Showing 33001 words to 36000 words out of 45645 words
baka yi mata shiru ba zan cillar da kai a dajin nan in ja mota ta, da me kake so ta ji? Da ciwon jikin ta ko da hayaniyar ka?”
Daga haka aka samu Malam Isa yayi shiru, bai kara magana ba har suka isa asibitin Malam Aminu kano.
Tun kafin su iso dama Sarham yayi waya da Dr. Babangida, wani babban likitan zuciya ne (cardiologist) abokin karatun sa a Jiddah da ya dawo yake aiki a nan AKTH, shi yasa aka karbi Inna cikin kulawa daga shigar su asibitin, aka yi imajensi da ita. Kuma da taimakon sanayyar sa da Dr. Babangida yasa ta samu attention din likitoci da yawa suka rufu akan ta, don binciken hakikanin abinda ke damunta.
Sai da suka kwana suka wuni a A&E ana bata taimakon gaggawa kafin a basu daki a kwantar da Inna, amma da Sarham ya zo asibitin a washegari sai yace a maidata dakin ‘Amenity’ ya kuma biya komai aka maida Hauwa da Inna kebantaccen daki wato ‘Amenity’ a sashen mata.
A kwana uku sakamakon gwaje-gwajen da likitoci suka yi wa Inna ya fito, da gaske tana da huda a zuciyar ta, wadda ke bukatar sai an yi mata aiki an cike ramin da zuciyar tayi. Madinah na can gidan kakannin ta tana jego, Sarham na jelen asibiti dasu Inna daga nasu gidan yake zuwa shi yasa bata san me yake ciki ba, sai dai duk sanda ta kira shi a waya zai ce mata yana asibitin Aminu Kano yana da ‘patient’ yana ‘busy’, ta kuma san shi sosai da Dr. Babangida shiyasa ta daga masa kafa, yau kwana uku bai zo Soron dinki ba balle ya ga Baby Hauwa da take kira (Waheedah) tun ranar sunanta.
Kowa ya dauka saboda Haj. Kulu Sarham ya sakawa ‘yar sa suna Hauwa, shi kuwa zai iya rantsuwa ya saka sunan ne don ya dinga tunawa da Inna da Hauwa a lokacin da ya neme su ya rasa.
Hatta a gida sun gane yana zirga zirga, kuma ba a wajen masu jegon ba, ko jiya ya saka Surayyah girki na hanta da koda da ‘vegetables’ da kunun gyada yace ta zuba masa madarar ruwa a ciki, Surayyah ta dauka shi zai ci, bayan ta gama ta gaya masa ta gama, sai yace ta shirya a basket ta kai masa mota, Mama ta bi Surayyah daki bayan fitar sa tana tambayarta ko wa Sarham zai kaiwa abinci? Surayya tace bata sani ba, yace dai yana da mara lafiya a asibiti ne.
Mama tayi wani dan tunani sai ta ce “in kika bibiya bazai wuce mutanen sa na Badala ya gano ba. sune kadai zai dauka da muhimmanci irin haka ya kasa nutsuwa in suna cikin matsala”.
Surayyah ta ce cikin mamaki “ba sun bar Kano ba? Ba sun bace masa ba tuntuni?” Mama tayi dariya tace “ko a ina suke in dai a fadin Najeriya ne na tabbatar miki sai Sarham ya nemo su, ki bar Sarham akan abinda yasa kan sa, ko yake kuma kauna da son taimakawa da zuciya daya”.
Surayyah ta kwana abun yana bata mata rai, na yadda ta zage ta shirya masa abincin nan da kyau, don ita bata son zancen su ma, yadda aka sakata girkin wahalar wasu kauyawa wai su su Innar Hauwa, tarkacen BADALA, don haka washegari da ya saka ta girkin again tayi maza ta ce kanta na ciwo bazata iya ba, dole sai Nancy sabuwar mai aikin Mama ya saka tayi masa ‘potatoe porridge’ da yaji ganyen alayyahu. Da dafaffen kwai.
Ita Hauwan ma da ake kaiwa garar abincin mai dan gina jiki, don a samu ta murmure ta tada komada daga muguwar ramar data yi da mokadewar da kashin wuyan ta yayi a Albasu, sam bata iya ci, bakin ta ya kasa karbar dandanon abincin don bata saba da cin mai lafiya da dadin dandano irin sa ba.
Ruwan bunu (lipton) ko na Milo kawai take iya zubawa a cikin ta ya zauna da dadin rai, ta zama kamar ka bushe ta ta fadi don kamar ma bata da lafiya, nan kuwa yunwa ce kawai ta zaman Albasu ta zauna a jikinta tayi mata illah. Abu daya ke faranta mata in ta tuna Inna na bisa karkashin kyakkyawar kulawar asibiti yanzu, kuma ana tabbatar mata da tana jin sauki kasancewar idonta a rufe yake kuma kullum ana mata karin ruwa kafin ranar da za’a yi mata aiki tazo.
Sarham ya biya komai ranar aikin, ya kuma saka hannu aka yiwa Inna aikin zuciya. Aka yi lafiya cikin nasara ba kamar yadda Inna ke tsoro ba.
A lokacin ne ya samu ya koma cikin hayyacin sa tun daga ranar da ya dauko su Inna sai yau ya samu nutsuwa, bayan an gama aikin an kai ta dakin hutu, inda Hauwa ta cigaba da jiran farfadowar ta.
Sai ranar ya samu ya leka su Baby Hauwa. Madinah bata iya fushi da Sarham ba, ko me yayi mata kuwa, komai girman laifin, amma yau a kwayar idonta ya gane tayi fushin, musamman da yaga tana ‘avoiding eye contact’ da shi, ya san tayi fushi mai ban mamaki ko bata furta ba.
Ya sa hannu ya dauki Hauwa cikin dan kyakkyawan gadon ta tana barci, ya zauna dab da Madinah yace “Likita matar Likita barka da yau, ya kuka kwana? Ya kukan daren uwar bil’adama?” Madina ta amsa fuska ba yabo ba fallasa, sai yace “ba sai an gaya min ba, na san nayi laifi wa GIWAR SARHAM, kuma na karbe shi tun ba’a bani ba (laifin), tun kwanaki uku baya ma fa ya kamata ace na koma Jeddah, amma inada uzurin da ya rike ni mai muhimmanci, kiyi hakuri kin ji Madindin din Sarham! Madinatul-Munawwarah my shelter, my eternal happiness, my home peace, my safety and my security, in sha Allahu nama fasa komawa, sai kin gama wankan jegon ki sai mu koma tare, zan yi amfani da lokacin (as annual leave) dina”.
Amma har ga Allah ya fasa komawa ne saboda lafiyar Inna, yana kuma son daukan ‘measures’ din da ya dace akan rayuwar su Inna kafin ya koma Jeddah.
Madinah da bata iya dogon fushi da Sarham ba jimawa ta yarda da uzurin sa ta kuma saki rai suka shiga hirar arziki da hirar soyayyar su da bata kodewa, suna yi suna kallon kyakkyawar fuskar ‘yar su Hauwa (Waheedah) wadda suka saka a tsakiyar su tana barci da sauke numfashi cikin koshin lafiya.
A lokacin Madinah da Sarham suka hau musu akan wanda Hauwa tafi kama dashi, shi yace da shi take kama completely, ita tace kalar su da gashin su ne kawai iri daya amma fuskar da yatsun, duk nata ne.
Madinah a idon sa kadai ta fahimci ya jima bai ci abinci ba, amma da yake a dabi’ar shi baya dorawa matar sa nauyin ta tashi tayi masa girki a duk sanda yake so, sai bai mata complain ba, ita da kanta da yake ta san kan kayanta, ta gane sosai yake cikin gajiya da yunwa, don tun haduwar sa dasu Inna bai samu nutsuwar cin kyakkyawan abinci ba sam, don haka ta tashi ta hado masa abinci mai rai da motsi, sai da yaci ya koshi suka gaisa da Kakarta Haj. Lailah, wadda ke falo, sannan yayi musu sallama ya wuce asibiti don ya tadda su Hauwa ya ga farfadowar Inna, don haka daga nan Soron dinki can ya nufa.
Saida ya tsaya a hanya ya yi musu sayayya sosai kamar yadda ya saba duk da ya lura Hauwa bata iya ci, yau sai ya saya mata fresh milk da yawa (unsweetened) kafin ya wuce aibitin. Da sallama ya murda kofar ya shiga dakin, bayan Inna tayi masa iznin shigowa, amma Hauwa a ciki ta amsa masa kamar yadda ta saba amsa sallamarsa tun fil azal, ya tadda su tare da Malam Isa ya zo dubata shi da dan gidan Inna wato Saleleh.
Malam Isa har gidan su Salele ya je ya gaya musu an ga Innar Hauwa, shine fa Salele ya biyo shi. Inna ta dubi Sarham tana daga zaune jikin filo. Ba don ba karamin sani tayi masa ba da bata gane shi ba, don ya canza gabadaya daga yadda ta san shi, dan siririn saurayin likitan nan na Murtala, ya girma ya kara cika ido cikin shekaru kalilan, ilmi da kwarjinin addini sun kara bayyanar da cikar zatin sa. Tayi murmushi a hankali, ta ce.
“Inda rai da rabo, likita Sarhamu! Ashe Allah yayi zamu gana?”
Sarham ya ja kujera a gaban ta ya zauna, yana kallon Hauwa tana shafa hoda irin mai like da mudubinnan a jikinta, saura kadan ya fashe da dariya, kasa amsawa Inna maganar data yi yayi saboda dariya dake cinsa, ya nuna wa Inna ita da baki, itama tayi dariya, tace “kuma ayi magana cibi ya zama kari ba!”.
Malam Isa ya juyo garesu yace “dariyar me kuke haka?” Inna tace “kai dai abar kaza cikin gashin ta, daga jiya zuwa yau na kirga shiga wankan ta ya kai goma! Wai biyan bashin wankan kwana bakwai da bata yi ba a kauyen Albasu take yi yanzu, tunda ta samu ruwan dumi da sabulu mai kamshi ai shikenan, har da yi wa Malam Sani Allah ya isa da yayi mata sanadin komawa zaman kauye”. Sarham yayi dariyarsa mai isarsa, har da sunkuyawa da rike ciki, sai lokacin Hauwa ta gane da ita suke.
Ta dan dakata da shafa hodar, duk ta sha jinin jikinta, ga mudubin a hannun ta, kai sai ka rantse tana ganin fuskar ta cikin mudubin, jin sun kara ninka dariyar ta ji haushi, ta mike ta fita daga dakin sai Sarham ya mike ya bi bayan ta don ya bata hakuri.
A jikin barandar dakunan ya same ta a tsaye fuskar ta ta hade kamar kunun kanwa. Tana tsaye kawai harde da hannuwa a kirji. Ya lallaba ya tsaya dab da ita shima ya harde nasa hannuwan a kirji irin yadda ta yi. Ya ce.
“Kuluwa, ni fa ba ke nake yiwa dariya ba, labarin da Inna ta ke bayarwa ne ya bani dariya”. Hauwa tayi narai-narai da idanu kiris ya rage ta fashe da kuka, tace “idan makanta abin dariya ce ai bata wuce kan kowa ba, idan gorin ido abun yi ne, ba komai ku cigaba da yi min”. Sarham ya kama baki cikin jin wani iri a ransa yace “kina nan a Kulun ki, Kululu, Kulun Majadun sarka mai rikicin gangan, har gobe baki canza ba, dama Inna ta ce ayi magana cibi ya zama kari. Yanzu saboda Allah ba dama muyi dariya sai ki ce rashin idon ki ake wa gori?
Idanun nan fa mun fi ki son su dawo, ta yaya zamu yi murna da halin larurar da suke ciki? Kawai dai kina ji da rikicinki ne na gangan.
Kullum addu’ar mu shine su dawo da gani kamar na kowa, idan masu dawowa ne, idan kuma ba masu dawowa bane Allah ya sa rashin su ya zama silar kaffara a gare ki da iyayen ki, ya baki aljannar Firdausi a madadinsu”.
Hauwa ta dan saki rai, sai Sarham yace, “Maijiddah, tunda muka hadu bamu gaisa ba, bamu zanta ba, bamu yi fadan namu ba, koda yake yau mun dan taba. Anyway, nayi kewar ki MAIJIDDAH, bayan a baya na zaci bazan taba yin kewar ki ba, tunda baki damu da ni ba”.
Hauwa ta yi murmushi ta ce a ranta,
“kwarai kuwa, don ni dai kam in ba na dauko littafin makaranta ba, sam-sam bana tuno ka, gara-garama a lokutan da kalamanka masu haska min rayuwa ke sawa in tunaka”.
Unfortunately, bata san cewa a fili ta fada ba.
Sai ji tayi Sarham yace cikin rashin jin dadi da sosuwar rai, “I know, ba tun yau ba na sani ai, Inna ce kawata, uwata, kuma ita ta damu dani. Ni din a wurinki ba kowa bane face…”.
Yayi shiru cikin tsananin damuwa da rashin sanin ta yaya zai yi ya kankare wannan tunanin daga zuciyar Hauwa-Kulu? Wanda ba tun yanzu ba ya lura yayi mugun samun muhalli a cikin ranta?
Hauwa tace “kaima da ita kadai ka damu (Innar), daga zuwan ka ai ko la’akari da halin dana ke ciki baka yi ba ka fara tsokanata a kauyen Albasu, wai idona kamar ana soya kosai cikin mai, baka san cewa kukan farin cikin ganin ka nake yi ba, baka san halin dana ke ciki ba a lokacin, don ji nayi kamar Yayana Zulkifilu ya dawo, kamar farin-cikin rayuwa gabadaya ya dawomin, duhun zuciya ya gushemin, haske ya dawo a cikinta”.
Da mamaki da jin dadi a muryarsa Sarham yace “to kiyi hakuri Maijidda, mu ajiye wannan a gefe, I’m happy to be your sourse of happiness, koda wannan kadai yau kin karramani, yanzu inaso ki bani labarin bayan rabo, da rayuwar ku gabadaya daga farkon tafiyata har ranar zuwan ku Albasu gidan mai magani”.
Hauwa ta nisa, kafin tace “dogon labari ne likita, amma mun sha wahala wajen neman na kan mu a tashoshin mota, mun yi girki iri-iri ba hutu tamkar injin girke-girke a kowacce rana daga safe har yamma hakarkarinmu bai hutawa, ba don komi ba sai domin kada mu yi bara. Allah ya sani, ba abinda nake gudu da nakasata irin bara! Alhamdulillah for being alive, and for everything, musamman karatuna na sakandire, wanda (against all odds) sai da Allah yasa na kammala shi.
A kullum inna sare da karatun, saboda wahalar zirga-zirga ta rashin idanu, kalaman ka nake tunawa suke zame min ‘inspiration’, kuma madubin dubawata a rayuwar lalurar dana tsinci kaina.
Kalaman ka likita sunyi tasiri sosai wajen karafafani domin ina matukar jin dadin su a lokutan da na bukacesu, cewa da ka yi “akwai iyawa cikin nakasa”, kuma ka ce min “ba nakasashshe sai kasashshe”. Wadannan jimlolin naka guda biyu su suka zame min food for thought; su suka sa na dage na jure da zuwa makaranta ba ido. ‘Obstacles’ da ‘hindrances’ da ke cikin lalurar makanta duka basu sa na bari ya salwanta ba.
Babu wani abin karaswa cikin labarin namu a bayan tafiyar ka, sai na bacin rai da wahala na zallan zalunci wanda kanin mahaifina ya sanya mu a ciki, a dalilin kwace gidan mu ya rusa shi. Ni ban sani ba ashe tun lokacin batan Baba, Inna ta fara ciwon zuciya, don likitan dazu ya tabbatar min ramin ya dade a zuciyar ta yayi akalla shekaru biyar, tana dai yin cuwuka a tsaitsaye tana kuma kula da shan magungunan gargajiya dake kara mata ‘immunity’, shiyasa bai ci karfin ta da wuri ba, bamu ankara ba sai da ya kayar da ita kasa warwas.
Likita rayuwar da muka yi gabadaya kaji-ka ji….” ta zayyano masa daga farko har karshe har labarin bugeta da Yaya Jamilu yayi da mota ya kuma dage daga baya zai aure ta, wanda duk shi ya janyo musu komai.
“Yanzu ina Jamilun? Me zai aura a wannan kankanuwar yarinyar? Bana jin lokacin ko SS2 kin gama, haba! This is sheer abuse. To ya san abinda Baban nasa yayi muku?”
Sarham ya tambayi Hauwa, (furious in anger), ji yake idon sa idon Jamilu da Babansa Zakari sai ya shake su. Hauwa ta ce.
“Yaya Jamilu ban kara haduwa da shi ba, bamu kara jin duriyar sa ba tun tafiyar sa Delta, kuma bana jin ya san abinda Baba Zakari ya yi wa gidan mu, saboda a lokacin yayi tafiya, ban dai sani ba ko idan ya dawo daga tafiyar da yayi wani ya bashi labari”.
Sarham ya dade kan sa a sunkuye, yana tunanin ta wace hanya zai gayawa Hauwa ya sake gine musu gidan su, da gini irin na zamani? Jira yake a sallami Inna daga asibiti ya dauke su ya maida su gidan su na asali, ya kuma yi karar Baba Zakari kan abinda yayi, ko ba’a yi masa komai ba hukuma ta shiga tsakanin sa da su”.
Sun dade a wajen suna labari shi da Hauwa, irin yadda bai taba jin tayi magana mai tsayin ta yau ba, sai da mamakin sa ya kasa boyuwa yace.
“Maijiddah, ashe dama kina magana haka? Da ni ne ba kya yi? To meyasa Maijidda? Me nayi miki haka da zafi?”
Ya tsareta da ido cikin tuhumar dalili, kai kace kamar tana ganin sa, Hauwa ta rufe ido cikin jin kunya, ta ce “ai don na dade ban ganka bane, daga yau zan rufe bakin ya koma kamar da” Sarham ya lumshe ido kamar tana ganin sa, idonsa a kan zara-zaran ‘yan yatsunta ya ce “a’ah ban yarda ba, a bude shi muyi ta shan hira abinmu, irin ta Yaya da kanwar sa da sukayi kewar juna, kin san ni mai baki ne, mai yawan hira ne, shiyasa tamu ta zo daya nida Inna. Maijiddah ina so in zama babban Yayanki daga yau, wanda kafin kowa ya ji damuwar ki nine mutum na farko da zan ji.
Zan bar miki waya don mu dinga magana don zan koma wajen aikina babu jimawa, na rako matata wankan jego ne, amma mun koma Jeddah da aiki tun da jimawa”.
Hauwa ta fiddo manyan idanun ta cikin mamaki ta ce “likita dama kana da mata?” Ya yi murmushi ya ce “mamakin na menene haka? Amsarki a baya itace, a’ah, na dai aure ta babu jimawa, bayan na kammala karatun dana tafi yi a Jeddah, a can muka hadu, duk da dai ba haduwar