Showing 78001 words to 81000 words out of 148918 words

Chapter 27 - Nihaad Book 1 Hausa Novel Complete

yayi ya bar wajen kamar zai tashi sama, Husnah tace "Sai ga mu ga ɗan rainin wayon nan yau" Nihad ta sauke wani ajiyar xuciyar takaici, Umma tace "Wato bai baki wayar ba dai" Nihad tace "Wallahi kuwa, ya ki bani" Umma tace "Mu je ciki, sai na ci kaxa kazansa, wato yanxu baya ganin kowa da gashi sbda Alhaji ya gama bada mu gabansa yayi mugun raina mu, yo ya bada mu mana tunda har xai dau yar sa ya basa, idan ma hadin yake son yi ina 'ya yan abokanansa?" Duk suka dukufa xuwa cikin parlon Umma na ƙare ma Khalil zagi su Husnah na tayata, shi kam tuni ya shige daki ya sa makulli, sabuwar waya dal Husnah ta siya ma Nihad har da sim card a ciki, murna wajen Nihad ba a cewa komai, gaba daya ta mance damuwar da take ciki, Umma tace "Kinga shikenan sai ki kwantar da hankalinki yanxu, tunda sun ga gida kullum kya gansu, kafin dai su dawo nan din gaba daya" Nihad ta marairaice tace "Umma fa kulle gate din yake yi kuma makullin na jikinsa" Naf tace "Amma fa kamar a jikin gate din ya bar makullin yanxu da ya bude mana fa" Husnah tace "Idan ko haka ne kawai cirewa xa mu yi mu je a yanko mana spare" Zully tace "Bari in duba" Mikewa tayi ta fita, sai ga ta ta dawo rike da makullin tace "Ai ko dai gashi" Umma tace "Toh Alhamdulillah, tunda dare bai yi ba yanzu me xai hana ku je inda ake yankan spare din a yanka maku?" Naf ta mike tace "Yanzu kuwa, kawai kudi za mu cika masu yau yau din nan xa a yanka a bamu" Naf da Zully ne suka tafi da makullin wajen yankar makulli, Nihad ta dauko ma Husnah makullin kitchen xata dafa masu taliya wai, Nihad na kallon Umma ta marairaice tace "Umma yau na shirya xan je makaranta ya hanani wai ya soke" Buda baki Umma tayi tana kallon Nihad, sai kuma tace "Toh ba a haifi ubansa ba balle shi, shi har ya isa ya soke maki karatu? Bari dai su yanko makullin kawai, ki kwantar da hankalin ki, ai indai da raina babu me cutarki a duniya Nihad, sannan nace maki ki wani manta da batun dreba kiyi rayuwarki yanda kike so, ga makulli nan xa a kawo ai, rayuwarki kawai za ki dinga yi yanda kike so kanki tsaye" Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Umma" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Yanxu shkkn har yau Aliyu ba neme ki ba ko?" Lkci daya hawaye ya kawo idon Nihad ta girgiza kai hawayen na sauka fuskarta tace "Ai blocking dina yayi Umma, kuma sim din ma na karya ai... Umma ban san waye yayi min haka ba kilan don a rabani da Aliyu ne." Kuka take yi sosai kamar ranta xai fita, cikin rawar murya tace "Wallahi ina sonsa Umma, gashi yanxu an rabani da shi" Umma tace "Aa ki daina cewa an raba ku, kina fara xuwa makaranta duk yanda xa ayi ki nemi numbersa ki nema, ba kince min a kawayenki akwai me numbersa ba?" Nihad ta gyada kai hawaye na gangarowa fuskarta tace "Naf tana da numbersa, dama can sun san juna a Uk" Umma tace "Toh ko wajenta ki amsa, kar ma ko da wasa ki wani ce ai Abbanki ya maki aure ko da xa ku fara magana da shi" Nihad dai tayi shiru bata ce komai ba, har kusan magrib Umma na parlor da Nihad, Husnah ta kawo taliyar duk suka ci, all this while kuma khalil na kwance daki ko masallaci bai fita ba, Karfe bakwai su Naf suka dawo da makulli, Umma tace "Yauwa yan albarka, gasu nan kuwa har uku, toh sannunku, Allah ya maku albarka" ta mika ma Nihad daya, ta saka daya a jakarta sannan ta basu su ma daya, tace "Toh kun ga dare yayi ni xan koma gida, ku sai anjima ko? Ko dai a nan xa ku kwana kawai?"




Nihaad* is 500 via Fcmb Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence via👇🏻
07087865788


Husnah ta kalli su Naf jin abinda Umma tace, Naf tace "Aa Umma bamu zo da kaya ba, mu ma kawai yanzu xa mu wuce, idan ya so ko gobe ne ma dawo" Umma tace "Toh shkkn, hakan ma yayi, Allah yayi maku albarka, tunda ba da mota na zo ba mu je kawai ku ajiye ni" Duk jikin Nihad yayi sanyi ganin xa su tafi su bar ta, babu yanda ta iya haka ta rakasu har bakin gate suka wuce sannan ta dawo cikin gidan tana ta kumbure kumbure. Sai da su Naf suka kai Umma har kofar gida tayi masu godiya tana sa masu albarka, sannan suka juya ita kuma ta shiga gate, Aminu na gaisheta ko bin ta kansa bata yi ba ganin Abba a tsaye balcony, karasawa balcony din tayi da sauri tace "Har ka dawo daga gidan Baffan?" Abba na kallonta daga sama har kasa yace "Daga ina kike?" Ta sauke ajiyar xuciya tace "Kayi hakuri ban ce maka xan fita ba, na fita babu izinu, wallahi Yallabai Nihad ce kira ba dare ba rana ko da yaushe cikin kuka, to shine yau da abun ya isheni nace bari dai in je in ga wani hali take ciki a gidan, kasan tun da muka kai ta ai ban koma ba" Abba dake ta sauraronta har ta kai aya yace "Toh daga yau kada ki sake xuwa gidan...." Da mamaki Umma tace "Kamar yaya fa Alhaji? Shikenan saboda iftilai ya fada ma yarinya sai ka sallama ma duniya ita, mu ma kuma ka nemi mu sallama ma duniya ita? duka duka nawa Nihad din take fisabilillahi Yallabai? Yarinyar da ko shekara ashirin bata yi ba a duniya, me ta sani akan rayuwa at this her early stage? so kake wani cutar yaje ya kamata a banza mu shiga uku? Kai kanka kasan wannan yaron tun zuwansa gidan nan ba shiri suke ba, jininsu bai ta6a haduwa ba amma ka rasa wanda zaka hadata aure da sai shi? Me yasa ma idan hadin ne baxa ka hadata da wanda bata sani ba bai santa ba, sai Dreban gidansu? Haba wannan ai babu adalaci yallabai, baka kyauta mata, wannan fa kaddararta ce, sannan ace duk soyayyar da kake mata amma ka rufe ido ka saka rayuwarta a garari kawai don an samu wasu shegu sun hada mata makirci?" Abba yayi shiru yana kallonta, can yace "Yanzu shawara kike bani a warware auren kenan?" Umma ta kalli Abba, ganin how sincerely he spoke, tayi kasa da kai tace "Ni ba haka nake nufi ba, kuma ai kai ba karamin mutum bane aji an daura aure kuma an warware sa, mutuncin da kimarka ya wuce haka, kawai dai ina jimamin abun ne, amma don Allah kar ka hanani zuwa wajenta ko ba komai zan dinga kwantar mata da hankali har ta hakura da wannan auren" Abba yace "Sumayya" Ta yi shiru tana sauraronsa, on a serious note yace "In har kina son zaman lafiya da ni toh na haneki da kara taka kafarki zuwa gidan nan, idan da wani abu xai kawota gida ba sai kin je, ina kara ja maki kunne babu ke babu gidansu, sannan ko mutuwa take ke kina tunanin zan sa a warware auren? Ai sai dai ta mutu a dakinta" Umma tace "Tabdi, to yallabai kamar yanda baxan yi shiru ba idan Nihal ce aka ma haka to Nihad ma baxan yi shiru ba don duk daya suke a wajena babu banbanci, don haka hanani zuwa gidan 'ya ta bai taso ba...." Abba yace "Good! Don Allah gobe ma ki shirya ki kara komawa gidan, ina me tabbatar maki a nan xaki ga the other side of me" Yana kai wa nan ya juya ya shige cikin gida, Umma ta bi sa da kallo sai kuma ta kyabe baki ta bi bayansa. Su Husnah na komawa hostel duk suka shantake a saman gado babu zancen sallah balle salati, Naf ta sauke wani ajiyar xuciya tayi kasa da murya tace "Amma don Allah ku ya ku ka ga wannan drivern? Isn't this strange?" Zully ta riƙe ha6a tace "Not as i expected, anya kuwa da gaske shine drivern? Ni fa har muka dawo ina kokwanto a raina gaskiya" Husnah tace "Kun ji ku, idan fa an bibiya irin shuwan nan ne fa wanda ba shi da galihu, farin fatarsa ce tasa ku ke kokwanto ko driver ne shi ko ba driver ba?" Zully ta kalleta tace "Aa maganar gaskiya duk da Umma ta tabbatar mana da shi din ne har xuciyata na kasa yarda, ta yaya wannan cikakken mutumin xa ace driver ne? His skin... Ko ku baku lura da shi ba, no plss he is so fresh abeg" Naf tace "Ohhhhoo ashe dai bani kadai ma lura da skin dinsa ba, ni wallahi da ba don kar inyi karya ba ma sai nake ganin kamar na ta6a ganinsa, ko me kama da shine oho" Husnah ta kyabe baki tace "Kanku ake ji" Zully tace "Kai amma gayen nan Allah ya xuba masa kyau frankly speaking, kawai mu fadi gaskiya, duk inda me kyau xai shiga shi ma xai shiga, kuma ina tabbatar maku Nihad haukan ta bai taba barin ta nutsu ta kare masa kallo ba" Husnah tayi wani dariya tace "Kai kuma da da wani zance, Ina amfanin kyau ba nera? kina jin mutum na tukin mota for a living, kun ishe ni da wani yana da kyau? kawai Nihad din ma kadai ya raina dan ya ganta er karamar yarinya ne, mu kuwa da muka kusa talatin a duniya baki ga da muka masa wankin soso da sabulu bai iya yace mana komai ba sai sissine kai da yake, ni fa baxan yi mamaki ba idan aka ce shege ne mutumin nan, kilan uwarsa a titi ta haifesa ta yarda shi shine yake ta garari har ya samu driving gidansu Nihad" Zully ta kwashe da dariya ita dai Naf bata ce komai ba, Husnah ta kalleta tace "Ya dai... Kin yi shiru" Naf ta ɗan tabe baki tace "No kawai ni dai i am not comfortable cewar shi din mere driver ne, he might definitely have a mission, haba u girls should think deep mana, sai kace ba big babes ba, ko kayan jikinsa idan kuka lura ai ba na banza bane, ni fa har takalminsa sai da na kalla, wallahi da kyar idan mutumin nan ba wani mission garesa ba" Husnah da Zully suka kwashe da dariya har da kyakyatawa, Husnah tace "Wllh shi ba kowa bane don ma ki ji in gaya maki, a wannan zamanin babu wanda xai bata lkcnsa ya zo gidan mutane for almost a year now wai da sunan mission, sai kace wani film ko novel, mission for almost one year ace ba ayi accomplishing dinsa ba har yanxu? Ke dai ki yarda ɗan talakawa ne mukus me shegen girman kai, don yaga fatarsa ja ce sannan gashinsa irin na halfcast shine yake wani feeling, ba ga ire irensa ba a can Ibadan da Lagos suna bara bakin titi, kilan shi ma daga can ya gudo arewa bayan ya girma" Zully tace "Kuma haka ne wallahi, gasu can a karkashin gadan lagos har Ibadan" Zully ta kyabe baki ta mike tace "Ni dai bari in je in yi wanka in zo in kira babyna, ba ruwana da wani batun shegen dreba can" Naf tace "Yanxu yaushe za mu je mata can din, kun san fa mun sa mata rai" Husnah tace "Mu bari kawai jibi don gobe kinga xa mu je minjibir park" Naf tace "Ehh haka ne kuma, Allah ya kai mu" Washegari tuesday da safe Nihad ta shirya tsaf xata makaranta abunta tunda ga makulli a hannunta, mayafinta ta yafa ta dau jakarta bayan ta feshe turare kusan kala biyar a jikinta ta fito daga dakin, yana jin fitowarta yayi saurain mayar da wayarsa dake hannunsa xuwa bayan kujeran da yake zaune, bata ko kallesa ba ta nufi kofa ta fita abun ta, da ido ya bi ta imagining if tsallake gate din xata yi, rabonsa da ita tun jiya bayan ya bude ma Umma gate da suka zo, can dai ya mike ya fita parlon ya tsaya bakin kofa yana kallon ikon Allah, tana isa gate ta bude jakarta ta ciro makullin tana kokarin bude gate din taji yace "Keee" bata fasa bude gate din ba ta juya ta kallesa bayan ta bude tace "Saboda baka yi karatu ba baka san muhimmancin karatu ba kana tunanin ka isa ka hana ni zuwa makaranta ko, to baka isa ba, ba a kuma haifeka ba" Tana gama fadin haka ta fice daga gate din, mamaki ne ya cika sa yayi saurin ciro makullin aljihunsa yana kallo yaga it's intact, then where did she get a space key?? bai yi attempting bin ta ba balle har tayi showcasing altitude dinta a bakin titi, ya juya ya koma parlor filled with surprise. Ba karamin mamaki su Husnah suka yi ba ganin Nihad a school, Nihad ta zauna aji jikinta duk a sanyaye don tun da ta shigo schl ake nunata, wai ga warce ke cikin video din nan, har ta iso ajin da suke lectures idon jama'a na kanta, bata kara jin damuwan video dinta da ya bazu duniya ba sai a yanzu, dama haka abun ya tafi viral, a ajin ma sai satan kallonta ake ana kuskus, kai har ma da masu shigowa duk da ba department dinsu ba don kawai a zo a ganta, sai a sannan tayi da ta sanin fitowa, kuma fitowar ma da ɗan karamin mayafi, daga karshe dole su Naf suka dauketa suka fita makarantar xuwa hostel dinsu, Nihad ta zauna gefen gado lkci daya hawaye ya kawo idonta, Husnah tace "Kin ji ki, meye abun damuwa, abinda ba kanki farau ba kuma ba kanki za a kare ba, duk dan iskan da ya isa ya tinkare mu yace ai kece a video yaga yanda xa mu ci ubansa, ni ai baki ce min xaki taho makaranta yau ba da na hanaki don su yanxu ma suke tashen labarin, kuma ana ta jira aga kin shigo makaranta sai ga ki yau, ni ban ta6a ganin munafukai yan sa ido marasa aikin yi kamar yan makarantar nan namu ba, abu kusan sati daya amma kullum maimaita zancen ake kamar yau ya faru" Nihad ta hade kanta da gwiwa tana shessheka tace "Da na sani ban fito ba" Naf tace "Surutun mutane zai sa ki fasa rayuwarki yanda kike so? Ai ba a biye ma mutane, gwara su yi ta ganinki din har su gaji su yi shiru zancen ya mutu, yanzu dai ina kika baro ɗan rainin wayon Drivern can?" Nihad na goge idonta cikin sanyin murya tace "Toh meye hadina da wannan kuma kike tambayata" Naf tace "Aa babu hadinki da shi kam, ni ai na ga kokarinki ma da kike iya kwana gida daya da shi, da ni ce kwasan kayana xan yi in bar gidan iyaka Abba yayi bambami a wuce wajen" Nihad ta kalleta tace "Abbanmu yace xai yi disowning dina if i try anything of such" sai kuma ta fashe da kuka sosai, Naf tace "Aa ba kuka xa kiyi ba, nema ma kanki mafita xa ki yi" Nihad tace "Don Allah ku dawo gidan mu zauna gaba daya a can" Naf tace "Dama gobe muka yi ai za mu je can din" Nihad tace "Tunda na fito yau don Allah ku dau kayanku kawai mu koma can gaba-daya, the house is nothing but a living hell for me" Naf ta kalli Husnah dake ta danna wayarta bata ce komai ba tace "Husnah ya kika ga" Husnah tace "Duk yanda ku ka yi" Naf tace "Toh kawai duk mu dau kaya ko kala biyar biyar ne mu tafi can din gaba daya" Nihad tayi murmushin jin dadi tace "Amma naji dadi Nagode wllh" Zully tace "What are friends for, ai amfaninmu kenan" Nihad tayi kasa da murya tana kallon Naf tace "How about Aliyu?" Naf tace "Hmm, kinsan he is off social media tun da abun nan ya faru, to in gaya maki 3 days ago mun yi chatting da wani frnd dinsa yake ce min ai ba shi da lafiya ma" Nihad tayi narai narai da ido tace "Da gaske?" Naf tace "Wllh kuwa bari ma in nuna maki chatting din" Jawo wayarta tayi ta bude ta shiga chatting dinta da wani abokin Aliyu ta mika ma Nihad wayar, Nihad ta amshi wayar jiki a sanyaye ta dinga bin chat din, abokin gaya ma Naf halin da Aliyun ya shiga bayan faruwan lamarin yake, ya kuma ce mata har su abokanansa yayi isolating din kansa daga cikinsu ba ma social media ba kadai, abokin ya dinga nuna yanda Nihad ta kwafsa ga shi Aliyu yayi trusting dinta sosai kuma ya sa ran zai aureta duk da tulin manya manyan babes dinsa, Nihad ta hade kai da gwiwa tana shesshekar kuka tace "I don't know who did this to me, i don't know who is this that ruined my happiness" Husnah ta sauke ajiyar xuciya tace "Na fi ki son mu gano wanda yayi maki haka Nihad, amma abun akwai rikitarwa ni wallahi kawai zuciyata ta kasa yarda cewar ke ce a video din, ke baki zama da undies haka kamar yanda mu muke yi, sannan duk party tare muke zuwa balle ace wani partyn kika je aka maki haka, abun dai akwai confusion sosai wallahi, wanda ya sanki sosai sosai ne yayi maki wannan abun, i wish Abba xai ajiye duk wani fushi ya tsananta binciken ta ina wannan video din ya fito" Zully ta sauke ajiyar xuciya tace "Ai na dau darasi ni kam, ko daga ni sai singlet da skin tide baxan sake xama a waje ba balle undies, na saka kaina a shoes din Nihad ya fi a kirga but luckily the shoe did not even size me, waiii

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login