Showing 51001 words to 54000 words out of 148918 words

Chapter 18 - Nihaad Book 1 Hausa Novel Complete

ya ci gaba da zama a gidan ko ko? Yau naga fitina" Aminu yace "Ae ba shi da matsala fa Hajiya, kowa a gidan ya shaida, kullum nan muke yini tare da shi" Inna tace "Aa rufe min baki Aminu, wllh in nice a gidan nan da ido daya zan dinga bacci" Tayi kasa da murya tace "Irinsu ne fa ke aikata mugayen abubuwa a duniya yanxu Aminu, ko kai baka ga siffarsa ba, wannan idan cacan baki ya hadaka da shi sai dai ya daga ka ya nana shege da kasa, to bai cuceka ba? Da nayi niyyar kwana amma gaskiya baxan iya ba da wannan mutumi a gidan nan, ina dalili" Dariya kawai Aminu yake, Inna tace "Bari in shiga mu gaisa da su kawai inyi fitowata in wuce" Daga haka ta wuce cikin gidan, tana zaune parlor da Mumy dake ta sauraronta Khalil yayi sallama bakin kofar, Inna tayi kasa da murya tace "Kaddai shi ne? Har nan ku ke bari ya xo maku??" Mikewa Mumy tayi ta nufi kofa, Khalil ya gaisheta da ladabi ta amsa tana tambayarsa ya aiki, yace "Alhamdulillah" ledan hannunsa ya mika mata yace "Sakon Hajiya ne" Mumy ta amsa ta juya ta koma cikin parlon, inna ta hangame baki ganin leda shake da manyan apples tace "Meye wanan din? a ina naga kudin biyan wannan apple cike a leda, amma dai wawa ne wannan yaron, maza ciro kwara biyu ga dari biyu ki basa, sauran kuma ya mayar yace ance baxa a siya ba" Mumy na kallon Inna tace "Wai da na nawa kika ce ya siyo inna?" Inna tace "Aa ni ban aikesa ya siyo ba, kawai cewa nayi yaje ya tambayo nawa nawa ne, ni ban aikesa ya kwaso min ba wallahi" Mumy tace "Atoh ina amfanin mayar da abinda aka riga aka karbo Inna" ko rufe baki Inna bata jira Mumy tayi ba ta mike ta fixge ledan tace "Ai ba sata nake yi ba da xan siye duk apple din nan, kuma 'ya yana ba kudin banxa suke samu ba" Tana gama fadin haka ta fita waje da sauri, can bakin gate ta hango khalil a zaune tace "Yau naga gantalallen mutumi, wa ya bamu kudin siyan wannan uban apple din, ko don ya ga makeken gida ya zata sata ake yi" Tana isa kusa da su tayi kasa da murya tace "Ɗan nan cewa nayi ka tambayo nawa nawa ne, bar ganina haka, wllh rufin asirin Allah kawai nake takama da shi, bani da komai, maza ka maida masu kace biyu aka aiko ka kaji" Khalil yace "Aa Hajiya na siya maki ne kawai ki ci" Inna tace "Ka siya min? Ko dai lemo ka kwaso min?" Tana fadin haka ta kara bude ledan da sauri tana lekan ciki, ai ko taga apple ne ya fi goma, Inna ta gwalo ido tace "Albashin naka ka kwashe ka siyo min apple din?" Khalil yayi murmushi kawai, Inna ta rike ha6a tace "Kaii amma wallahi nagode, Allah yayi maka albarka, ko jikokina babu wanda ya ta6a min haka cikinsu, dari uku uku fa ake siyar da duk guda daya" Shi dai khalil murmushi kawai yake, Tace "Amshi ledan mu shiga Maryam ta maka godiya" Da sauri yace "Aa Hajiya" Inna tace "Amsa kawai mu tafi nace" Amsan ledan yayi tana gaba ya bi bayanta har main parlor, tana ganin ya tsaya bakin kofa tace "Aa shigo kanka tsaye" Still yaki shiga, Inna tace "Wai ba ni nace ka shigo ba, ni fa na haifi me gidan" Mumy dake kallonsu tace "Ka karaso" Shiga parlon yayi da sallama, Inna ta kulle kofa tana nuna ma Mumy ledan tace "Wllh Maryam ashe siya min yayi da albashin sa, kin dai ga bare ne fa amma yasan kyautata ma tsohuwa" Mumy tace "Toh Allah ya saka da Alkhairi, maa sha Allah" Inna tace "Allah sai naji ya fiye min Hamid da su Farooq sau dubu" Mumy dai bata ce komai ba, Inna ta rike ha6a tace "Allah yayi maka albarka ka ji" Yace "Ameen Nagode" Bude kofar parlon aka yi Nihad ta shigo, still tayi bakin kofar tana kallon Khalil da mamaki, sai kuma ta kalli Inna da Mumy tace "Me wannan kuma yake yi har cikin parlor?" Mumy tace "Uwarki yake yi" Nihad ta hade rai tace "Mumy parlon mu fa, privacy dinmu, this is uncalled for gaskiya, ko su Aminu da suka yi shekara da shekaru a gidan nan xa a bari su shigo nan balle wannan driver din..." Mikewa Mumy tayi tana ganin haka tayi hanyar stairs da sauri, Mumy bata fasa bin ta ba, Inna tayi kasa da murya tana kallon Khalil tace "Wallahi duk hakuri muke da ita, duk ta fi karfin kowa in gaya maka, shi yasa kwanaki da ta je ta kai karar ka gu na wai in sa a kore ka nace waa? Me ka min xan maka sanadin aikin ka, wllh naki biye mata shine ta kullace ni har yau, dama dai bansan mugun halinta bane shine xan biye mata amma ai kaga ban biye mata ba gashi har yanxu kana aikinka cikin rufin asiri har da siyo min apple, ni duk inda harkar rashin gaskiya take ba ni a ciki, Nihad kam bata da gaskiya wllh" Khalil dai kansa na kasa, Inna tace "In ji suna baka abinci isasshe dai?" Yana murmushi yace "Ehh ana bamu" Inna tace "Toh shkkn, can gidan Habubakar din ma ka iya dinga xuwa kullum, ai yanxu kam ka zama Ι—an gida" Murmushi yayi yace "Nagode Hajiya" Tace "Yauwa je ka" Juyawa yayi ya fita daga parlon. Da daddare Nihad na kitchen tana pancake da xata ci kafin ta kwanta Sudais ya shigo kitchen din, cup din hannunsa ya ajiye a sink yana kallonta yace "Lahh Aunty Nihal ma tace mana tayi pancake ta ci yau a makaranta" Nihad na juya pancake dinta ba tare da ta kallesa ba tace "Did u spoke with her today?" Yace "Yess, Uncle driver ne ya kira mana ita, muna ta magana da ita for long" Juyawa Nihad tayi ta ajiye spatula din hannunta tace "Who is uncle driver?" Yace "Wannan da yake kai mu school" Ta bude baki, sai kuma tace "Yaushe ya kira maku ita?" Sudais yace "After magrib prayer" Sake baki Nihad tayi tana kallonsa, jin kaurin pancake dinta ta kashe gas din da sauri ta fita daga kitchen din, sama ta tafi bangaren Umma, har bedroom ta shiga ta sameta tace "Umma kinsan da wa Nihal ke waya yanxu?" Umma tace "Wa?" Nihad tace "Wai driver, yanxu su Sudais suke ce min ai ya kira masu ita, ranan da xa mu je shopping ne fa ya amshi numberta, toh a ranan da xa mu kai ta school ma ya kirata ya fi a kirga, sai ga yanxu su sudais suka xo suna gaya min ai driver ya kira masu ita" Da wani expression Umma tace "Driver? Wani drivern ni Sumayya?" Nihad tace "Driver dae da kika sani" Umma tace "Ko dai Nihal ta fara hauka ne?" Nihad ta kyabe baki ta zauna gefen gado, Umma ta dau wayarta ta hau kiran Nihal, yana fara ring Nihal ta daga, Umma tace "Nihal kiran me ku ke yi ke da drivern gidan nan?" Nihal tace "Driver kuma?" Umma tace "Ban sani ba" Nihal tace "Wallahi ba komai Umma kawai wani lkcn yana ba su Sudais ne mu yi magana da su" Umma ta kunduma mata zagi tace "Kanin uwarki ko na ubanki? Banda xubar da aji meye na wani waya da drivern gidanku? Sa'anninki na waya da mutanen arxiki ke kina waya da driver, ke wace irin yarinya ce? to wllh xan ci kaza kazanki idan baki kama kanki kin goge number tasa ba, kaji min gantalalliya dai" Nihal dai tayi shiru, Umma tace "Na dai gaya maki tun wuri ki goge number nan ko in ci maku ke da shi" Umma na kai wa nan ta katse wayar, sosai ranta ya baci, ita kam wace irin yarinya ce Allah ya bata, duk abun kaskantar da kai ta iya shi, banda haka meye ya kai ta dinga waya da driver, Nihad tace "Wllh Nihal is so annoying, how comfortable is she making call with that wretched man" Umma tace "Ki kyale mahaukaciya mana" Nihad ta mike ta tabe baki ta fita daga dakin, Zaga dakin Umma ta dinga yi. Nihad na gama pancake din ta shiga bangaren Abbanta, bayan ta gaishesa tayi shiru saboda Mumy dake zaune a parlon, Abba ya kalli Mumy, murmushi kawai tayi ta mike ta bar masu parlon, Abba na kallonta yace "Ya aka yi daughter?" A hankali tace "Abba na tambayi wata kawata gyaran screen din wai 150k ne" Abba yace "Har 150k?" Ta marairaice tace "Eh Abba" Shiru yayi, can yace "Ohk gobe zan tura maki, amma baxa ki wajen gyaran ke kadai ba, ko ku je da farooq?" Da sauri tace "Aa Abba ba kace driver ba?" Abba yace "Ohk, no problem sae ku je tare, kin gyara account din naki ne?" Tace "Aa sae next week, I'm busy with lectures throughout this week" Abba yace "Ohk xan sa kudin a account din Farooq sae ya baki" Ta hadiye abu da kyar sai kuma tace "Abba driver din bashi da account?" Abba yace "No I don't know" Tace "Abba idan yana da shi kawai ka sa mashi tunda tare xa mu, ba sae ka tura ma ya Farooq ba" Yace "Ohk, Allah ya kai mu goben" tace "Ameen" mikewa tayi bayan ta ma Abba sae da safe ta fita tana Murmushi, tana da kusan 70k a account dinta, ga kuma dala dari biyu da Aliyu ya bata, now with additional 150k from her father, latest iphone is sure gobe. Washegari Nihad na ta kallo ta window har Khalil ya tafi ajiye su Amina a makaranta, Hijab ta saka har kasa ta sauko, gun Aminu ta nufa yace "Barka da Safiya Hajiya" Tace "Aminu ina son tambayarka ne don Allah" Aminu yace "Toh Allah ya sa na sani Hajiya" Tace "Yaron nan Driver yana da account number ne?" Aminu yace "Anyaa, gaskiya ban ta6a jin yace xai cire kudi ba" Ta ta6e baki tace "Okay" Juyawa tayi ta koma ciki, tun jiya take avoiding ya farooq wannan ne ma yasa ta ki zama a parlor, ta koma dakinta tana jin dawowar Khalil ta sauko kasa da sauri, hade rai tayi ganin Ya Farooq a parlor ta gaishesa tayi ficewarta ba tare da ta jira ya amsa ba, Direct wajen khalil ta nufa babu yabo babu fallasa tace "Ehm ya ma ake kiranka? Abbana yace ka bada account number" Khalil ya kalli Aminu kamar dai yana jiran Aminu ya bata amsa, a fusace tace "Malam ai ba Aminu xaka kalla ba, da kai nake ni xaka kalla" Ya kalleta yace "Ohk, bani da account" Ta masa wani kallo tace "I thought as much" sai kuma ta ja tsaki ta juya ta koma ciki, Aminu yayi kasa da murya yace "Alhaji fa ya tambayi account din naka kasan ko ihisani xai maka" Khalil ya girgiza kai yace "To ai bani da account din ne" Aminu yace "Kashh" Nihad ta daidaici lkcn fitan Abbanta ta fito parlor da sauri yana ganinta yace "Yauwa kin amso account din" Tace "Abba bashi da shi, kawai ka sa a na kawata Husnah ita ta ma san wajen gyaran don nata ma ya ta6a lalacewa kamar nawa, don haka ita xata raka mu" Yace "Okay, forward the account to me via Sms" Tace "Toh Abba nagode, Allah ya kara budi" Yace "Ameen" Daga haka ya fita parlon Mumy tayi masa Allah ya tsare, Umma na tsaye bakin kofar kitchen tana kallonsu, Bayan fitan Abba Nihad ta juya da sauri xata bar wajen Mumy tace "Zo nan me xa a gyara?" Tace "Mumy laptop dina ne yake bani matsala shine xai tura min kudin gyara" Mumy tace "Toh amma lallai sai an sa kudi account din Husnah? Me yasa baxa ki je ki gyara account dinki ba, kuma nace maki bana son alakar ku da yarinyar nan kin ki ji, wai sai na fara nakada maki duka a gidan nan xaki nutsu Nihad?" Nihad ta marairaice tace "Mumy Coursemate dita ce fa, dole muna haduwa a class ko ban kulata ba ita tana kulani kuma ita kadai tasan inda ake gyara laptop din nan tunda nata ma ya ta6a lalacewa" Farooq yace "Dauko laptop din naki da ya lalace ki kawo min" Juyawa tayi ta kallesa, Umma ta karaso parlon tace "A saboda ka fara gyaran laptop??" Mumy tace "Ta dai je ta dauko masa laptop din da ya lalace" Umma tace "Toh naga ai ba shi ya bada kudin gyaran ba da xai hau tuhumarta" sum sum Nihad ta wuce sama, cikin lkci kankani ta shirya ta dau jakar laptop dinta ta fito, Umma kadae taje tayi ma sallama Umma tace "Toh Allah ya tsare daughter" Aminu ya kalli Khalil bayan ta fita yace "Kai fa yanxu huta roro, adaidaita take hawa xuwa duk inda xa ta." Nihad bata dawo gida ranan ba sai da sabon Iphone dinta dal a kwali, babu wanda ta sanar ma ta canza waya banda Nihal da Umma, Umma na jujjuya wayar tace "Gaskiya ne er daddy, yanxu duk kawayen naki su ma irin wannan ke hannunsu kenan?" Nihad ta washe fararen hakoranta tace "Ehh wllh Umma, shi yasa nima na dage sai da na canza, ai abun kunya ce ace ni kadai ce ban canxa waya ba a cikinsu" Umma tace "Ai ko kina da gaskiya abun ki" Nihad tace "Umma kinsan me?" Umma tace "Aa sai kin fada" Nihad tace "Umma xa mu fara exams nan da kamar sati uku kuma wllh ina son in koma hostel don in dinga karatu sosai, nasan Mumy da Ya farooq xa su xuga Abba kuma baxai bari in koma ba, pls ko xaki taya ni convincing Abbana?" Umma tace "Gaskiya ya kamata ki koma hostel din don ki maida hankali kiyi karatu sosai, amma kinsan me xai faru?" Nihad tace "Aa" Umma tace "Zan ce ma Abbanku Mijin Kamila xai yi tafiya kasar waje kuma xai yi kusan wata biyu a can, tace ki je ki dinga tayata kwana idan ya so daga can sai ki dinga xuwa makaranta, ita ma Kamilan xan sa ta kira Abban naku" Nihad ta wara ido cike da farin ciki tace "Yauwa Ummana, wannan shawarar taki tayi wllh" Umma tace "Kinga kawai daga nan sai kiyi komawarki hostel har sanda xa ku gama jarabawan, babu wanda xai san baki gidan Kamila" Nihad tace "Ai kuwa Umma, don Allah gobe da safe kiyi ma Abba maganar da wuri, on Thursday ma nake son in koma ni dai" Umma tace "Toh shikenan, Allah ya kai mu goben, ai gobe Wednesday" Nihad ta fita dakin cike da farin ciki, shi yasa take son Umma, haba she will be free for a while, babu me takurata. Da safe babu wani bata lkci Umma tayi convincing Abba, yace "Toh Allah ya kai mu alhamis din" Umma tayi murmushi tace "Ameen Yallabai, sai kayi ma Maryam magana da kanka ko?" Yace "Aa kema xa ki iya yi mata ai, menene a ciki" Umma tace "Aa gwara dai kai kayi mata, kace mata Kamila ce ta roki alfarman Nihad ta koma wajenta na kwana biyu mijinta xai yi tafiya" Abba yace "Ohk, amma suna da driver ne a can da xai dinga dropping dinta school?" Umma tace "Anya, da yake kasan shi yake ajiye kamilan duk inda xata je" Abba yace "Toh duk safiya sai Ibrahim ya dinga xuwa can yana daukarta ya ajiye ta makaranta, when ever her lectures is terminating sai ta gaya masa yaje ya dauketa ya maida ta gida" Umma tace "Hakan ma yayi kam" kafin Abba ya fita aiki ya shiga bangaren Mumy, nan ya sanar mata abinda Umma tace masa, Mumy tayi shiru alamar ta ma rasa abinda xata ce, Abba yace "Sai ki gaya ma Nihad din ta fara shiri" Mumy ta sauke boyayyen ajiyar xuciya tace "Alhaji idan Nihad taje gidan Kamila babu me kwaba mata, kasan ta da rawan kai fa, tana nan gida ma ya aka karke balle bata gida" Abba yace "So what are u insinuating?" Mumy ta girgiza masa kai kawai, Abba yace "Kar taje ta taya er uwartata xama kenan?" Mumy tace "Ko daya ba haka nake nufi ba" Abba yace "Toh Maa sha Allah, gobe alhamis ta shirya ta koma can gidan" Daga haka ya fice daga parlon, har ran Mumy bata son xuwan Nihad gidan Kamila amma to ya xata yi? Hakan ya sa ta tunani iri iri.




Barka da sallah fams, Allah Ubangiji ya maimaita mana


07087865788✍🏻


πŸ’–πŸ’– *NIHAAD*πŸ’–πŸ’–




By _Khaleesat Haiydar_✍🏻




Har daki Umma ta tadda Nihad tace "Toh Abbanki ya amince sai ki fara hada kayanki" Cike da farin ciki Nihad ta mike ta rungumeta tace "Nagode sosai Umma" Umma tace "Sai dai fa Abbanki yace driver xai dinga xuwa duk safiya yana daukarki ya kai ki makarantar sannan idan kun gama lectures ya maida ki gida" Nihad ta zaro ido tace "Toh Umma ya xan yi?" Umma tace "To na dai amsa ma Abbanki, amma ke yanxu sai ki samu Drivern kice masa ba sai ya je ba, xaki dinga tafiya da motar Kamila, should Incase Abbanki xai masa magana...." Nihad tace "Toh shkkn Umma" Umma tace "Xaki makarantar yau?" Nihad tace "Ehh ina da lectures karfe sha biyu" Umma tace "Da sauran lokaci ai, sai ki fara harhada kayanki against tomorrow..." Daga haka Umma ta juya ta fita dakin, Murna a wajen Nihad ba a cewa komai, she is going to have enough freedom yanxu, wanka ta shiga bandaki tayi sannan ta fito ta shirya, bayan ta shirya ta fita xuwa bangaren Mumy, Mumy na gyaran bedroom dinta Nihad ta jingina da kofar dakin da damuwa tace "Mumy kin ji abinda Abba yace?" Mumy ta kalleta tace "Na me kenan?" Nihad ta marairaice tace "Mumy ni ba son zaman gidan Aunty Kamila nake ba, it's so boring there, ni kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login