Showing 81001 words to 84000 words out of 148918 words

Chapter 28 - Nihaad Book 1 Hausa Novel Complete

ai ni kashe ni kawai xa ayi a gida wallahi" Naf ta tabe baki tace "Koma waye da kansa zai tona ma kansa asiri nan ba da dadewa ba" Nihad ta share hawayen da ya ki tsaya mata tace "Pls Naf try calling Aliyu ki ga ko zai daga" Naf tace "Toh Allah ya sa ya daga, ko kuma ma dai Allah ya sa ya shiga" Contacts dinta ta shiga tayi dialing number Aliyu, ai ko ya fara ringing, gaban Nihad ya dinga faduwa tana kallon wayar, su kansu gaba daya kallon wayar suke, sai gashi kuwa ya daga, sai da Nihad taji xuciyarta ya kusa shigewa cikinta, Naf tace "Hello Aliyu what's up?" Daga daya bangaren cikin cool voice yace "Fine Nafisah, how are you doing" Tace "Cool, ya garin" Yayi shiru, tace "Are u there?" Yayi kasa da murya yace "U saw how ur frnd played with my heart right?" Nihad ta kauda kanta hawaye sai zarya yake a fuskarta, Naf tace "Calm down Aliyu, duk wannan abun set up ne ba wani abu ba, ka fi kowa sanin halin Nihad, sannan mu da muke tare da ita always xa mu shaideta, wllh wllh Nihad bata tsayawa a cikinmu daga ita singlet balle undies, wannan lamarin da rikitarwa yake, wa ya sani ko anyi hakan ne don a raba ku tunda anji xaka turo gidansu" Aliyu yace "But i have warned her severally Nafisah, na sha ja mata kunne duk yawace yawacen zuwa party ta daina, but unfortunately bata daina ba, and ga abinda ya faru daga karshe" Naf tace "Kai wai wa yace maka a wajen party aka yi mata haka? Ko a gida baxa ayi iya yi ma mutum haka ba sai wajen party kawai? Kai dai kawai ka kyale makiyi Ali" Aliyu yace "I am so heartbroken Nafisah" Naf tace "So is she also" Yace "Tana ina yanxu?" Naf ta kalli Nihad sai kuma ta ɗan yi murmushi tace "Mun zo gidansu ne daxu ganin halin da take ciki shine nace bari dai kawai in kiraka" Yayi shiru, tace "In kai mata wayar pls?" Nan ma dai shirun yayi, tace "Don Allah kar kace A'a, ko sai kaji ta mutu xaka fara da ka sani an kai mata wayar? Wallahi she is seriously sick" Yace "Kai mata" tace "Yauwa my guy" kallon Nihad tayi tana Murmushi, ita dai Nihad ta sunkuyar da kanta kawai, Naf ta kamo hannunta ta saka mata wayar a ciki, a hankali ta kai kunne tayi sallama. Aliyu yace "Now u get the reason why nake rabaki xuwa party?" Bata iya ta ce masa komai ba ta a goge idonta, yayi kasa da murya yace "Why Nihad, why?" Cikin rawan murya tace "I don't know how everything happened, kayi hakuri don girman Allah" yace "In yi hakuri Nihad? Ta yaya iyayena xa su amince da aurenmu bayan duk sisters dina babu warce bata ga wannan video din naki ba, hatta mum dita ta gani, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Nihad dai bata ce komai ba, Yace "How will we mend this damage?" Nihad tace "Abbana yace min wai ya min aure" Aliyu yace "Ban gane yayi maki aure ba, kina nufin aure Abba xai maki?" Cikin kuka tace "Ehh har ya min" Aliyu yace "Stop it Nihad, yaushe yace maki haka" A raunane Nihad ta sanar masa yanzu ita da khalil suke zama gida daya, kuma Abba ya sanar mata wai yayi mata aure da shi, lkci daya ya birkice mata yace "Baby yanxu kina nufin aure aka maki, aure da drivern nan na gidanku?" Nihad ta girgiza kai da sauri tace "Ni ba a min aure da shi ba, kawai Abba ne ke fadan hakan, ni ban yarda an min aure da shi ba" Aliyu yace "Nooo, it can never be, not when i am alive, hakan baxai ta6a yiwuwa ba, na yi isolating kaina from everything na kwana biyu ne but nasan baxan ta6a iya rabuwa dake ko da nayi attempting din yin hakan ba, i know i will come back to you, kuma ko iyayena bana jin xa su hanani in aureki don sun san ina son ki, ko da nude video dinki ne yayi yawo i stil love u Nihad, and i will still marry u" Nihad dai ta yi kasa da kanta ta kasa cewa komai yace "Ki kulan min da kanki Nihad, do not break my heart for the second time pls, sannan ta ina xan dinga samunki ko 2 days ago i tried ur number naji switch off" a hankali tace "Xan kiraka da sabon line dina idan na koma gida" Yace "I will be expecting pls" Sallama suka yi, Naf ta amshi Wayarta tace "Alhamdulillah" Nihad ta ɗan yi murmushi, Husnah tace "Gaskiya Aliyu ya san kaddara, yanxu ke kuma sai ki san duk yanda xa kiyi ku raba jaha da wancan driver din, koma yaya xa ayi kawai ya sake ki tunda Aliyu is still willing to marry u" Nihad ta kalleta tace "Ya sakeni?? To da aurena yayi da xai sakeni? Ai kawai xama muke gida daya bisa umarnin Abba, but i am for Aliyu alone" Zully tace "Atoh, kunsan akwai wani aure da xaka ji sa kamar wasan yara, to irin auren nan naku da drivern kenan, ko ni bana kallonsa a matsayin mijin Nihad wallahi, kilan kawai Abba is playing u, amma ta yaya ma xai ce ya maki aure da dreba" Nihad tace "Toh kun ga lkci na wucewa mu tafi pls" Naf tace "Bari in kara watsa ruwa" Zully ta mike tace "Ina zuwa in kwaso kayana" daga haka ta fita daga parlon, Husnah ta kalli Nihad tayi kasa da murya tace "In baki shawara? Toh wallahi kar ki yarda su wani bi ki, gwara kiyi tafiyarki ke kadai daga baya ni kadai sai in biyoki gidan, idan ba haka ba akwai matsala" Nihad tace "Matsalar me fa?" Husnah tace "Toh shkkn ki tsaya tambayar ta me, naga dai ni kika fara sani kafin su, kuma ta dalilina kika san su, don haka kawai yanxu kice masu gidanku xa ki daga can ne xaki wuce gida kina komawa gida kuma xaki kira kice mu taho gaba daya" Nihad tace "Toh shkkn" Mikewa Husnah tayi ta fita daga dakin. Khalil ya fito compound jin ana Knocking gate, yana bude gate din ya ga Farooq a tsaye, welcoming dinsa Khalil yayi with smile all over his face, Khalil ya rufe gidan suka koma can parlor tare, Farooq na cewa "Gobe xan koma aiki shine nace bari in shigo yau dai" khalil yace "Allah sarki" Suna shiga parlon Farooq na bin ko ina da kallo yace "Ina take?" Khalil bai basa amsa ba kawai ya tafi kitchen don ya dauko masa ruwa, Farooq ya dau throw pillow da ke kan kujeran da yake kokarin zama sai ya ga Iphone, duk tunaninsa na Nihad ne duk da a gabansa Abba ya kwace Iphone din nata, Farooq ya zauna yana jujjuya wayar amma sai ya ga ba na Nihad bane, dai dai nan khalil ya fito daga kitchen with bottle water and glass cup, still yayi yana kallon Farooq.....




Nihaad is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah

And u show ur evidence of payment via 👇🏻

07087865788


Farooq ya daga kai ya kallesa har sannan kuma wayar na hannunsa yana jujjuyawa, karasowa parlon Khalil yayi ya ajiye ruwa da glass din hannunsa, ya ki yarda su hada ido da Farooq yace "Oh kamar fa na makotanmu ne da suka shigo daxu, babu tantama wayar daya daga cikinsu ne, ban ma kula ba sai yanxu...." Farooq dake ta kallonsa ko kiftawa babu kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Now tell me who you are Khalil!!!" Khalil ya ɗan yi jim, can yace "Ban fahimce ka ba" duk wannan abun ya ki yarda su hada ido da Farooq, mikewa Farooq yayi ya dafa sa yace "Tell me what ur mission is, what is ur intention of coming to stay with us? ka gaya min kai wanene, menene manufar xuwanka gidanmu" Sai a sannan khalil ya daga kai ya kallesa amma bai ce komai ba, Farooq yace "From day one, i know u are not who u claim u are, u lied about ur personality to us, you have a mission definitely, be it revenge, spy, Dss.... And what have u!" Khalil ya girgiza kai a hankali yace "I have no mission Farooq, and my intentions of staying with u people is pure, aiki kawai ya kai ni gidanku, baya ga shi kuma babu wani abinda ya kai ni gidanku...." Farooq na kallonsa keenly yace "I will like to know u more" Khalil ya koma ya zauna, kamar baxai ce komai ba sai kuma ya sauke ajiyar xuciya yace "Duk abinda na gaya maka a kaina a baya hakan yake, i am a nobody like i said earlier, i was just opportune to go to school, i was opportune to be a literate, nayi diploma a fce nan kano wanda har yau ban samu aiki ba, bayan wannan komai game da ni na gaya maka a baya, u can even call Habib and confirm" Farooq yace "But meyasa kace iyakarka secondary?" Khalil yace "Ina tsoron kar a ki bani aiki a gidan ne" Farooq dai kallonsa kawai yake as if forcing himself to believe him, Can yace "Wani course din kayi?" Ba tare da Khalil ya kallesa ba yace "Business Admin" Farooq ya koma ya zauna kamar me naxari, ta gefen ido Khalil ke kallonsa hoping he is fully convinced, Farooq na daga kai Khalil yayi saurin dauke idonsa daga kansa, Farooq ya sauke wani ajiyar xuciya yace "Ohk then, in sha Allah xa mu yi magana da Abba, nasan xai yi iya kokarin ganin ya samar maka aiki dai dai da qualifications dinka" Khalil yace "Toh nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Farooq yace "Ameen" Bayan few minutes Farooq yace "Ina Nihad din?" A hankali Khalil yace "Ban san inda ta tafi ba" Da wani expression Farooq yace "Ban gane baka san inda ta tafi ba, isn't she under ur control now?" Khalil yace "Nayi kokarin hanata fita amma ta ki" Farooq yace "What? Sai kai kuma ka saka mata ido har ta fita?" Khalil dai yayi shiru. Nihad ce ta sauka bakin gate ita da Husnah da tayi ma kawayensu karyan xata je park ta amso sako, nan kuma ta gaya ma Nihad inda xata jira ta su hadu sannan su taho gidan gaba daya, Sosai gaban Nihad ya fadi ganin motar ya Farooq a waje, Husnah ta zaro ido tace "Toh yanxu ya xa mu yi kenan?" Nihad ta hade rai tace "Toh ba daga makaranta nake ba, shiga kawai za mu yi, ai ba yawo na tafi ba" Husnah tace "Aa, kinsan yayan nan naki ba saiti garesa ba haka kawai inje ya ritsa da ni" Nihad tace "To me xai min? Kawai mu shiga idan ya so sai ki zaga bayan gidan ki nemi waje ki zauna, idan ya tafi xan fito in gaya maki sai ki shigo" Husnah tace "Toh gwara haka dai" A tare suka shiga gidan Nihad ta kulle gate, duk da yanda gabanta ke faduwa hakan bai hanata dakewa ba ta nufi cikin gidan kamar wata boss, Husnah ma dai duk a tsorace take, tayi sauri ta zaga bayan gidan ta nemi waje ta zauna, a hankali Nihad ta murda kofar parlon ta shiga ciki da sallama, ta kara kicin kicin da fuska ta karasa cikin parlon tana kallon yaya Farooq da ya bi ta da ido, ta ɗan durkusa tace "Yaya ina yini" Mikewa yayi, yayi ball da ita cikin xafin nama, yace "Daga gidan uban wa kike?" Ta fashe da kuka ta mike xata gudu ya fincikota, jikinta na rawa tace "Yaya wallahi makaranta na tafi ba ko ina ba, ka kira makarantar ma ka tambaya" Duk a gigice take don a wajen duka xa a iya ba Farooq A1, Ya kai mata wani wawan mari yace "Uban wa ya baki izinin tafiya makaranta?" Ta rushe da kuka jiki na rawa tace "Wallahi na gaya ma Umma kafin in fita, ita tace in tafi, ka kirata ka tambayeta" Hauri ya kai mata yace "Ke da Umma ce a gidan nan? Ko Umma ke da iko dake yanxu?" hankali tashe tace "Don Allah kayi hakuri yaya baxan kara ba wallahi, kaji har na rantse maka" Shi dai khalil na xaune bai ce komai ba sai kallonsu yake, Har baya Husnah ke jiyo muryar Nihad tana ihun neman agaji, ba shiri ta mike ta nufi gate da gudu tun kan Nihad tace tare su ke, da hannu farooq ya dinga makan Nihad, mari kuwa yayi mata har sau uku, kuka take iya karfinta tana basa hakuri tana cewa baxata kara fita ba, daga karshe yayi ball da ita ta mike tsaye da gudu ta shige dakinta ta sa makulli tana rusa kuka, Farooq yace "Gobe ko nan da gate ki fita in samu labari ki ga yanda xan faffasa maki jiki da belt, munafuka kawai" Ko minti uku bai kara a gidan ba yayi ma Khalil sallama, khalil ya rakasa har mota, farooq na kallonsa da kyau yace "Kar ka kuskura ka raga mata ko na second daya idan tace xata dinga kawo maka raini" Khalil ya ɗan yi murmushi kawai, Farooq yayi masa sallama ya ja motarsa ya bar layin, juyawa khalil yayi ya koma cikin gidan, ya zauna saman kujera ya dau Iphone dinsa hade da sauke ajiyar zuciya, tashi yayi ya tafi daki ya ajiye wayar, Nihad na jin ya bude kofar dakinsa ta fito da sauri, parlor ta tafi ta tabbatar da gaske yaya farooq ya tafi, sai da ta kara duba takalmansa nan ma taga babu alamar dai ya tafi, share hawayenta tayi ta nufi dakin nasa ta bude hade da turawa da karfi, tana kallonsa cike da rashin mutunci da tsiwa tace "Toh da ka kirasa ka gaya masa sai aka yi yaya? Nace sai me da ka kirasa? Mutuwa ka ga nayi bayan muguntan da yayi min? Kuma ka zata xan fasa fita in tafi makarantana ne ko in tafi duk inda nake so? To wallahi karya kake yaro don ko gobe ma ba a haifi wanda xai hanani xuwa makaranta ba kaji in gaya maka, Kuma da kai da ka kirasa da shi da dokeni Allah ya isa ban yafe maku ba...." Wani tsaki ta ja tana hararansa cike da tsana, ya girgiza kai yace "Akwai lkcn da matsayin tsayawa bakin kofar dakina ma baxa ki samu ba balle ki gwada min halinki na rashin tarbiya... bari kiji ba bakin kofar dakina ba har bangarena ma sai ya haramta gare ki wataran wallahi...." Sai kuma ya mike ya nufeta, sosai gabanta ke faduwa ganin yanda ya daure fuska amma ta dake ta tsaya bakin kofar, ya tsaya dab da ita yace "Kinsan me yasa baxan ke kulaki ba idan kina nuna rashin tarbiyar ki? Saboda ke din ban dauke ki a bakin komai ba, ban dauke ki mace ba, ba kuma kallon mace nake maki ba, kallon yar titi kuma er bariki nake maki, na dai girmama mahaifinki na amshi tayinki da yayi min don shi din mutum ne me daraja da kima a idona, banda haka ko da duk arxikin duniya aka hadani da ke wallahi wallahi baxan aureki ba don ni ba ajinki bane ta ko ina na fi karfin ki...." Nihad ta zaro ido hade da bude baki tana kallonsa, sai kuma ta cakumo kwalarsa cike da tsiwa tace "Ni kake ce ma yar titi kuma er bariki??" Shaketa yayi ya hadeta da kofa ba shiri ta sakesa gabanta na mugun faduwa, ya dinga kallonta fiercely yace "ina me baki shawara da kakkausar murya, Kar ki sake gigin kai hannunki jikina, idan ko kika sake yin wannan kuskuren to xaki sha mamakin abinda xan maki a gidan nan" Yana gama fadin haka ya turata waje ya kulle kofarsa, kiris ya rage ta fadi, tana huci bayan tayi regaining balance dinta tace "Kai din banza zaka bani shawara da kakkausar murya, aa sai dai karyayyen murya, waye kai kuma me kake takama da shi, kuma wallahi ni ba er titi bace don ina da gatana kuma da arxikin iyayena, kai kuma fa? Naga sai kayi tuki kake samun na xubawa a aljihu?" Sai kawai ta fashe da kuka ta shige dakinta ta fada kan gado tana rera kuka, duk Abba ne ya ja mata yau wai driver din gidansu ke kiranta yar titi kuma yar bariki, kuka take kamar ranta xai fita, gaba daya ta mance da wata Husnah, sai da taji ana kiran magrib sannan ta tashi ta goge idonta ta xauna saman gadon, tana jinsa ya fita masallaci, banda muguwar tsanarsa babu abinda ya cika xuciyarta, wallahi ta tsanesa, she hate him with passion, tana jin ya fita masallaci ta mike ta dau mayafinta ta fita xuwa baya wajen Husnah, wayam ta ga wajen, ta juya ta koma ciki, wayarta ta fiddo can kasan jakarta ta hau dialing number Umma, Sai da ya kusa katsewa Umma ta daga, bayan sun gaisa ta fashe da kuka tace "Umma ya farooq ya zo har gida ya zane ni saboda na tafi makaranta wai" Umma ta bude baki tace "Shi farooq din?" Cikin kuka tace "Ehh Umma" Umma tace "Yi shiru xan yi maganinsa don ubansa" Nihad na shessheka tace "Toh Umma yace kada in sake fita makarantar kuma" Umma tace "Ai ba shi ya haifeki ba da xai hanaki xuwa makaranta, kanki tsaye gobe ma ki shirya kiyi tafiyarki duk inda xa ki ba ma makaranta kadai ba, ki kyaleni da shi kawai xan yi maganinsa" Nihad tace "Toh" Umma tace "Kar ki sake asaran hawayenki a banza, kinji abinda nace maki" A hankali Nihad tace "Na ji" Umma tace "To sai da safe" Daga haka ta katse wayar, mikewa tayi direct ta tafi dakin farooq, luckily ta samesa xai fita Masallaci, strictly tace "Farooq daga yau sai yau in har ba baki kake son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login