Showing 39001 words to 42000 words out of 45645 words
ninkuwa, ta ji yaron ya kara kwanta mata a rai, wato ba ita kadai ba, ba ‘yar ta kadai ba, hatta dabbobin ta ababen kulawa da darajjawa ne a gare shi. Ya Allah! Da me zata biya wannan bawan nasa banda addu’ar alkhairi mara yankewa gareshi, da iyayen da suka kawo shi duniya da zuri’ar sa???
Sukayi sallama ya tafi, ta koma gida tana labartawa Hauwa abinda ya faru a gidan Malam Isa da zauren su. Hauwa tafi Inna fusata, tace zata je ta tadda Talatu Maikosai ta gaya mata ba abinda zai kawo su gidan ta koda zasu koma kwana a kan kwalbati in sha Allahu.
Inna ta hana ta tace “tura mata aniyarta mutuncin Malam Isan zaki duba, na gaya miki ashe dabbobina duka suna garken sa yana kiwata mini har yau”. Wannan ne ya dan sanyaya ran Hauwa ta daina jin haushin Malam Isa amma sosai ta shaka da Maikosai.
**** ***** *****
RACE COURSE, KANO
A
wajen kallon Polo na Dawakai wato a filin sukuwa (Race Course) dake unguwar Nassarawa, Salele ya ga Jamil Zakari a matsayin wanda ya lashe kofin gasar dawakai (sukuwa) wanda akayi a ranar, dama dai Jamilu kwararren dan Polo ne, sun dade suna haduwa da Salele a wurare mabanbanta na tseren Dawakai, suna gaisawa, don ya san shi tun a jinyar da Hauwa tayi, sanda ya kadeta da mota.
Yau da Jamil Zakari ya lashe kofi Salele ya shiga sahun samari masu kutsawa suna gaisawa da Jamil Zakari Dan Agundi, Salele yana cikin samari ‘yan kallo masu cike da fata da burin watarana su zama manyan ‘yan Polo kamar Jamil Zakari Dan Agundi.
An fara watsewa kenan Jamilu ya shiga farar motar sa kirar (kia picanto) zai tafi sai ya hango Salele yana ‘waiving’ dinsa daga nesa wato yana ta dago masa hannu, har ya kunna motar ya dakata har Salele ya iso da gudu yana haki yana dariya. Jamilu ya fiddo gudar naira dari ya baiwa Salele, wadda a yanzu zata yi kimar kamar ace naira dubu daya. Salele don murna bai san lokacin da ya hau barin zance ba.
“Yaushe zaka zo gidan su Innar Hauwa ne? Sun dawo bada jimawa ba, sun gine gidan su ya koma sabo dal, sun tare tuntuni, jiya ma Innar Hauwa ta shiga gun Innata sun gaisa har Innata ta zo gidan ta yiwa Hauwa kitso”.
Jamilu yayi sakare! Yana sauraron Salele, kafin ya ji zuciyar sa ta harba, tsohon mikin son Hauwa-Kulu da yake kwana yake tashi da shi ya motsa kansa a kasan ransa, bai san sanda yace da Salele ya shigo gaban motarsa su je ba.
Salele ya kame a gaban mota suka dauki hanyar Kofar Na’isa.
Inna da Hauwa a tsakar gida, Inna na tankaden garin tuwo Hauwa na sallar la’asar akan dardumar sallah anan tsakar gidan su mai yalwa da sanyin sabon siminti, saidai yanzu babu shukokin su na Umbrella da bishiyar dalbejiya, don haka basu fiya zama a tsakar gidan da rana ba sai da yamma irin haka ko da daddare.
Sai sallamar Salele suka ji, yace Inna kuna da bako” Inna da yake ta san Sarham zai zo sai tace “gidan bakon sa ne da zai tsaya a waje ya turo ka? Ko ba sallama yake da kansa ya shigo ba? Yau nake ganin sabon salo banbarakwai wai namiji da suna Hajara, kace ya shigo, kuma daga yau kada ya kara aikomin yaro idan yazo, shi da gidan su?”
Salele ya koma yace da Jamilu Inna tace ya shiga.
Inna da Hauwa sai ganin Jamilu Zakari suka yi a kan su, yayi sallama kamar an jefo shi. Ya shigo tsakar gidan su cikin kyakkyawar shiga ta hawan Polo.
Idanun sa akan Hauwa ya hau sakin Hamdalah a fili kafin ya zube gaban Inna kamar mai neman gafara. Zai fara gaisheta Inna ta ce “tsaya-tsaya, wa nake gani kamar Jamilu? Wai dama kai ne ka aiko Salele?” yace “ni ne Inna” tace “to sawunka a likkafa Jamilu ka juya ka koma inda ka fito, kafin ka janyo min tijara, yau ko gaisuwa babu tsakanin mu wallahi ka ji na rantse ka tashi ka fice mana daga gida, kada ka kara zuwa balle ka janyo min bacin rai Ina fama da ciwon zuciya, zuciyata tayi rauni kuma bata da lafiya bazata iya daukar bakin cikin ubanka ba”.
Inna ta soma hawaye, tana rokon Jamilu ya tafi. Tun ba'a kaiwa Zakari labarin an ganshi a gidansu ba. Jamilu ya mike ba shiru, yana kallon Hauwa da wani sabon so a cikin idanunsa, musamman da yaga ta kara girma tayi wani irin kyau ta yi bulbul da ita, datar ta tayi sumul. Likita Sarham ya tsaya mata da shan (freshmilk) wato danyar madara tana Nan fal firinjinta tun dawowarsu ita take daddaka don bata iya cin abinci sosai.
Jikin sa yana rawa ya soma ja da baya. Tace “ko a lahira wani kan ci albarkacin wani, albarkacin ka Zakari ya ci ban yi karar sa hukuma ta kwatar min hakkina da tozarcin da yayi min a kan ka ba.
Don haka tun muna shaida juna muna kuma ganin sauran mutuncin juna to ka fita daga inda muke”.
Jamilu ya juya a hankali ya fice, saida ya tsaya a zaure ya share zufa da hawaye, shi ya san da gaske yake son Hauwa, son da yake mata ba shi ya dorawa kansa ba Allah ne. Saboda ita har yau ya kasa yin aure, alhalin ba abinda bai mallaka ba na rufin asiri a rayuwar sa.
Daga nan gidan su Inna gidan Hajiyar sa ya wuce, ya kafa mata kahon zuka kan taje ta baiwa Inna hakuri, kada ta hukunta shi da laifin da ba nashi ba. Hajiya Rumanatu na jin an ga su Inna ta dauki mayafin ta tace su je ya kaita. Don dama zaman Jamilu har yau ba aure ya dameta.
A mota Jamilu ya zauna, bayan Hajiyarsa ta shiga gidan, ya kifa kai a kan sitiyari ya rasa inda zai sa kansa da damuwa. Bai san yana son Hauwa bama sai yanzu, data kara girma ta zama cikakkiyar budurwa komai ya kai ya kawo. Hajiyarsa ta shige gidan da sallama.
Inna sai ganin Haj. Rumanatu tayi tayi sallama, Inna ta amsa fuska ba yabo ba Kuma fallasa don ta gaji da nacin Jamilu da uwarsa.
Inna ta yiwa kawarta tun ta kuruciya wato Rumanatu tarba ta mutunci, irin ta tsofaffin kawaye, bayan sun gaisa kafin Hajiya Ruma tace komai Inna ta hau rokon ta kan ta raba Jamilu da zuwa inda suke, ya rabu da Hauwa. Tace, “ku yi hakuri, ni babu wani aure da zan yi wa Hauwa-Kulu fau-fau, balle na dauketa da hannuna na kaita cikin zuri’ar Zakari a hallakamin ita da niyya sabida ‘yan ubanci irin nasa, muddin Zakari yaji labarin Jamilu na zuwa wallahi zai juyo da rashin mutuncin sa kan mu”.
Iyayen suna can dakin Inna suna zantawa suna kuma fahimtar juna, Haj. Rumanatu na mai gamsuwa da hujjojin Inna akan bazata iya aurar da Hauwa ba, ba ga Jamilu kadai ba har ga kowanne namiji ma. A lokacin Salele yazo zai wuce, sai Jamilu ya roke shi ya sadada a hankali don Allah ya kira masa Hauwa su gaisa.
Nan da nan Salele yabi umarnin ubangidan sa ya je yace da Hauwa tazo ana kiranta za’a bata sako, tace a baiwa Inna mana! Yace tana da bakuwa ne sun kule suna sirri. Haka ya kalallameta ta taso ta tako da hijab mai hannu har kasa a jikin ta zuwa soron su.
Sai ta ji muryar Yayan ta Jamilu ya ce “Hauwa!” Ya saki ajiyar zuciya ya sake cewa, “Hauwa nine Jamilu, ni nace Salele ya kira ki, Hauwa ina kuka tafi duk tsayin shekarun nan kusan uku sai dawowa nayi daga Delta na nemeku na rasa? Ko kinsan har yau ban yi aure ba ina tsumayin dawowar ki Hauwa?”
Hauwa ta dan waiga kamar me tsoron ko Inna na wajen, tace “Yaya Jamilu ne da gaske?” “Nine Hauwa’u, I missed you so much, and I truly love you kin sani Hauwa”. Hauwa ta ji duk ta rikice, ta kasa cewa komai domin maganar sa ta yau ta mata gingiringin, ta mata nauyi, rana ta farko da wani da namiji ya furta mata kalmar so da bakinsa da nata, taji kunya har kasan ranta, Jamilu yace.
“Ki bani dama don Allah Hauwa, in turo magabatana gun Inna, in sha Allahu zamu yi aure ko a boye ne in ya so mu bar Kano gabadaya ba tareda Babana ya sani ba, ina mai baki hakuri kan abinda ya faru, na ji komai bayan dawowata kuma ba inda ban neme ku ba cikin Kano da wajen ta ban samu ko wanda yace ya san inda kuke ba.
A kan ki Hauwa Babana ya kusa tsine mini, Inna kua ta kasa gane karfin son da nake miki ba irin wand azan iya hakura bane, don Allah Hauwa ki manta da komai, ki duba ‘yan uwantakar dake tsakanin mu, mu yi auren mu cikin alfarmar zumunci da kaunar juna, dama Bankinmu zasu yimin transfer kwanannan zuwa Ikeja, in yaso sai mu koma can”.
Hauwa ta rasa abinda zata ce, domin Jamilu ya matukar bata tausayi, ya tafi da imaninta, ya kuma gama saye zuciyarta da wannan kauna da ya nuna mata, tayi shiru kawai tana sauraron Jamilun da zuciyarta da kunnuwanta, tana mai yarda da kowacce kalma da kowanne harafi dake fita daga bakinsa, zuwa can ta ce.
“Ni fa Yaya Jamilu banida matsala, amma babu ruwa na a kan maganar aure. Allah ya sani ban rike ka da komai a raina ba, sannan kuma bana kin ka, ina ganin abinda yafi, ka nemi amicewar Inna ba tawa ba, ni din da komai nawa ababen ikonta ne kuma ni mai son yin biyayya ce a gareta, don haka duk wani hukunci da Inna tayi akaina, inaso ko bana so, bani da ja a kansa”.
Jamilu ya gyada kai cikin gamsuwa da kalamanta, at least ya fahimci Hauwa bata kin auren sa koda bata furta tana son shi ba, tofa babu kiyayyarsa ko kadan a tare da ita, ya rausayar da kai yace,
“ni kuma na yi alkawarin zan lallashi Inna, idan ta bani ke zan kuma kula mata da ke kamar yadda zan kula da kaina. I can understand her fear, kuma kwarai nake la’akari da abida take hangowa (taking the marital responsibility of a blind person will never be easy) amma abinda ta manta ni dan uwanki ne, jinin ki ne, I can possibly endure it fiyeda bare, aure sunnar Manzon Allah ne SAW bai yuwuwa ace saboda lalura ta makanta baza’a yi shi kwata-kwata ba tunda ke din ‘yar adam ce kamar kowa mai lafiyar yin aure, ni Jamilu na yi alkawarin zan zame miki miji abin alfahari kuma dan uwa wanda zamu raba rashin idanun ki tare, sannan wanda zai tsaya wajen ganin kin zamewa ‘ya’yan ki uwa tagari a yadda Allah ke son ganin ki, tsan tsaya tsayin daka wajen ganin cewa lalurar rashin gani bai sa kin kasa basu kulawa ba.
Ni da kaina zan taya ki rainon ‘ya’yan mu Hauwa’u”. sai Hauwa ta kai tafuka ta rufe fuska cikin jin kunya tana murmushi kamar tace kasar ta tsage ta shige cikinta.
Maganar Jamilu ta karshe kai tsaye ta sauka a kunnuwan Dr. Sarham Abbas ne, a lokacin da ya kashe motar sa “opel astra’, ya tako zuwa gidan ya sawo kai soron, cikin takunshin nan mai sauti gab-gab-gab na bakin cover shoes ma matukar daraja, ya shigo zauren su Hauwa, yayi harr da idanunsa a fuskokin su.
Yana sanye da shirt fara kal, wadda aka yi rubutun ‘Dolce&Gabbana’ a jikin ta, da bakin Trouser ne na ‘Tokyo Jeans’. Kansa babu hula, sumar nan tasa baka wuluk ta fulanin Shanono ta cika kan sa har ta nannade (curl), a kafafun shi bain takalmi ne sau ciki na bakar fata kirar Italy. Da farko he was shocked, da ganin Hauwa tsaye da namiji a zaure, da abinda kunnuwansa suka jiye masa Jamilu na fade, da kuma yanayin da yaga Hauwa wanda kiri-kiri yana nuna tadin soyayya. Amma da yake shi din shine Sarhamu, sai ya bagarar, yashare, ya hadiyefirgicewarsa yayi kamar bai ji kalaman Jamilu ba, yayi musu sallama da dusassar muryarsa ya kuma baiwa Jamilu hannu suka yi musabiha, ya dan kalli Hauwa yana mamaki yana karawa, sannan ya shige cikin gidan.
Inna ta rako Babar Jamilu zata tafi suka yi kacibusa da shi yana shigowa tsakar gidan, kafin Jamilu ya samu zarafin tambayar Hauwa ko wanene shi ya isa dakin Inna, shigowarsa tasa hankalin Inna ya koma kansa, a gurguje suka yi sallama da Haj. Rumanatu ta wuce, bayan ta tabbatar mata cewa kwarai ta fahimce ta, zata yi iya yinta wajen lallashin Jamilu ya hakura, ko don kwanciyar hankalin Inna da zaman lafiyar su da Babansa dan jidali (Zakari).
Sarham ya zauna a falon Inna yana jiran ta har ta shigo ta zauna akujerar dake fuskantar sa, suka gaisa, sai ya koma cikin kujera ya kishingida yayi shiru, har da dan juyawa ya kalli taga yaga ko Hauwa taji kunyar idonsa na abinda ya tarar tana yi (soyayya) tayi maza ta baro saurayin ta shigo gida ko a’ah? Amma ina! Ko keyarta bai gani ba, tana can suna sallama da Jamilu kamar bazasu rabu ba, Sarham ya mike dogayen kafafunsa a kasa. Bai iya kara cewa komai ba don al’ajabi da mamakin Hauwa.
Can jimawa sai ga Hauwa ta shigo, tana tafe abunta kanta tsaye, babu ko lalube irin na makafi, tsabar ta gane hanyar dakinta, tasa kai zata wuce dakinta taci uban tuntube da kafafun Sarham, saura kadan ta kifa ta ci da baka. Ko sannu bai mata ba balle yayi ‘apologizing’. Cikin fushi tace.
“Inna wa ya saka min kafa zai kayar da ni haka?” Inna ta yi mata shiru, kafin tace “daga ina kike?” tace “Yaya Jamilu ne ya kira ni soro”.
Haba! Sai Inna ta balle da fada kamar ta rufe ta da duka, cewa take “da iznina kika fita zance gun Jamilu? Kece da zuwa zance Hauwa da wane idon zaki ga saurayin?” Saida Dr. Sarham yace “ya isa Inna, kinsan kinada matsalar zuciya, kada ki dinga bata ranki irin haka kan kananan abubuwa har ya tabo zuciyar ki”. Hauwa ta wuce dakin ta a sanyaye, bayan ta gaishe shi. Dr. Sarham yaki ko amsawa balle ya nuna ya san tana gaishe shi, har ta wuce tana mamakin me ta yi wa Dr. Sarham yau?
Gashi dai yau bai kira sunanta da yake mararin kira na MAIJIDDAH cikin farin-ciki, yalwar fuska da far’ar nan tasa ba, bai kuma amsa gaisuwar ta da kulawa da (attention) kamar yadda ya saba ba. to me ta yiwa Likitan Inna?
Ji yayi gabadaya yau ya kasa zama ya dade a gidan yadda ya saba, ya kuma kasa hira da Inna yadda suka saba, ita kadai take ta babatunta, daga karshe da Inna taga shirunsa yayi yawa sai ta dago ta dubeshi tace,
“ko lafiya kake kuwa likita? Na ganka ba’a yadda na saba ganinka ba”.
Sai kawai ya mike yana cewa “bari in karasa gida Inna, kaina ke min ciwo, yanata sarawa, idan na ji sauki zuwa gobe ko jibi in sha Allah zan shigo”.
Inna tace “ni ai ban sani ba, gashi har nayi maka tuwon Acca kuwa, da miyar da kake so ta zogale” Sarham ya juya a lokacin yana saka takalman sa a bakin kofar falon, yace “ba komai Inna, some other time, zan ci”.
Suka yi sallama dukkansu jiki babu kwari ya juya ya tafi. Ko sallama bai yiwa Hauwa ba.
Yana tuki yana hada gumi kashirban, duk da sanyin AC din motar sa. Abun ya daure masa kai matuka. Ya kuma sakashi a damuwar da ya kasa sanin ma’anarta. Yana isa gida yaji ana murnar zuwan Sumayyah, wadda ta zo hutun karshen shekara da barkar haihuwar Waheedah.
Kamar bai ga Sumayyah ba, bayan kuma har ido sun hada a falon, ya dauke kai yasa kai ya wuce zuwa dakin sa bayan yace musu cikin jam’u “sannun ku da gida”.
Mama ta bi shi da kallo, Sumayyah kuma ta ce. “Bhaiya lafiya kalau yake? Kaamr bai ganni ba Mama?” Mama ta ce “oho muku, kun fi kusa”. Surayyah ta ce “nafi tunanin wani ne ya bato masa rai daga waje, baki ga fuskarsa kamar hadarin da ya nausa yayi gabas ba?” Sumayyah sai ta mike ta bi bayan sa zuwa dakin nasa.
Sallama tayi daga bakin kofa, sai da ya bata iznin shiga ta shiga dakin ta same shi zaune akan ‘study chair’ ya rafka uban tagumi, ta ce.
“Bhaiya baka ganni bane ka wuce bamu ko gaisa ba?”