Showing 150001 words to 153000 words out of 174346 words

Chapter 51 - Diyam Book 1 Hausa Complete

07 Jan 2025

1093

"ina so" yace "to sai kin fadi sunana tukunna. Ya sunana" a hankali tace "uncle Aliyu" yayi murmushi ya shafa kanta yace "good girl".

Suka biya ta mall suka ciko leda da kayan zaki sannan suka karasa airport. A airport din sai yaga duk walwalar data fara dazu ta ragu, tayi shiru kamar mai shirin yin kuka, sai ya durkusa a gabanta yace "menene kuma? Ba kya murnar ganin Mommy? Ko in kira ta a waya ince mata ta koma ba kya son zuwanta?" Sai tayi sauri ta girgiza kai, yace "to me kike so?" Tace "rannan da muka zo nan da mommy, sai police suka zo suka tafi da Daddy na kuma har yanzu basu dawo min dashi ba" sai hawaye suka zubo daga idonta ta dago tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta ta sake cewa "mommy tace zaka fito min dashi ko?" Ya saka hannu ya share mata hawayen fuskarta yace "daddyn ki zai fito little girl. I promise you" sai kuma yayi murmushi yace "amma sai kinyi min wani alkawari, promise me daga yau mun zama friends" ya fada yana mika mata dan karamin finger dinsa, ta goge hawayen fuskarta ta saka nata karamin finger din a ciki sannan ta gyada kai tana murmushi. Ya daga ta masa ya dora ta akan kafadarsa yace "now, let's wait for your mommy".

Diyam tana fitowa ta hango su, and seeing them smiling together ya saka taji wani irin joy a zuciyarta marar misaltuwa, tana kallonsa ya sauke Subay'a kasa ita kuma ta taho da gudu gurinta sai ta durkusa ta bude mata hannayenta ta shige zuwa kirjinta ta rungume ta taba ajjiyar zuciyar dadi, ta dago fuskarta tayi kissing goshinta tace "I miss you so much little girl" Subay'a tace "I miss you too mommy". Ya karaso ya tsaya a kansu yace "na gane matsayi na" ta mike tana kokarin daukan Subay'a yace "ke! Careful kar kisa a daga min biki" ta harare shi tace "wato bikinka ne a gaban ka ko?" Yace "a yanzu, yes" Subay'a tace "uncle bikinka za'ayi?" Ta fara tsalle, "zanje gidan ka inga amaryarka" ya daga ta sama yace "karki damu, kece yar zaman daki".

Daga airport basu yi cikin gari ba sai suka dauki wata hanya daban. Diyam tace "ina zamu je?" Bai kalleta ba yace "kawunan ku zanje in siyar" tayi dariya "ni kaina yafi karfin babarbare ya siyar" ya kalleta yace "siya na nawa kuma? Sai ya kalli Subay'a ta mirror yace "kinci sa'a we have company" ta murguda masa baki, yace "ki cigaba, ba dai rashin kunya ba, akwai ranar kin dillanci".

Titin bypass suka hau sannan suka shiga unguwa uku, suka sauka daga babban titi suka shiga wani layi sannan yayi packing a gaban wani gida yace "Mrs Abatcha, welcome to your home" ta bude vaki tana kallon gidan sa yake gabanta sannan tace "wow" yayi murmushi yace "shall we?" Kafin ta bada amsa Subay'a ta bude motar ta fita da sauri tana cewa "uncle gidanka ne wannan?" Ya fito yana cewa "gidan mu ne princess, ni da mommyn ki da ke" sai ta kwasa a guje ta kama gate din tana cewa "Mommy ki kira inna kice ta aiko min da kayana" Diyam da Sadauki suka yi dariya a tare.

Malam iliyasu ya fito yana bude musu gate. Diyam ta kalleshi sannan ta kalli Sadauki shi kuma ya daga mata kafada yana murmushi. Sai ta juya tana amsa gaisuwar da malam iliyasu yake yi mata amma bata ce masa komai ba sannan suka taka da kafa suka shiga gidan. Tsayawa bayyana tsari da kyawun gidan zai tsawaita labarin mu amma dai tabbas Moon construction company sun kure adakar su a wannan gidan. Daki daki suka bi a nutse Sadauki yana yi mata bayanin komai kuma tana neman gyaranta in akwai amma ita bata jin akwai wani gyara da za'ayi a wannan tsararren gidan. Bayan sun gama sun fito ne suka zagaya baya gurin wani dan karamin gurin shakatawa mai lullube da grass carpet da kuma madaidaicin swimming pool mai dan karen kyau wanda ganinsa kawai ya isa ya saka mutum yaji yana son yin wanka. Suka zauna a wasu daga kuherun gurin ita kuma Subay'a ta bazama tana zagaya gurin a kuje. Diyam tace "amma gidan nan yayi kyau, irin sosai din nan fa" yayi murmushi yace "am glad you like it. It will be our Kano home insha Allah. Zamu yi wani a Maiduguri saboda muke sauka in munje, and for Oxford we have to get a bigger apartment dan wanda kuke ciki yanzu yayi mana kadan".

Sai ta dauko wasu takardu ya mika mata sannan ya gyara zama yana kallonta. Ta karanta ta kuma karantawa, ta fahimci cewa wata yarjejeniya ce signed by Aliyu Umar Abatcha cewa ya yafewa Saghir Muhammad Kollere kudaden sa daya satar masa. Akwai saka hannun lawyers dinsa, akwai saka hannun alkalin da yayi waccan shari'ar sannan akwai saka hannun Saghir. A kasan inda Saghir ya saka hannun ya rubuta "thank you".

Ta dago da sauri tana kallon Sadauki, sai kuma ta kasa magana. Yaushe Sadauki yayi wannan shawarar? Shin hakan yana nufin Saghir ya fito ko kuwa bai fito ba?

Jin bata ce komai ba yasa yace "lokacin da Saghir ya fada min wannan maganar a kanki ba rufe shi nayi niyyar yi ba, zuciyata abinda take gaya min shine in kama shi inyi ta dukansa har sai ya daina numfashi sannan in kaishi daji in ajiye shi dabbobi su cinye shi da rai" ya danyi dariya ganin kallon da take yi masa yace "babu irin imagination din da bana yi that's why I decided to set a trap for him and luck him up, a hakan zaiyi paying for what he did and he will be out of my reach yadda bazan yi masa lahanin da duk zamuyi dana sani ba. I didn't know his friend will set him up for drugs. Niyyata shine a lokacin da naji zuciyata tayi sauki a kansa sai in yafe masa ya fito but as fate have it ba wannan ne kadai case dinsa ba, so, har yanzu yana can kamar yadda alkali ya fada har sai an samu nasarar kama abokin nasa kuma sai abokin ya karbi laifin shi ya bashi ajjiyar drugs din" Diyam ta gyada kanta tana kallon Subay'a da take wasa a can nesa dasu sannan take murya can kasa "thank you. Mun gode Allah ya kara arziki" baice komai ba shima yana kallon Subay'a sai zuwa can yace "zanyi kokarin ganin ya fito, dan Subay'a taji dadi. But bazan bashi aiki ba kamar yadda kika bukata daga farko, ruwansa ne yayi hankali ruwansa ne kuma yayi akasin hakan. Na riga nayi magana da Ahmad, duk da dai kamar baya goyon bayan fito da Saghir din but yace zai taimaka min, matsalar shine su iyayen Kabir din sunki vada goyon baya su fadi inda dan nasu yake" ya juyo yana kallonta yace "naso ya fito kafin auren mu, naso yazo ayi dashi dan anan ne zan tabbatar da nadamarsa ko akasin hakan. But it is beyond me dan haka sai bayan biki".

?? DIYAM ??

By

Maman Maama

Episodes Seventy & Seventy One : The Wedding

The chance of you dying with COVID-19 is 1% while the chance of you dying anywhere anytime by any means by Allah's wish is 100%. Wanne ya kamata muji tsoro? Corona virus ko Allah? Then why the panic bayan mun yadda da kaddara munsan komai rubutacce ne?

Mafita kawai shine mu koma ga Allah mu rungumi Alqur'ani da Azkar, mu yawaita istigfari sannan kuma mu bi dokokin da ma'aikatan lafiya suka kafa.

Idan Allah ya riga ya rubuta cewa Corona virus itace sanadin mu muna rokon Allah ya karbi shahadar mu (mutuwar annoba shahada ce), idan kuma ba ita bace ba Allah ya bamu rayuwa mai albarka ya dawwamar damu cikin imani Ameen. Allah kuma ya kyautata karshen mu.

Diyam...............

Diyam taji dadi sosai a ranta. Tabbas ko da Sadauki bai fito da Saghir ba to kuwa yafe masa ma da yayi ya nuna cewa his stone hard heart is now soft. Yanzu ya yi part dinsa ya rage nasa kuma ya taimaka wa Saghir ko yaki duk ganin damarsa ne, taimakon yana da kyau sosai musamman saboda xuri'ar da aka riga aka hada, amma kuma ba wajibi bane ba. Dan haka ba zata sake yi masa magana ko kokarin tursasa shi zuwa haka ba dan in yayi din ya zamanto niyyarsa ta kyautata.

Tayi masa kyakykyawan murmushi tace "hakan ma mun gode sosai, Allah ya bar zumunci" yace "Ameen, Mrs Abatcha" ta harare shi, "bana so" yace "okay, madam kike so?" Ta mike tsaye kamar zata yi kuka "bana so wallahi" ya mike shima yana mata dariya "gaya min to, me yasa ba kya so?" Tace "sai in ji na zama kamar wata katuwar ?edara, wai Madam" yayi dariya sosai yana matsowa kusa da ita yace "to me kike so ince miki?" Ta juya ido tace "Diyam" yace "Sadiyam" tayi masa gwalo tace "sholoki" sai ta bar gurin da sauri ta tafi gurin Subay'a tana waigensa. Ya daga murya yace "zan kama ki ne ai, not now but on the 25th" bata waigo ta kalleshi ba but she blushed.

Wayarsa tayi kara ya duba sannan ya taho gurinsu yana cewa "time off, Inna ta gaji da jira tasa yar asama ta kira mu" Diyam ta mike straight tana cewa "Allah sarki inna ta, nima nayi missing dinta sosai" ta mika masa takardun hannunta suka tafi Subay'a tana ta fushi wai ita ta dauka sunzo kenan.

A kofar gida ya ajiye su yace bazai shiga ba. Subay'a ta fita da gudu tana ta dokin bawa Asma'u labarin sabon gidan da suka je. Diyam ta yi masa sallama zata fita kenan sai ya miko mata wani card ta karba tana dubawa taga credit card ne sai yace "ki dauki kudin da zaki bukata a ciki, ki kuma dauki na su Murja da kika yiwa alkawari" kafin tayi masa godiya sai yace "birth year din ki shine pin din" ta gyada kai tana murmushi, ta sake bude baki zata yi godiya yace "bana son ji. Ko ki fita ko kuma in tafi dake kuma bazan dawo dake ba sai dai a biyo ki da kayan ki".

Bata san tayi missing inna har haka ba sai da ta ganta tukunna, ta tafi da sauri ta rungume ta tana dariya, itama innar dariyar take yi amma sai ta ture ta tana cewa "kar ki karya ni" Asma'u ma ta kankame ta tana cewa "nayi missing dinki, sosai Adda ta" Diyam ta kalleta tace "oh, Asma'u kin kara girma fa. Inna wannan ai itama kamata yayi a hada bikinta da nasu Murja" Asma'u ta fara buga kafa tana cewa "shikenan zaki kunto min ruwa, dama inna kiris take jira ta dawo kaina" ta karashe maganar tana tafiya daki. Inna ta bita da kallo tana cewa "yayanki ne ya daure miki gindi ai, daga ke har shi kun tsaya kuna ruwan ido amma ace yarinya kamar ki har yanzu bata da saurayi?" Diyam dai tana tayi musu dariya saboda ta fahimci wanne yayan ake nufi, shi har yanzu kallon Asma'u yake kamar wata jaririya.

Diyam ta lura da chanji a gidan su, an bude part din Ummah an kwashe kayan ciki sannan an gyara shi amma ba'a zuba komai a ciki ba. Ta shiga daki tayi wanka ta shirya tayi sallah sannan ta dawo palo suka zauna cin abinci da Inna, Asma'u da Subay'a da take ta zuba mata hira tana kokarin bata labarin duk abinda akayi a gidan sanda bata nan. Sai Diyam taji tamkar gidan yafi ko ina dadin zama.

Bayan ta kwana biyu ta huta sai shirya da niyyar zagaya gidajen yan uwa ta gaishe su. Inna tace "sai kiyi musu sallama kuma dan ba lallai ne ki sake samun zuwa gurin su ba". Tare da Asma'u suka fita, gidan Alhaji Babba suka fara zuwa, wannan shine zuwan Diyam gidan na farko kuma taji dadin yadda taga gidan, ba kamar dai nasu nada ba amma kuma basa cikin kuntata. Babban abinda ya kara mata jin dadi shine ganin Alhaji Babba ya chanja sosai ya samu nutsuwa fuskarsa ta saki ta rage nuna damuwa. At last ya daina blaming makiya da sauran al'umma for his misfortune. Da fara'a sosai ya amsa gaisuwar tata har da tsokanar ta da cewa "munji ki shiru har ina tunanin ko sai dai kawai mu daura auren anan in yaso angon ya biki can?" Ta rufe fuskarta tana jin kunyarsa. Sai kuma yayi mata godiyar kudin haya data biya masa sannan ya dora da bayanin neman yafiya a bisa abubuwan rashin adalcin da yayi mata. Ta katse shi da sauri "Alhaji ni na yafe ai, tuntuni na yafe muku tun ma kafin mu rabu da Saghir. Komai ya wuce sai fatan Allah ya kara gyara mana zumuncin mu" yace "ameen" ya dora da "ina son kuma ki sake yi min godiya gurin yaron nan Aliyu. Satin daya wuce naje na gano Saghir kuma ya gaya min abinda yayi masa, ya gaya min ya yafe masa kudaden daya daukar masa" ya fada yana dauke hawaye da babban yatsan sa. "Kudade masu yawa amma yace ya bar masa su. Kuma yace min ya hada shi da lauyoyinsa zasu taimaka masa akan maganar kwayoyin nan. Allah ya saka masa da alkhairi, Allah yaji kan mahaifiyarsa, matar da har ta mutu Allah bai bamu ikon neman yafiyarta ba".

Ta shiga dakin Hajiya ta dauki Muhammad, kyakykyawan yaro har ya warware yana ta shan madarar sa. Sai kuma ta shiga dakin Hajiya yalwati inda acan ne tafi dadewa suna ta hira da Murja da sauran yammatan, suna ta competition gurin farantawa Diyam.

A gidan Kawu Isa shima ya karbe ta sosai shi da iyalinsa. Sun jima suna hira yana tayi mata nasiha a game da aure, sai taga kamar wani chance ne ta samu na kokarin gyara tsakanin su da Alhaji Babba. Tace "Kawu, mu kuwa zamu ji dadi idan komai ya wuce tsakanin ka da Alhaji, kune iyayen mu, ta yaya zamuyi zumunci idan ku ba kwa yi?" Sai ya girgiza kansa yace "uwata shi zumunci yi min ne inyi maka, shi Alhaji Babba son kansa da son dansa ne ya jawo igiyar zumuncin sa da mutane duk ta gutsire. Ni fa wai kyautata wa ce na yiwa yaron nan na dauki yarinyar nan nace na bashi ita a daura musu aure saboda in gyara zumuncin da nayi tunanin kamar ya samu baraka, amma kinga sakayyar da ya saka min dashi. Dana je gurin uban na gaya masa ga abinda dansa yayi maimakon ya nuna alhinin sa kuma ya kira yaron nan ya nuna masa laifinsa sai ya shafawa idonsa toka yace shi ba dansa ne yayi ba, ko tambayar yaron ma fa baiyi ba. Yanzu gashi nan ya ga sakayya ai. Ni kuma gashi an barni da yarinya, ni ina ganin na kaita Kollere ta haihu a can ina tunanin kamar na rufe maganar ashe duk jama'a kowa ya sani. Jiya jiyan nan na fito daga masallacin unguwa naji ana maganar. Yanzu waye zai aureta da wannan tambarin? Menene makomar rayuwarta dana zuri'ar da zasu fito daga gareta?" Diyam tayi shiru tana tunani sai tace "Yanzu Kawu zaka hakura idan Saghir ya fito ya auri Suwaiba? Suka bude sabuwar rayuwa suka kuma rike dansu? Zaka yafe masa ka dawo da zumuncin ka da Alhaji?" Yayi shiru yana dan jujjuya kafa sai yace "yaushe Saghir din zai fito?" Diyam tace "very soon, insha Allah" sai yace "Allah ya fito dashi lafiya, abinda zasu yi shida mahaifinsa idan ya fito din shine zai zama tubalin cigaban alaka a tsakanin mu".

A cikin gidan sai Diyam taga bata ji dadin ganin Suwaiba ba duk ta rame, duk da cewa ita mai kiba ce amma yanzu duk ta sirance, farin ma ya ragu amma sai Diyam ta danganta hakan da haihuwar da tayi. Sai da Diyam tazo tafiya sannan Suwaiba ta biyo ta da niyyar rakata sai tace "Diyam kinga Jawad a gidan Alhaji?" Diyam ta gyada kai tana kallon ta, sai tayi murmushi kawai, anan Diyam ta fahimci problem din Suwaiba, kewar jaririnta take yi, sai tace "Diyam naga abban mu ya sakar miki fuska, dan Allah ko zakiyi masa magana ya karbo min Jawad" Diyam tayi shiru bata ce mata komai ba saboda ita dai ba zata iya wannan rashin kunyar ba. Sai dai kuma ta tausayawa Suwaiba saboda tasan zafin rabuwa da ?a musamman ma wannan da yake dan jaririn da ko nono ba'a barta ta bashi ba. But hausawa sunce idan bera da sata to kuwa daddawa ma tabbas da warinta. Tabbas Saghir yayi laifi amma kuma itama Suwaiba da akwai nata laifin da har ta bari dadin bakinsa da kyawun fuskarsa suka rude ta ta bude masa kafafuwanta yayi mata ciki. Abinda ta shuka ne itama take girba.

Sai Diyam tayi tunani akan lalacewar zumuncin zamani. Babban dalili a fahimtarta shine son kan mu da muke dashi da kuma nuna son yayan mu a fili. Yes, an sani kowa yana son dansa amma hausawa sunce kaso naka ne duniya ta kishi ka kuma ki naka duniya ta so shi. Duba misalin uwa in ta kama danta tana duka idan yayi laifi, sai kuga mutane sun tafi da gudu sun karbe shi a hannunta suna bata hakuri suna kuma lallashinsa. Amma idan da ace zaiyi laifin ta goyi bayansa ta nuna cewa ba laifi yayi ba sai kuga mutane suna yi musu tsinuwa daga ita har shi. Daga nan kuma zasu fara ja baya dasu, zasu yanke zumunci dasu, in yayi laifin ma babu mai kwabar sa babu mai hana shi. Wannan tsarin na daga ni sai yayana shine tsarin daya tarwatsa zumunci.

A gidan Mama suka kai har dare. Diyam ta tambayeta shawara akan kayan dakin da zata yiwa su Murja, shin ta siya musu kayan ne ko kuma ta basu kudi kowa ya siya da kansa? Sai Mama tace "ina ganin ki sai musu furnitures, sai kuma ki basu kudin da zasu sai sauran kayayyakin anfaninsu tunda kowa da irin taste din ta"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login