kokarin lullubeta Khalil ya shigo Bukkar ya nufo Nihad yana kallonta, Gwaggwo tace "Wallahi mugun zazzaɓi ne ya rufeta yanxun nan sai hararwa take" Khalil ya duka yana kallonta ya kai hannu jikinta wanda yayi zafi kamar wuta, cike da damuwa Gwaggwo tace "Akwai wani karamin asibiti a gidan Darho, kauyen da xaka wuto kafin ka zo wannan, ko xaka kai ta a dubata a bata magani ɗan nan?" Khalil yace "Toh xa mu je can" juyawa tayi ta fita daga Bukkar, Hannu ya kai goshinta duk da idonta a kulle yake yace "Ina ke maki ciwo" Ta fashe da kuka ta tura hannunsa daga goshinta tace "Ni ka maida ni gidanmu, idan ba haka ba sai Allah ya kama ka" kallonta ya tsaya yi, can ya gyada kai ya koma gefe yace "Ohkk" tayi karfin halin mikewa cikin kuka ta kamo hannunsa tace "Don Allah kayi hakuri ba don halina ba ka maida ni gida" Yace "Toh ina ke maki ciwo?" Tana shessheka tace "Kai na, kuma ina jin yunwa" Ya mike yace "Sakko" Da sauri ta mike xaune amma ta kasa tashi daga saman gadon duk yana kallonta, ya mika mata hannunsa ta rike sannan ta mike tsaye a hankali, dukawa tayi yana rike da hannunta ta dau Hijab jikinta na rawa ta saka, sannan ta dau handbag dinta, ko bin ta kan atamfarta na karshe da kayan shafe shafenta bata yi ba, a haka suka fita daga Bukkar, Gwaggwo da matan gidan suka taso, ana mata sannu in chorus, Gwaggwo tace "Can asibitin ku ka nufa ko?" Yace "Ehh" Nan dai aka dinga mata Allah ya sauwake, Fure dake tsaye kusa da wani ɗan mariki da aka daure tace "Gwaggwo in rakasu asibitin" Da sauri Nihad ta kalleta, murya can kasa Nihad ke girgiza ma Khalil kai tana cewa "Aa baxa mu je da ita ba" Ya ɗan kalleta ta gefen ido, Gwaggwo tace "Toh ko kama maka ita ai sai fure ta dinga yi a asibitin ko" Da sauri Nihad na Murmushi tace "Aa mama xan iya ai" Gwaggwo tace "Toh shkkn, Allah ya baki lafiya sai kun dawo" Nihad dai bata ce komai ba a ranta kuwa tunani take ina din xa su dawo da take ce masu sai sun dawo? Dalilin ma da yasa bata son Fure ta bi su kenan don in sun tafi da ita ai dole su dawo da ita kauyen, ita kuwa bata fatan abinda xai sake dawowa da ita kauyen nan, suna isa inda Khalil ya ajiye mota ya saketa ya zaga daya side din, a hankali ta bude front seat din ta shiga, bayan yayi warming motar ya ja motar, matan gidan da suka taru bakin kofar shiga gidan har da masu daurin kirji, ga yaransu duk ba wando a tsattsaye su ma, sai daga masu hannu suke kana ganinsu dai kaga yan kauyen kayau, haka ma sauran makota da suka fiffito jin karar mota, Nihad ta sauke wani ajiyar xuciya, at long last!!! har taji xaxxabin ya tafi sai kuma bakar yunwan da take ji, tafiyar minti talatin suka yi ta ga alamar sun fara shigowa gari, farin ciki gunta ba a cewa komai, bata ta6a tunanin xata fito daga kauyen can da ranta ba, ta zata sai buzunta, so truly akwai mutane irin haka a rayuwar nan, akwai mutane dake rayuwarsu cikin kauye haka? lkci daya jikinta yayi sanyi, and they are leaving happily abunsu babu wani damuwa, ko pole din wuta ita bata gani a garin ba balle a je ga an ja masu wuta, parking ta ga khalil yayi dai dai wani pharmacy, duk da bata san inda suke ba amma tasan sun shigo cikin gari gaba daya, ya kashe motar ya sauka yana kallonta yace "Sauko malama" A hankali ta bude motar ta sauko ta bi bayansa tana jan kafa saboda jiri da take gani, suka shiga pharmacy din, bayan sun gaisa da me Pharmacy din ya koma gefe ya tsaya yana kallon Nihad da ta jingina da kofar pharmacy din bata shigo ba, har ta rame tayi wani uban duhu kamar ba Nihad ba, Ya kalli me Pharmacy din yace "Ita ce bata da lafiya" Me Pharmacy din yace "Sannu Hajiya karaso" Tana jan kafa ta tafi gaban table dinsa ta xauna, Tunda aka haifeta ba a taba kawo su pharmacy idan basu da lafiya ba, sai dai asibiti, amma wai yau ita ce a pharmacy xa a mata treatment bata da lafiya instead of hospital, muryar Pharmacist din ne ya dawo da ita duniyar tunanin da ta tafi, ta sauke idonta kasa a hankali tace "Zazzaɓi nake ji da ciwon kai" Yace "Kina amai ne?" Ta gyada masa kai tace "Ehh nayi daxu" Yace "Ohk" Kallon khalil yayi yace "Xa a maganunguna da allurai...." Khalil ya rungume hannunsa yace "Sai dai magungunan kadai, don kauyen da muke akwai nisa, baxai yiwu mu