Showing 42001 words to 45000 words out of 148918 words
KJay, har garinmu na kai ta wajen matata Jiddah" Nihal dai bata ce komai ba, Khalil yace "Bayan kusan sati uku da sallamata da aka yi daga gidansu Nadeeyah, shine Habibu yayi min hanyar wannan aikin a nan gidan, kin ji takaitaccen tarihi na...." Ta daga kai ta kallesa, kallonta yyi jin bata ce komai ba, a hankali tace "Allah ya taimake mu baki daya" Yace "Ameen" Aminu ne ya shigo compound din rike da leda, yana ganinta da farko sae da gabansa ya fadi don a xatonsa Nihad ce, sae ya ga ba ita bace, Aminu ya washe baki yace "Barka da dare Hajjaju" yana fadin hakan ya shige dakinsa da ledan hannunsa, Khalil yace "Karfe nawa xa kiyi tafiyar gobe?" Tace "Da safe in sha Allah" Yace "Ohk, ke kadai ce ai ko?" Ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Aa yawanci tare da Nihad muke tafiya, idan sun ajiyeni sai su juya" Yace "Ohk" ajiye takalmin hannunta tayi tace "Idan Aminu ya fito ka basa inji ya Farooq" Yace "To" Tace "Sai da safe" Yace "Allah ya tashe mu lfya" Juyawa tayi ta nufi cikin gidan ya bi ta da ido letting out a Sigh. Washegari da safe Khalil ya fito ta dalilin aika Aminu da Abba yayi ya kirasa, A balcony ya tadda Abba ya gaishesa da ladabi Abba yace "Xaka ajiye Nihal a Zaria, tare xa su tafi da yar uwarta sai ku dawo tare" Khalil ya sunkuyar da kai yace "Na gane... Amma sai dai na tashi yau bana jin dadi ranka shi dade" Abba yace "Me ke damunka?" Khalil yace "Ina jin ko malaria" Abba yace "Ya salam, Allah ya sauwake, baka da net ne?" Khalil ya girgiza kai yace "Aa bani da" Abba yace "Toh anjima xan baka kudi kaje ka siya" Khalil yace "Toh nagode Abba" Abba yace "Madallah, Amma ko kai da Saminu ne ku je asibiti a duba ka yanxu" Khalil yace "Toh in sha Allah" Abba yace "Kafin ku tafi ka sanar da ni" Yace "Toh nagode" Abba yace "Ba damuwa tunda farooq na nan sai yaje ya ajiyeta, kaje kawai" Khalil ya sakema Abba godiya sannan ya bar wajen, da Nihal kadai ce xai kai ta, but kasancewa tare da Nihad ne shi yasa ya gwammace yace bashi da lafiya, dalilin da yasa ma ya tambayu Nihal jiya kenan ta sanar masa tare da Nihad ne, tun jiyan kuma yayi deciding he won't be going shi yasa ya tashi da wannan plan din, he just can't withstand driving that far with Nihad in the car... Abba na shiga parlor ya ga Nihal har ta fito da jakunkunan kayanta, yace "Nihal ki jira in yi magana da Farooq ya kai ki, driver yace baya jin dadi" Shiru Nihal tayi tana kallon Abba, sai kuma ta nemi kujera ta xauna, Abba kuma ya tafi dakin Farooq, sai ga Nihad ta fito rike da handbag dinta tana kallon Nihal tace "Ke wai wannan yaron ne xai kai mu har Zaria? Ni gaskiya i can't withstand seating that long in the car with him, in har da shi ne gwara in fasa kawai, kar ma yaje da gangan ya kasheni a hanya idan muna dawowa" ko kallonta Nihal bata yi ba balle ta tanka ta, sai ga Abba ya fito yana kallonsu yace "Ku fita da kayan Farooq xai kai ku yanxu" Nihad ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Better" Trolly din Nihal daya ta dauka ta fita waje, tana ta tsaye a bakin motar har Nihal ta fito tare da Amina dake rike da wani Trolly din, Bayan farooq ya fito duk suka shiga motar, Mumy na tsaye balcony bayan tayi ma Nihal addu'ar Allah ya kai ta lafiya Allah ya tsare, Ummu ma na balcony din a tsaye, a duk sanda Nihal xata koma makaranta sai ta ji kamar xata yi xaxxabi, duk cikin yaranta babu wanda take ji har ranta kamar Nihal, a haka har farooq ya gama warming motar ya fita, Aminu ya daga masu hannu yana cewa "Allah ya bada sa'ar karatu, ku kuma Allah ya maido ku gida lafiya" Nihad da ke xaune back seat ita da Nihal ko kallonsa bata yi ba, Farooq da Nihal kadai suka amsa da Ameen.... Bayan sun dau hanya wayar Nihal dake jakarta ya fara ring, Nihad ta juya tana kallonta, bude jakar tayi ta fiddo wayar tana kallon screen din ta ga Khalil, Nihad ta kikkifta ido don ta kara tabbatar da sunan da ta gani a jiki, bata san sanda ta bude baki ba don mamaki, Nihal ta daga kiran ta kai kunne, Dubara Nihad tayi ta matsa dab da ita ko xata ji abinda xai ce, daga daya bangaren Khalil yace "Kin tashi lafiya Hajiya?" Nihal tace "Alhmdlh, ina kwana?" Yace "Lafiya, ban samu damar kai ki ba, kuma kin tafi ba mu yi sallama ba, Allah Ubangiji ya tsare hanya, ya kai ku lafiya, ya baki sa'ar abinda aka je nema" Ta sauke idonta kasa tace "Ameen nagode" Yace "Sai anjima" Tace "Nagode" Katse wayar yayi, Nihad ta matsa tana kallonta da kyau tace "Nihal ba driver din nan bane ya kira ki?" Nihal ta ki cewa komai, Nihad ta saki baki tana kallonta, Farooq dake jin su yace "Wani Driver?" Da sauri Nihad tace "Ji fa yaya, driver din gida fa, meye hadinta da shi har ma zai kirata yanxu??" Farooq dai sai kallon Nihal yake ta madubi, Nihal ta hade rai tace "You have problem Nihad, komai ke sai kin san yanda kika yi kika canxa masa ma'ana, what's wrong with me having the drivers number, naga har number Saminu ina da shi me yasa be xama laifi ba? Ke lkcn da Habibu yake nan baki da numbersa? Waye yafi communicate da Habibu a gidan banda ke?" Nihad tace "Noo, ae Habibu daban wannan daban, kuma Habibu sai ta kama muke magana da shi a waya...." A fusace Nihal tace "Toh wannan din ma kamawa yayi muka yi maganar a waya" Farooq yace "Toh wai ke Nihad ina ruwanki??" Kallonsa Nihad tayi, lkci daya ta hade rai bata ce komai ba, yace "Ke ce ai kika dau girman kai kika daura ma kanki but there is nothing wrong to have people that are under you phone number" All through the journey Nihad bata sake cewa komai ba amma fuskarta a daure yake. Satan kallon Nihal take taga tana bacci, a hankali ta dauke wayarta dake kafarta ta bude don ita bata sa password, ta shiga call logs tayi blocking number Khalil sannan tayi deleting ta mayar mata da wayar ta ajiye. Har Nihad suka kai Nihal Zaria bata ce ma kowa komai a motar ba, Farooq ya kalleta yace "Sauka ki kama mata kaya ku shiga hostel" Ta ɗan daure fuska ta bude motar ta sauka, nan ta taya Nihal suka kwashe kayanta xuwa hostel din, bayan Nihad ta ajiye jakar karshe ta juya xata wuce Nihal tace "Are u still angry? Toh kiyi hakuri" Nihad ta kalleta tace "Baxan yi ba, ba dai driver ya fi ni ba" Nihal tayi Murmushi tace "Ya xa ayi driver ya fi ki, kema kinsan babu wanda ya fi ki a wajena, kiyi hakuri i didn't mean to make u angry" Nihad ta harareta tace "Kamar da gaske" Rungumeta Nihal tayi tace "Wllh kema kinsan da gaske nake blood" Nihad tace "Toh shkkn na hkura" Nihal tace "Toh nagode" a tare suka koma gun mota inda Farooq ke jiran Nihad, Nihad ta bude jakarta jin wayarta na vibrate, ganin Aliyu ke kiranta ta daga, bayan sun gaisa yace "Xan shigo kano in the evening, ki turo min address din gidanku" Nihad ta wara ido tace "Are u coming to our house" Yace "Ki turo ina jira" daga haka ya katse wayar, Farin ciki ne ya lullubeta, bai ta6a cewa xai je gidansu ba sai yau, a baya babu yanda bata yi da shi a kan ya xo gidan nasu ba amma sai ya ki, har ta kagu ta gansu a gida ta tambayi Umma abubuwan da xata dafa masa, nazari ta shiga yi... or is he coming because of that useless driver?? Ohh God that will be very great.
07087865788✍🏻
💖💖 *NIHAAD*💖💖
By _Khaleesat Haiydar_✍🏻
14.....
Karfe biyu saura Nihad suka iso gida tare da farooq, yana kashe motar ta bude ta sauka, kallon direction din Mai gadi dake kulle gate tayi bata ga khalil ba, ta juya ta wuce cikin gida, direct part din Umma ta tafi, Umma dake parlonta tace "Oyoyo, har kun dawo?" Nihad tace "Ehh Umma, yau dai in gaya maki bata yi kuka ba da xa ku tafi" Umma tace "Toh ai gwara haka, kukan ba shi da amfani" Nihad ta xauna gefen Umma tace "Umma guess what?" Umma tace "Aa... ni kinsan i am not a good guesser, gaya min abinda ya faru daughter" Nihad na Murmushi tace "Umma Aliyu xai xo gidan nan yau" Shiru Umma tayi tana kallonta babu ko kiftawa, can tace "Wani Aliyu?" Nihad ta wara ido tace "Aliyu dai Umma" Umma tace "Amma ba kince min ya daina daga kiranki ba?" Nihad tace "Ehh wllh, kawai sai na ga kiransa jiya Umma, he called me him self" Umma ta girgiza kai tace "Nihad.... Nihad, bakya ji Nihad, baki jin magana wllh, na gaya maki ki raba kanki da Aliyun nan kin ki ji, ban san yanda xan yi da ke ba kuma, Aliyu ba komai xai yi ba illa ya yaudareki ya kama gabansa, nace ki daina hada kanki da ya yan masu kasar nan, Aliyu ya fi karfinki, ki kula dai dai ke amma kin ki ji, yaudarar ki kawai yake idan kin bibiya ma an sa masa rana, su da junansu suke aure basa auren kasa da su" Nihad tayi narai narai da ido tace "Umma wllh ba yaudarata yake ba, Aliyu yana so na, kuma yace min ina shiga level 3 xai turo iyayensa wajensu Abba, wllh haka yace min ranan nan Umma" Umma ta bude baki tace "Ehh Lallai ke shashasha ce mahaukaciya, shi Aliyun ne xai turo iyayensa gun Abbanku? Nihad nace ki daina kai kanki inda Allah ba kai ki ba, shi uban Aliyun ne xai bari ya aureki ko uwarsa?" Nihad ta hade rai tace "Ni dai kawai Umma ki gaya min abinda xan girka masa..." Umma tace "Girki? Shi yace ki yi masa girki?" Nihad tace "Aa, amma daga Abuja fa xai biyo flight ya xo, kin ga ai ya kamata in ajiye masa abinci" Umma tace "Aa babu wani abinci, a xuwan farkon ne xaki yi masa wani girki? Ai ba a girki sai in mutum ya xo ya fi sau biyar, kawai ruwa xaki ajiye masa da lemo..." Nihad tace "To snacks fa?" Umma tace "Toh shkkn xan maki small chops ki ajiye masa" Nihad tace "Toh Umma nagode, sai in taya ki?" Umma tace "Aa ba sai kin taya ni ba, kawai ke dai kije ki shirya" Nihad tace "Toh Umma, amma parlon visitors din Abba xan shigo da shi ko?" Umma tace "A wani dalili mutumin da babu wanda ya san sa a gidan xaki shigo da shi parlon baƙin Abbanku? Ai daga waje xaki ajiye masa kujera fari ya xauna" Nihad tace "Umma fa har na gaya ma Ya farooq shi yace in ajiyesa parlon baƙin Abba" Umma tace "Toh shi wannan wawan me ya sani? A xuwa na biyu ko uku shine xa a shigo da shi cikin gida" Nihad dai tayi shiru, Umma tace "Yanxu dai tashi ki je ki shirya, nima xan tashi inje kitchen in yi abinda xan yi" Nihad tace "Toh" Daga haka ta mike ta fice daga parlon Umma ta bi ta da kallo, Nihad na komawa dakinta wanka tayi ta dauro alwala ta fito, tana xaune kan darduma bayan ta idar da sallah tana danna wayarta Mumy ta shigo dakin, Nihad ta ajiye wayar tana kallonta tace "Umma ina yini..." Sai kuma tayi saurin cewa "Au Mumy ina yini?" Mumy tace "Ban yini ba, dama jira kike in shigo in gaisheki da ku ka dawo?" Nihad ta xaro ido tace "Aa wllh Mumy, dama yanxu nake son idan na gama addu'a in je in gaisheki" Mumy tace "Toh yayi kyau, ai naha addu'ar kike yanxu" Nihad tayi Murmushi tace "Ya jikin su Sudais Mumy?" Mumy tace "Ban sani ba, kin shiga duba su ne da kike tambayata" Nihad ta marairaice tace "Umma wllh yanxu nake son in je" Mumy tace "Kika sake ce min Umma xan bata maki rai wllh Nihad" Rufe baki Nihad tayi, Mumy ta juya ta fita daga dakin, tashi Nihad tayi ta bi bayanta, suna komawa bangaren Mumy tace "Ina suke Mumy?" Mumy tace "Suna tsakar gida, hope Nihal bata yi kuka ba yau, na dai kirata daxu tace tun 11 ku ka ajiyeta" Nihad tace "Ehh Mumy bata yi kuka ba ta fara xama big girl, Mumy Kinsan me?" Mumy tace "Ina jin ki" Nihad tace "Mumy Aliyu xai zo yau" Mumy tace "Wani Aliyu?" Nihad tace "Lahh, Aliyu da nake baki labari mana" Mumy tace "Ohk, toh Allah ya kawosa lafiya" Nihad tace "Ameen" Mumy tace "Me xaki tanadar masa?" Nihad tace "Mun gama maganan wannan da Umma" Shiru Mumy tayi tana kallonta, Nihad tace "Bari in dubo su Fadil" Daga haka ta fita daga parlon, ganin basa main parlor din gidan kawai ta fita compound, nan ma ta bi compound din da kallo bata ga kowa ba sai Aminu a bakin gate, ta karasa tace "Kai Aminu ina su Fadil?" Aminu yace "Barka da dawowa Hajiya" Nihad tace "Su sudais nake tambayarka" Aminu yace "Ayyo suna can tare da khalil, da a nan ma suke" Ta wani yamutse fuska tace "Waye kuma haka?" Aminu dai yayi shiru yana sosa kansa, tace "Wai wannan driver din?" Aminu yace "Ehh Hajiya" Tace "Kan bala'i, me suka je yi wajensa" sai kuma ta juya da sauri ta bar wajen ta nufi chalet ai ko ta ga takalmansu a bakin kofa, nan da nan taji ranta ya baci, yanxu cikin kazantaccen wajen nan ya shiga da su salon su ki warkewa, k'in shiga parlon tayi ta xaga ta bayan windown dakin da tasan yake ciki, ai ko a bude ta tadda window din an dage labule, can ta hangosa xaune far end of the bed da waya karama kare a kunnensa, su kuma kannen nata suna kwance kan gadon ta jikin bango suna game, ƙafafuwan su kadai take hangowa, a fusace tace "Uban meye ku ke a nan Sudais?" Da sauri Khalil ya juya yayi stretching hannunsa ya amshi wayar hannun Fadil keeping the phone under the bedsheet, duk kannin nata suka taso suna kallonta, Sudais yace "Aunty Mumy ce tace muje mu yi ball a waje" Tace "In fasa maka kai a wajen, ball din kenan? Kun shigo nan salon wari ya kashe ku ko? To wllh idan baku taso ba ku ka bari na shigo duk sai na xane ku a wajen nan, meye hadinku da shi?" Duk suka nufi kofa, ita ko ta dinga hararan khalil da ko kallon inda take bai sake yi ba, ta ja wani dogon tsaki ta juya ta bar wajen. A bakin kofar chalet din ta tarar da su suna sa takalmansu, ta ce "Uban meye ma ku ke yi a ciki? Waye yace ku shiga ciki?" Fadil yace "Game mu ke yi da wayarsa ya ba mu" Ta tafe hannu tace "Shi game din nokia phone din ne ya burge ku? Toh daga yau na sake ganin ƙafafuwan ku a hanyar wajen nan sai na xane ku da dorina" Tana gama fadin haka ta fixgo hannunsu suka bar wajen, Sudais yace "Aunty irin phone dinki yake da shi" Nihad ta kallesa tace "Wa xai basa irin phone dina?? Ai har ya mutu" Fadil yace "Irin naki da na Aunty Nihal ne, exactly the type of ur own..." Nihad tayi dariya tana jinjina shashancin kannen nata tace "He can neva have the type of my phone till he die Fadil, my phone is over a million, kasan kuma meye million?" Sudais yace "Har da Diary Milk chocolate ya ba mu each, Kuma Aunty yana da su da yawa a jaka, ni dai i want him to be my frnd..." Muryar Umma ta ji tana kiranta ta sake kannin nata ta shiga parlor da sauri tace "Na'am Umma?" Umma tace "Yauwa nayi kokarin in ma Hafsah transfer taje kasuwa tayi min chefane babu network, ke idan kina da network ki mata ta je da sauri ta dawo yanxu" Nihad tace "Umma ba akwai abubuwan a freezer ba? Meye babu?" Umma tace "Aa ba komai bane akwai Nihad, ki mata transfer din in gaya mata abubuwan da xata siyo min" Nihad tace "Toh bari in dauko wayata" Daga haka ta wuce sama xuwa dakinta, tana dauko wayar ta tura ma Hafsah dubu sha biyar, tace "Umma na tura mata 15k" Umma tace "Toh shkkn, je ki ki shirya" Nihad ta koma sama. Tana fito da kayan da xata saka wayarta ya fara ring tana dubawa ta ga Aliyu ne, ta daga yace "Flight dinmu xai taso yanxu in sha Allah" Nihad ta wara ido tace "Toh sai ka iso, Allah ya tsare" Yace "Ameen" katse wayar yayi, nan ta hau shiryawa da sauri, kaya kawai ta saka bata shafa komai a fuskarta ba ta fito, tana sauka downstairs fridge ta fara dubawa taga wani drinks ne a ciki, duk yawancin drinks din Aliyu bai damu da su ba, his favourite drink is Can coke, sai kuma Hollandia milk, rufe fridge din tayi ta koma dakinta ta dauko Atm card dinta ta fito, ta gyara dankwalin dake kanta ta fita compound, gun Aminu ta nufa, yana xaune da Khalil a gefensa, ko kallon khalil bata yi ba tace "Aminu xan ɗan aikeka supermarket yanxu" Yace "Toh Hajiya" Ta mika masa Atm card dinta tace "Pack din coke na gwangwani xaka siyo min ka bude kunnenka da kyau na gwangwani na aikeka ba na gora ba, sannan ka siyo pack din Hollandia milk,