Showing 144001 words to 147000 words out of 148918 words

Chapter 49 - Nihaad Book 1 Hausa Novel Complete

ba, ta cuceta ta gurbata mata rayuwa" Khalil ya lumshe ido ya bude bai dai ce komai ba, Aunty Maryam tace "Me yasa kace admission letter xata amsa a garin nan bayan ba haka bane?" Sai da khalil yayi stiff a inda yake zaune, Aunty Maryam tace "She told me her dad sent her away from his house" Sosai gaban khalil ya fadi jin abinda Aunty Maryam ta kara cewa, shikenan ya ma san ta riga tace an masa aure da ita tunda har ta iya buda baki tace an koreta a gida, jin tayi shiru Khalil yayi karfin halin cewa "Sai me kuma ta gaya maki Aunty?" Aunty Maryam tace "Iya abinda ta sanar min kenan, sai kuma wanda kai zaka kara min, sannan tace video dinta bata san garin yaya aka mata ba har ya fita.... Na kuma yarda da ita don babu alamar karya a duk zantuttukan ta" Khalil dai kallonta kawai yake, can ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya da ya fahimci iya abinda ta sanar ma Aunty Maryam kenan da gaske, yayi kasa da murya yace "Haka ne Aunty, but bansan ta ina xan fara gaya ma Mami all this ba, ni kuma mahaifinta yayi min halaccin da baxan iya kyaleta ta shiga duniya ba bayan ya koreta gidansa saboda offense din da ba yin kanta ba, her stepmom is behind all that happened to her amma bata sani ba ta kuma ki kwantar da hankalinta ta gano hakan, makira ce matar kuma azzaluma, ta lalata mata rayuwa ta dora ta a kan abubuwa da yawa da basu dace ba, wanda ita nata yaran bata basu wannan tarbiyar ba, duk nutsattsu ne babu na banza a yaranta, farkon faruwan incident din ai mahaifin nata bai koreta daga gidan ba amma matar nan ta san yanda tayi har ya koreta after almost one month da faruwar incident din, and i am telling you ba directly take abubuwanta ba, ni nasan mahaifinta baya cikin hayyacinsa ya koreta daga gidansa, coincidentally kuma nima na masu sallama xan bar gidan kenan in taho Abuja bayan Abba ya kirani, kawai naga baxan iya barin ta tafi wani wajen ba, And you know what Aunty.... bamu ta6a shiri da yarinyar ba duk tsawon xamana a gidan, amma sbda kirkin mahaifiyarta na tausaya mata muka taho nan Abuja tare" Aunty Maryam ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Dangin mahaifiyarta fa?" Ya girgiza kai yace "Babu su a nan" Aunty Maryam tayi shiru cike da tausayin Nihad, can tace "Kai yanzu menene next plan dinka Khalil?" Ya girgiza kai yace "I don't know Aunt, i am confuse, ban san ta yanda xan yi convincing Mami har ta zauna nan zuwa sanda mahaifinta xai huce ba, gashi jiya da daddare ma sai da tace min ta amshi abinda xata amsa yau ta tafi sbda gobe weekend" Aunty Maryam tace "Kar ma kace mata komai don ba lallai ta fahimta ba, kawai dai ko da zata sake maganar admission letter din kace still fa ba a samu ba.... Nihad have to stay here kafin a samu wani solution din gaskiya, she is too young for this trauma at her age, kishiyar uwarta bata mata adalci ba, gashi ni kilan nan da sati biyu xamu yi tafiya" Khalil yayi shiru sai kuma a hankali yace "Aunty to me yasa baxan samar mata admission din ba kawai, sai ta zauna Abujan a zuwan dai karatu take" Aunty Maryam tace "Eh wannan ma shawara ce mai kyau kuwa, amma wani makarantar xaka samar mata?" A hankali yace "Nile or Baze University...." Buda baki Aunty Maryam tayi tana kallonsa da mamaki tace "Did you know the tuition fees of those Universities kuwa?" Ya ɗan yi dariya yace "Ohhh nawa ne ma?? shi su Mimi ke zuwa i think?" Tace "In ba dai ko Abbanku ya hada har ita ya dinga biya ba, tunda kowa ma biya ma kudin makaranta yake ai naga" Khalil yayi murmushi yace "I will process the admission for her as soon as possible in sha Allah" Aunty Maryam tace "Toh Allah ya rufa asiri, kaga dai dai kenan ma tunda sabon session xa su shiga" Bai ce komai ba, Aunty Maryam tayi shiru tana ta nazarin abubuwa iri iri, can ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Yanzu duk wani hanya da xa a bi a gano ta inda wannan video din nata ya fita babu shi kenan? Ai bai kamata ayi shiru babu bincike ba, kamata yayi anyi ta bincike har Allah ya sa a gano wanda yayi wannan ta'asar, duk da babu tantama ni nasan da sa hannun matar ubanta, sannan ina zargin kawayenta ma, don ta gaya min ko su waye" Khalil dai bai ce komai ba, Aunty Maryam tace "Amma tunda har ta iya tashi cikin dare ta kai ma Allah kukanta ni nasan komin daren dadewa wataran gaskiya zai bayyana, ta yanda komai ya faru duk Allah xai nuna ya tona asirin koma wanene, Allah Ubangiji ya kare mana zuri'a ya sa mu fi karfin zuciyarmu" Sai wajen karfe goma Khalil ya sauko downstairs daga parlon Aunty Maryam, Babu kowa parlon kasa ya nufi guess room da Nihad take, ya bude kofar dakin a hankali ya shiga ya ganta kwance tana bacci, for almost 4 days sai yau take bacci peacefully kuma me nauyi, ya karasa cikin dakin yana kallonta, juyawa yayi daga karshe ya fita ya kulle dakin. Ba laifi throughout ranan Nihad ta saki jikinta a gidan Aunty Maryam she really felt at home, Aunty Maryam bata barta ta zauna ita kadai ba, har fita suka yi tare da yamma ta rakata xata yi siyayya a shopping mall sae dai ta bata nikaf ta saka saboda yan kwakkwafi masu gane mutum farat daya, Aunty Maryam ta bata baki sosai a kan kar ta wani damu kanta in Allah ya yarda asirin wa enda suka mata haka zai tonu, kuma xata ga yanda Allah xai yi da stepmom dinta, hakan yasa damuwan Nihad ya ragu sosai ta samu relieve, bayan sun dawo daga shopping Mall din Aunty Maryam ta ware mata nata abubuwan da ta siyo mata ta bata, Nihad ta amsa a hankali tace "Nagode Aunty, Allah ya saka da alkhairi" Daki ta kai ta dawo ta zauna parlon, Aunty Maryam na ba Mus'ab dinta abinci Nihad tayi kasa da murya tace "Aunty don Allah xaki iya ara min wayarki in kira Mumyna?" Aunty Maryam ta dau wayar ta mika mata, Nihad tayi dialing number Mumy sannan ta kirata, lkci daya jikinta yayi sanyi jin wayar a kashe, ta mayar ma Aunty Maryam tace "Wayar a kashe yake" Aunty Maryam tace "Anjima sai ki sake trying" Nihad tace "Toh" Wayar Aunty Maryam ya fara ring ta dauko ganin Mami ce ke kiranta ta daga, bayan sun gaisa Mami tace "Ya ake ciki ta amsa kuwa Maryam?" Aunty Maryam tace "Kinsan sabon session ne Mami, so ina jin sai zuwa next week xa su fara badawa gaskiya, har yanxu bata samu ba kam" Mami tace "Wai wani makaranta ne?" Aunty Maryam tace "Toh ban dai sani ba gaskiya" Mami tace "Toh Allah ya kyauta, amma na so ace ko yau ko gobe ta koma gida" Aunty Maryam tace "Toh tunda Allah bai nufa ba sai mu saurari yanda ya tsara" Mami tace "Yana nan gidan naki ne Khalil din?" Aunty Maryam tace "Aa" Mami tace "Ohk tun safe ya fita naga kuma bai dawo gida ba" Aunty Maryam tace "Kilan yana can gidansu budurwarsa" Mami tace "To a gaida Mus'ab" Aunty Maryam tace "Xai ji" Daga haka suka yi sallama ta katse wayar, Aunty Maryam ta dinga tunanin ta yanda xa su bullo ma yayartata. Aunty Hassana ce xaune bangaren Hajiya Amina tana kallonta rai a dagule tace "Yanzu dai kin kara tabbatar da cewar bayan malaman da fatima ke bi na kasar nan har kasansu ma malamai yi mata aiki suke ko?" Da sauri Hajiya Amina tace "Aa na yarda wallahi...." Aunty Hassana tace "Wai ni yau yaya zai buda baki yace in bar masa parlonsa sbda na kawo masa shawarar kar ya tura Khalil Zanzibar, yaushe har ya dawo gidan balle a san ko ya sauya hali ko bai sauya ba, har zai kara yarda da shi ya daura sa kan miliyoyin kudinsa, kar ki dada kar ki raga shine yaya ya hayyako min har yana cewa in bar masa parlonsa cikin tsawa" Hajiya Amina tace "Toh wai yanzu me malamin yace maki da ku ka yi waya" Aunty Hassana tace "Ta lalata mana aiki, kuma da tsafi aka lalata aikin" Hajiya Amina ta rike ha6a tace "Aikin kusan miliyan daya fa?" Aunty Hassana ta sauke ajiyar xuciyar takaici tace "Wato an bata sa'ar dai dai sanda xata gaya masa ya shigo gidan babu wanda xai hanasa, shine ya shigo kansa tsaye asiri kuma yayi tasiri aka xuba masa ido babu wanda ya dakatar da shi, uban ma ya kasa cewa komai har yanzu shine ya billo da turasa Zanzibar yayi masa business" Hajiya Amina tace "Toh ni ance ba shi kadai ya dawo ba, kuma har yanzu ban ga yarinyar da aka ce ya dawo tare da ba, kinga ai ko yau naje bangaren, kuma har dakin Hajiya Fatiman na shiga kai tsaye ko yarinyar na ciki amma ban ganta ba" Aunty Hassana tace "Farhana tace fa bata gidan, tun da suka gane ita ce me wannan video din na kwanaki ya fitar da ita wai daga gidan, kinga tabbacin tsiyarsa kawai yaje ya tsula a duniya ya dawo, babu tantama kuma karuwarsa ce" Hajiya Amina tace "Wai daxu baki ga uwar yarinyar da ake son makala masa ta zo ba kuwa??" Aunty Hassana tayi wani dariya tace "Ai ko zata mutu baxai auri er ta ba sai dai in har ba Hassana sunana ba, Nadiya take ko wa? Toh wallahi baxai aureta ba, ba dai dukiyar yayana ake hari ba? to sai dai su gani su hanga daga nisa, ita fatima ta zaci ta fi kowa wayo shine take kokarin xata makala masa yar aminiyarta tunda kasarsu daya su hadu su wawushi dukiya ta ko ina su ci karensu ba babbaka, su yi wandaka son ransu su gayyato jajayen danginsu da abokai ayi biki a ci uban kudi, to kuwa xan ga ta yaya, don da dai in bari ya auri yarinyar nan gwara ya dauwama babu auren har ya mutu, yanzu in zai yi auren ai dukiya ne ba ta wasa ba yaya xai kashe, don har lefe shi xai yi masa, toh kiyi imagine nawa xai basu su yi lefen, ai miliyan 10 ma albarka" Hajiya Amina tace "To ke yanzu baxa ki yi ma Malam magana ayi duk yanda xa ayi ya auri ko Farhana ko Sajida ba? Ai gwara yan gida su mora da yan waje" Aunty Hassana tayi wani dariya kawai ta kyabe baki bata ce komai ba, Hajiya Amina tace "Allah kuwa da dai ya auri yarinyar nan gwara anyi haka kawai mu san har yanzu mu ne" Aunty Hassana na girgiza kafa tana wani Murmushi tace "Ke kin zata a banza ne har yanzu ba ayi auren nasa da Nadeeyah ba, sai yayi ta ce masu ba yanzu ba har ya bar gidan nan?" Hajiya Amina tace "Toh yanzu gashi ya dawo ga kuma uwar yarinya har ta fara mana sintirin gida" Aunty Hassana tace "Xata yi ta gama, baxai auri er ta ba, balle wata kuma can"





Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788




Umma ta shigo dakin da taga Nihal ta shiga for almost ten minutes bata fito ba, wato dakin Nihad, dube dube ta sameta take yi a dakin, tun da Nihal taga shigowar Umma ta dakatar da abinda take ta zauna gefen gado, da mamaki Umma tace "Me kike nemar mata a daki tun daxu?" Nihal dai bata ce komai ba, Umma ta kyabe baki tace "Ke idan fa kika ce xaki tafi makaranta a haka ba tare da kin saki ranki kin dawo yanda kike harkokinki da ba to ina me tabbatar maki zaki samu matsala a makaranta wannan time din, abinda baki ta6a ba, eh ansan er uwarki ce kuma ba dadi to amma so kike ki targada naki future din ne? Ko damuwar nan ne xai dawo maki da Nihad, to ma ta dawo ta maki me? yarinyar da ke can kauyen mijinta" Ita dai Nihal bata ce komai ba still kuma bata kalli Umma ba, Umma ta kara kyabe baki ta karaso ta zauna gefen gado tace "Ba kwanaki can kina da number shi dreban ba, ni da ma kin kirasa in ji ko kauyen nasu na nan garin suka tafi ko Zarian ya tafi kauyen uwarsa da yace" Nihal dai bata ce komai ba, Umma tace "Ba da ke nake ba kika min shiru Nihal?" Nihal ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace "Bani da number sa" Umma tace "Toh amma ai farooq bazai rasa ba tunda shi ma Allah ya zuba masa shisshigi kira min shi ki tambayesa yanzu ina jira" Nihal ta dau wayarta tayi dialing number Ya Farooq ta sa handsfree, yana fara ringing ya daga bayan ta gaishesa tace "Yaya wai kana da number Khalil?" Farooq yace "Wa ke tambayar numbersa?" Duk da alamar da Umma ta dinga yi mata kan cewar kar tace ita ce ke tambaya amma Nihal bata kalleta ba tace "Umma ce" Farooq yace "Noo bani da shi, sai anjima" Tace "Toh sai anjima" Katse wayarsa yayi, Umma ta hade rai tace "Akan meyasa xaki ce masa ni ce ke nema?" Nihal tace "Nima na tambayesa Shekaranjiya yace bashi da, don ki tabbatar da hakan yasa na sake kiransa amma ni nasan bashi da number" Umma tace "Toh ai shikenan, dama wai da sai mu ji kauyen da suke, in ya kama mu je sai mu je kafin ki koma makaranta" Daga haka ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin, Nihal ta mike ta ci gaba da duba takardun da take. Ranan asabar da rana khalil na zaune parlon Mami sai ga kiran ya Farooq gaba daya ya mance sun yi waya few days ago yace masa xai shigo zaria, Ya ɗan kalli Mami dake parlon, bai daga wayar ba har ya katse, Ya farooq ya sake kira, mikewa yayi ya nufi kofa yace "Mami sai later" Daga haka ya fita daga part din gaba daya sannan ya kira Ya farooq, ya farooq na dagawa bayan sun gaisa ya sanar masa zai taho zaria from kaduna, Khalil yace "Ohk amma kaga muna gidan wata kanwar Baabata mun je gaisheta" Farooq yace "A ina kenan?" Khalil yace "A Abuja take" Farooq yace "Ohk, babu damuwa Usman na Abuja, so xai je inda ku ke in sha Allah" Khalil bai iya yace masa komai ba da farko, can kuma yayi saurin cewa "Toh Allah ya kai mu" Farooq yace "Zan tura maka numbersa yanzu ko da xai kiraka" Khalil yace "Ba damuwa" Daga haka suka yi sallama, kamar ance ya daga kansa ya ga Farhana a tsaye tana sauraron wayar da yake, ya hade rai yace "Ke ya kika tsaya min a kai?" Bata ce masa komai ba tana rungume da laptop dinta ta wuce tana ta6e baki, ya bi ta da wani mugun harara. Khalil na shirin xai fita da yamma sai ga kiran number da Farooq ya turo masa daxu, wato number Usman, yayi jim yana kallon wayar, can ya daga ya kai kunne, gaisawa suka yi, Usman yace "Yauwa wani anguwan ne a Abuja?" Khalil ya ɗan buda ido sai kuma yayi saurin cewa "Bari in tambaye Kanwar Baabar tawa" Usman yace "Ohk ina jira" Katse wayar yayi yana tunanin abinda xai yi next, bayan ya gama shiryawa ya fito zuwa bangaren Mami sannan ya kira Usman, yana dagawa yace "Tace Suleja ne" Usman yace "Ohk, akwai tazara sosai tsakaninmu, amma idan na shirya zuwa zan kiraka" Khalil ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Toh Allah ya kai mu" Usman yace "Ba Nihad din wayar mu gaisa" Khalil yace "Idan na shiga gida xan kiraka yanzu ina waje" Usman yace "Alright" Daga haka ya katse wayar, Mami da ta fito parlon tana kallonsa tace "Waye a Suleja?" Yace "Wasu ne" Tace "Ohk" Sannan ta zauna saman kujera a hankali tace "Ina son za mu yi wata magana da ke damuna Khalil" Ya kalleta yace "Toh ina ji Mami" Tayi kasa da murya tace "It's High time kayi settling down son, tun baka bar gidan nan ba almost 2 years ago Abbanka ke maka magana har Allah ya kaddara tafiyarka, babban burina a rayuwa a yanzu shine in ga kayi aure...." Khalil ya sauke ajiyar xuciya yace "Mami kinsan fa she aure lokaci ne, idan time din yayi sai kika nayi Mami...." Tace "I am not talking about you settling down wai saboda ina son ka auri Nadeeyah, No son, idan da wata warce kake so daban fine, present her to us xa mu yi accepting as far as tana da tarbiyya, i can never force u on marriage son, kar kaga ko Nadeeyah yar aminiyata ce shi sa nake so ka aureta, a'a idan dai kasan da wata warce kake so da aure go ahead ka nemi aurenta just make sure yar gidan mutunci ce me tarbiyya ce like i said, sannan she should be from a reputable family, ka dai san halin Abbanka ai" Khalil yayi murmushi yace "Toh Mami ai ba ke kika hada mu da Nadeeyah ba, i met her abroad without knowing she is ur friends daughter, ba ta dalilin ke da Mumy muka san juna da ita ba, kawai Allah ne ya hadamu..." Mami tace "Haka ne, amma kaga ai yan sa ido gani suke mu muke cusa maka ita ka aura, don ta Hajiya Safeenah ma ta fi son Nadeeyah tayi aure a can Yemen tunda danginta suna can, kuma dama ita a can din ta tashi" Khalil yace "In sha Allah, as soon as i come back from this business trip xan kai ma Abba batun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login