Showing 27001 words to 30000 words out of 45645 words
nata mijin daban ne a fannin shimfidarsa da matar sa, ta iya kalamai masu sanyi da sanyaya zuciyar miji a duk halin da yake ciki, ta kalmashe shi da iya girki na zamani, da iya kula da shi a shimfida, ta kware wajen taya shi kula da tsaftar jikin sa, kula da kannen sa wadanda ta gama lura baya hada kaunar su da komai a ransa saboda irin ‘upbringing’ din da iyayen su suka yi musu kenan na kaunar junan su da hadin kai a junansu, kasancewar basu da yawa a wurin iyayen su.
Madinah irin matan nan ne masu nacin shiga (educational programs) da ake yi a Saudi-Arabia, duk wasu programs irin na (marriage coaches) na mata musulmi masu burin karawa juna sani akan ilmin zaman aure da zamantakewa da ake yi a kasa mai tsarki ko na likitanci komai nisan gari zaka samu Dr. Madinah na kokari ta halarta, wannan ya karawa Madina (exposure) akan ilmin data ke da shi.
Domin bata tsaya ga bangaren karatunta na likitanci kadai ba, a’ah, tana kara fadada ilmin ta a kan zamantakewar aure da zamantakewar al’umma, tana da yawan rubuce-rubuce (wadanda bata wallafawa) akan sha’anin mata da aure musamman da bata fara aiki da kowanne asibiti ba a lokacin, kullum cikin bincike take a yanar gizo kan yadda zata kara inganta kimar ta a gidan auren ta.
Ko wata uku ba’a rufa ba da auren su, Madinah ta fahimci yaron ciki na wata guda a tare da ita.
Ciki irin silent dinnan (mara laulayin nan), cikin data kira da suna DAN SO. Yo dan ta da Sarham ai dole ta kira shi DAN SO wanda tarihin soyayyar shekara goma ne ya samar da shi ‘sharp-sharp’ kamar a dokin kofa tayi tuntube da cikin sa. Koda cikin ya soma girma ya shiga watanni biyar bai hana ta komai daga harkokin ta ba, amma yasa ta fasa karbar tayin aikin da ta samu da Dr. Siddiqah hospital, domin ta zauna a gida ‘fully’ ta raini dan So, ta kuma baiwa ubansa kulawar da zata gusar da hankalin sa daga kan sauran mata.
Addu’ar ta kullum Allah yasa abinda ke cikin ta namiji ne, tana fatan yayo kamannin Sarham, da halayen sa da kwakwalwar sa. cikin ‘yan watannin da ta kasance kullum a gida Madinah ta kara kaimi wajen ganin ta samarwa kanta kyakkyawan matsugunni a zuciyar Sarham, ko dama matsayin ta mai girman ne, to ta kara girman matsayinta ta hanyar kula da shi da bukatocin sa, ta tsare masa cikin sa, ta kware wajen iya girke-giren zamani dana larabawa, ta mallakawa Sarham duk wata kauna, soyayya, kulawa da yardar da diya mace kan yi wa namiji.
‘Yan gidan su Madinah na yawan zuwa gidanta, haka Daddy din ta da kan sa sai ya dauko Hajjah Ramlah a gaban mota ya tuko da kansa su zo ganin ta, musamman da cikin ta ya soma girma, dokin su ga haihuwar Madinah kamar a kan ta zasu fara samun jika bayan kuwa jikokin su sun kai goma daga yayyen Madinah, don cikinsu Usman ne kawai bai yi aure ba.
Amma a wajen Hajja Ramlah da Dr. Sorondiki na auta Madinah na musamman ne tunda ko cikin ‘ya’yan su ita din ta musamman ce. Don haka sayayya sosai ake ana tarawa don jiran haihuwar.
Cikin Madinah na da watanni takwas Hajjah Ramlah tace a dawo da ita Sorondinki ta haihu a can, ita bazata iya zamar mata jego ba (zaman dabaro), da farko Sarham yace bai yarda ba amma Mama ma sai tace a kai ta, ai haihuwar fari ce, normally a wancan lokacin ana zuwa wankan gida. Don haka bada son ransa ba ya fara ma Madinah shirin tahowa haihuwa, don dama sun riga sun gama sayayyar haihuwar su tuntuni, shi yayi, su Daddy sun yi, Sumayyah ma ta tara kayan baby da yawa iya karfin ta ta bashi da zasu taho, koda bata yin Madina tana maraba da isowar dan ta ko ‘yar ta daga Bhaiya.
Sarham yana cike da damuwar yadda zai rayu a gidan su shi kadai ba tareda Madinah ba.
Shi ya kai Madinah gun kakanninta, weekend kawai ya samu yi tare da su Mama ya koma Jeddah.
Tafiyarsa da sati uku Madinah ta haihu, ta haifi lafiyayyar diyar ta mace, mai kama da ita, amma kalar fatar jikin da bafulatanar sumar ‘yan Shanono yala-yala ta Sarham ce, Surayyah ce ta fara kiran sa tayi masa albishir, cike da doki. Sannan Mama ma ta kirashi don duk suna asibiti tareda ita aka yi haihuwar, Daddyn Madinah tuni ya fara shirin tahowa Kano tarbar amaryarsa da aka haifa ranar Laraba, “Laraba Tabawa Ranar Sa’a” inji Haj. Kulu. Tana mai jan hancin yarinyar dan sirit da shi.
Ranar da Daddyn Madinah da Sarham suka sauka a Kano kwana shidda cif da haihuwar, da yammacin ranar ya je gidan su Madinah a Sorondinki ya dauki yarinyar yana kallon ta da wani irin paternal love, kafin Madinah ta fito daga daki, ta sha ado, kamar ba itace ta dawo daga kofar lahira kwana shidda a baya ba, Sarham ya daga kai yana duban ta da wani irin murmushi, amma sai me? Sai kwakwalwar sa ta gaya masa cewa kawai ya saka ma baby din Madinah suna HAUWA’U ya dinga kiranta da Maijiddah, in the memory of his lost blind sister (miskiniya KULU).
Madinah ta fito ta same shi da yarinyar a hannu amma yayi nisa cikin tunani, yana murmushi shikadai, sai da ta sakala hannayen ta a wuyan sa ya dawo hayyacin sa, ya sumbaci goshin yarinyar itama Madinah ya sumbaci goshin ta, Madinah duk ta kumbure a hakan ma ta dan sace, “an sha gumurzun haihuwa an zama uwa”, da ya dube ta yaga yadda hancin ta da bakin ta suka bubbude leben ya zama tafkeke saiya fashe da dariya.
Madinah ta san me yake yi wa dariyar don yanzu itama ta gama kallon kan ta a mudubi kamar ta fashe da kuka, amma wannan yasa ta kara kaunar Hajjah Ramlah, ko ba komai ta ga yadda ta kawo ta duniya ba wasa bane, ta kuma kara girmama lamarin ta fiye da na Daddyn ta. Yo Sarham yana can Jeddah cikin ofishin sa yana shan rabar AC tana labour room tana gumurzu kamar ta sheka barzahu.
Kwafa tayi ta cuno bakin gaba tace “ai na gama daga wannan babu kari” Sarham ya sake darawa ya ce “ah haba Madam Dr. yaushe aka yi daren garin zai waye? Yanzu muka fara saka kwallo a raga, sai kin yi dozen Hajjaju wannan ta ladan noma ce, ki rubuta ki ajiye na gaya miki” ya hada su ita da jaririyar ya rungume su, yayi musu kyakkyawar sumba a bakunan su, sannan ya yi mata sannu da sauka, ya kuma saka mata albarka, daga bisani yace.
“Allah ya raya mana Nana Hauwa’u, AKA Kuluwa, Kulun Majadun”.
Madinah ta zaro ido ta ce “sunan tsofaffi zaka saka mata? Ka rufa min asiri don Allah ka sa mata ko sunan Sumayyah mana”, yace “Sumayyah ce ta taya ni haihuwar ta? ko sanda nake shan yakushi da cizo a Riyadh Sumayyah ta zo ta taimake ni?” Madinah ta rufe ido cikin jin kunya tace “kai don Allah SARHAM!” Yace, “of course, sunan da na ga yayi min daidai kenan, Hauwa’u, Hauwah uwar al’ummar duniya, Hauwa uwar matan duniya bakidaya, uwar bil adama”.
Sai da ya kama hanya a mota zai koma gida yana cikin matsanancin nishadi, akwai contentment mai yawa on becoming a father, ya tambayi kan sa “why HAUWA? Me yasa sai Hauwa zai sakawa ‘yar sa? Bayan in don yake tuna su ne, sunan Inna ya kamata ya saka wato Safiyyah?
Murmushi yayi, a lokacin yazo zai wuce ta kofar Na’isa, yana kallon kofar wadda aka sake ginewa aka sabuntata, bayan hawan sabuwar gwamnati, sai kawai ya tuna da Malam Isa, kawai sai ya karya kan motar sa ya nufi gidan Malam Isa mutumin sa.
Tun daga nesa ya hango ginin da yasa ayi na gidan su Hauwa ya kammala, gini ya fito sosai na zamani, amma ba’ayi fenti ba tukunna.
A zaure ya tadda Malam Isa yana shirya itacensa, ya yi masa sallama, tun daga nesa da Mal. Isa ya hango shi sai ya saki hamdala, Sarham na isowa tun kafin su gaisa yace “Dan nan kana lafiya? Ina ka shiga shekara guda da watanni ina neman ka? Tuntuni nake ta jiran zuwan ka, gashi ban san gidan ku ba, aikin gini tuni an kammala, wayar da ka bani kuma na kasa magana da ita tun lokacin da ta fada ruwan wanka na ta lalace, na sunkuya sai ta fado daga aljihuna ta shige bokitin ruwan wanka, shirun ka yayi yawa baka leko ni ba, in ce ko dai lafiya? Kusan shekara da rabi kenan ban ji daga gareka ba.
Tun bayan tafiyar ka da kadan nake ta son in yi magana da kai abu ya faskara, in labarta maka abinda ya faru.
Wato cikin ikon Allah kwanaki Mai kosai (matar sa) ta je tashar Kano line zata hau motar Zaria ta ce min ta ga wata mata kamar Innar Hauwa tana sayar da abinci a tashar, amma bata yi mata magana ba ta fasa tafiya Zaria tazo ta gaya min, don ta san irin neman da mukeyi mata. A take na bar abinda nake yi na bita muka je amma bamu same ta ba, sai wasu mata guda biyu a wajen dake yi mata aiki, muka tambaye su ko anan Innar Hauwa take, tana da ‘ya makauniya, suka tabbatar mana anan take sana’ar ta saidai ba kullum take zuwa ba yanzu, don bata da lafiya, su suke rika mata aikin yanzu, amma tabbas bamu ga Hauwa a wajen ba.
Wallahi tun lokacin nake so in gaya maka na rasa hanyar isa gare ka, ni kuma ban kara komawa tashar ba har yau, don a washegarin ranar Sunusi dan waje na ya zo ya tafi damu Ikko, can inda yake sana’ar sa, mun jima bamu dawo ba sai jiyan nan muka dawo nida Maikosai”.
Sarham bai cika katse mutum kafin ya kai aya ba, amma hakika yau ya gundura da dogon bayanin Malam Isa, kawai ya ce masa ya ga Innar Hauwa mana ‘short and simple!’ Mikewa tsaye yayi jikin sa yana dan tsuma, yace.
“Sako takalmanka Malam Isa mu je ka raka ni inda ka gan su suna sayar da abinci din”.
Malam Isa ya ce” ai ka bari ka fara duba ginin daka bar min amanar aikin sa ko? Kafin mu je neman nasu, tunda takamaimai bamu sani ba ko har yanzu suna can” Sarham ya kufula, kamar ya kaiwa Malam Isa naushi, don ji yake kamar yayi fiffike ya tafi shikadai.
Malam Isa ya ce “to tunda naga ranka ya baci, bari to in kira Halilu ya zo ya zauna min akan itacen nan, in yaso in muka yi la’asar sai muyi maza mu tafi”. Kawai sai Sarham ya samu kansa da ce masa “ai nayi sallah kafin na zo don Allah Malam Isa, ka daina ja min rai, bani da hakuri wani lokacin kamar zawayi nake”.
Malam Isa yayi dariya yace “ai wallahi sai ka jira ni na yi tawa sallahr, na kuma kora dan farau-farau a cikina, baka ji shi ba kamar bakin akuya tun dazu sai kururuwa yake”.
Sarham ya koma kasa ya zauna, dabas! Kamar kayan wanki, dole ya jira Malam Isa yayi alwallah a gefe ya hau buzunsa ya tada sallah, ya gama ya jawo kwanon sha a rufe ya sha farau-farau din sa ya koshi, sannan ya dubi Sarham wanda ya kai kololuwa wajen hadiye fushi, Malam Isa yayi dariya yace “irin wannan zama a kasa haka duk ka bata farar shaddar ka, wai ni ko son Kulu kake yi ne, don itama haka take da kyau tubarakallah kamar ka, koda idanun suka makance sai suka kara zame mata gwanin kyau” Sarham bai tanka ba don bacin ran bata masa lokaci da yake yi, yace
“in ka gama muje ko Malam Isa”. Yayi gaba ya bar shi yana masa dariyar shegantaka wai matuka zai dace da Kulu, don idan ta yi fushi haka fuskarta take komawa kamar balam-balam yadda ya koma dinnan”.
Sarham yayi masa banza. Ya budewa Malam Isa gaban mota ya shiga ya rufe ya zagaya shima ya shiga, Sarham ya wani irin juya sityarin a guje da hannu daya saura kadan hular Malam Isa ta fado, da haka ya bar kofar Na’isa, suka hau titi sambal.
Malam Isa da yaji sanyin AC ta ratsa shi sai ya hau sakin zance ba kai ba gindi, ya ce “na so hada Kulu da Sunusi, tun tana yarinya, na gayawa Malam Bilyaminu kuduri na, sai cewa yayi “shi yafi so ‘yar sa Kulu ta je makaranta, baya son auren wurin nan da muke yi wa yara, ka ga yanzu da ya barta ta auri Sunusi, da ta tara yara sun kai biyar, don bana tantama Innar ta ma irin sa ce shiyasa suke zaune lafiya baka taba jin kansu, su dai makaranta-makaranta kamar goyon Mungu Park, don har bayan data makance wallahi mutanen nan basu raba ta da boko ba, haka muka ga sun samar mata dan jagora kullum sai ta je, ban taba ganin masifar son boko irin na Innar Kulu ba, bayan ita ko a zaure bata taba zama da sunan karatun bokon ba”.
Sarham ya juya kan mota cikin kwarewar tuki suka shiga tashar Kano line, ko tanka masa bai yi ba yana mamakin surutu maras ma’ana irin na Malam Isa, fadi ba’a tambaye ka ba, da alama bashi da matsala a rayuwarsa sai ta saida itacen sa.
Malam isa ya wuce gaba kuma har zuwa lokacin bakin sa bai yi shiru ba, yana gaya masa shi ya san dama Innar Hauwa bazata zauna babu sana’a ba, musamman ta abinci, don aljanunta na girki da tsaftane. In ta fara girki duk gidan sa sai miyau ya tsinkewa kowa, saboda kamshin girkin ta, yanzu ma ashe shiyasa ta zabi sana’ar abinci, Malam Isa ya kara da cewa Sarham,
“to Allah yasa ba’a tashar suke kwana ba, ko don ‘yar makauniyar nan Hauwa-Kulu, kada mazan tasha su dinga yi mata dan kira”.
“A’uzubillah!”
Sarham ya fada a zuciyar sa, lokacin sun kawo kofar rumfar abincin Inna mata biyu da dattijuwa daya suna ta kula da kwastomomi daya na zuba abincin in anzo saya, sukayi musu sallama, suka amsa suna tambayar su “me za’a zuba musu?” Kai tsaye Malam Isa ya ce nawa kwanon shinkafa da wake da miya da nama?
Sarham yayi masa kallon takaici ya ce “Malam Isa abinda ya kawo mu kenan?” ya ce “au, yi hakuri na manta ne, ‘yammata Innar Hauwa-Kulu muke nema”.
Dattijuwar mai zuzzuba abinci ce ta basu amsa. “Ayyah ai Innar Hauwa jiki ya ki dadi, yau wata guda kenan bata zo shagon nan ba, na ji ance ma bata gari, wani makwabcin su ya kai ta gidan mai maganin gargajiya na ‘ciwon zuciya’, a can wani kauye wai Albasu, don Innar Hauwa sam-sam ta ki zaman asibiti.
Allah ne yayi Innar Hauwa na da nisan kwana da yanzu wani zancen ake akan jinyar ta ba wannan ba”.
Sarham yace cikin yanayina gigicewa “na roke ki da Allah da Manzon sa ki raka ni gidan nata yanzunnan”.
Numfashin sa har gwamuwa yake tsabar yadda ya saka Innar da son ganin su a ransa, dama tace watakila bazasu kara ganawa ba, watakila sallamar su kenan, Allah ya gani yayi duk iya kokarin sa a kan ya san halin da suke ciki a wancan zuwan nasa Allah bai yi sun hadu ba.
Matar ta sallami kwastomomi sannan ta baiwa ‘yammatan sallahun abinda zasu yi mata kan ta dawo, daga nan ta bi bayan Sarham da Malam Isa zuwa mota.
Suna tafe tana basu labarin ai Innar Hauwa ta dade a kwance, watakila tayi shekara tana jinya, shagon ma yanzu ya zama nata.
Don dama haya muke kamawa, a da ina mata aiki ne da ta kwanta ta bar sana’ar sai nikuma na kama rumfar hayar, ba don ‘yar ta makauniyar nan mai kokari ba da tuni Innar Hauwa babu, da tuni ta kashe kanta da ciwo a gida, don bata son maganin asibiti.
Sarham ko magana ya kasa, yana jin ta ita da Malam Isa suna ta maganar kin asibiti irin na Innar Hauwa, yace ai tun sanin da yayi mata a haka take da akidarta ta amanna da maganin gargajiya.
Malam Isa yace “kuma fa akan kin asibiti ne har idon Hauwa ya mutu da hakiya, ni nan ba yadda ban yi da ita ba akan ta kai ta asibiti tun yana apolon sa, sai da ta ga ‘yar ta gama makancewa sannan ta kaita, a lokacin aka ce ido ya mutu, yadda suka je haka suka dawo.
Matar na nunawa Sarham hanya har suka isa wani dan mitsitsin gida a wata unguwa can ciki, kamar duk rabin unguwar kwatami ne, kasancewar unguwa ce ta masu karamin karfi sosai. Amma gidan nata sai suka same shi a kulle.
Sarham kamar ya dora hannu aka yayi kuka, don matuka ya saka ran sa da ganin