Showing 114001 words to 117000 words out of 174346 words

Chapter 39 - Diyam Book 1 Hausa Complete

07 Jan 2025

1107

gida kawai. Ni zan zauna in cike wasu takardu yanzu zan biyo ku" kamar ba zasu tafi ba sai kanin Hajiya wanda dama tunda muka zo naga yana ta nuna alamar ya gaji yace "in mun zauna ma babu abinda zasuyi mana fa, zasu iya wulakanta mu gwara mu koma gida sai asan yadda za'a bullowa lamarin" sai naci sa'a suka bishi suka tafi ni kuma na koma ciki na cike form din da aka bani, aka kaini wani daki na zauna ina jira, shiru shiru tun ina kallon agogo gar na fara zama frustrated ina jin tamkar na shekara a dakin sai aka bude kofa aka shigo.

Saghir ne, amma kamar ba Saghir ba. Daga shi sai singlet da gajeren wando, fuskarsa babu inda bai kumbura ba dan idanuwansa da kyar suke budewa. Sai kawai naji zuciyata ta karye na rufe baki na kama kuka. Officer din daya shigo dashi yace "na gaya miki ai" sai ya zaunar da Saghir akan benchi ya juya ya fita. Na tsaya kawai muna kallon kallo. Sai can yace cikin wata irin murya "kinzo ne dan ki sakani a gaba kiyi ta kallo kina cewa Allah ya kara ko kuma kinzo ki karasa aikin da tsohon saurayinki ya fara?"

Na zauna ina facing dinsa nace "Saghir me yasa ka daukar masa kudi? Why? In zaka dauki kudin kowa a duniya me yasa zaka taba na Sadauki bayan kasan abinda yake tsakanin ku?" Yace "menene a tsakanin mu din? Ke? Dan ke akayi min wannan abin na sani kuma yayi da dan halak. Sai na rama duk ranar da na bar gurin nan sai na chanja masa kamanni kamar yadda yasa aka chanja min nawa" na girgiza kai cike da takaici, he is still being arrogant, nace "ni so nake in tabbatar, ka daukar masa kudi ko ba ka daukar masa ba? Ina so insan gaskiyar maganar nan saboda in san ta inda zan bullo mata" ya dauke kai yace "I don't need your help. Kiyi tafiyar ki kawai. Ki je ki gaya masa cewa tarkon daya kafa ya kama shaho" na girgiza kaina a raina nace 'he have no idea how much trouble yake ciki' sai na bashi labarin case dinsa da yan drugs. And that broke him down.

Hannu biyu yasa ya dafe kansa, ya jima a haka sannan ya dago yana kallona yace "wannan duk yana cikin irin kiyayyar da kike yi min Diyam? Me yasa baki fada min ba kika barni na dawo kasar? Me yasa kika barni na fada tarkon da makiyana suka kafa min" naji tausayinsa har cikin raina, nace "Saghir, ko daya ba naki gaya maka ne saboda bana sonka ba, naki gaya maka ne saboda nasan in na gaya maka ba zaka dawo ba and that means trouble for Alhaji, wanda babanka ne shi mahaifi dan haka dawowarka yafi maka alkhairi akan kin dawowarka" yace "really? To case din Sadauki fa? Shima kamanin da yayi yafi min alkhairi akan rashin kamani? Waye ya gaya masa zan dawo da har yasa aka tare ni a airport?" Nace "duk abinda zan gaya maka ba lallai ka yarda ba. Amma duk da haka zan gaya maka. Bani da idea akan abinda ya faru tsakanin ka da Sadauki. Na san dai yana buying time for something but bansan menene ba. Kuma ina so kasan cewa zanyi iya kacin kokari na na ganin ka fita daga gurin nan but for that ina bukatar ka gaya min gaskiya. Ka dauki kudin Sadauki ko baka dauka ba? Drugs din da aka samu a dakin ka da motar ka, naka ne ko ba naka ne ba?"

Ya jima shiru kamar ba zaiyi magana ba sannan kuma sai ya danyi murmushi yace "that former boyfriend of yours is smart, na bashi credit anan. Tunda yaron nan ya dauke ni aiki, ina jin ma ai na taba gaya miki, babu aikin da nake yi. Sai ya dauki wani a matsayin assistant dina to duk aikin da ya taso shi ake bawa yake yi and I tot 'huta roro' tunda dai ana bani salary na mai kyau ai bani da problem. Shekara da shekaru, ko banje gurin aiki ba bani da matsala, I should have known tun a lokacin that something is off but ni ta constant monthly income dina nake yi. And then lokacin da na koma aiki, suddenly it was all work for me. A lokacin ne nasan ma how much money ne a cikin account din Company and it was a huge money. Kullum kudi suna shigowa wadansu suna fita, kudi masu yawa. Shi yayi tafiyar sa, and duk takardar da aka kawo zaiyi signing sai a kawo min ace yace inyi a maimakon sa. Duk kudin da za'a fitar ni za'a saka in fitar dasu haka duk kudin da za'a shigar. It was like cewa ake yi Saghir dauki kudin nan. And I saw my chance. Mutumin nan yaci amana ta yayi making fool of me for years, dan haka dole ce ta saka ni na cigaba da aiki under him saboda babu inda zanje in samu din. Dan haka sai na dauka as a revenge for what he did to me kuma dan in kafa kaina nima in daina aiki under him. Nasan zai gani amma kuma nasan yana tsoron kar in bata masa image dinsa with that scandal so I expected him to keep quiet. Da kudin na sayi gidan dana gaya miki na kuma saya mana motoci ni da ke da Fauziyya and I gave some part of the money to Kabir da niyyar zamu hada share muyi business tare. Sauran kuma dasu nayi wannan tafiyar wadansu kuma suna account dina da niyyar su zasu rike mu kafin business din da zan fara ya kankama".

A gyada kai, my mind already thinking ta yadda za'a harhado kan wadannan kudade. Ya cigaba:

"Drugs kuma, wadanda aka samu a daki na, a kasan gadona, ba nawa bane ba. You know I don't do drugs. Na Kabir ne ya bani ajjiya saboda yana da iyali karsu taba masa ni kuma tunda zanyi tafiya shine yace in ajiye masa, a mota ta kuma alcohol zasu samu".

Na gyada kai nace "so, where is Kabir now?" Ya daga kafada yace "ta yaya zan sani tunda ina nan a rufe?" Nace "but ta yaya akayi suka kai mamaye gidan ka?" Yace "I have no idea. Ask that smart boyfriend of yours maybe shi yana da idea".

Na mike tsaye nace "thanks for telling me the truth. Zan je gidan Alhaji zamu zauna muga ta yadda za'a bullowa lamarin. Insha Allah, you are getting out of here. Zamuyi reporting cewa stuffs din Kabir ne ba naka ba." Na juya zan fita sai yace "why?" Na juyo ina kallonsa nace "why?" Yace "why are you trying to help me bayan duk abinda nayi miki? I tot ke celebrating zakiyi ma cewa you are finally getting rid of me" nace "kamar yadda Hajiya ta gaya min rannan. Kai dan'uwa na ne, mijina, kuma uban yata".

Daga bompai gidan Alhaji Babba na koma, a can na same su harda inna duk sunyi jigum jigum har aunty Fatima itama tazo. Na zauna na lissafa musu tas abinda ya faru. Saghir dai ya dauki kudi ba sharri ne akayi masa ba, ya kuma admitting to ajiye drugs a gidan sa amma yace ba nasa bane ba na Kabir abokin sa ne.

Nan take Alhaji Babba ya dauko waya ya kira Alhaji Murtala mahaifin Kabir yana tambayarsa in yasan inda Kabir din yake amma sai yace shima nemansa yake yi bai san inda yake ba, ya dauka ma tare suka fita da Saghir, da yake duk halin daya ne. Nan fa hankalin Alhaji ya sake tashi. In ba'a samu Kabir ba Saghir ne a ruwa.

Out of the confusion na fita waje na zauna a compound. Sai na dauko wayata nakira Fauziyya. Tunda na ganta a airport sanda aka kama Saghir ban kuma waiwatarta ba kuma babu wanda ya kuma kiranta. Bugu biyu ta dauka. "Halima ya ake ciki?" Naji haushin da bata kirani taji ya ake ciki ba sai yanzu? Amma sai nayi mata bayanin duk abinda na fahimta da kuma halin da ake ciki a yanzu. Sai ta tabbatar min da cewa tabbas taga sanda ya ajiye drugs din a day to tafiyarsu yace ajjiya aka bashi but bata san menene ba a lokacin kuma bata san waye ya bashi ajjiyar ba. Sai na ce mata ta shirya ta taho gidan Alhaji itama ayi komai da ita.

Sai can yamma ta zo, tana ta dari dari dan duk yan gidan ba sonta suke yi ba kar ma Hajiya taji labari, tace tsohuwar karuwa ce. Ita ta sake tabbatar musu da cewa Saghir shi ya ajiye drugs din da hannunsa, ta kuma gaya musu zancen gidan daya siya wanda su sam sam basu san da zancensa ba. Tace gidan yana unguwar rijiyar zaki dan haka muka yi shirin gobe zamuje a ga gidan sai kuma a nemi mai siya. Za'a karbi motarta da tasa a hada da wadda yace ya saya da sunana duk a siyar, sai a hada kudin da sauran kudin da yake account dinsa aga abinda za'a tayar kafin a nemi inda Kabir yake a dankashi a hannun NDLEA a kuma karbi kudin Saghir na hannunsa. Sauran kudaden kuma da Saghir ya riga ya kashe bansan inda za'a same su ba. Da Fauziyya zata tafi tace min "Mr Abatcha, ai yana jin maganar ki ko? Zaki iya sakawa ya saki Saghir ko?" And I didn't answer her.

Muna komawa gida na kira shi da wayar Asma'u tunda ba zai dauki tawa ba amma still sai yaki dauka, I guess yayi tunanin Inna ce take nemansa da gaske. Amma ita inna tunda taji zancen cewa Saghir ya dauki kudin Sadauki da gaske sai tayi shiru bata kuma cewa komai ba. But like I told Saghir, zanyi iyakacin kokari na gurin fito dashi so I decided to see Sadauki the next morning.

Da safe muka sake komawa gidan Alhaji Babba, Fauziyya ma tazo za'a tafi sabon gidan Saghir sai nace musu suje kawai, na gaya musu inda zanje. Abatcha Motors.

Na tarar da gurin kamar wancan zuwan nawa ana ta hada hada, sai dai yau kamar gurin yafi cika kuma motocin gurin sunfi nada yawa har bazan iya kirgasu ba, na samu receptionist din nace masa "ina son ganin ogan ku" sai ya tsaya yana kallona yadda na hade rai ya dauki waya yayi magana a ciki sai kuma ya kalle ni yace "ya ga shigowar ki ta CCTV. Yace kije office dinsa. In kika bi nan...." Na daga masa hannu nace "nasan inda office dinsa yake thank you" sai kuma na tafi inajin haushin kaina for being rude ga wanda bashi yayi min laifi ba.

Na ga wannan kyakykyawar secretary din nasa, ta yi min sannu da zuwa sannan tazo ta bude min kofa kamar ranar nan na shiga but sai na bar kofar a bude na tsaya ina kallonsa a zaune yana kallona shima.

Nace "let him go" sai ya taso ba tare daya ce min komai ba yawuce ni majestically ya rufe kofar dana bari a bude. Ya juyo ya samu kujera ya zauna yace "he took, or rather stole my money" nace "kudi, kudi, kudi dai? Shikenan abinda yake da muhimmanci a gurin ka kudi? Look at what you have, lokacin da naga amount din kudin da Saghir ya dauka I tot ya kassara ka but ni banga alamar anyiwa companyn nan ko da scratch ba" yayi murmushi yace "you are right. Amma dai ya dauka. So, dole zai biya in kuma ba zai iya biya ba sai ya tafi gidan maza har zuwa ranar da iyayensa zasu samu kudin da zasu biya masa" na tako nazo gaban table dinsa na tsaya, ina jin kamar in rufe shi da duka. Nace "me yasa? Tarko ne ka dana masa na sani but why? Me yasa? You could have just let me take him to court kamar yadda nayi niyya ya sake ni and that'll be all. Zumuncin dama ai a lalace yake menene saura. Why do you feel the need to lock him up?" Yace "kamar yadda kika ce in kika kai shi court ya sake ki that will be all. Meaning duk abinda yayi miki yayi a banza kenan? What he did to you and said to my face shikenan yayi a banza kenan?" Ya fada with bitterness in his voice, ya cigaba "wannan abinda yayi, kuma ya gaya min yayi, shine greatest mistake dinsa a rayuwa kuma shine abinda zai paying for in prison for as long as possible" na zauna a kujerar da take facing dinsa nace "ni yayi wa, ba kai ba...." Yace "da ni yayi wa da sai abin yafi zuwa masa da sauki" naji zuciyata ta karye nace "Sadauki.....komai ya faru fa ya wuce. Ni duk na yafe kowa saboda a yanzu kowa yayi paying price dinsa. Tun daga ranar da aka kaini gidan Saghir nake addu'a cewa Allah ya saka min akan duk wanda ya zalinceni, kuma a yanzu bayan shekaru duk wadanda suka zalinceni din babu wanda bai karbi hukuncinsa ba. Inna, tun ranar da aka kaini gidan Saghir har yau Inna cikin regret take, har yau bata samu peace of mind ba saboda bana jin akwai abinda yafi ciwo irin ace uwa tayi destroying rayuwar yarta da kanta. Alhaji Babba a yanzu fa bashi da komai, ka tuna dukiya da izza irin ta Alhaji Babba amma yanzu rigar da zai saka ma sai in na debo na Saghir da baya sakawa na aika masa saboda shi ba zai bashi din ba. And Saghir, Saghir fa ta kare masa, ko da bakayi trapping dinsa ya daukar maka kudi ba Saghir already yana da case, NDLEA sun samu drugs a dakinsa dan haka suna nemansa. So you see? You don't have to do anything Allah yana planning komai accordingly" yace "na yarda, kamar yadda na yarda cewa Allah yana using people to furnish other people. Alhaji Babba da kike magana fa har yanzu baiyi regret ba, ko ya taba kiranki ya baki hakuri akan abinda yayi? Har yau da zaki tambayeshi cewa zaiyi taimaka miki yayi ya aura miki Saghir, dukiyarsa kuma cewa zaiyi makiyane suka saka masa hannu. So dole ya cigaba da zama gida daya da kaji da raguna ya cigaba da having sleepless nights for as long as I had, which will be like forever tunda har yau ba baccin nake yi ba"

Na mike tsaye ina jin haushinsa nace "how thick is your skull? In kana furnishing Alhaji su kuma iyalansa fa? Me sukayi maka? Makota fa? Me sukayi maka? Gidan gona tunda ka bawa Asma'u zan saka ta ta chanja masa guri. Batun Saghir kuma za'a biya ka kudinka, za'a siyar da duk abinda ya siya da kudaden sannan a nemo sauran a cika maka a baka kayanka ba shikenan ba?" Ya mike tsaye yana murmushi yace "me da me za'a siyar, gida da motoci? You are kind of late because I already bought the house and one car about two weeks ago" na juyo da sauri nace "what?" Ya gyada kai yace "bayan ya debi kudina I asked someone to track duk abinda zaiyi da kudin, naji ya sayi gida da motoci and I became worried cos zai iya siyar dasu ya biya ni. Luckily for me, sai ga report cewa one of his friends..." Ya duba wata takarda a gefe yace "Kabir, ya saka gidan da mota daya a kasuwa zai siyar, he was in a kind of hurry sai na taimaka masa na siya, yanzu har na zuba yan haya a gidan. Shi abokin daya siyar din yanzu ance min ya gudu ya bar kasar" ya sake murmushi "hard luck for him".

Na dafa kujera na zauna ina kallonsa. Na fahimci lissafin sa tsaf kuma na gane mai ya faru. Saghir ya saci kudi, Kabir set him up with the drugs sai ya siyar da gidan ya hada da sauran kudaden ya gudu. Meaning yanzu Saghir bashi da abinda zai biya ga kuma case din drugs a kansa. Sai na mike ba tare dana sake cewa komai ba har nayi hanyar waje kuma sai na tuna abinda ya faru rannan dan haka na juyo nace masa "open the door" yace "Please Diyam, stay out of it. Let him take the fall. He more than deserve it" na dawo gabansa nace "tell me something. Me yasa ka yafe wa Inna? Inna tafi kowa musguna maka a duniya amma ita mai yasa ka yafe mata?"

Ya dago kai yana kallona yace "she gave birth to you".


?? DIYAM ??

By

Maman Maama

Episode Fifty Six : A Walk To Freedom

"She gave birth to you"

Maganar ta daki kunnuwana sannan ta wuce har cikin zuciyata, sai naji tamkar ta kunno min emotions din dana ke ta kokarin dannewa a cikin zuciyata, sai hawaye yazo idanuna ya fara zuba kan kuncina a hankali na fara rera kuka sai ya taho inda nake da sauri yace "Diyam....." sai kuma ya dakata ya juya ya koma bayan table dinsa ya danna button din bude kofa yace ba tare daya kalleni ba "good bye Halima".

Na juya nima da sauri na fita ina kokarin goge hawayen fuskata. Na sauka daga stairs din cikin sauri na fita daga building din. So nake kawai in samu seclusion din da zanyi kuka na son raina har in gode Allah. Na tsaya a bakin kenan naga mota tayi packing a gaba na sai driver din ya fito ya zagayo inda nake ya bude min kofar baya yace "oga yace ki shigo a kaiki gida" har nayi tunanin kin shiga sai kuma nayi lissafin gwara inyi kukana a cikin mota ni kadai da ac akan inyi a cikin napep mutane suna kallona.

Na shiga ya rufe kofar ya zagayo gurin driver sannan na masa kwatancen gidan Alhaji Babba muka tafi. Na jawo hijab dina na rufe fuskata nayi kuka na na koshi amma ni kaina bansan kukan menene ba, kukan tausayin kaina ne ko na Sadauki? Kukan abinda ya faru da ne ko kuma wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login