Showing 102001 words to 105000 words out of 148918 words

Chapter 35 - Nihaad Book 1 Hausa Novel Complete

chocolate masu uban yawa a jakar, kai....a ina ya samu kudin siyan wannan uban chocolate din, ko da yake kudin babanta ne, wato saboda samun waje har da su siyan chocolate, wani hoto ta gani ta dauka tana kallon matar da ke jikin hoton warce baxata wuce shekaru 54 ba, kana ganinta kaga halfcast, keenly Nihad ke kallon hoton tana ji a jikinta kamar ta ta6a ganin wannan matar, amma a ina?? Duk yanda ta so tunawa ta kasa, as in, she k6s sure ta ta6a ganin hotonta but where?? Bude kofar dakin aka yi ta mike a rikice, da sauri ya nufota ya warce hoton daga hannunta ya hadeta da bango yana mata wani mugun kallo lkci daya kamanninsa suka sauya, Sosai ta tsorata jikinta na rawa tace "A bude fa naga jakar xan...." Turata yayi har sai da ta fadi kasa rigijib, ya dau jakar gaba daya ya fice daga dakin. Da safe karfe tara saura khalil na zaune parlor Nihal ta fito, ta tsaya jikin kujera ta gaishesa ya amsa yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah, Nihad bata tashi ba har yanxu?" Duk da tun jiya da daddare rabonsa da dakin bayan ya fita amma haka yace "Probably" Tace "Ohk, ni xan tafi" Yace "Ina za ki tafi?" Ta sunkuyar da kanta tace "Umma ta aikeni gidan wata frnd dinta in amsar mata sako, so karfe tara matar ke fita aiki, shine tace in je kafin tara" Khalil yace "But baki yi breakfast ba ai" Tace "Na tashi da azumi yau" Shiru yayi yana kallonta tace "Idan ta tashi kace mata naje amsar ma Umma sako" Yace "Toh mu je in ajiye ki" Da sauri tace "Aa ba fa nisa, kuma in sha Allah xan dawo anjima" Yace "Are you sure?" Tace "Sure" Yace "Toh Allah ya tsare" Tace "Ameen" Daga haka ta nufi kofa ta fita. Goma saura Khalil ya tashi ya shiga dakinsa don wanka yake son yi kuma yaga bata da niyyar fitowa, kwance ya sameta a kasa, ya tsaya bakin kofa yana kallonta, ta mike xaune cikin rawar tace "Ba shkkn ba hankalinka ya kwanta kafana na min ciwo yanzu" Kallon kafar yayi, kafin ya karasa kusa da ita ya durkusa ya daga kafar, ta sakar masa kuka ta janye, hade rai yayi yana kallonta sai kuma ya sake jawo kafar, ihu ta kwala tace "Wallahi ciwo yake min" Targade ya ga tayi a kafar, ya mike ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, da kyar ta iya daurewa ta shiga bandaki da asuba ta wanke bakinta da mouth wash ta dauro alwala ta fito tayi sallah, kamar kar ta ɗan motsa xuwa bandakin shine kafar yayi mata tsami kafin gari ya waye, dawowa dakin yayi ta daga kai tana kallonsa, ya karaso gabanta ya durkusa ya bude man zafin hannunsa, ita dai kallonsa kawai take, bayan ya debi man zafin ya kamo kafarta, zaro ido tayi tana kokarin janye hannunsa a kafarta ya daure fuska yace "Kar ki sake ta6a ni Malama" yana gama fadin haka ya fara ja mata kafar yana kokarin gyara mata targaden, ai bata san sanda ta yunkuro ta rirrikesa ba tana kukan azaba tace "Nashiga uku Abba" Bai sarara mata ba har sai da ya tabbatar kafar ta dawo dai dai, kuka kawai take ta kankamesa duk ta hada zufar wahala, bayan ya sakar mata kafa shi ma ta sakesa tana komawa baya, kallonta kawai yake, ta turo baki tana share idonta, yace "Sallan asuban ma yafe maki aka yi sbda kinyi targade ko" Ta hade rai tana kallonsa tace "Ai ni ba kafura bace" Bai ce mata komai ba ya mike ya nufi kofa, da sauri tace "Ka kira min Nihal plss" yace "Warce kika kora ko wacce?" daga haka ya fita dakin, a hankali ta lallaba ta mike ta hau saman gadon ta kwanta tayi lamo a saman pillow, wato tafiya Nihal tayi upon all her pleas. Kafin azahar Nihad taji tana iya taka kafar, a hankali take dingishin ta fito daga dakin, ta shiga nata dakin, kallon katon ledan dake saman gado ta dinga yi, kafin ta karasa ta bude ledan, abaya ta gani masu ɗan karan tsada sun kusa kala goma, da mamaki ta dinga kallonsu tana warwaresu, sannan ga undies da cream din shafawa da turarurruka duk a cikin katon ledan, da sauri ta fito parlor tana kallonsa tace "A ina ka samu kudi ka siya min abayan nan?" Ya kalleta a takaice yace "Kudin babanki mana" Nihad tace "To amma wa ya zabo abayan?" Yace "Ni ɗan aike ne, kasuwa kawai aka aike ni naje na amso" Ta kyabe baki tace "I thought as much" Daga haka ta juya ya bi ta da kallo har ta shiga daki, wani Murmushi yayi ya maida idonsa kan tv da yake kallo. Bayan ta yi wanka ta shirya cikin daya daga abayan, sosai yayi mata kyau ya amshi fatarta, ba laifi haskenta ya fara dawowa amma ramar na nan, ta fito parlor, kallo daya yayi mata ya dauke idonsa, ta wuce kitchen sauran abincin da Nihal ta dafa daren jiya ta kara dumamawa ta xuba ta koma daki ta ci, har kusan la'asar Nihad na ta xuba ido taga ko Umma xata zo yau din ko sai gobe, amma bata zo ba, wajen karfe biyar ya bude kofar dakinta yace "Ki sameni a mota" Da ido ta bi sa har ya bar wajen, sai kuma ta mike ta dau mayafinta ta bi bayansa, duk da yana cikin motar ta ki shiga, she can't take that risk anymore, tana kallonsa da kyau tace "Ina za mu je?" Yace "Gidanku" Ta ɗan yi jim, sai kuma dai ta shiga bayan motar ta kulle, suna barin gida taga sun dau hanyar gida, ta ma rasa ko farin ciki xata yi ko akasin hka, the only good thing of going to that house is that xata ga Umma bayan nan ita bata marmarin ma zuwa gidan.... Sai da suka kusa yace "Ki bude kunnuwanki ki saurareni da kyau, zan kai ki gida ba don komai ba sai don ki gaida mahaifiyarki da bata da lafiya, idan Abba na nan shi ma ki gaishesa, bayan haka xa mu fito daga gidan..." Da mamaki Nihad tace "Kana nufin sai in shiga har gidanmu in fito ban je bangaren Umma na gaidata ba??" Dai dai nan suka shigo layin, yana kallonta da kyau ta madubi yace "Ba don ki je bangarenta ki gaidata na kawoki gidan ba, a duk inda kika hadu da ita a nan xaki gaisheta babu xancen xuwa ɓangarenta, idan kuwa kika ce baxa ki bi umarnina ba, Billah na maki alƙawarin muna fitowa daga gidan xan maida ke garinmu da zama na har abada" Shiru Nihad tayi bata ce komai ba, bayan yayi parking yace "Kin ji ko baki ji ba?" Ta hade rai tace "Na ji" Bude motar yayi ya sauka ita ma ta sauka fuska daure, har sannan dingishi take, Aminu kamar xai goya Khalil tsabar farin cikin ganinsa, Nihad ta kara tsuke fuska ko kallonsa bata yi ba ta shige cikin gidan, Aminu yayi kasa da murya yace "Ciwo ta ji a kafar take dingishi?" Khalil yace "Zan fito yanxun nan" Daga haka ya bi bayan Nihad, Umma ta fito daga bangarenta kenan ganin Nihad ta hau tafa hannu tana cewa "Oyoyo oyoyo" Nihad ta ɗan saci kallon Khalil dake bayanta yana kallonta, ta sunkuyar da kai a hankali tace "Umma ina yini" Umma tace "Karaso mu shiga ciki daughter" Nihad tayi karfin halin cewa "Xan shiga wajen Mumy ne tukunna" Umma ta saki baki tana kallonta, tuni khalil yayi part din Mumy, Nihad ta bi bayansa kamar xata yi kuka, haka Umma ta bi su da kallon mamaki, kai ko makaranta Nihad ta dawo ba wani lallai taje bangaren Mumy ta gaidata ba, Umma kuwa dama kafin ta fita sai ta shiga ta gaya mata ga inda xata, haka kuma idan ta dawo, abinda Nihad tayi yanxu sai yayi mugun daure ma Umma kai. Nihad ta kasa hada ido da Mahaifiyarta bayan sun shiga parlon, Mumy ta amsa gaisuwar khalil da fara'a, Yace "Ya karfin jikin?" Tace "Alhamdulillah jiki da sauki" Nihad na wasa da veil dinta tace "Mumy ya jikin?" Mumy dake kallonta tace "Alhmdlh" cousin din Mumy ce ta fito daga bedroom suka gaisa da khalil cikin mutuntawa, Nihad dai sae kallonta take, ganin ta juya ta koma daki ba tare da ta bi ta kanta ba, Nihad ta mike a sanyaye ta bi bayanta, gaisheta tayi, maimakon ta amsa sai ta hau ta da fada, tace "Ban kara tabbatar da cewa ke mahaukaciya bace shashasha sai yanxu, ace uwarki ba lafiya tun da kika bar gidan nan amma kika rasa inda xaki samu wayar kiranta? nan kuwa a duk sanda matar nan Umma ta shigo sai tace ai kunyi waya, anya kina son gamawa da duniya lafiya kuwa Nihad? Kullum bawan Allahn nan sae ya shigo gidan nan gaida uwarki amma sbda ke ba yar halaq bace baki ta6a cewa xaki biyosa ki duba jikinta ba, to duniya ce dai wanda bai zo ba ma jiransa take, idan kuma Umma ce tayi nakudarki ta haifeki xa mu ji" Nihad ta zauna hawaye na sauka idonta tace "Aunty ni tsoro nake ji shi yasa ban kirata ba, kuma wallahi bai ta6a ce min xai zo nan ba ban biyosa ba" a fusace Aunty Zulai tace "Sai yace maki xai zo?? Shashasha kawai kin bi kin ja mana abun kunya a duniya wanda har yanzu kukan wannan mugun abun naki muke, wallahi sai nan gaba xaki yi kukan gaske da hawayenki a kan wannan video din Nihad, nan gaba xaki san illar da kika ma kanki a duniya a kan video din nan, kuma yau da ace wannan mijin naki iyayensa da danginsa yan boko ne ko a cikin gari suke wllh baxa su ta6a bari ya aureki ba ko da kuwa shi ya ganki yace yana so balle wannan manna masa ke kawai aka yi sbda babanki ya yaba da hankalinsa, amma da ace ɗan birni ne wllh gori wajen danginsa da yan uwa ma kawai ya isheki ki hadiye xuciya ki mutu wataran, kina ganin kamar abu ya lafa ai shkkn an manta, yarinya sai nan gaba xaki gane abinda nake gaya maki ba yanzu ba, don haka in zaki rungumi mijinki ki bisa ki masa biyayya ki lallaba aurenki, to gatanki, idan kuwa kin ce ba haka ba kika kuskura kika bari aurenki da bawan Allahn nan ya samu matsala to idan ba kauyen ubanki xai sake komawa ya samo maki wani mijin ba ina me tabbatar maki babu wanda xai aureki don ma in gaya maki ki ji da kyau" kuka kawai Nihad take tana kallonta, Aunty Zulai tace "Shikenan ni abinda xan gaya maki kenan, tashi ki bani waje" Nihad ta mike tana goge hawayen da ya ki tsaya mata ta fito parlor kanta a kasa, zaunawa tayi saman Carpet ta dago kai a hankali ta kalli Mumy taga kallonta take, cikin sanyin murya tace "Mumy ina su Sudais" Mumy tace "Sun tafi makaranta" Nihad bata kuma cewa komai ba, bayan few minutes Mumy tace "Kin ga wancan bawan Allahn dake zaune?" Nihad ta daga kai ta kalli Khalil da Mumy ke nuna mata bata dai ce komai ba, Mumy tace "In har kina son gamawa da ni lafiya to ki zauna lafiya tare da shi, idan kuwa kince ba haka ba, ba baki na maki ba amma baxa ki ta6a ganin daidaituwar lamarinka ba, don haka kika kuskura kika kashe auren nan naki sae dai ki nemi warce ta haifeki ba ni ba" Nihad ta fashe da kuka sosai tana kallon Mumy, shi dai Khalil bai iya ya daga kai ya kallesu ba, Mumy ta kallesa tace "Ku gaida gida Ibrahim.... nagode sosai, xan shiga ciki" Yana kallonta cikin sanyin murya yace "Allah ya kara lafiya" Ta amsa da Ameen ta mike ta shiga dakinta, kuka kawai Nihad take kamar ranta xai fita a parlon, bayan few seconds Khalil ya mike ya fita daga parlon, mikewa ita ma tayi tana kuka ta bi bayansa.




*Nihad* is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah



And u show ur evidence via👇🏻


07087865788




Assalamu alaikum er uwa, kina neman organic Supplement irin masu gyaran jiki ciki da waje? Ko kuma mai fitar Maki da duk wani infection komai nacinsa? Sannan mai maido Maki martabar fatarki? Ko kina fama da dry HQ? Ko hips ne matsalarki da boobs? To kwantar da hankalinki *GHT Organic supplement care gat ur back*


Domin karin bayani ki tuntubi wannan number 👇🏻

+2347057607751✍🏻




*Masu forwarding min novels daga nayi posting to other groups su sani hakkina bazai ta6a barinsu ba don good 4 hours nake using wajen ganin na hada just 1 page, babu ruwana da wai mutum daya ya siya a group sai ya tura ma saura tunda ni ba er iska bace ban yarda da wnn iskancin ba, duk me yin hakan taje ita da Allah, kuma Allah zai saka min, dama ɗ'an abinda mutum ke rainawa yake maida shi ba komai ba bai san shine doom dinsa ba a rayuwa, wani ba wai bai da 500 din biya ba, kawai kyashi ne baxai barsa ba amma ya iya karatu ya ji dadi, sannan masu min posting a facebook suma su da ALLAH!!!* Na gaji da zuba maku ido kuma haka.




Suna fitowa parlor Nihad na kallon khalil cikin kuka tace "Don Allah ni ka barni in je in gaida Umma" Juyowa yayi yana kallonta yace "Akwai wata Umma bayan warce kike gaida da muka shigo daxu?" Muryarta na rawa tace "Toh kawai a parlor xan gaisheta?" Yace "Eh" Kuka kawai take tana kallonsa ta wuce sa kamar xata tashi sama ta nufi kofar fita parlon, bin bayanta yayi ya sameta jikin mota tana kuka kamar ranta xai fita, ya zaga driver seat ya bude ya shiga, bude bayan motar tayi ta shiga don ita har yanzu Drivern gidansu ne shi, Aminu ya marairaice bayan Khalil ya fito da mota waje yace "Ina ta rokon Saminu ya jira min gate in kawo maka ziyara amma ya ki..." Khalil na kallonsa yace "Wataran ma baxa kayi gadin ba gaba daya, sannan matsayinka xai dawo dai dai da na kowa a duniya" Aminu ya daga hannu biyu sama yace "Allah Ubangiji ya amsa bakinka, Allah ya dubemu yanda ya dubeka lkci daya, wannan gagarumin ci gaban da ka samu Allah ya sa mu a danshinka, wayyo wa yaga Aminu ya daina gadi, duk basur ya cinye ni sbda zama kan benchi daga safe har dare, na ma ji Alhaji yace xa a dubo sabon driver tunda kai yanxu ai ba batun tuki kuma" Murmushi kawai khalil yayi ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu daya ya mika masa yace "Ga wannan ka sha kankana" Aminu ya karba hannu bibbiyu yana cewa "Allah ya taimakeka oga" Wani shegen kallo Nihad ke ma daga Khalil din har Aminu tana jin kamar ta hadiye zuciya don takaici, nan ta kara jin wani sabon tsanar Khalil ya dirar mata, wato fafa yake yi sbda Abba ya aura masa ita, ji yake babu ya shi a duniya, Bayan sun bar layin tana kallonsa ta madubi tace "Kai yanzu kawai jin kanka kake saboda Abbana ya daukeni ya aura maka ko? Gani kake ka fi kowa sa'a a duniya tunda yanxu kudin da Abbana ke baka ya ninku linkin ba linkin har da su kyautar dubu daya, shkkn xaka dinga amfani da ni kana cin kudin Abbana" Khalil yayi wani murmushi bai tanka ta ba, ta murguda baki tace "Ai shi dama talaka bai iya samun waje ba, nasan yanxu alfahari kake yau gani matarka ko?" Yace "Ohk" Ta kara murguda baki bata kuma ce masa komai ba har suka isa gida, sauka tayi daga motar bayan ya bude gate tayi shigewarta ciki kamar xata tashi ciki, yayi wani murmushi kawai ya motar ya shigar da shi compound din. Bayan Nihad ta idar da magrib ta fito parlor ta samesa kwance saman dogon kujera yana waya, ganin bai lura da fitowarta ba duka a hankali ta rarrafa har bayan kujeran ta kasa kunne tana sauraron wayar da yake yi, A hankali taji yace "Nan da wata daya in sha Allah xan dawo, idan kuma na dawo baxan sake fita ba sai bayan aurenmu" Yana fadin haka babu sunan da ya fado ran Nihad sai Nadeeyah don har ta haddace sunan nata a xuciyarta, ta ɗan kyabe baki tana tsugunne bayan kujeran tana kara kasa kunne, Taji yace "Aa, akwai dalilin da ya sa na dade wannan karan Nadeeyah, ba wai da son raina bane, amma in sha Allah na kusa gama abinda nake yi, ni kaina na gaji da USA haka" Buda baki Nihad tayi hangangan jin sunan kasar da ya kira, Tunda aka haifeta bata ta6a ganin me lafta karya kamar wannan mutumin ba, wato USA?? Mutumin da ko ruwa ta kasa sha a garinsu balle ta ci abinci shine yake karyan yana USA, ya ma san full meaning din USA din kuwa?? Taji yayi dariya ya mike zaune yace "Wai da gaske??" Magana yake amma bin parlon kawai yake da idanuwansa don banda kamshin Nihad babu abinda yake ji a parlon, amma kuma bai ga alamarta ba, don haka ya koma ya kwanta a hankali yace "Ke ce farko kece karshe Nadeeyah, in sha Allah baxan hada ki da kowace mace ba, don kin min hallacin da baxan manta ba, in dai kuma ba baturiya kike son in auro mu dawo Naija tare in hada ku gida daya ku zauna ba, kinga ai nasan baxa kiyi kishiya da ita ba" bayan few seconds yayi murmushi yace "Ya na ji kin yi shiru?" Mikewa Nihad tayi tana tafe hannu tace "Ni wallahi ban ta6a ganin inda babba yake karya ba sai kai..." tuni Khalil ya katse wayar, ya mike tsaye yana kallonta, da mamaki Nihad tace "Kasan ma'anar USA kuwa? Kasan ina ne Usa? Me yasa baka tsoron yin karya a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login