Showing 69001 words to 72000 words out of 174346 words

Chapter 24 - Diyam Book 1 Hausa Complete

07 Jan 2025

1100

kwanta sai kuma na saka hijab dina na dauko ruwan naje na kai masa. Yana kwance ya kashe fitila ya rufa da bargo, na ajiye ruwan ba tare dana ce masa komai ba. Zan fita yace "Diyam" na juyo ina kallonsa ya nuna kusa dani a kan gado yace "come here" na watsa masa harara na juya yace "kin san dai hakkina ne ko?" Na juyo nace "kai wanne daga cikin hakkokin ka ka sauke?" Yace "ki bani chance ki gani. Kuma nasan so far I have been trying my best" na fara tunanin wanne ne best din nasa. Sai ji nayi yace "zanyi Allah ya isa in baki zo ba" na juya da sauri ina kallonsa nace cikin mamaki "are you for real?" Ya daga kafada yace "bani da wani choice ai, ina bukatar ki kin ki bani, bazan iya miki dole ba so my only choice is to do Allah ya isa, ta rago" na juyo kamar wadda aka saka wa remote ina tunanin yadda aljanna ta take kasan kafarsa amma a lokacin babu abinda nake so irin in shake kyakykyawan wuyansa har sai ya daina numfashi. Na zauna a bakin gado na juya masa baya ina jin hawayena yana zuba a cinyoyi na, ina jinsa ya matso ya zare rigata sannan ya jawo ni zuwa jikinsa, ina jinsa yayi duk abinda yake ganin zai iya yayin da ni kuma kukana yake kara tsananta har ya gama abinsa. Ya sake ni yana mayar da numfashi. Na mike zaune na jawo rigata na saka ba tare dana kalleshi ba na mike sai ji nayi yace "shikenan kuma? Ko dan curdle din nan ma, irin falling asleep together din nan na masu aure babu, na juyo ina kallonsa da kumburarrun idanuwana, yayi murmushi nace "shima in banzo ba Allah ya isan zaka yi?" Yace "well, yes" na juyo na dawo na kwanta. Ya matso da pillon sa kusa dani ya jawo ni jikinsa sannan ya jawo bargo ya rufe mu.
[2/7, 4:27 PM] +234 706 813 0709: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Thirty Seven : Abatcha Motors

Da assuba na tashi kamar kullum, na cire hannayensa daga kaina na mike ina kallonsa yana ta sharar baccinsa, ban tashe shi ba tunda ni dai dama ban taba jinsa ya fita masallaci ba, na tafi dakina na shiga toilet na kunna wa kaina shower wai ko zata sanyaya min zuciya, inna wanke jiki na sai in sake wanke wa in sake wanke gani nake kamar duk Saghir dinne a mammanne a jikina, ji nake ina ma ace zan iya cire fatar jikina in sake wata wadda Saghir bai taba ba? Nayo wanka na na fito na saka doguwar riga ta hijab nayi sallah ina addu'a Allah ya kawo min karshen auren nan, sai kuma na chanja nace idan auren shine mafi alkhairi a gare ni Allah ya cire min Sadauki daga zuciyata ya shiryar da Saghir ya saka min sonsa a raina. Ko da banso shi ba at least in rage tsanarsa hakan zai dan rage min zafin da nake ji a zuciyata.

Ina nan kan sallayata har gari yayi haske rana ta fito, sai naji an bude kofar dakin da nake, na juya ina kallon Saghir daya dau wanka yasa gayunsa kamar kullum sai kamshi yake, ya tako har tsakiyar dakin da takalmin sa a kafarsa yace min "ki zo ki bani breakfast zan fita" na dauke kaina gefe saboda wani takaici da ganinsa ya saka min nace "ka kawo abin breakfast din ne?" Yace "ki duba dakina akwai kayan tea sai ki hada min tea, akwai kuma kwai a kitchen sai ki soya min" daga haka ya fita, na tashi nayi abinda yace na kawo masa palon sama yana zaune yana kallo, na zauna ina kallonsa har ya gama ya karkade jikinsa zai tashi nace "mu kuma fa? Me zamu ci" ya tsaya yana kallona yace "babu abinci a store?" Nace "ka ajiye ne?" Yace "bana son maganar banza in babu kawai kice min babu" nace "ai ka fini sanin babun" yace "ku sha tean mana to, kafin lokacin abincin rana ai zan dawo" yayi hanyar waje nace "in baka dawo ba nima zanyi Allah ya isa" sai kawai ya juyo ya kalleni yayi murmushi ya fita.

Bai dawo ba din kuwa. Haka na samu wata guntuwar shinkafa a store muka dafa fara dama uwani tayo guzurin yaji muka ci da mai da yaji. Bai dawo ba sai dare, daren ma sai bayan mun kwanta kuma nasan maybe yayi hakan ne dan kar inyi masa mitar bai ciyar dani ba. Da safe ina kasa muna gyaran gida sai gashi ya sauko, ya leka wajeya kira mai gadi sai naga sun hau sama tare ya bashi akwati ya sauko dashi kuma daga ganin akwatin nasan da kaya a ciki, akwatin cikin kayan lefe nane. Nabi mai gadin da kallo har ya fita sannan na hau saman muka hadu dashi yana kokarin saukowa nace "wancan kamar kayana naga an fita dasu, ko dai ido na ne?" Bai kalle ni ba yace "aro na dauka, zan siya miki wasu idan wadansu kudina da nake jira sun zo" nace "ko aron ne ai ana tambayar mutum kafin a dauki aron kayansa, kuma ni ban bayar da aron ba a dawo min da abi na" yace "ta yaya zamu zauna da kaya cikin akwati alhalin store din abincin mu babu komai? Ai ba kyauta nace ki bani ba aro ne kuma zan biya ki kin dai san ni ba talaka ba ne ba ko?" Kafin in bashi amsa ya fice. Na shiga dakina na tarar duk ya hargitsa min kaya, kusan duk kayan lefe na masu tsadar ya dauke. Bakin ciki ya kama ni kawai sai na zauna ina kuka, sai na tambayi kaina, wai yaushe ne zanyi farin ciki ni kam, yaushe ne zanyi murmushi, irin geniun smile din nan mai zuwa har zuci.

Ya siyo mana kayan abinci sosai, ya kuma bani 10k ya ce kudin cefane "saura kuma a karar dasu da wuri ace min babu" sauran kudin kuma bansan me yayi dasu ba.

Kwana biyu bayan nan, tunda rana naga yana tayi min fara'a sai nasha jinin jikina, da dare ina kwance a daki sai gashi ya bude kofa ya shigo nayi sauri na rufe idona dama fitila a kashe take, yace "Diyam, Diyam" nayi banza na rabu dashi. Sai ya hawo kan gado na sai nayi juyi na fara munsharin karya, irin wannan munsharin mai kamar kakin majina, sai yayi tsaki ya tashi ya fita. Na gyara kwanciya ta a raina nace "sai dai kaje ka rungumi pillow bani ba" and that got me thinking, this is his second attempt a kaina a cikin sati daya da dawowa ta, amma wancan karon wata na bakwai a gidan sa tun randa yayi raping dina bai kuma kallata da wannan maganar ba, menene ya chanza yanzu? Sai nayi realising cewa da yana da kudi yanzu bashi dasu, meaning da yana iya siya a waje yanzu ba zai iya siya ba, wato wannan shine dalilinsa na yarda da dawowa ta irin ga banza ta fadi dinnan ko? Ni kuma indai haka ne bazan yarda ba sai nasan yadda nayi na karbar wa kaina yanci. Sai kuma nayi mamakin kaina yadda nayi realizing Saghir yana neman mata amma ko a jikina wai an tsikari kakkausa, ko kadan banji raina ya baci ba alhalin ko a yanzu da nake matar wani in nayi imagining Sadauki da budurwa ba karamin baci raina yake yi ba ballantana inyi imagining dinsa yayi aure. I can only imagine yadda Sadauki yake ji a ransa a yanzu da make matar wani, har na haihu dawani. Ko ya yake ji? Ko ya yake coping?

Washegari ya tashi yana ta fushi, ni ko kallo bai ishe ni ba. Zai fita yace "zanyi baki anjima, abokaina ne manyan mutane ne sun takura wai sai sunzo sun ganki. Please don't embarrass me, kiyi musu abinci kuma kiyi shiga mai kyau kisa kayan da zasu kara miki girma". Bai jima da tafiya ba dai sai gashi ya dawo da kaji wai duk ayi musu. Mukayi abinci ni da uwani muka jera a dining, muka gyara gida tsaf yana ta kamshi na tafi sama nayi wanka na saka wata doguwar riga ta atamfa, dama ba kwalliya nake yi ba, na saka hijab nayi sallah ina zaune akan sallaya ya shigo yace "gasu sunzo, kuma please ki cire wannan dogon abin" ya juya ya koma, na tsaya ina tunanin menene dogon abin, doguwar rigar ko kuma hijab din?

Na tashi na gyara hijab dina na bishi, suna zaune a palon kasa kusan su biyar duk irin sa, yayan masu kudi masu ji da kansu. Na zauna a hannun kujera na gaishe su suka amsa, suna tsokana ta wai amaryar da ake boyewa, ina kallon Saghir yana ta harara ta nayi kamar ban ganshi ba sai cewa yayi "kin zo kin zauna kin saka mutane a gaba, ba zaki tashi ki kawo musu ruwa ba?" Na fahimci lallai so yake ya dizga ni a gaban abokan sa ya nuna musu ba sona yake yi ba, ni kuwa bai san yadda nake jin haushinsa yafi yadda yake jin nawa ba. Na mike sai cewa yayi "au ina miki magana ba zaki tsaya ki gama ji ba sai ki wani tashi ko?" Na dawo da baya na tsaya a gabansa nace "wanne daga ciki kake so Saghir? In tsaya kayi min fadan ne sai in kawo musu ruwan ko kuma in tafi in kawo musu ruwan sai kayi min fadan which one will you like first". Kusan gaba-daya suka kwashe da dariya. Ya kasa cewa komai ya tsaya yana kallona, sai na daga kafada nace "abinci yana kan dining, you can serve them in ka gama fadan" na juya nayi hayewata sama. Ni kaina nasan na gama da Saghir, amma kuma shi ya jawo wa kansa, me yasa zaiyi tunanin bara ya wulakanta ni a gaban abokan sa? Ko yana ganin hakan zai kara masa class ne a cikin su.

Ina nan zaune naji fitarsu a motoci sai kuma naji yana hawowa, nasan zuwa zaiyi mu yita amma sai naji bana jin tsoronsa, ya shigo har dakina ya karaso gabana ya tsaya, kawai sai jin saukar mari nayi a fuskata, saboda karfin marin har saida na daina gani for some seconds sannan ya sauke min a daya side din. Sai da naji taste din jini a bakina. Ya nuna ni da dan yatsa "ke har kin isa ki ce zaki gaya min magana a gaban abokaina, me kika dauki kanki ne? Wallahi ki bini a hankali Diyam in ba haka ba watarana sai na kai gawarki gida" Ya juya ya fita.

Na rike fuskata na zauna a bakin gado, bazan iya tuna sanda aka taba marina ba, to ni waye ma mai dukana in banda inna itama kuma mostly a kafa take dukana. Hawaye ya fara bin kuncina ina lissafa irin abinda zai faru da ace da ne wani yayi min wannan marin a gaban Sadauki. Nice kuka har magrib ina tayi, daga yin Sallah kuma sai zazzaɓi mai zafi ya rufe ni. Uwani ta hawo taji ni shiru sai ta tarar bana jin dadi sai ta zauna a waje na har saida Saghir ya dawo sannan ta sauka.

Tun daga ranar ban kuma lafiya ba, yau zazzaɓi gobe amai jibi ciwon ciki. Saghir kam fushi yake yi dani sosai ni kuwa ta kaina nakeyi, bai ma kula cewa bani da lafiya ba ballantana yayi tunanin kaini asibiti. Bayan nayi kusan sati ina jinya rannan uwani tace min "Diyam anya kuwa ba zaki yiwa Saghir magana ya kaiki asibiti a gwada ki ba? Ni fa ina ganin kamar juna biyu ne dake" sai naji wani amai ya taso min, naje nayi na gama na dawo nace "ciki fa uwani? Wanne irin ciki kuma?" Tace "ni dai na fada miki, kuma kije a gwada ki gani" sai na hau sama da sauri ina jin kamar labarin mutuwa ta uwani ta fada min, na fada kan gado na kama kuka, na shiga uku ni Diyam, sai na fara addu'a "Allah ka dube ni Allah, Allah kasa kar maganar uwani ta zama gaskiya" amma kuma nasan rabo na da period tun ina gidan mu, ga kuma abinda ya faru ranar dana dawo.

Ina nan kwance Saghir ya hawo yana kwalla min kira, na tashi na same shi a tsaye a kofar dakinsa yace "ki shiga ki gyara min dakina" na wuce shi na shiga na fara harhada uban lodin kayansa duk daya barbaza a dakin, ga zazzaɓi gashi jikina babu kwari saboda amai. Shi kuma ya tsaya a kofar dakin ya harde hannayensa yana kallona. Na daga wata riga kenan naji kamshin turarensa ya doke ni sai amai, da kyar na karasa toilet na fara karara wa sai ya biyo ni ya tsaya a bakin toilet din yana kallona har na gama sannan yace "baki da lafiya?" Bance masa komai ba yace "me yake damunki?" Nace "zazzaɓi" yace "da amai?" Na girgiza kaina da sauri nace "warin turarenka ne ya saka ni aman" yace "amma ai kullum shi naje sakawa baki taba aman ba sai yanzu. Are you pregnant?" Nayi shiru bance masa komai ba sai yayi tsaki "ke bansan wacce irin mace ba ce ke, daga an taba ki kadan sai ciki" naji wani abu ya tsaya min a kirji na wuce shi na dawo daki ina cewa "tunda dai bani na hau kan kaina nayi wa kaina cikin ba ai da sauki. If you hate me that much ka sallameni mana in tafi" ya biyo ni yana cewa "and who says I hate you?" Na tsaya ina masa kallon kar ka raina min hankali, sai yace "idan da bana sonki Diyam da tuni kina gidan ku wallahi ko dan wannan rashin kunyar taki. Kuma yanzu ko dan wannan samun cikin da ake yi ai ya kamata ki fahimci cewa we are meant to be together. Ki kwantar da hankalin ki muyi rayuwar aure kinki, kin ki cire that Sadauki of a person daga zuriyar ki kuma... " Ban karasa jin abinda zai fada ba na fito daga dakin na koma nawa.

Washegari shi ya tashe ni da safe wai in shirya muje asibiti, muna zuwa ya samu doctorn dana lura kamar sun san juna yace "PT zaka mata Please" sai doctorn yayi dariya ya kira wata nurse ya hadamu muka je tayi min. And it came back positive. A ranar nayi kuka kamar idona zai fita.

Tunda muka koma gida ya tare a dakina yana jinya ta, shine bani magani shine yi min sannu da su hada min tea, ni duk na dauka jinyar Allah da annabi ce sai daya sauke bukatunsa a kaina sannan na fahimci inda jinyar ta dosa.

Kayan lefe dai mun cinye su, babu biya babu ranar biya. Sai kuma yazo ya dauki set din kayan kallo na palon sama ya siyar, daga nan sai set din gadon extra dakin da bama amfani dashi a sama, sai deep freezer. Duk abinda aka siyar daga an dan siyo kayan abinci an dan bani kudin cefane bana kuma sanin inda sauran kudin sukayi. A haka har cikina ya tasa yayi wata biyar.

Ranar nan na shiga kitchen na rasa me zan dafa mana na hawo sama na same shi akwance a gado yana daddanna waya. Nace "babu fa abinda za'a ci a gidan nan" sai ya saka hannu a aljihu ya zaro min yadin aljihun na karkade min ya cigaba da danna wayarsa. Sai na samu kaina da tambayar kaina menene role din Saghir a auren mu? Shi aikinsa kawai shine yayi min ciki? Na shigo ciki na zauna a kan bedside nace "Saghir idan ni da kai da uwani mun zauna da yunwa wannan" na nuna cikina, "bai san babu ba" ya kalli cikin nawa sai ya ajiye wayar yace "to wai me kike so inyi? Ni fa ko kudin man da zan zuba a mota in fita bani dashi, ko so kike a ganni a daidaita sahu ake nuna ni a gari? Ko kuma so kike in ke bin gidajen masu kudi ina cewa allazi wahidi? Ko kuma dako kike so in dauka ko lebura ko kuma aikin mechanic? Na fahimci abinda yasa ya fadi mechanic din, so yaje muyi fada inyi zuciya in rabu dashi amma sai nace "eh, so nake kayi duk abinda ka fada indai zaka samu halak dinka. Wai kai ba kayi karatu bane ba? Ina takardun ka, ka karkade su ka fita kane gurin abokan Alhaji su hada ka da connections din da zama samu aiki. At least if you can't be a good husband try to be a good father".

Bansan ya akayi ba kuma ina daki sai gashi da folder din takardu yace zai je gida ya kaiwa Alhaji, sai kuma yace "in na samo kudi a hannun Hajiya sai in taho mana da wani abun a hanya". Ni dai na rabu dashi a raina ina cewa lallai gata mugun abu. Na tuno Sadauki da rashin zamansa a guri daya, tun yana dan karamin sa Baffa ya nuna masa neman kudi. Sai nayi murmushi ina lissafin irin kudin da Sadauki zai tara in dai ya samu hanya.

Ban kuma tabbatar wa cewa Alhaji Babba ya fada kwata ba sai da muka je gidan few days after that. Mota daya ce a compound din, ita ma kuma daga ganin ta nasan an dade ba'a hau ta ba, komai babu, ni sai naga gidan kamar har wani duhu yayi. Shi kansa ya rame, kayan jikinsa sun tsufa, na gaishe shi ya amsa yana ta yake baki. Muka shiga cikin gida suna ta kallon cikina, Hajiya Babba har da yar min da magana wai da Inna ta hanani komawa bayan ni ina son mijina, ni dai bance mata komai ba. Itama naga dakinta yar aiki daya ce kawai kuma itama na tabbatar yan uwanta ne suka dauko mata. Hajiya Yalwati kam Allah ya taimake ta ƴaƴanta manya su uku sunyi nce sun fara teaching dan haka su suke daukan nauyinta da kannen su.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login