Showing 114001 words to 117000 words out of 148918 words

Chapter 39 - Nihaad Book 1 Hausa Novel Complete

sauri, Nihad ta fito daga bandakin bayan tayi alwalan ta nufi inda xata kwanta Husnah tace "Don girman Allah ki shanye guntun malt din nan saura kadan, ta6a ki ji" Nihad ta girgiza kai tace "Aa baxan sha ba kawai ki ajiye" Husnah ta dinga kallonta sai kuma tace "Ohhh sai yanxu ma na gane, wai kyankyami yasa baki son ki sha kamar warce ta zuba na bakinta a ciki?" Nihad ta kalleta tace "Ni nace maki haka?" Husnah tace "Aa haka ne mana, banda haka meye don na sha malt na rage maki ki ki shi Nihad?" Nihad tace "Ke dai kin san yanda xa ki bi ki juya magana, ni na gaya maki haka? Ko daxu da kika dau ruwana kika sha gani kika yi na zubar?" Husnah ta mika mata gwangwanin tace "Ni dai gashi babu yawa ki sha don bana son Allah ya kamani da walakanci da abinci" Nihad tace "Wai ba daxu kika ga na dau malt na sha ba salon inyi ta tashi cikin dare fitsari" Tsaki Nihad ta ja ta amshi gwangwanin hannun Husnah ta kwankwade lokaci daya ta ajiye gwangwanin, Husnah sai kallonta take tayi wani Murmushi, Nihad ta kalleta, da sauri Husnah ta dauke kai ta lulluba da duvet tana cewa "Ki kashe mana wutan sai da safe" Nihad na yamutse fuska tace "It has a different taste" Husnah tace "Aa hajiya sai dai bakinki ne" Nihad na kallonta tace "Amma tsakaninki da Allah babu abinda kika zuba a malt din nan Husnah, ni na sha gaya maki bana son irin abubuwan nan kuna forcing dina sai na sha, dama shi yasa kika dage sai na sha?" Dariya kawai Husnah tayi tace "Oho dai, ko ba komai yau xaki yi bacci me dadi brain dinki yayi relax, habaa" Daga haka Husnah ta shige duvet, Nihad ta dinga mata wani irin kallo, can ta ja tsaki ta yi kwanciyarta, she wish ta gano abinda Husnah xata mata kenan da baxata sha malt din ba ko me xai faru, ko minti goma ba ayi ba Nihad ta bingire da wani nannauyan bacci, Husnah ta juya tana kallonta tana Murmushi, har sannan kuma ruwa ake kamar da bakin kwarya. Sha daya dai dai Husnah ta cire duvet din jikinta, ta sauka daga kan gadon, ta zaga ta inda Nihad take bacci kamar warce tayi tseren awa biyu, janye pillon kanta tayi ta ciro makullin ciki sannan ta ajiye pillown nan gefenta ta bude jakarta tayi shafe shafen da xata yi sannan ta nufi kofa, bude kofar tayi a hankali ta fita, taga duk an kashe wutan gidan, tana lalubawa ta nufi dakinsa, murda kofar dakin tayi slowly ta bude, she saw him kneeling a kusa da gadonsa ya daura kansa saman gadon wearing just his trousers, ta shigo dakin da sauri ta kulle kofar da makulli tace "Subhanallahi, me ya faru? Lafiyarka kuwa?" Lkci daya ya dago da fierce eyes yana kallonta, tayi kasa da murya ta karasa kusa da shi ta durkusa gabansa tana kallon broad chest dinsa tace "Ko dai baka da lafiya ne?" Bata jira me zai ce ba don she was more than Randy a moment din, ta kai hannu chest dinsa, lkci daya cikin dubara tayi loosening din igiyar rigarta, rungumesa tayi gam murya can kasa tace "Ka gaya min me ya sameka...." rufe idonsa yayi sai kuma ya bude da sauri, da duk karfinsa yayi karfin halin hankadata gefe har sai da ta fadi, sai kuma ya mike cikin husky voice dinsa yace "Me ya kawo ki dakin nan?" Daga sama har kasa take kallonsa, dariya ma ya bata, a wannan yanayin da take kallonsa daga sama har kasa har yake da karfin halin tambayarta me ya kawota dakinsa, wani er dariyar bariki tayi, tasan yau TBD straight up, cike da kissa ta cire rigar jikinta ta jefar nan gefensa tana masa wani shu'umin kallo da lumsassun idanuwa, kauda kai yayi cikin zafin nama ya nufi belt dinsa dake saman jaka bata ankaraba sai jin saukan belt tayi a jikinta, gigicewa tayi saboda azaba, ya dinga zabga mata belt din iya karfinsa, ihu take tana jin kamar ranta ake zarewa sbda azaban belt, ta dinga neman yanda xata kubuta daga hannunsa ta ihu a gigice, duk inda ta yi haka ya dinga bin ta yana sauke mata belt din duk inda ya samu a jikinta, a wannan daren Husnah ta ga jalala, kawai ta sa ma ranta karshen rayuwarta ne ya zo, tun tana rokonsa da muryarta har muryar nata ya daina fitowa, dukanta yake iya karfinsa da belt kamar an aikosa, ga shi ta garkame kofar dakin balle ta fita, har bandaki ta shiga ya bi ta yana duka daga karshe ta fito da rarrafe, dukan da yake mata ya sa shi jin saukin axaban da yake ji a lkcn, sai da ya gaji don kansa bayan yaga yayi mata lilis sannan ya jefar da belt din after 30mins kenan, nan ya bude kofar dakin yana sauke numfashi, tsabar yanda ta jibgu ga kofa a bude amma ta kasa motsawa daga inda take balle ta fita, ya nufota ya kalla mata wani wawan mari har sau biyu a fuska ya dau shegiyar rigar baccinta ya hada da ita yana janta ya fito da ita parlor yayi wani hajijiya da ita sannan ya cillar da ita da rigar ya koma dakinsa, gudun kar ya sake dawowa ya sa ta karfin halim rarrafawa da kyar ta nufi kitchen, gaba daya jikinta shatin belt ne rudu rudu ga bakinta sai zuban jini yake, idonta daya kuwa ya kulle, tana shiga kitchen din hannunta na rawa da strength dinta na karshe ta saka makulli kafin ta fada kasa rigijib. Tun Khalil na daurewa yana cijewa, daga nan ya koma can, daga can ya mirgina ya koma nan kamar me labor har dai yaji he is going to harm himself, he couldn't bear it anymore, Mikewa yayi kamar wanda aka tsikara ya fice daga dakin, tsaye yayi corridor ya hade kansa da bango corridon, yana ta tsaye a haka for almost 5 mins sai kuma ya kalli kofar dakin Nihad, murda kofar yayi amma bai bude ba, can ya runtse ido ya sa kafa ya tura kofar staggering inside the room, ya manna hannunsa jikin switch din dakin yana sauke numfashi, standing there for another 2 mins kafin ya kunna wutan dakin a hankali, tana saman gado ta dukunkune can saman jikinta da hijab daga kasan waist dinta har ƙafafuwanta kuma babu wani obstacle sai na lingerie dinta and she is sleeping heavily, hade kai yayi da bango ya rufe ido yana sauke breathing dinsa a hankali, can ya bude idanuwansa da suka yi jajir, ya kashe wutan dakin ya nufi kan gadon, gefenta ya fada yayi rub da ciki, perceiving her scent all over, da yayi attempting kai hannunsa jikinta sai wasu abubuwa suka dinga fado masa a xuciya, and all of a sudden ya janye hannunsa ya zamo kasa a hankalii ya daura kansa gefen gadon, yana ta durkushe a hakan har kusan karfe biyun dare, zuwa sannan yayyafi kawai ake ruwan ya tsagaita... Da kyar Nihad ta bude idonta ta dalilin fitsari da take ji, ana ta kiraye kirayen sallahn asuba ta sauko daga saman gadon tana layi xata bandaki, gaba daya jikinta is so weak, tutunbe ta ji ta ci da mutum a kasa lkci daya kuma ta fada kansa, wani ihu ta fasa a mugun tsorace tana tattabasa amma lkci daya hankalinta ya ɗan kwanta jin kamshin turarensa, zamewa tayi ta sauka daga jikinsa ta zauna gefe tana kallonsa cikin duhun don jikinsa taji xafi kamar me, nan da nan mugun baccin da ke idonta ya washe gaba daya, da sauri ta mike ta tafi ta kunna switch din dakin, kwance ta gansa nan kasan tiles ko riga babu a jikinsa, ya bude jajayen idonsa, ta dawo ta duka gabansa tana kallonsa, bata san sanda tace "Baka da lafiya ne?" Bai ce mata komai ba yayi karfin halin mikewa zaune, ta koma baya bata kara ce masa komai ba, Mikewa tsaye yayi taga yana layi kamar wanda ya sha ya bugu, ta tashi tsaye da sauri kafin tace komai yayi baya zai fadi, xaro ido tayi ta jawosa ita a dole xata tarosa, amma ya rinjayeta sai ga su a kasa, ta zaro ido cike da azaba tace "Wayyo bayana" Cike da karfin hali ya dagata ya fada gefenta can underneath his breathe ba tare da yasan ya fada ba yace "Sorry" daga haka ya kulle idonsa, ta mike zaune tana kallonsa sosai jikinsa yayi zafi, bubbuga gado ta shiga yi da sauri tana cewa "Husnah, Husnah ki tashi" Amma jin shiru ta daga kai taga wayam babu Husnah a dakin, mikewa tayi da sauri ta fita parlor nan ma ta dudduba bata ga Husnah ba, kamar xata yi kuka tace "Toh ina ta tafi?" Sai kuma ta marairaice tace "Toh ni ya zan yi yanzu?" Juyowa tayi da sauri ta dawo dakin ta durkusa gabansa tana kallonsa, sai kuma tace "Toh Abba xan kira da wayarka?" Ya bude jajayen idonsa da sauri yace "Aa" Tashi tayi ta kara fita parlor dai dai nan taji kamar ana bude kofar kitchen, tsorata tayi tayi hanyar daki da sauri tana lekan kofar kitchen din, sai ga Husnah baki ya kumbura suntummm lebbenta ya koma kamar na rakumi, ga fuskarta yayi jajir kamar nama, jini kuma ya kwanta a idonta daya, dayan idon kuwa ya manne, kayan baccinta ne a jikinta, Nihad ta dafe kirji a tsorace tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Husnah what happened" Husnah na dingishi da kyar tace "Aljanun dare" Nihad ta jingina da bango a mugun tsorace tana zaro ido tace "Aljanun dare kuma?" Husnah ta gyada kai da kyar tace "Akwaisu a gidan nan wllh, Dauko min jakata da hijabi na" Nihad da hankalinta yayi mugun tashi tace "Ganinsu kika yi?" Husnah na sauke numfashi tace "Nace ki dauko min jakata da hijabi" Nihad taki motsawa daga inda take saboda tsoro, Husnah tayi zaman dirshan a kasa ta rasa inda xata sa ranta ta ji dadi, gaba daya shatin belt din jikinta yayi jajir gasu rudu rudu, Nihad dake ta kallonta a mugun tsorace tace "Husnah kalli jikinki fa" A fusace Husnah tace "Ki dauko min jakata da hijabi nace" Nihad ta juya ta koma daki da sauri bata ga Khalil kwance inda ta bar sa ba, cikin second biyar ta fixgo hijabi, jaka da wayar Husnah ta fito da gudu daga dakin, Husnah na ganinta ta mike ko ina na jikinta na rawa ta amshe jakarta da hijab da waya, bayan ta saka hijab din ta nufi kofa da sauri, Nihad ta fashe da kuka tace "Tafiya za kiyi ki barni Husnah?" Ko tsayawa Husnah bata yi ba balle ta juyo ta saurari Nihad tuni ta bude kofar parlon ta fice da sauri ta saka takalminta luckily taga lock kawai aka sa ma gate din babu key ta bude ta fice daga gidan. Nihad ta koma dakin Khalil da gudu ta kulle kofar, kan darduma ta gansa sallan ma ya kasa tashi tsaye, ta durkusa nan kusa da gado tana kallonsa kana ganin idonta kasan ta tsorata sosai, har ya idar taga ya fada kan darduman ya kwanta ya kulle ido, ita dai tana ta zaune maganar Husnah na mata yawo a kai, can ta mike a hankali ta nufi bandakinsa, a bude ta bar kofar, bayan ta kama ruwa ta dauro alwala ta fito da sauri... Tana idar da sallah ta juya tana kallonsa, tashi tayi ta koma inda yake ta duka hucin zafi take ji a jikinsa, ta dinga kallonsa, a hankali ya bude idanuwansa jin ta a gefensa, ta 6ata fuska tace "Toh kuma kace kar in kira Abba" Wayarsa da ta hango gefen gado ta kai hannu ta dauka, yayi karfin halin kwace wayar a hannunta ya lumshe ido, tagumi tayi tana kallonsa, a hankali tace "Toh ni ya zan yi?" Tana ta zaune gefensa har gari ya waye gaba daya, tun da ya amshe wayarsa a hannunta bai sake bude idonsa ba, duk da baccin da take ji amma bata yi ba tana gefensa a zaune, lkci daya taga ya yunkura ya mike zaune, ta zaro ido ta koma baya tace "Amai zaka yi" Ya sunkuyar da kansa bayan few minutes ya koma ya kwanta ya kulle ido, a hankali ta kai hannu forehead dinsa taji har sannan da xafi, ya bude ido yana kallonta, tace "Toh safiya yayi yanzu ka bani wayar in kira Abbana" murya can kasa taji yace "Dauko takarda da biro" Tace "Takarda da biro kuma??" Jin bai ce komai ba ta mike har ta nufi kofa sai ga ta ta dawo da gudu ta tsugunna kusa da shi kamar xata yi kuka tace "Wallahi Husnah tace min akwai Aljanun dare a gidan nan, duk sun mata duka bakinta ya canxa yayi wani iri"




Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, kiyi subscription ki karanta cikin salama er uwa!!!!

Ur evidence via👇🏻


07087865788✍🏻






Assalamu alaikum manyan mata!!

For your Egyptian Abaya's, mad gowns, laces and handbags and all sort of jewelries... Give me the privilege to be ur plug plss, and u will never regret it🥰

Message via👇🏻
https://wa.me/c/2349090591769

To view our catalogue🥰



Nihad tayi shiru tana kallonsa jin bai ce komai ba, bayan few seconds cike da karfin hali yace "Baxa ki dauko min ba?" Ta marairaice tace "To wai ba nace maka tsoro nake ji ba, ni baxan iya fita ni kadai ba wallahi, bayan Husnah tace min aljanun dare na gidan nan" Da kyar ya mike zaune ya nuna mata jakarsa murya can kasa yace "Bani shi" Mikewa tayi ta tafi ta dauko jakar ta ajiye masa tana kallonsa, ya jingina da gado, kana ganinsa kasan ba shi da strength, bayan few seconds a hankali ya bude side din jakar ya ciro jotter da biro ya ciri jotter daya ya daura kan main jotter din ya fara rubutu da biron, iya layi hudu yayi rubutun sai kuma ya rubuta digit hudu sannan ya ajiye biron ya kwanta breathing slowly, ta dau takardan tana ta kallon rubutun sai kuma ta kallesa tace "Wa ya koya ma rubutu haka?" Ya nuna mata makullin mota yace "Ki je pharmacy ki basu, akwai Atm card dina a nan, ga pin na rubuta, current account" Sake baki tayi ta kallesa ta sake kallon takardan hannunta, can tace "lallai, kai ne xaka wani rubuta ma kanka magani, a ina ka san magani da har zaka rubuta ma kanka? Ko mutuwa kake so kayi?" fizge takardan hannunta yayi a fusace yace "Bar shi ma" Ta wani hararesa ta kwace takardan tace "Toh a ina aka ce ka siya maganin nan ka sha tunda kai dai ba likita bane" Kamar baxai bata amsa ba don shi kadai yasan me yake ji a jikinsa, sai kuma yayi karfin halin cewa "Likita ya turo min jiya da daddare" Tace "Wannan da ya zo ya dubani ranan?" Mika mata hannu yayi yace "Idan baxa ki je ba bani takardan" Tabe baki tayi ta mike ta tafi inda makullin motar yake ta dauka tare da makullin gida da Atm card dinsa, sai kuma ta kallesa tace "Savings account?" Ba tare da ya buda idonsa da ya kulle ba yace "Current" Tsayawa tayi tana kallonsa, sai kuma tace "Kasan meye current account kuwa?" ya bude ido a hankali yace "Bani, ba sai kinje ba kuma" Ta turo baki tace "To ai ni dai ba ruwana idan naje aka sa current aka rufe maka account dinka" Daga haka ta nufi kofar har ta bude sai kuma ta dawo ta marairaice tace "Ni fa tsoro nake ji" Lumshe ido kawai yayi, tayi shiru tana kallonsa, can ta bude kofar a hankali ta fita kafin kiftawar ido sai ga ta a compound tana maida numfashi, gun motar ta nufa ta bude ta shiga ta kunna tana warming, sauka tayi ta tafi gate amma ta kasa turawa har xata koma ta gaya masa sai kuma a hankali tace "Toh ai shi ma ba iyawa xai yi ba tunda ba shi da lafiya" bude gate din tayi ta fita kofar gida, ganin wani mutumi tace "Don Allah ka tayani bude gate din nan xan fita da mota" yana shigowa zai bude mata ta tafi ta shiga motar, bayan ya bude ta fita da motar waje, tana ganin ya kulle gate din ya fito tayi masa godiya sannan ta sauka ta kulle gidan da makulli ta hau motar xuwa pharmacy, bayan magunguna har da allurai taga an hada mata, ta basu Atm card dinsa da har xata ce masu Savings don bata yarda da current da yace mata ba, sai dai kuma tace "Current" Suka cire kudinsu suka mayar mata da atm card din ta amsa ta dinga jujjuyawa tana kallonsa, daga karshe ta amshi ledan maganin ta fito ta tafi zuwa inda tayi parking. Nihad na isa gida sai da ta kara neman wanda ya bude mata gate ta shiga da mota sannan ya kulle, godiya tayi masa ta nufi kofar shiga ciki ta bude ta tsaya tana bin ko ina na parlon da kallo, to ta ina Aljanun dare xa su shigo gidan bayan ko ina a kulle? sai kuma tayi karfin halin shiga tana tafiya a hankali ta karasa dakinsa ta bude ta shiga, kwance ta samesa yanda ta barsa ta ajiye ledan maganin hannunta ta durkusa tana kallonsa tace "Ga maganin na siyo" Ya bude ido a hankali yana kallonta, ajiye makulli da Atm card din hannunta tayi ta fita daga dakin zuwa kitchen, ba a dau lkci ba ta dawo dakin rike da cup din shayi ta ajiye masa tace "Gashi" Tashi yayi ya zauna ya bude ledan maganin da ta kawo ya fiddo su gaba daya, ta dau cup din shayin ta mika masa tace "Gashi" Ya kalli cup din ya kalleta sai kuma ya amsa, komawa gefe tayi ta zauna, lkci lkci take satan kallonsa kamar yanda shima yake satan kallonta, da sun hada ido kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login