Showing 18001 words to 21000 words out of 45645 words
bai fada ba bai kuma bai doketa ba.
Mama ta shigo da sauri jin kukan Sumayyah, tana tambayar su “me ke faruwa ne haka a falon nan ake kuka har da kururuwa?”
Sarham ya ce cikin kololuwar feeling of disappointment “Mama kin gan su, su duka sun ci amana ta!” Mama ta ce “kada Allah ya nuna mini ranar da zan haifi Da maci amanar dan uwan sa, sun dai yi kuskure wanda ba wanda yake sama da aikata shi, ka yi hakuri Sarham ka yafe musu kaji! Duk da ban san girman laifin ba”.
Sarham ya dubi Surayyah (feeling disappointed) ya ce “Surayyah idan abinda kika yi kyautatawa ne ga zumunci na da ke, na gode. Allah ya saka da alkhairi.
Ke kuma Sumayyah baki yi min laifin komai ba, amma daga yau na san matsayina a wajen ki, na kuma ga ajin da kika ajiye ni, tunda bazaki zame min ‘yar uwar da a bayan raina zata kula da haula ta ko abinda na bari ba”.
Sai ya sa kai ya fita, makwallaton sa har motsi yake don tsananin bacin rai, ba tare da ya tsaya yi wa Mama bayanin laifin da suka yi masa ba.
Mama duk suka saka ta a duhu, ta rasa gane komai, sai da Sumayya ta share hawayenta ta gaya mata komai cikin muryar kuka.
Mama ta kasa tuno mutanen da ake matsalar a kan su, ta san dai ire-iren jama’ar sa ne da baya rabo da kyautatawa, da irin jajibe-jajibensa, amma hakika ta harzuka da abinda Surayyah ta yiwa Yayanta, bata san ko su waye wadanda yake turowa kudin ba duk wata tun daga Jeddah ba, ba kuma tareda ta damu da ta sani ba, amma tunda har ya dauki tsahon shekaru uku yana turo musu kudi duk wata bait aba mantawa ba to masu muhimmanci ne a wajensa, kasancewar ta san halin sa akan son tamakawa mutane da son kyautatawa na kasa da shi da marassa lafiyansa, sai hakan bai zame mata wani sabon abu cikin halayen dan nata Sarham ba, Mama tace.
“Da gaske wannan cin amana ne, kuma zai fi bakanta masa rai ne kasancewar mutane mafiya kusanci da shi ne suka yi masa”, ta dube su cikin fushi ta sake cewa “a duniyar nan in dan uwanka ciki daya bai rike maka amana ya rufa maka asiri ba, in bazaku kashe ku rufe kai da shi ba, ba tareda ko iyayen ku sun ji ba, waye zai yi maka?
Sannnan da wa zaka yarda a duniya, kuma da wa zaka aminta?
Kin yi kuskure Surayyah, ba dan uwa irin naku ake badawa kasa a idanu ba, saboda shi din dan uwa ne har dan uwa guda har da rabi, ko in ce Yayan da babu irin sa, ko don son da yake muku da kulawar sa da kyautayinsa gare ku”.
Surayyah ta gama dukkan nadamar da mutum zai iya, a lokacin da yasan bai kyauta ba aka kuma ankarar dashi. Cikin kuka ta ce.
“Mama don Allah ki bashi hakuri, na tuba na bi Allah na bi shi, zan biya shi duka kudin sa da zarar na fara aiki, dama ban kashe da niyyar bazan biya ba, kawai ya zo ba ‘notice’ dina ne, nayi niyyar in bata ta kai musu kafin lokacin zuwan sa, wallahi zan biya shi”, Mama ta wani harareta ta ce “ta baya ta raggo.
Duk abinda zaki biya shi yanzu bazai karba ba, kuma bazai masa amfanin komai ba. Surayyah an yi bokon banza tunda shi ya koya miki son abin duniya, kayan kwalliyarbanza kayan kwalliyar hofi, saboda Allah da me iyayen ki suka rage ki banda son kyale-kyalen ki na banza da wofi da kika dorawa kan ki tun shigar ki jami’a, da son lallai sai kin hada kafada kin goga da kawaye da suka dauki karyar rayuwa suka dorawa kan su?
Kullum ina nuna miki ‘reality’ akan barin sayen abubuwan nan masu tsada da suka fi karfin aljihun ki ko na iyayen ki, kina ganin kamar ni kaina ban waye ba, tunda bana sayen turare su ‘designer’ sai Humrah sai Oud, har ni zaki nunawa sanin ya kamata akan rayuwar duniya Surayyah? Yaushe aka haifeki har kikayi wayewar??”
Mama tayi ta fada ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, daman tana cike da halin Surayyah din kan irin tsarin rayuwar ta mai tsada, fadan da Sarham bai tsaya ya yi musu ba don bacin rai shi Mama tayi ta yi musu ta wanke Surayyah tas. Wankin babban bargo. Surayya dai sai hakuri take baiwa Mama ganin har tafi Sarham daukar zafi da al’amarin.
Aka ce dan uwa rabin jiki, ganin yadda duk ta muzanta sai ta koma baiwa kanwar ta Sumayyah tausayi, Summy ta ji kamar a maida laifin ya koma kanta, ita a cigaba da yi mata fadan ita kadai, ta koma taya ta suka yi ta baiwa Mama hakuri da rokonta kan ta bashi hakuri in ya dawo, sunyi alkawarin bazasu sake yin kuskure makamancin wannan ba, Sumayyah dai ta ari laifin suka yafa shi tare da ‘yar uwar ta.
**** **** ****
SARHAM
D
a ya fita cikin zafin rai, wata motar Abbansa (Peogeot 504) ya dauka wadda tun saukarsa da ita yake amfani, kasancewar bai kai ga sayen motar kansa ba tun dawowar sa, ya fizgeta a guje ba tareda ya san wajen zuwa ba, yana dai so yayi nesa da gida don shi kansa ya san bai iya fushi ba, baya son ‘yan kannen sa su ga launin fushin sa mara kyau, ana he’s jovial amma in yayi fushi kamar zawayi yake komawa don rashin hakuri, musamman akan Surayyah da baya son wasu halayenta.
Sai ya samu sitiyarin nasa na sarrafa shi, ya dauke shi yayi hanyar titin da zai sada shi da kofar Na’isa. Yana tafe yana gayawa kan sa ya yafewa Surayyah duniya da lahira, ya yafe mata, amma hakika ta ragewa kanta matsayi a idon sa. kuma ‘outing’ din da yayi niyyar fita dasu zuwa Dam, don tayata murnar kammala degree ya gayawa kansa ya fasa.
Duk da Mama ta ce zata bashi hakuri inya dawo, amma hankalin su su duka bai kwanta da fitar sa cikin fushi ba da kuma ganin tsayin lokacin da ya dauka bai dawo gidan ba.
Ya isa kofar Na’isa da yamma lis, ya karya kan motar sa zuwa titin da zai kai shi lokon su Hauwa, yana tafe yana tunane-tunane akan su, ko a wane hali zai same su? Ko Hauwa ta gama makaranatar sakandire yanzu? Ko yaya suke rayuwar haka babu tallafin kowanne namiji? Ko Baban su Malam Bilyaminu ya dawo? Ko yaya idanun Hauwa? Allah Masani! Bai san meyasa zuciyar sa ta damu da al’amarin su ba, take kuma daraja su, yana saka damuwar su a ran sa in ya tuna a hannun sa Hauwa ta karbi shaidar makanta da lasisinta, daga zuwa neman magani. Shi ya san da ace ba shi yayi mata aikin nan ba, da bazai damu ba don an samu mishkila.
Har gobe kuma ya kuma kasa yafewa kan sa a kan makancewar Hauwa, ya ki cire abun a ran sa, duk da ya san kaddararta ce, shima kuma ba yin kansa bane amma har gobe Sarham yana ganin negligence dinsa ne wato (sakacinsa da rashin iya aikin sa), su suka janyo har Hauwa ta kai ga rasa idonta completely.
Haka tunda ya tafi Jiddah yau shekara uku bai taba kasa tuno su ba kullum, har Allah-Allah yake a yi albashi don kawai ya tura musu, ranar Allah dai-dai ce da baya tuna su, tare da yi musu addu’a da fatan alkhairi. Ya san kuma kudin da yake aiko musu daga albashin sa zai ishe su kananan bukatocinsu na yau da kullum da makarantar Hauwa.
Bayan motar Abban sa da ya tuko, shake yake dankam da tsarabar su Inna rankatakaf! Wadanda tun daren jiya ya saka su a mota yana jiran ya samu nutsuwa ya je kofar Na’isa, yayi ido hudu da Innar sa Safiyya, don ba Hauwa yake kewa ba Inna yake kewa. Eh mana, Hauwa da bata son sa kuma take kullace da shi. Hauwa danger Hauwa hukuma.
Har sabuwar waya nokia karama ya sayowa Inna, da alkawarin yanzu in ya koma Jiddah kai tsaye zai ke kiran su. Idan har Hauwa ta kammala sakandire da kyakkyawan sakamako ya fara tunanin bincike akan yiwuwar cigaba da karatun ta a jami’a, idan hakan mai yuwuwa ne.
Zai nemi dai wanda zaiyi ‘coaching’ din sa akan ilmin ‘visual impaired’, ba zai koma Jeddah ba sai ya tabbatar rayuwar su bata da matsala ta zama ‘stable’ kuma Hauwa na kan turba ta tafiya zuzzurfan ilmi.
Wanda shine kadai zai zame mata gata a dukkan rayuwar ta, a matsayin ta na mai nakasar da ake kira mutuwar tsaye.
To amma me? Sai zuwa yake yana dawowa a inda ya san lokon gidan su Inna yake situating, amma baya ganin gidajen da ya sani a wurin sai fili fetal. Da aka zagaye da langa-langa. Ya ilahi! Ko dai yayi batan kai ne? Ko makuwa yayi? ko kuma ya manta hanya ne?
To amma da mamaki ai ace ya mance hanyar gidan su Hauwa, ko shekaru goma yayi baya nan ba uku ba, in dai ba juyewar kwakwalwa ya samu ba ko shafewar tunani wato ‘amnesia’. Kuma dai ga Kofar Na’isan nan dai tana nan bata je koina ba.
Da ya gaji da zuwa da dawowa wato ya gaji da safah da Marwah a cikin mota sai ya fito yayi ta zagaye wajen da kafafun sa, amma ya kasa ganin gidan Malam Bilyaminu, ya kuma tabbatar anan gidan yake, sai ma yaga ‘pure water’ na leda ake bugawa a filin wajen. Kamar an maida wajen kamfanin ruwa leda.
Ya tambayi wani saurayi cikin masu buga ruwan ledan don Allah ko inane gidan Malam Bilyaminu dan Kofar Na’isa? Ya ce da saurayin “kamar na maku, don na jima bana nan”. Saurayin yace shima bako ne a unguwar, amma bari ya hada shi da Malam Isa mai faskare shi da ya dade a unguwar.
Gidan malam Isa ne kawai ba’a rushe ba cikin gidajen wurin don gidan yayi gefe sosai, saurayin ya raka Sarham suka samu Malam Isa a zauren gidan sa yana aikin itacen sayarwar sa, ya yiwa Malam Isa bayanin wanda Sarham ake nema ko ya san shi? Wai gidan Malam Bilyaminu.
Malam Isa ya bar abinda yake yi ya juyo ga Sarham sukayi musabiha, sai ya bashi wajen zama kan buzun sallahr sa yace ya zauna, da ya tambaye shi ko wa yake nema a gidan Malam Bilyaminu? Sarham yace.
“Innar Hauwa”.
Sai Malam Isa ya tambayi Sarham “kana da alaqa da Innar Hauwa ne?” Sarham yayi dan jim! Kafin yace “eh, amma na dade bana kasar, ina fatan ba wani abu ne ya faru da su ba?”
Malam Isa ya nisa yace, “eh toh, samari, ai Innar Hauwa ta gamu da sharrin wani azzalumin kanin miji, ya sayar da gidansu, rana daya muka ga an zo ana rushe gidan, aka maida wurin wajen hayar neman kudi kala-kala, na so ta zauna mu je kotu a kwato musu hakkin su ni da sauran makwabtan su, kasancewar a gaban mu Zakari ya sayarwa da dan uwan sa gidannan aka raba rigima tun a lokacin a gaban marigayi mai unguwa, amma matar nan ta ki tsayawa, ta gudu daga gidannan bamu sani ba, yau kusan shekara uku zancen nan da nake maka, bamu kara jin duriyar su ba ita da ‘yar ta Hauwa-Kulu”.
Sarham ya ji idon sa har rawa yake banda fatar idon dake raurawa itama, da kyar ya iya yace wanene kanin mijin nata? Ya ce.
“Zakari sunan sa, don kawai dan sa ya zo yace zai auri Hauwa-Kulu, shine ya sayar da gidan don ya kore su ko ince yasa aka rushe shi, to ya ci galaba kam don daga ranar da aka zo aka rushe gidan su basu kara waiwayar kofar Na’isa ba, kuma ba wanda ya kara jin duriyar su, ina tabbatar maka bazasu zauna a Kano ba yadda suka fita a tagayyare, wutsiya zage, kuma cikin mummunan bacin rai.
Jifa aka dingayi da komai nasu. Tausayi yasa na tattara tumakin ta da akuyoyin ta na kado su gida na, na hada na nawa na cigaba da kiwata mata, muje in nuna maka su cikin shekaru uku gasunan suna ta hayayyafa ban san ya zan yi da su ba”.
Sarham ya rasa a halin da yake ciki tsakanin tashin hankali da gigicewa, yace da Malam Isa “basu da wasu ‘yan uwa da zasu iya zuwa wajen su?” Malam Isa yace “eh, toh, ai dukkan su ‘yan cikin Badalar nan ne a sanin da muka yi musu, in ma suna da su, to mu bamu san su ba, basu da wasu ‘yan uwa da bamu sani ba, dangi kam sun kare ai, kuma bana jin a zuciya irin ta Innar Hauwa zata yarda ta rabi wani nata in ma tana da shi.
Tun tali-tali tanada wani irin hali, tafi gane rayuwa ta tsayuwa akan kafafun ta fiyeda ta rabu da wani ya taimaka mata, har kuwa bayan batan mijinta, bata taba neman taimakon kowa ba”.
Sarham yace “shin a ina wannan Zakari din yake?”
Zai so kwarai yayi ido hudu da wannan Zakarin, don kwatarwa su Inna hakkin su, zai so kwarai yayi shari’ah da shi, daganan har kotun daga ke sai Allah ya isa! Domin ya kwatowa Inna hakkin ta, a daure shi har sai igiya ta yi rara, amma Malam Isa ya gyara murya ya kuma gyara zama, yace masa “ka manta da Zakari kawai, ka nemo su Hauwa din shine mafi a’ala, ganin Zakari bazai kare ka da komai ba sai karin bacin rai, don zai iya yi maka mummunan bita da kulli, idan ya gano su Safiya suna da wani gatan bayan shi a duniya.
Ai sanin cewa basu da kowa da zai tsaya musu ne yasa yayi musu haka!”.
Sarham yayi shiru, can yace Baba ina so in sake saye filin wajen ne, ina nufin filin gidan nasu daga hannun wadanda suka saya”. Malam Isa yace, ai hakkin mallakar filin ya bar hannun Zakari tuntuni, wannan mai kamfanin ruwan shi ke da wajen yanzu, kana iya tuntubarsa ko zai sayar maka, amma lallai sai ka nunnunka masa kudi”.
Tare suka je har gidan mai kamfanin ruwan ledan da ya kafa rumfa a filin gidansu Hauwa yana sana’ar ruwa, suka gaisa, Sarham yana hadiye hawayen sa yace, so yake ya sayar masa da filin wajen, inyaso ya yanka masa kudin ko nawa ne zai biya shi, ya bashi takardun mallakar kangonnan.
Hakan kuwa aka yi, da mutumin ya ga kudi ya amince, ya yanka kudin da yaga dama Sarham ba musu yace gobe zai kawo masa su (in cash) ya karbi takardun wurin bisa idanun shaidu kwarara da sabon mai unguwa.
Bayan ya bar Kofar Na’isa kasa komawa gida yayi, ya kuma kasa tuka motar, ya koma gefen titi ya kashe motar ya kifa kansa a kan sityarin, yana tuno fuskar HAUWA-KULU da kyawawan manyan idanun ta da ya nakasta mata su bisa kuskure, da kuma murmushin Innar ta. Daga baya ya ja motar ba tareda ya san wurin zuwa ba, haka yayi ta yawo kwararo-kwararo titi-titi a cikin BADALOLIN KANO, ya taho tun daga Kofar Na’isa, ya isa Kofar Gadon kaya, ya bi ta kofar Dukawuya, ya bulla ta kofar Kabuga, daga can ya karya kan motar yayi kofar Kansakali, ya taho har Kofar Ruwa, bai ga ko mai kama da Inna ko diyarta Hauwa ba, ya dawo baya ta cikin gari ya bulla ta Sabuwar Kofa, kafin ya isa kofar Nassarawa ya dawo da baya ya isa kofar Dan agundi yana ta fatan Allah yasa ya ga Inna da Hauwa koda a hanya ne, amma har duhu ya baibaye sararin samaniya, wanda yasa ya daina shaida fuskokin mutane, kuma man motarsa ya kusa kafewa, ko mai kama da su bai gani ba, duk kuwa da irin kallon kurillar da yake yiwa mata da musaki bisa tituna da Kofofin Kano, da cikin unguwannin Badala.
Allah sarki Dr. Sarham! Kafin ya koma gida har rama yayi, yayi zuru-zuru yayi dan wuya sabida yunwa da damuwa da gajiya da bacin rai. Kamar ba sabon ango ba, na Madinah bada kanka a sare! Ya koma gida a jigace, wajen karfe goma na dare, amma sai ya kasa zaman falon duk kuwa da cewa ya gansu a zazzaune duk zaman jiran dawowar sa suke yi har Abba, domin a bashi hakurin laifin Surayyah gareshi.
Ganin yana nema wucewa dakin sa bayan ya gaida Abba da Mama, ba tare da ya ko zauna an yi hira yadda aka saba ba. Abba ya dakatar da shi, ta hanyar bashi kujera da hannun sa ya ce ya zauna, Sarham ya tsaya a tsaye kamar mai ciwon kafa, sai Abba yace,
“lelen Abba daga ina kake haka, kamar an maka dukan tsiya? Ka gan ka kuwa?”.
Sarham bai yi aune ba yaji wata irin hajijiya na neman kayar dashi saboda yunwa da gajiya, ba shiri ya lalubi kujerar