Showing 3001 words to 6000 words out of 174346 words
ba" Wayar Diyam tayi kara ta kalleta kawai ta dauke kai. Judith ta dauka tana kallon sunan mai kiran har ta katse sannan ta ajiye tace "ban taba ganin marar zuciya irin mutumin nan ba, wulakancin da kike masa Diyam ya isa haka" Murjanatu ta daga hannu tace "hey, yayan nawa kike cewa marar zuciya?" Tana yin shiru wayar ta tana yin kara, ta langwabar da kai tace "Please Diyam, kinga ya kira a wayata. Please just for today" Diyam ta harare ta bata ce komai ba, Murjanatu ta daga wayar ta gaishe da wanda ya kira tana kallon Diyam tace "lfy lau take, yanzu muka dawo daga lecture wallahi duk mun gaji yaya. Eh bata zuwa da motar wai exercise ne zuwa school din. Eh shikenan for today. Gata nan tana cin abinci. Bata ci da yawa wallahi yaya, wai tuwo take so. Ah ah ni ban sani ba wallahi. Yaya ni Wallahi ban iya tuwo ba. Okay, sai anjima" ta ajiye wayar tana turo baki fuskarta kamar zata yi kuka tace "wai inyi miki tuwo yau da daddare ince with love from him" duk suka yi dariya, Diyam ta tashi tana rawa tana yiwa Murjanatu gwalo ita kuma ta dauki pillow ta bita da gudu suka shige corridorn da bedrooms dinsu suke.
Diyam.......... writing
[1/2, 9:01 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Three
Bayan tafiyar su Diyam, ya jima zaune shi kadai, yana ta sakawa yana kwancewa yana kuma zukar hayaki zuwa hunhun sa. Sai da ya ga kwalin ya kare sannan ya jefar da shi ya duba agogon hannunsa yayi tsaki ya mike. Cab ya tare zuwa hotel din da ya ke. Yana shiga dakin ya zauna akan gado yana kare wa dakin kallo kamar yau ya fara ganinsa, idonsa ya sauka akan hoton wata yar kyakkyawar budurwa akan study table dinsa tana murmushi. Ya lumshe idonsa ya bude. She have been the reason for everything daya ke ciki a yanzu, for all his pain and his agony. Ya dauko wayarsa yayi dialing number dinta for the hundredth time amma yanzu ma kamar ko yaushe bata dauka ba. He wandered me yasa ba tayi blocking dinsa ba dan gwara ya kira bata shiga ba akan ya kira ba'a dauka ba, meaning ta gani kenan, meaning tasan all what he is going through but she just doesn't care.
Fatima sunanta, Khausar suke kiranta, he had been in love with her for as long as he can remember, maybe tun da yasan menene love din but he failed to tell her. Daga baya kawai sai yaji labarin wai zata auri brother dinsa, that has been the beginning of his agony, wannan ne asalin dalilin fara shan sigarin sa. Yayi iyakacin kokarinsa tun a lokacin dan ganin cewa ya cire ta a ransa and he succeeded a little, but then sai auren baiyi da brother din nasa ba and his brother ended up marrying another. Wannan turn of events din ba karamin faranta masa rai yayi ba, he saw it as another chance na auren wadda yake so.
Shekara guda kenan da faruwar hakan. A cikin shekarar ne kuma yayi failing terribly in his course of study a Abuja, amma sai ya alakanta hakan da cewa dan baya son course din ne, yace yafi son yabi footprints din maternal grandmother dinsa wadda ta kasance lawyer, da kyar yayi iyakacin kokarinsa har ya samu aka barshi ya taho UK karatu duk da cewa iyayensa basu so hakan ba sunfi son ya zauna tare dasu amma saida ya taho tare da daurin gindin kakar tasa, yayi hakane saboda ita, saboda Khausar, for she now lives in UK tare da auntyn su. But sai me kuma? He realized bayan zuwansa cewa ai she is already dating his cousin kuma, wannan yasa ya daura damarar ganin ko sama da kasa zasu hadu sai ya raba wannan relationship din, wannan ya jawo rigima ba yar kadan ba tsakanin sa da cousin dinsa Ayan and he failed miserably. A karshe Khausar looked into his eyes and said "I will never marry you ko mazan duniya sun kare", and that made him mad, so mad that when his aunty tries to resolve the issue he looked into her eyes and said "go to hell".
Sati biyu kenan da faruwar hakan. Tun daga ranar ya hado kayansa ya dawo wannan hotel din da zama shi kadai. Kuma tun daga ranar babu wanda ya neme shi kaf family dinsu not even his Mami.
But wannan duk ba shine babban problem dinsa ba. Problem dinsa shine satin sa daya da barin gidan auntyn sa parents dinsa sukayi blocking dinsa out of their family bank account. Tun tashinsa da wannan account din suke amfani gaba daya gidan, kowa yana da access da shi sai dai kawai a karshen wata kayi bayanin abinda kayi da kudin daka dauka, yanzu babu. Shi kuma ba aikin yi ba, dan haka blocking dinsa daga family account ya mayar dashi almost koboless. Bashi da komai, hatta kayan abinci bashi dasu kuma kudin siyan abincin nasa has almost run out, zuwa karshen satin nan yasan ko na abinci bashi dashi.
Yasan wannan duk hikimar Mami ce, they want to fish him out ya kawo kansa ya karbi laifinsa, shi kuma yana jin tsoron yadda hukuncin sa zai zama, ba zaiji da dadi a gurin daddyn sa ba. Kuma yasan he have lost Khausar for good. Yayi biyu babu. Abinda yake bukata a yanzu shine karfin gwuiwar facing family dinsa, accepting mistake dinsa da kuma repenting, but to do that yana bukatar courage, yana bukatar wani yayi masa magana at least ko fada ne ayi masa a gaya masa yayi ba dai dai ba.
Bai san mai yasa yarinyar dazu ta fado masa a rai ba, Diyam. Ya kwanta ya rufe ido yana tunano fuskarta, tabbas tana da courage. From her looks, yadda take ware kanta daga cikin mutane zuwa yadda turancinta bai gama nuna ba yasan cewa she is from a poor background, maybe irin yayan talakawan nan ne da gwamnati take dauka take basu scholarship suke tahowa kasashen waje suyi karatu. But she really does have courage, daga yadda tayi magana rannan a class da kuma yadda tayi facing dinsa straight in the eyes ta gaya masa maganganu. Har dare yarinyar tana cikin ransa, amma kuma ya kasa yanke mata hukunci a ransa.
Washegari kamar kullum Diyam ta riga kowa tashi. Tayi wanka tayi alwala tazo ta bude al'qurani tana bita har akayi assalatu sannan ta je dakin Murjanatu ta tashe ta tazo ta tayar da sallah. By seven har ta gama komai, ta dumama sauran tuwon jiya ta zauna tana ci Judith ta fito tayi joining dinta sannan Murjanatu ta fito itama, but sai taki cin tuwon ta hada tea da bread ta sha. Suna yi suna hirar abubuwan da suka shafi karatun su, Murjanatu tana ta mitar takura musu da Diyam take yi suke zuwa school a kafa bayan ga mota an ajiye musu musamman saboda zirga zirgar su.
Suna shiga makaranta Murjanatu tana haki ta kalli Diyam tace "you and yaya na deserve each other. Kafiya ce daku da naci akan abinda kuka sa kanku. At the end kuma ku wahalar da wanda yake tare daku. Ni dai daga yau na daina turturing kaina wallahi, motar zanke shigowa koda ni kadai ce" Diyam ta daga gira daya tace "ba sai ki shiga ba, in kin iya driving din" suka yi dariya tare da Judith, ita kuma Murjanatu ta tura baki tayi gaba tana kunkuni ta barsu tunda ba department dinsu daya ba, suna dan yin gaba kadan suka rabu da Judith itama sannan Diyam ta karasa department dinsu ita kadai.
Tun daga nesa ta gane shi. Yana tsaye kamar kullum da headphone a kunnensa da kuma sigari a hannunsa. Ta duba agogon hannun ta taga it is not 8:00 yet amma har ya fara zuke zuke, maybe ko breakfast baiyi ba. Ta dauke kai ganin cewa bai ganta ba dan kamar yayi zurfi cikin tunani.
Har suka yi nisa da lecture din tana ta saka ran ganin ya shigo amma shiru bai shigo ba, sai da aka fara concluding sannan ya shigo dan haka ko zama bai gama ba malamin ya fita, and she felt sorry for him. Suna nan wani malamin ya sake shiga ya gama ya fita daga nan kuma zasuyi one hour break sai su sake wata shikenan. Ta fita ta nemi coffee shop ta zauna aka kawo mata coffee da cake taci duk da dai ba yunwa take ji ba but she just need to eat something saboda suna da wata two hours lecture din, Madam Sally. Tana zaune ta hango wucewarsa yayi hanyar gate. She wonders ina zaije tunda suna da wata lecture din? Sai kuma ta daga kafada tana mamakin me yasa ta damu da business dinsa.
Har suka tashi a ranar bata kara ganin sa ba. Da daddare suna cin abinci ta bawa su Murjanatu labarin encounter dinta da guy din tace "I am just feeling sorry for him. He obviously is distracted, confused maybe" Murjanatu ta harare ta tace "ni dai babu ruwana. Daga tausayi kuma sai muji wata magana ta daban. Kinsan in yaya yaji wannan maganar zai iya harbo nuclear bomb ya tarwatsa Oxford gaba-daya" Diyam ta daga kafada tace "Allah yasa uranium zai harbo ba nuclear bomb ba. I will talk to whoever I want to talk to" Murjanatu tace "you are not going to give my brother a break are you?" Diyam ta mike tsaye tace "no i am not, har sai yayi abinda nace masa" Murjanatu tayi murmushi tace "maybe baki san shi ba kamar yadda kike tunani" Diyam ta wuce daki da sauri tana jin zafi yana taso wa a zuciyarta.
Da safe basu da lecture da wuri dan haka suka yi baccin su sosai. Sai after ten Diyam ta tashi ta fita parlor ta tarar Judith tana kitchen tana hada musu breakfast. Ta dawo dakin ta ta shiga wanka. Tana fitowa wayar ta tana ringing amma ko kallonta bata yi ba ta dauke kanta ta cigaba da shiryawa amma a zuciyarta tana mamakin yadda yake keeping track din komai nata, yasan sanda take da lectures yasan kuma sanda take free. Wayar tana katsewa taji text ya shigo, ta dauka takaranta, sakon barka da safiya ne mai hade da tsadaddun kalaman da sai da suka huda zuciyarta amma sai kawai ta tabe baki ta ajiye wayar. Ita dashi a ga wanda yafi taurin kai.
Diyam......... writing
[1/3, 10:07 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Four
Tana saka kaya Murjanatu ta shigo dakin, daga ganin fuskarta Diyam tasan akwai problem, ta ajiye skirt din hannunta tana bawa Murjanatu data zauna a kan gado dukkan attention dinta. Ta daga gira daya sama tace "me yace kuma?" Murjanatu tace "he asked me about Judith" Diyam ta hade rai tace "what about her" Murjanatu tace "he asked wai bata kawo mana maza gida? Na gaya masa bata kawo wa but he didn't sound convinced." Ta sunkuyar da kanta kasa tace "am afraid he is going to send her away" Diyam ta dafe kanta tana zagaye dakin da bacin rai a fuskarta sannan tace "tell him nace Judith is my friend, if he wants to get to her he will have to go through me. Ni na kawo ta gidan nan, in yana son ya kore ta sai ya fara kora ta tukunna" Murjanatu ta saka hannayenta biyu ta toshe kunnuwanta tace "ba dani ba, bani Murjanatu ba. Uwata ta daina haihuwa ballantana ta sake haifo ni" Judith ta bude dakin ta leko kanta tace "hey girls, food is ready" sai kuma ta tsaya tana kallon yadda suke kokarin kakaro murmushi.
A bayan lecture hall dinsu ta hango Sadiq. Shi kadai kamar kullum, da sigari a hannunsa kamar kullum, tayi saurin dauke kanta ganin yana kokarin juyowa. Amma sai ta tsaya a kofar hall din bata shiga ba tana so taga yau zai shiga ko yauma zamansa zaiyi a waje. Sai da aka kusan fara lecture din sannan ya taho, a gabanta a jefar da sigarin hannunsa ya saka kafa a murje ta, zai wuce Diyam tace " you know smokers tend to die young ko?" Ya kalleta for some seconds, ya busa mata hayakin bakinsa yace cikin husky voice "says who? I can't believe malama kamar ki ta yarda da wannan saying din. Kin manta kaddara? Ina islamiyyar taki ta tafi?" Ta sa hannu ta kade hayakin daya huro mata tace "maybe ni da kai munyi understanding kaddara differently. Tell me why do we pray? Why do we struggle? Me yasa muke neman duniya kuma muke neman lahira in dai har an riga an rubuta komai, me yasa ba zamu kwanciyar mu ba mu jira abinda aka rubuta mana yazo ya same mu. Yes kaddara rubuyacciya ce, major abubuwan da zasu faru a rayuwar mu a rubuce suke but what is in between depend on choices din da muke making. Wannan shine fahimtata. Yes, kamar yadda ka fada shekarun da aka rubuta maka ba zasu chanza ba amma how you are going to spend them depend on you, ko dai kayi spending dinsu healthy and happy in ka daina shan sigari ko kuma kayi spending dinsu with lung cancer in ka cigaba da smoking" ya kalle ta daga sama har kasa yace "go to hell, both you and your preaching" ya shige class din ya barta a tsaye. Taji zafin maganar sa amma sai ta hadiye ta bishi a baya.
Suna shiga class din wani guy ya kalli Sadiq yace "the Nigerian guy. Why do you skip madam Sally's class yesterday, don't you want to depend your country anymore?" Sadiq yayi banza dashi ya shige ya samu guri ya zauna. Sannan yan ajin suka juyo gabaki daya suka zubawa Diyam ido, ta yi gyaran murya tace cikin harshen turanci "abinda na fada rannan gaskiya ne, gaskiya ne based on sani na. Shima kuma musa min din da yayi gaskiya ne based on sanin sa. We may have come from the same country but we live in different worlds. Muna zama cikin different mutane, muna kallon rayuwa from different perspectives. My being right doesn't makes him wrong. You as potential lawyers should know that" duk yan ajin suka kada mata kai cike da gamsuwa sannan ta wuce ta shige seat din karshe ta zauna.
Madam na shigowa ta fara tambayar Diyam "will you like to continue with that day's argument?" Diyam ta girgiza kai tace "no ma'am, it's okay" ta juya gurin Sadiq tace "what about you, are you satisfied as well?" ya gyada kai yace "am okay ma'am. We now understand each other" sai ya juya a hankali ya kalli Diyam, itama ta dago kai suka hada ido and she smiled at him, a take ya fahimci cewa she have the brightest smile he have ever seen.
Bayan sun gama dukkan lectures dinsu, ta fito tana tsaye tana jiran Murjanatu sai gashi ya taho, ya tsaya dan nesa da ita kadan yace "waiting for a friend?" Ta daga murya tace "yeah" sai kuma taga ya zo zai wuce ta, tace "my name is Haleema. Haleema Usman Kollere. But people call me Diyam" ya gyada kai yace "I am Sadiq, Sadiq Abubakar Sadiq. Most people call me Bassam. You can call me that as well".
Tayi murmushin ta mai kyau tace "nice to meet you Bassam" ya danyi dariya yana jujjuya kai yace "You have a beautiful smile, very beautiful. Ban san me yasa ba kya yawan yinsa ba. Ta daga gira daya sama tace "if it is beautiful than it is precious kenan. Abu mai tsada kuma kasan ba'a ko ina ake ajjiye shi ba" ya sake dariya, his eyes twinkling, amma bai ce komai ba, tace "and you. Ban dauka ka iya dariya ba" ya gyara fuskarsa yace "believe me, I do laugh alot. Yanzu ne dai I am in kind of not laughing situation. But na miki alkawari in na fita daga ciki we will laugh more" daga haka ya juya da sauri ya bar gurin.
Yana tafiya Murjanatu tana karasowa. Tana kallon bayansa tace "who is that guy? Amma ya hadu fa" Diyam tayi murmushi bata ce komai ba, Murjanatu ta sake cewa "ko shine rannan kuke maganar sa da Judith?" Suka jera suna tafiya da Diyam tace "yeah shine" Murjanatu ta bata rai tace "then it is official, gaskiya ina taya yayana kishi. Lallai ma Diyam din nan" ta turo baki, Diyam tace "oh ashe baku hadu ba daga ke har yayan naki tunda insecurity yana damunku. Ashe kujerar taku bata kafu ba, ai hausawa sunce fargaba asarar namiji" Murjanatu ta harari bayan Bassam da har yanzu suna iya hango shi tace "ohh dama wancan namiji ne? Ai na dauka macece ta aske kanta ta saka wando. Ai wannan yana ganin yayana zai narke a gurin dan tsoro. Wannan daga ganin sa rainon madara da cerelac ne, yayana kuwa tuwon biski yaci da kunu dan haka ba sa'an sa bane wallahi" Diyam da take ta dariya tace "naga alama kam. Tuwon biskin ne yasa kansa yayi tauri da yawa" ta fada tana lakucewa Murjanatu hanci, Murjanatu tace "ouch, sai kin nane min hancin kinsa na rasa mashinshini?" suka yi dariya baki daya, sannan Murjanatu ta fara rokon Diyam akan ta fita dasu yawo yau da yamma "Please, Please Diyam, this routine is killing me slowly, ai ance taba kida taba karatu ko?" Diyam tace "sai jibi weekend sai muje muyi siyayyar abubuwan da bamu dasu a gida"
Washegari Friday, Diyam tana zaune a seat dinta tana rubutu taji ance "hi Diyam" ta dago tana kallonsa bata ce komai ba, sai kuma ya shafa kansa yace "Assalamu alaikum" tace "ameen wa alaikas salam Bassam" ya kalli seat din kusa da ita yace "can I?" Ta gyada kai ba tare data dago ba. Ya zauna ya fito da book dinsa pretending to be reading amma ita tasan ba karatun yake ba. Can ya ajiye littafin yayi tagumi yana kallonta yace "can I ask you something?" Ba tare da ta kalleshi ba tace "sure" yana