Showing 42001 words to 45000 words out of 174346 words

Chapter 15 - Diyam Book 1 Hausa Complete

07 Jan 2025

1095

jan charbin ta sai kuma tace "zo inga kunnen" na rarrafo nazo gabanta, ta duba kunne na ta shafa min vaseline.

Ranar haka na karasa ta cikin kuncin rai da kunan zuciya tare da fargaba, ni bawai fadan Alhaji Babba ne ya dame ni ba illa furicin da yayi akan sadauki, cewa da yayi zai sa a kama Sadauki duk sanda ya sake zuwa gidan nan, na kuma san alkawarin da Sadauki yayi min cewa zai dawo yayi updating dina akan duk abinda ake ciki dangane da mahaifinsa kuma nasan Sadauki baya karya alkawari idan yayi kuma bana jin zai fara daga yanzu. Option dina daya ne dole in nemi Sadauki in yi warning dinsa kuma in hana shi zuwa duk da cewa hakan yana nufin zamu kara nisanta da juna, amna gwara hakan akan abinda za'ayi masa in yazo din.

Bayan kwana biyu duk na kara diriricewa, ko yaya naji hayaniya a waje sai inji gaba daya hankalina ya tashi inyi tunanin ko Sadauki ne yazo aka kama shi. Rannan dai sai wata dabara ta fado min. Da daddare muna zaune da Inna nace mata "ni kuwa Inna ina so in tambayeki ko muma za'a saka mu a islamiyya ni da Asma'u. Kinga duk ana wuce mu a karatu muna zaune a gida" Inna tace "Wallahi nima zancen islamiyyar nan yana raina tunda muka zo na dauka za'a saka ku amma har yanzu shiru. Amma bari in hafsa tazo sai insa Mukhtar ya kai ku ko kuma in saghir ya zo gari in roke shi ya saka ku" nace "Inna yanzu islamiyya ma sai mun jira wani yazo ya saka mu? In kin yarda kawai in bi su murja in tambayi malaman abinda ake bukata na sabon dauka" ta danyi tunani tace "shikenan, ki bisu din". Ai kuwa na samu chance.

Washegari na shirya na kama hannun Asma'u muka je islamiyya na tambayar mana komai aka yi min bill, kamar yadda nayi tunani sai yasaiyadin yace mu shiga aji mu zauna, dai na tura Asma'u ajin su ni kuma nace zan je in dauko Alqur'ani na daga nan sai na kama hanya. Bani da ko kwandala dan haka na dauki hanya a kafa ina ta zabga sauri kamar zan tashi sama amma a raina sam banga nidan tafiyar ba, nasan gidan Alhaji Bukar inda yaya ladi take anan bayan layin mu yake dan haka nan na dosa, a ringa bi ta lunguna in tsallaka wannan titin in shiga wannan lokon bansan cewa na gaji ba sai da na ganni a kofar gidan, na tsaya a gaban mai gadi ina haki shikuma yana kare min kallo, sai da na gama tsaida numfashi na sannan nace "dan Allah baba Sadauki nake nema. Allah yasa yana nan" ya ajiye radiyon hannunsa yace "dazu ya shiga, bara in dubo miki shi" sai naga ya doshi boys quarters ana jima wa sai gasu sun fito a tare Sadauki ya doso ni da sauri fuskarsa cike da damuwa "Diyam? Lfy? Daga ina kike haka?" Na danyi masa murmushi sai naga yayi ajjiyar zuciya, ya kalle ni yace "kar dai kice min a kafa kika taho" na gyada masa kai sai ya jani zuwa kujerar mai gadi na zauna shi kuma yayi kneeling a gaba na yana mammatsamin kafata yace "me yasa kika taho a kafa Diyam? Ko menene ba zaki bari inzo ba sai ki gaya min? Yanzu da wani abin ya same ki kuma fa?" Nace "You don't understand, gaya maka zanyi kar kazo din ai" sai na bashi labarin abinda Alhaji Babba yace.

Sai naga fuskarsa ta chanja gaba-daya yace "Diyam mai nayi wa mutanen nan ne wai? Su kansu ba zasu taba iya fadar abinda nayi musu ba haka nan kawai suke ji a ransu basa sona" ya dago kai yana kallona yace "Diyam ni nasan ba zasu bani ke ba" nayi saurin girgiza kaina nace "da sauran lokaci ai Sadauki, ka tuno abinda Baffa yace? Sai na gama makaranta na shiga jami'a tukunna? Kafin nan zasu chanja ra'ayinsu zasu fahimci ko kai waye ne. Yanzu ka yarda Alhaji Bukar ya kai ka gurin abbanka tunda wannan zai kara sassauta zuciyarsu tunda suna cewa baka da asali" ya gyada kai yace "you are right. Gobe dama nayi niyyar zanje in gaya miki cewa jibi zamu tafi. Maiduguri yace zamu je" na bude ido ina mamaki, sai kuma na fara sharar hawaye, yace "sarkin kuka, kukan menene kuma kike yi?" Nace "Maiduguri fa da nisa" yace "kuma ce miki akayi a can zanyi ta zama. Nima ai bazan iya zama a can ba zanje in gansu ne kawai in dawo nan ko dan makaranta ta ma" sai kuma ya bani labarin wani abokin Baffa da Baffan ya hada su dan yayi masa hanyar admission, yace "ranan nan bayan nayi welcome back din layina sai ya kirani yayi min gaisuwar Baffa yace min insha Allah wannan admission din dani a ciki. Kinga zan dawo ko dan makaranta ta, besides, ni bazan iya rayuwa nesa dake ba"

Na makale kafada nace "Allah yasa dai kar Borno tayi dadi ka manta da Diyam" yayi murmushi yace "maganar kike so, sau nawa zan gaya miki cewa babu rayuwa a tare da Sadauki in babu Diyam ba. Life without you will not be just unbearable it is unimaginable. I can't imagine me without you". Sai kuma muka shiga hira kamar bamu da wani problem, yana ta tsara min yadda yake yana planning din rayuwar mu tare, hatta fasalin yadda zai gina mana gidan mu a filin da Baffa ya siya masa sai da yayi min. Ga iskar gurin tana yi mana dadi. Jin mu muke a saman gajimare, tamkar together zamu iya facing duk mutanen duniya

Mun jima tare sannan ya duba agogon hannunsa yace "Diyam, tashi maza in raka ki ki hau daidaita ki tafi, ashe lokaci ya tura bamu sani ba". Sai naji kuma kamar bazan iya tafiya ba kamar inyi zamana a gurinsa mu tafi Maidugurin tare amma nasan hakan ba zai yiwu ba, shima ganin yadda na damu sai duk jikinsa yayi sanyi. Ya dauko biro ya kama hannuna ya rubuta min number dinsa yace "ga numberta nan, ba wai rubutawa zakiyi a wani wajen ki boye ba a'a haddacewa zakiyi a kanki, if anything happens kafin in dawo, if you need anything ko menene ki samu aron waya ki kira ni. Kafin ki koma makaranta insha Allah zan dawo. Ki ringa yi mana addu'a" na gyada kai ina karajin jikina yana kara sanyi.

Ya raka ni waje ya tarar min adaidaita ya bashi address ya biya kudin, sai kuma ya tambaye ni in inason kudi. Na girgiza masa kai, kamar ba zai matsa ba yana kallon fuskata sai da mai adaidaitan yayi masa magana tukunna sannan ya ja baya muka tafi. Na waiga ina kallonsa sai yayi murmushi ya daga min hannu.

Daga dan nesa da gidan Alhaji Babba nace a sauke ni, ina sauka na juya da niyyar in karasa sai naji daga bayana ance "Diyam daga ina kike?" Na juya muka hada ido da kawu Isa shida wani mutum suna tafiya a kasa, na durkusa na gaishe su fuskata cike da rashin gaskiya, ya sake maimaita min tambayar, cikin in ina nace "Inna ce ta aike ni gidan Mama" ya gyada kai yace "to ki gaisheta, amma dan sahun ai daya karasa dake ciki" sai nace "zan biya ne ai ta islamiyya in tafi da Asma'u".

Nayi sa'a ina zuwa gida na tarar an taso yan makaranta na shiga cikin su muka shiga cikin gida. Bana jin dadi kuma bana so Inna ta gane dan haka nace da Asma'u ta tafi ta gaya mata mun dawo ni kuma na bi Murja muka tafi part din Hajiya Yalwati. Muna zuwa na kwanta a kujera ina jin kamar zanyi zazzaɓi, Hajiya Yalwati ta tambayeni "lafiya?" Sai na gyada mata kai inajin kamar zanyi kuka, sai kawai ta rabu dani tana tunanin ko Baffa na tuno.

Kwana biyu bayan nan, ranar da nake lissafin su sadauki sun tafi Maiduguri, mun fito zamu tafi islamiyya sai muka tarar da Alhaji Babba, kawu Isa, Inna da Hajiya Babba suna zaune a babban palo da alama magana mai muhimmanci suke yi. Muka gaishe su har zamu wuce sai ji nayi kawu Isa yace "Amina ki daina aiken Diyam ita kadai gwara kiyi wa Hafsan waya ta bawa Mukhtar ko menene ya kawo miki" na kara sauri kamar zan tashi sama, na kusa gate kenan naji an kwalla min kira, na runtse idona na kasa motsi, "Diyam ki zo ana kiranki" murja ta dafa ni tace "number dinki ta fito, good luck, ni nayi gaba"
[1/24, 9:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episodes Twenty Five : A Day To Remember

Na juya ina kallon kofar palon amma na kasa motsa kafata ballantana in tafi, Inna na gami ta budo kofa a zuciye tana kallona "ba kiranki ake yi ba?" Na taho a hankali ko wacce gaba ta jikina tana rawa, ina shiga Inna ta tunkuda keyata na durkusge a tsakiyar palon kaina a kasa. Kawu Isa yace "Diyam, shekaran jiya da na ganki kin fito daga adaidaita sahu daga ina kike?" Ban amsa ba kuma ban dago ba, Alhaji Babba yace "idan anayi miki magana kina yin banza da mutane sai na kakkarya ki anan gurin, ba zaki ansa ba" na fara rera kuka "dan Allah kuyi hakuri kar ku dake ni, dan Allah" Kawu Isa yace "ba zamu dake ki ba indai kika gaya mana gaskiya. Ina kika je ranar nan?" na cigaba da kuka na "wallahi Kawu na daina bazan sake fita ba". Na dago kai muka hada ido da Inna ta rafka tahumi tana kallona, nayi sauri na sunkuyar da kaina, tace "ba zata fadi inda taje ba fa, amma ni nasan inda taje, ba zai wuce gurin wannan bakin mayen ba" ta juya tana kallon Alhaji Babba tace "rannan ba kace in ya sake zuwa gidan nan sai ka kama shi ba? To shine ita ta tafi gurinsa tunda shi an hana shi zuwa. Wato dalilin da yasa kika nace sai na saka ku islamiyya kenan ko?" Na girgiza kaina da sauri "wallahi Inna ba haka bane ba, ranar nan ne kawai naje kuma bazan sake zuwa ba" Kawu Isa yace "to me kika je yi ranar? Me ya kaiki gurinsa?" Ina sheshsheka ina kuma wasa da fingers dina nace "ce masa nayi kar ya kuma zuwa gidan nan" Alhaji yace "au saboda nace zan saka a kama shi shine kika je kika gaya masa ko? To in nayi niyyar rufe sadauki kaf garin nan akwai wanda ya isa ya hana ni ne? Yanzun ma kuma zan tura har gidan da yake takama dasu din insa akama shi a dan lallasa min shi yadda nan gaba ko kince masa zaki je shi da kansa zai hana ki" Kawu Isa yace "tashi ki tafi" nayi sauri na mike nayi hanyar waje sai Alhaji Babba ya ce "kar ki fita daga gidan nan. Kin gama zuwa islamiyya ai. Zo ki wuce ciki" na juya na bi inda yake nuna min, muka hada ido da Hajiya Babba wadda tun da aka fara maganar bata ce komai ba tana dai bina da kallo kawai.

Kitchen din gidan na shiga, na rakube a jikin kofa na cusa kaina a tsakanin cinyoyi na, me yasa ni bani da sa'a ne? Me yasa duk sanda nayi wani abu sai an kama ni? Karya sam bata karbe ni ba? Sai kuma na kama addu'ar Allah yasa Sadauki ya tafi dan kar Alhaji Babba ya aikata abinda yace.

A palo bayan na tashi inna tace "na rasa yadda zanyi in raba yarinyar nan da wannan nataccen yaron wallahi. Nayi nayi, Allah ma ta gani nayi iya kokarina amma abin ya faskara, ni farko na dauka soyayyar yarinta suke yi, na dauka in suka fara hankali zasu saki hannun juna amma kamar kara tunzura su ake yi" Alhaji Babba yace "wai soyayya suke yi?. Diyam din yanzu harta isa yin saurayi? Shekarar ta nawa?" Inna tace "sha hudu zata yi nan da wata daya" ya gyada kai yace "ta isa kam. Matanen mu na ruga basu kaita ba ma ake musu aure. Kuma wannan tunda har tasan a raba ta da saurayi ita kuma ta dauki hanya ta bishi to lallai ita ma ta isa auren" inna tayi ƙoƙarin kare ni "ya shanye tane fa, babu maganar wanda Diyam takeji sai tasa" Alhaji Babba yace "anyi daya ai, ba za'a sake biyu ba, mu ba zamu kuma hada jinin mu da mayu ba, yadda bakin cikin Manu ya kashe Inno ba zamu bar bakin cikin Diyam ya kashe Hardo ba dan haka kija mata kunne. Babu ita babu shi, in taki kuma duk abinda ya biyo baya ita ta jawo wa kanta".

Shikenan kamar magana ta wuce, zuwa washegari na shiga harkokina sosai kamar babu abinda ya faru amma cikin raina kuma cikin sallolina ina yiwa Sadauki addu'ar samun nasara, sai inke tambayar kaina ko ya samu mahaifin nasa? Ko wacce irin karba a samu daga danginsa? Hankalina rabi yana tare dani rabi kuma yana gurin Sadauki har ya kwana uku da tafiya. A ranar da daddare aka aiko Alhaji Babba yana kiran Inna, ta dauki hijab dinta ta fita shiru shiru har na gaji da jiranta mukayi shirin bacci ni da Asma'u muka kwanta, amma sai na kasa baccin kuma nayi ta juyi ina jin wata irin muguwar faduwar gaba. Na rasa me yake yi min dadi kawai na tashi na zauna na rafka tagumi sannan sai gata ta shigo, sai kawai naga idonta kamar wadda tayi kuka amma sai ta maze tace "ke kuma me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba?" Nace "bana jin dadi ne kawai Inna. Baffa nake tunowa" sai kuma na fara matsar kwalla, ta dauke kai tace in an tuno mamaci addu'a akeyi masa ba kuka ba" sai ta wuce can karshen gado ta zauna ta jingina kanta da jikin gadon, naso in tambayeta in wani abun yana damunta amma nasan ba lallai ta bani amsa ba dan haka sai nayi shiru na koma na kwanta ina kalllon ceiling, mun jima a haka sannan tace min "Diyam Baffanku ya mutu ya huta, mu da muke duniyar mu mune cikin wahalarta" na runtse idona ina tunanin ma'anar maganar ta ta.

Washegari bayan na tashi da assuba nayi sallah sai na koma baccin safe, cikin bacci na kawai naji muryar mama a dakin na farka ina mamakin me take yi a gidan da sassafe? Sai naji Inna tana cewa "ni wallahi Hafsa kinfi kowa sani, bana son yaron nan sam zuciya ta bata sonsa ballantana har inyi sha'awar ya zama surukina amma duk da haka saghir fa...." Sai kuma suka ga ina kokarin mikewa sukayi shiru. Na tashi na gaishe da Mama, sai naga fuskar Inna still akwai bacin rai idonta kamar batayi bacci sosai ba, sai kawai naji ina son inji maganar da suke yi. Sai na bude toilet na shiga na rufe na kunna pampo kamar zanyi wani abu amma sai na dawo na sakakunne na a jikin keyhole.

Sai naji Mama tana cewa "wannan gajeriyar matar tasa ce zata kissima masa, shi kuma ya hau ya zauna saboda son kansa, amma suma kansu sunsan ai Diyam ba sa'ar auren Saghir ba ce ba, ya ninka ta a shekaru fa, gashi da budadden ido ita kuma fa? Yarinyar da junior waec kawai ta rubuta? Akwai cutuwa sosai a hadin su" Inna tace "babu fa abinda ban gaya masa ba jiyan, sai yaji haushina ma wai ina so in nuna ni na haifi Diyam basu ba, wai ita suke wa gata, wai baza ta taba samun miji irinsa ba, wai gata suke yi mata albarkacin zumunci albarkacin maraicinta" ta danyi tsaki tace "ni da ace Diyam ta fi haka girma ne, da ace misali ta gama makaranta ne wallahi da bani da dumuwa. Ni yanzu abinda nake so kice masa idan kinje shine, ki roke shi a bar yaran su daidaita kafin ta gama makaranta".

Na sulale ma zauna a kasa a jikin kofar. Naji dai suna maganar aure, kuma naji sun ambaci sunana sun kuma ambaci sunan Saghir. To tambaya ta anan itace auren wa za'ayi? Aurena za'ayi ko auren saghir za'ayi? Dan kaina ba zai iya daukan aurena da saghir a sentence daya ba ballantana ƙwaƙwalwa ta ta fahimci cewa aure za'a hada ni da saghir. Na wanke fuskata nayi brush na fito ina murmushin yake, suma duk yaken sukayi min har na zauna na fara breakfast sai na lura duk sun zuba min ido suna kallona. Sai na samu kaina da tattauna abincin amma makogwarona yakasa budewa ballantana in iya hadiyewa.

Muna nan zaune babu mai magana sai ga aike aba kiran Mama inji Alhaji Babba, ta tashi ta tafi muka cigaba da zama ni da Inna sai ga wani aiken wai inna taje itama, tana tafiya na rufe abincin gabana na tashi na kwanta a kan gado trying hard not to think, trying hard not to let my brain assess maganar da naji su Inna suna yi. Ba zan iya tuna adadin mintina ko awannin da suka wuce ba sai ga yarinya an aiko wai inzo inji ana kira na a palon Alhaji, na tashi na saka hijab dina still trying not yo think na fara tafiya blindly zuwa part din Alhaji Babba.

Na murda kofar na shiga da sallama. Duk suka dago kai suna kallona kamar yadda nima nake bin su da kallo. Alhaji Babba, Hajiya Babba, Inna, Kawu Isa da kuma Mama. Na durkusa na gaishe su da muryar da a kunnena naji kamar ba tawa ba. Suka amsa sannan duk suka zuba min ido suna kallona. Alhaji Babba ne yayi magana "Diyam a matsayin mu na iyayenki wadanda baki da wadanda suka fimu kaf duniyar nan mun yanke shawara a kanki. Zamu hada auren zumunci tsakanin ki da yayanki Saghir".

"Dama an jima da bani shawarar cewa babban abinda zai saka Saghir ya zauna a guri daya ya nutsu shine in na samu kyakykyawar yarinya na aura masa, tun a lokacin Diyam ce ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login