Showing 24001 words to 27000 words out of 45645 words

Chapter 9 - Hauwa Kulu Book 2 Hausa Novel Complete

Takori   

30 Dec 2024

133

kadai ‘weakness’ dina a duniya (zuciyarsa)”.
Finally, daga yau dai, sunansu ya tashi da ‘honorifics’ tunda ya koma Mr&Mrs. Dr. Shanono. Bayan tarihin fafutukar soyayyar shekaru goma!!!
**** ***** ****
A kwanaki bakwai din da Madinah tayi a gidansu Sarham, ta saba da kowa, kuma ta samu karbuwa ba laifi a wurin iyayen sa musamman Abba Prof. da yake ganin girman Kakan ta mai rasuwa Alkalin Alkalai, duk da ba wai sanayya ce a tsakanin su ba, amma yayi masa farin sani a matsayin daya daga cikin iyayen Kano. Ta fannin Mama kuma, ta zauna ne daga gefe tana laqantar Madinah a ma’auni na adalci da son sanin hakikanin halayen ta, inda a dan zaman su tare ta fahimci Madinah wayayyace, Madinah mai ilmi ce, bata da matsala sai ta rashin kawaici a kan Sarham, in bata gan shi ba sai ta ishi kannen sa da tambayar ina yake, wanda ke nuna zata yi kishi akan sa sosai, idan ya fita bazata nutsu ba sai ta ji shigowar sa gidan, tana da bala’in jan aji amma akan Sarham babu ajin ko kadan, don bata iya boye son da take masa a gaban iyayen sa da kannen sa.
Gata da halaye na kowa tasa ta fishshe shi, wato halayen nasara, kai bazaka ce girman kasar larabawa bace, amma kuma duk da haka tana girmama su, musamman su iyayen sa, ta fahimci Madinah ta san abinda take yi yadda ya kamata, tunda duk rashin kawaicinta data fahimta, a duka kwanakin nan bakwai data yi tare dasu, bata tsallake su ta kebe da Sarham ba, ko ta bi shi inda dakinsa yake, ita da shi sai ko a waya, ko in ya shigo ya taddasu duka a falo, sai ya zauna ayi hirar tare da shi, amma baya sakewa musamman in Mama na wajen, tana kallon Madinah na kashe shi da murmushi.
Shi da kan sa Sarham ya fahimci wani abu, wato tun bayan zuwan Madinah, mu’amalar sa da Sumayyah ta ja baya, Sumayyah ta daina shiga sha’anin sa sam, ko wuri ya shigo tana dariya sai ta daina, ta yi fuska. Ta daina kai masa abinci ko gyaran dakin sa wanda aikinta ne. A’ah, tun baya damuwa har ya fara tunanin laifin me yayi mata don wannan ba halin ta bane, me yasa ta daina ajiye masa abinci ko kiransa yazo ya ci, da gyara masa daki alhalin ta san ba wai Madinah ta tare bane, da zata cigaba da yin wadannan hidimomin da tazo ta tarar tana yi masa.
Yau ya fita can karshen layin su yana wata irin romantic waya da Madinah, don hakurinsa kusan ya fara karewa da takunkumin da ya sanya musu, haka suke yi yanzu kullum da yamma in jama’ar gidan basa nan ko suna wasu sabgogin a kitchen, ko can dare in kowa ya kwanta, sai ga Sumayyah ta karyo kwana tana tafe cikin nutsuwa, ta zo har inda yake ta gifta shi bata ce masa ko sannu ba, har ta zarta shi kadan ya kashe wayar ya saka a aljihu, ya ce,
“Sumayyah!”.
Sumayyah ta dan dakata amma bata juyo ba, ta daure fuska sosai, ya ce “ko ba da Sumayyah nake magana bane?”
Ta dawo ta tsaya a gaban sa tana tura baki gaba, ya ce “kin gama hada kayan naki?” Ta ce “hada kaya kuma? Ina zani?” yace “eh, Abba bai gaya miki da ke zamu tafi Jeddah ba, zaki zauna a gida na ki fara MBBS? Tukunnama wai me nayi miki kike gaba da ni haka? What’s wrong with you?”
Sumayyah mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki, nan da nan ta soma hawaye na babu gaira babu dalili, tace “wallahi in dai a gidan ku zan zauna to na fasa karatun a can, ni ba don kai da matar ka zan je Jeddah ba, ba ‘yar zaman daki kuka samu ba, zani jami’ar Sarki Abdulazeez ne, zaman karatun kaina, kowa yayi rayuwar sa a inda yake zaune duk da muna gari daya”. Cikin madaukakin mamaki Sarham ya ke duban Sumayyah, da babbar murya yace “Summy! Kina cikin hankalin ki kuwa? Ko kin fara shaye-shaye ne?” Sumayyah ta murgude baki gefe tace “Allah ya sauwake in yi shaye-shaye, kawai dai… ni bazan zauna a gidan ku bane, in ba hostel za’a kaini na zauna ba, to a nema min admission a BUK”.
Cikin kokarin hadiye fushi da bacin rai da ke tunkudo masa Sarham ya ce “to na ji, matsalar ki ce wannan yin karatu a Jeddah ko barin sa bakidaya, amma ki gayamin dalilin ki na kulla gaba da ni, da fita sha’ani na alhalin ba haka muke nida ke ba, sai yanzu da na yi aure, bayan kinsan mata ta bata tare ba balle ta cigaba da yimin hidimar da kike yi min”.
Sumayyah ta ce “Bhaiya, kaima gashi nan aika fada da bakin ka, “KA YI AURE!” Tunda kayi aure ni ba ruwa na da harkar ka gaskiya, kada wataran azo an araba ni dambe da matarka don na fahimce ta mai kishi ce, sannan na san wannan matar taka mai kama da larabawan aljannah, ba zata barni da kai ba sai ta raba mu, ga shegiyar kissa da kinibibi da rashin kawaici a kanka, tana wani kalmashe murya kamar kyanwa, shiyasa tun yanzu na raba kaina da kai, ba sai ta raba mu in zo ina jin zafin ta ba”.
Sarham baki bude yake kallon Sumayyah, yaki yardarwa kansa bata sha kwaya ba, yana ji ana cewa wai kanne na kishi da matan yayyun su, bai taba yarda ba sai yau.
Sai ya kwantar da ido da murya ganin Sumayya na share hawaye kuma, tana tuno irin tsananin shakuwar dake tsakanin ta da Bhaiya, yau ga wata ta zo ta shiga tsakani, ta fita kusanci dashi, kuma ta san ta shigo rayuwar su kenan har abada, bazasu kara samun kusancin da suke da shi ba ita da shi yanzu, saboda matar sa.
Yanzu kam ya yarda Sumayyah bata sha komai ba, ‘inner feelings’ dinta kenan, wanda ya sabawa hankali, shi take fada masa ba karya take ba, ba kuma hassada take yi wa Madinah ba, a’ah tata damuwar ce ta karan-kanta, saboda yadda ta damu da zumuncin da ke tsakanin ta shi.
Yace “Sumayah kada Allah ya baiwa kowacce irin mace da zan aura iko a kaina, ba a kan ki ke kadai ba, har iyayena da Surayyah, kada Allah ya dora min soyayyar da zata rufe min idanu in canza muku da wani abu saboda mace, ko in yanke zumuncin dake tsakanin mu, ko in kasa kyautata muku da kula da rayuwar ku”.
Sarham ya ja mumfashi a hankali, kafin yace “My sister Sumayyah, ki taya ni addu’a kin ji?”
Sumayyah tace “ai son da kake mata yayi yawa ne, Yaya Sarham ban so ka auri macen da son da kake mata ya rinjayi nata ba, don tsaf! Zata raba ka da kowa naka”.
Sarham yace “Sumayyah wannan tunanin ku ne irin na mata, ki bari ki ga kamun ludayin Madinah tukunnah, ina tabbatar miki Madinah daban take da sauran mata, don bata tashi anan ba, kuma bata tashi cikin mata ba sai ‘yan maza, duka wadannan halayen na mugunta bata san su ba, I assured you.
Madinah mai ilmi ce kuma mai hankali, ta san abinda take yi kin ji?”
Da wadannan kalaman ya samu yayi ta lallashin Sumayyah, har ta dan saki fuska ta daina kukan, amma tayi masa rantsuwa akan ita ba zata zauna a hannun Madinah a Jeddah ba, a makaranta zata zauna. Sarham yace “in aka barki kika zauna a makarantar shikenan baki da damuwa?” tace “eh, saboda matar ka ce raina baya so” ya ce cikin rashin jin dadi, “to na yarda, ban kuma isa in sa ki so ta dole ba, amma don Allah Sumayyah kada ki kulla gaba da Madinah akan haka, mai son naka masoyinka ne ba makiyin ka ba, ki bata dama ki ga irin halayenta”.
Sumayyah tace cikin jin tausayinsa “toh!” ya ce “zaki gyara min dakin nawa yanzu? Yau kwana bakwai baki share min ba, ban ci girkin ki mai dadi ba kanwata ta kaina”, tayi dan murmushi tace “zan gyara dakin, for now, amma ka cire ni daga dafa maka abinci da gyara maka daki kaima daga yau, ka koyi cin na matar ka”.
Da wannan suka tako a tare zuwa cikin gida. Sumayyah ta je ta gyara masa dakin sannan ta tafi hada kayan ta da zata tafi da su Jeddah, tana cikin hada kayan Mama ta kirata tace taje ta zo da Madinah, zasu fita ssallama gidan Hajiya Kulu su kuma gaishe ta bata jin dadi.
Sumayyah ta bata rai, tace “Mama why not Surayyah ta kira miki ita? Tunda tasu ta zo daya?” Mama ta ce “ke bana son rashin hankali kishin kannen miji, ki raba kan ki da wahalar da bata da amfani, tunda ke dai bazai aure ki ba, ita din da baki so ita Allah ya halatta masa”.
Sumayyah tana kokarin ta hadiye bacin ranta, ta ce “Mama Allah ya sawwake in yi kishin Yaya na, kawai ni I DON’T LIKE HER! AND I DON’T KNOW WHY?” Sai tasa kuka.
Mama ta rungume Sumayyah tana lallashin ta, a lokacin tayi ta kokarin ganar da ita hakan bashi da amfani kuma kuskure ne, in har tana so ta zauna lafiya da dan uwanta dole taso matar sa wadda bada jimawa ba zata zama uwar ‘ya’yan sa. Ta tilasta mata kan ta je ta kira Madinah da kanta su tafi Gadon Kaya tare.
Ko da ta shiga dakin Madinah na waya da Sarham, ana kalmasa harshe da larabci ziryan, cikin wani ‘accent’ dinta da shi kadai take yiwa magana da shi. Kyabe baki Sumayyah tayi ta ce,
“in kin gama an ce ki zo mu tafi Gadon kaya”. Ta juya tayi ficewar ta.
Batun yau ba Madinah ta fahimci Sumayyah bata yin ta, ba kuma don tayi mata wani laifi ba sai don a matsayin ta na masaniya akan halayen mata ‘yan uwanta psychologically ta gane Sumayyah irin kannen mijin nan ne masu kulafucin zumunci da yayyensu. Wanda hakan ke sawa su kasa shiri da matan su na aure don a ganinsu zasu raba su, amma ta san Surayyah sosai take yin ta, halinta daban dana ‘yar uwarta, itace ‘yar dakin ta, tasu tafi zuwa daya, kullum sai ta zo mata hira.
Madinah tasa a ranta daga yau zata fara kyautatawa Sumayyah. In har kyautatawa na sawa a so mutum, to Sumayyah sai ta so ta, don an ce zuciya na son mai kyautata mata.
Sun je sun gaida Haj. Kulu Surayyah ce ta tuka su a motar Mama su uku, daga nan suka dan zazzaga da Madinah taga gari, sune har Gidan Makama Museum da Gidan Dan hausa, Madinah ta roki Surayyah bayan sun gama zagayen da su je ‘main house’ din su a SoronDinki.
Tun daga gate suka tabbatar sun zo babban gida, kuma tun daga karbar da akayi musu suka yarda gidan su Madinah gidan karamci ne da karrama baki. Sannan ana ji da Madinah a family dinta. Basu jima sosai ba tayi sallama da Kakar ta da sauran ‘yan uwan ta suka koma gida.
Washegari ya kama ranar da zasu koma Jeddah, shiri sosai Mama ta yi musu na kayan abincin da babu a can, su maggi dunkule, ta kuma yi musu dambun nama mai yawa, gasu alkaki, dubulan, nakiya, bakilawa da gireba na cikin garar Madinah da aka kawo, duk tasa an shirya musu a jakunkuna daidai kilo dinsu, Sarham yayi sallama da iyayen sa da Kakar sa Haj. Kulu. Surayyah ta dauke su a motar Mama tayi musu rakiya zuwa filin jirgin malam Aminu Kano, suka tashi su uku wato, Sarham da Madinah, da kanwar sa Sumayyah wadda zata fara karatun medicine karkashin kulawar Yayan ta a birnin Jeddah.
****** ***** *****
S
umayyah Allah-Allah take su sauka a Jeddah, ta kama hanyar makaranta, ta kyale Sarham da matar sa, don ta gaji da ganin salo da rashin kawaici irin na Madinah.
Bayan saukar su a Jeddah hidimar makarantar Sumayyah ya fara yi, tun ma kafin su tare a gidan su, Madinah ta sauka wajen iyayen ta kafin a gama shirya musu gidan su da Saudi-German suka basu a gidajen likitocinsu, cikin kwanaki uku da saukar su har Sumayyah ta fara karatun ta, aka bata daki a hostel din dalibai kamar yadda tafi so, shi kuma yayi ‘documentation’ na karbar aikin sa a cikin kwanakin da asibitin kwararrun ido na Saudi-German.
Dr. Sarham Abbas Shanono ya zama cikakken likitan fidar ido (ophthalmic surgeon), daya daga cikin manyan likitocin idon da Saudi-German ke ji dasu da alfahari su.
Saida ya kammala ‘documentation’ din sa aka kuma gama shirya musu gidan nasu daga dukiyar gidansu Madinah, daga nan gidan su ya dauketa suka wuce babban birni wato (Riyadh) ta jirgin sama domin barje gumin amarci, abinda larabawa suke kira ‘Shahar Al-asal’ wato (honeymoon) da harshen larabci, inda acan Sarham ya gama gane aya da tsakuwa wato AVM Alkali bai yi masa barnar da yake tsoro ba, tuni ya ware aka barji amarci gangariya da matar da yakewa so gangariya, wanda shi kan sa ya san son da yake wa Madinah mai yawa ne, da har wani lokacin yake tausayin kan sa.
Daga ‘first-night’ din su, Madinah ta idasa tashin kan Sarham, domin abinda yake zato ba haka ya sameshi ba.
AVM bai yi masa barna ba, bai kuma bar masa sudi ba, domin kuwa shi ya bare alewar sa a leda.
Suna Riyadh ana barzar amarci a wani babban hotel na kasar, har tsayin sati guda kafin su dawo Jeddah. Dr. Sarham Abbas, ya kama aikin sa ka’in da na’in a asibitin “SAUDI-GERMAN”.
**** **** ****
Kullum amarcinsu sabo dal yake komawa basa taba gundura da juna. Amma duk da haka Madinah tana ta zuba idon taga Sumayyah ta dawo wajen su da zama bayan dawowar su gida daga honeymoon, amma bata gan ta ba, bata kuma ji Sarham yayi maganar dawowar ta wajen su ba ko sau daya, sai ta tambayeshi a wani maraice.
“Ni Dr. ina Sumayyah ne? Sumayyah ba a wajen mu zata zauna bane? Ta yaya muna gari daya amma zamu barta ta zauna a hostel?”
Yace cikin rashin damuwa da maganar “kada ki damu, zabinta ne”. Madinah bata gamsu ba, tace “amma dai Mama bazata ji dadi ba in taji bama tare da ita, kamar mun kasa rike ta zata gani” ya ce cikin kosawa da zancen “Madinah ki yi abinda ke gaban ki kin ji! Ki manta da Summy. Ban san ki da shiga sharo ba shanu ba.
Summy wata irin hutsuwa ce, bata son shiga harkar mutane kamar yadda kema bakiso kowa ya shiga taki in ba ke kika saka kanki ba, itama haka take”.
Ya fadi hakan ne don bazai iya gaya mata gaskiyar cewa Sumayyah bata yin ta ba, wanda gaskiyar maganar kenan, jininsu bai hadu ba, wato bata a layin mutanen dake son ita Madinar, ta bangaren ahalinsa. Amma duk da hakan data fahimta da kanta ba tareda ya fito fili yayi bayanin ‘fear’ din Sumayyah a kanta ba, Madinah bata fasa kyautatawa Sumayyah ba, haka kawai zata yi shopping niki-niki ta dauka a bayan mota ta kai mata har dakinta na hostel din, ko kayan abinci ko na shafa. Daidai gwargwado Madinah tayi kokarin jan Sumayyah a jiki ko don ta samu ‘yar uwa mace, kasancewar nata ‘yan uwan duk maza ne amma abin mamaki ko kadan Sumayyah ta kasa son Madinah, ta ki sakar mata jiki.
Sarham ya sha zama yana lallashin Sumayyah a bayan idon Madinah, kan ta bude zuciyar ta wa Madinah, ta dauka ita da shi ba banbanci, wato ta dauketa matsayin Yayar ta kamar yadda ta dauke shi Yayanta, amma taurin kai irin na Sumayyah akan Madinah ya ki canzuwa, Sarham ya danganta hakan da rashin haduwar jini kawai a tsakanin su, tunda shi kam ai zuwan Madinah bai sa ya canza ma kannen shi ko iyayen shi da komai ba.
To haka Surayyah ma dake can gida tana shan aiken kaya daga Dr. Madinah duk lokacin da ta samu mai zuwa Kano, lazim ne ta yiwa Surayyah aike. Haka koyaushe suna like a waya tasu kam ta zo daya, amma Sumayya kullum ranta kara nesanta yake da shiga harkar Madinah, saidai ta yarda auren sa da Madinah, da kuma uwa uba zazzafar soyayyar da yake mata kamar ya hadiye ta duk basu sa Sarham din ya canza musu ba su kannen sa da iyayen sa.
“Madinah-Munauwarah”, cikin watanni uku ta zama GIWAr mace a gidan ta, shi da kan sa Sarham in yayi nishadi GIWAR SARHAM yake kiranta, Madinah ta samu fada a wajen mijin ta yadda ba’a zato, saboda tarin baiwarwakin da Allah yayi mata musamman na iya masa da duk fitinar sa a shimfida, Madinah ta yarda da gaske ko a cikin maza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login