Showing 81001 words to 84000 words out of 174346 words
dauki Subay'a muka tafi sama saboda naji dadin jikina sosai, na tafi da niyyar inyi mata wanka nima inyi, Asma'u kuma ta tafi kitchen tana gyara abinda muka bata. A lokacin Saghir ya dawo, yaga motsin Asma'u a kitchen sai ya leka, yana ganin ta yace "ke! Yaushe kika zo gidan nan?" Ta dan tsorata saboda bata san shigowar sa ba tunda shi dama ba sallama yake yi ba, ta gaishe shi sannan tace "dazu muka zo duba Adda, ni da Inna" yace "ita Addan taki ce tace muku bata da lafiya? ina gwoggon take?" Ta nuna masa daki a ranta tana tunanin yau Inna zata sha kunya in suka hadu da Saghir.
Ya tura kofar ya shiga, Inna tayi saurin tashi duk ta diririce saboda ganin sa haka a cikin dakin gashi tana kwance dan ma dai ba kaya ta cire ba, ya tsaya a tsaye yace "gwoggo Amina barka da zuwa, ashe waccan makaryaciyar cewa tayi bata da lafiya?" Inna tace "uhm uhm Saghir ba karya tayi ba, kowa yaga Diyam ai yasan bata da lafiya" ya daga kafada yace "to ai sai kuzo ku tafi tun kafin dare ya sake yin nisa kuma" Inna tace "mu tafi kuma?" Asma'u data shigo tace "dare ai ya riga yayi, ballantana daren damina? Anan zamu kwana da safe Inna zata tafi ni kuma zan zauna sai sunday" ya girgiza kansa "no, kuzo ku tafi yanzu. A Kano ai dare baya yi ko sha biyu kuka fita zaku samu abin hawa" ya ciri dari biyar ya ajiye a kusa da Inna "gashi ku hau adaidaita" ya juya ya fita.
Suka tsaya cirko cirko suna kallon juna, Asma'u tace "hamma Saghir bashi da mutunci Inna, bara inje in gayawa Adda tayi masa magana, yanzu ina zamu fita a wannan unguwa tasu duk kango? Ga shi har yanzu yayyafi ake yi" Inna ta girgiza kanta, "kar ki gaya mata. Dauko mayafin ki mu tafi. Allah yana nan ai shi zai kaimu gida lafiya" Asma'u bakin ciki ya ishe ta, Inna ma wani irin zafi zuciyarta take yi mata amma bata son gaya wa Diyam, shi da yayi din ai yasan ba dai dai bane kuma Diyam sai dai ta bata ranta kawai amma ba zata hana shi abinda yayi niyya ba, tasan ko bare Diyam ta aura ba zai musu wannan wulakancin ba ballantana ɗan yayanta, ɗan yayan mijinta. Ko Sadauki Diyam ta aura ba zai wulakanta Inna ba.
Mayafan su kawai suka dauka, lokacin karfe goma har ta gota Asma'u dan bakin ciki ko kayanta bata dauka ba suka fita ni ina can ban sani ba, ga duhu ga yayyafi anayi ga uban sanyin da yake kadawa. A bakin gate suka yiwa maigadi sallama, yace "Hajiya tafiya a cikin ruwan nan? Ku bari mana sai da safe ko kuma ayiwa mai gidan magana ya kaiku a mota" Asma'u tace "maigidan ai shi ya kore mu kuma yafi kowa sanin yana da mota".
Hanya duk ruwa ya kwanta haka suka ringa haskawa da wayoyinsu suna tafiya karnuka suna tayi musu haushi, babu alamar mutum ballantana abin hawa har suka fita bakin titi. Suka tsaya suna ta karkarwar sanyi amma babu abin hawa babu alamun sa. Asma'u ta fara kuka "Inna mu koma mu gaya masa bamu samu ba. In baya son mu kwana a gidan sa ba sai ya kaimu gida a mota ba? Ai muma muna da gidan ba'a titi muke ba" Inna dai bata ce mata komai ba. Can bayan sun gaji da tsaiwa sai suka fara tafiya a kafa suna saka ran maybe in sunzo round din yan kaba zasu samu adaidaita a can, ko babur ne ma in suka samu hawa zasuyi in dai zai kaisu gida. A lokacin sha daya na dare har ta wuce. Suna cikin tafiya ne wata mota ta tsaya a bayansu, suka juyo suna tunanin ko taimako ne tazo musu amma sai ji suka yi anyi musu fito, daganan suka gane yan iska ne dan haka suka kara sauri. Aka sake biyo su a baya aka ce "yan mata ji mana" Inna ta kankame hannun Asma'u suna sauri kamar zasu tashi sama amma sai motar ta sha gabansu, aka haske musu fuska da fitila sai wani yace "ashe ma tsohuwa ce da yarinya. Kyakykyawar yarinya" Inna ta tura Asma'u bayanta a lokacin da maza biyu suka fito daga motar. "Haba baba, Menene na boye ta? Rage mata hanya kawai zamuyi fa" dayan yace "kema in kina so sai mu rage miki hanyar amma a boot" suka kwashe da dariya sannan suka yo kan su Inna a tare. Da gudu su Inna suka diba, Asma'u tana gaba inna tana binta a baya mazan suna binsu a baya, daya yace "kunga tsohuwa ita ma ta iya gudu? Lallai itama da sauranta ashe". Basu yi wani nisa ba suka cimmasu suka kama su, Asma'u tana ta ihu, Inna tana ta rokon su su rabu dasu "me muka yi muku yaran nan? Ku sake ta dan Allah marainiya ce" daya yace "nima maraya ne, kinga mun dace kenan".
Sanda suke tisa keyar Asma'u cikin mota ne wata mota ta hawo ta bayan su a hankali, har ta gibta kuma sai tayi reverse da sauri ta tsaya. Asma'u ta fara kokawa dan ta samu karfin ganin taimako yazo mata wannan ya hana su tayar da motar har na cikin bakuwar motar ya fito da sauri ya taho gurinsu. Wanda yake rike da Asma'u ya fara zarowa daga motar yayi masa naushi biyu take sai ga jini a gaban rigarsa. Ba shiri ya sake ta ya shige motar, wanda yake seat din driver yayi saurin tayar da motar dan yana gudun karbar nasa rabon suka bar gurin a guje. Asma'u ta fadi a gurin tana mayar da numfashi cike da tsoro sannan ta juya tana kallon wanda ya taimaka mata, sai taga Inna ma shi take kallo amma maimakon tsoro mamaki ne kawai a rubuce a fuskarta. "Sadauki?" Ta fada da rawar murya "Sadauki!" Asma'u ma ta fada, tabbas, wannan fuskace da baza ta manta ba duk kuwa da cewa rabon data ganshi tun tana shekara tara a duniya yanzu kuwa shekarar ta goma sha shida. Sai ta mike da gudu ta tafi ta rungume shi. "Yar Asama" ya fada yana rabata da jikinsa, fuskarsa dauke da murmushi.
Ni ina can ina yiwa Subay'a wanka naji shigowar motar Saghir, har na gama yi mata wankan na shirya ta nima na shiga nayi na fito na tarar har ta yi bacci na shimfida sallaya na tayar da sallah, sai dana idar sannan na sauka dan in tabbatar su inna basa bukatar komai kafin in kwanta, amma sai naga dakin ba kowa, kitchen ma haka. Wasa wasa na chaje gidan amma babu su babu alamun su, hankalina ya fara tashi na koma sama na dauko waya da niyyar kiransu amma naji ance min "your account is not sufficient to make this call" bank da kudi, da zan kira Inna jiya ma ranta nayi a network dina. Hankalina in ya kai dubu duk ya tashi a lokacin dole na tafi dakin Saghir da sauri na fara buga masa kofa. Ya bude ya tsaya yana kallona nace "su Inna, ban gansu ba, ka bani aron wayarka dan Allah in kira su" yace "sun tafi gida. Ni nace su tafi. Da iznin waye kika gayyato min mutane zuwa gidana?" Na fara girgiza kai na saboda mamaki nace "mutane? Su Inna da Asma'u ne mutane?" Yace "ohh, aljanu ne ba mutane ba?" Ban jira sauran maganar saba na shiga dakina da sauri na dauko hijab dina, nayi hanyar stairs, nima gidan zan bari tunda har zai iya ya kori uwata daga gidan nan toni zaman me zanyi a cikin sa? Da sauri naga yazo ya wuce ni ya riga ni sauka, ban fahimci me yake yi ba sai dana ganshi a bakin kofar fita daga pallon, ya saka key ya rufe kofar sannan ya juyo ya wuce ni hau stairs yana kallona yace "nasan in na ce miki in kika fita a bakin auren ki da sauri zaki fita tunda abinda kike so kenan".
Na bishi a guje ina ihu "ka bude min kofa Saghir, ka bude min kofa nace" sai ma ya shiga dakinsa ya rufe kofa ya rabu dani. Na dawo kasa da sauri ina neman hanyar fita amma babu, duk windows din gidan akwai burglers a jiki, kofar kitchen ta baya kuwa dama tun ina amarya data lalace har yau ba'a gyara taba mun dai a amfani da ita. Sai na kama kuka ni kadai kamar mahaukaciya ina zagaye gidan. Ji nake a raina gwara in kwana a titi a ranar akan in sake kwana a gidan Saghir. A haka har karfina ya kare na zauna na jingina kaina da jikin kujera ina ajjiyar zuciya. A raina ina aiyana abinda zanyi wa Saghir in wani abin ya samu su Inna.
A lokacin ne waya ta tayi kara, nayi saurin dauka na duba naga sunan Inna da sauri na amsa nace "Inna me yasa zaku tafi a cikin daren nan? Kuna ina Inna?" A nutse naji muryar ta, hakan ya kwantar da hankali na sosai tace "ki daina kuka Diyam, muna gida mun iso lafiya" nayi ajjiyar zuciya nace "alhamdulillah. Inna hankali na ya tashi sosai" sayi shiru sai kuma tace "Diyam, Sadauki ne ya kawo mu gida. Ba dan Sadauki ba Diyam yau da bansan me zai same mu ba. Sadauki ne ya taimake ni Diyam a lokacin da Saghir ya wulakanta ni".
?? DIYAM ??
?? DIYAM ??
By
Maman Maama
Episode Forty Two: A backlash
"Sadauki?" Na maimaita cikin tsananin mamaki "a ina Sadaukin ya ganku?" Sai ta bani labarin abinda ya faru dasu bayan sun bar gidan. Wannan ya kara ruda tunani na, me Sadauki yake yi a wannan hanyar a wannan lokacin har ya gansu ya taimaka musu? Duk da bansan a wanne hotel yake zaune ba amma nasan babu hotel a kusa damu, sannan unguwar mu wajen gari ne ballantana inyi tunanin ko wani abu ya fito nema kuma ma ai mutane masu kudi irinsa ba zasu fito neman abu ba sai dai suyi order a kai musu har inda suke. Tabbas ina bukatar yin magana da Sadauki. Amma dai ko menene yake yi a gurin am greatful da taimaka musu da yayi saboda I can only imagine irin horror din abinda zai faru dasu da bai zo din ba, wannan kuma sai ya kara hura wutar kiyayya da nake yiwa Saghir saboda shine ya kusa jefa su cikin wannan halin. Naso in tambayi Inna a game da Sadauki amma sai tayi min sallama tace dare yayi sai gobe zamuyi magana. Anan palo na karasa kwana saboda saman gani nake kamar na kara kusa da Saghir.
Sa safe Subay'a ce ta tashe ni tana neman abinci, da yake ban samu nayi bacci sosai ba shi yasa na makara. Na jata muka shiga dakin kasa mukayi sallah tare sannan muka shiga kitchen na dora mata noodles na soya mata kwai, ina cikin aikin Saghir ya shigo Subay'a ta tafi gurinsa da gudu ya dauke ta suka tsaya a bakin kofa yana kallona yace "me ake dafa mana ne?" Ko kallo bai ishe ni ba, shi har yana da karfin halin pretending kamar babu abinda ya faru? Subay'a ce ta bashi amsa, sai yace "Subay'a mommy fushi take yi da Daddy saboda yace zaiyi aure" na juyo na watsa masa harara, ni har na manta ma da yace zaiyi aure. Ina jin Subay'a tana tambayarsa menene aure, na bar musu kitchen din sai ya biyo ni yana cewa "wai duk kishin ne haka? Ni na taba ganin anyi kishin wanda ba'a so?" Har zan wuce kuma sai na dawo na karbi Subay'a daga hannunsa nace taje kitchen ta dauki abincinta taci sannan nace masa "Saghir ko matan duniya zaka aura ko a tafin kafar Halima. Ni din ce dai ba zaka samu zuciya ta ba wallahi. Kuma su Inna sunje gida lafiya babu abinda ya same su, sun samu wani bawan Allah wanda yasan mutunci da darajar mutane ya taimaka musu kuma ya kaisu har gida a mota, bawan Allahn da basu hada dangantaka ta jini dashi ba" yace "ohh there is that, ashe fushin biyu ne" wato shi a nufinsa har ya manta da abinda yayi. Yace "to yanzu wanene bai san darajar mutane ba? Ni mutum ne mai ka'idoji kin sani kuma, ni bana son a shiga rayuwata sam bana son ake kawo min mutane cikin gidana" nace "gida? Amma dai kasan muma muna da gida ko? Kasan ba'a titi muke ba ko?" yace "sai su zauna a gidan naku kar su zo min nawa gidan, as simple as that" na girgiza kaina nace "ni Saghir bani da sauran karfi, na zuciya da na jiki da zanyi fada da kai, ka fadi duk abinda kake son fada ka kuma yi duk abinda kake son yi. Duniya ce, akwai ranar kin dillanci kuma ina sanar maka da cewa tana daf da zuwa" ban jira abinda zai ce ba na haye sama. Ina jinsa ya bude kofar palo ya fita, na leka naga shi da Subay'a ne suka fita a mota, na sauko kasa da sauri na tura kofa naji a rufe, wato rufe ni yayi daga waje ya tafi da key din.
Ina zama Inna tana kira na, dama tun dazu nake ta zuba idon ganin kiranta amma sai naji muryar Asma'u tace "Adda inna fa kuka take yi tun da muka dawo jiya da dare, tun da taga Sadauki take kuka na rasa dalili" na gyada kaina, ni nasan dalilin, nace "me Sadaukin yace sanda ya dauke ku?" Tace "baice komai ba fa, kawai tsokana ta yayi tayi har muka zo gida. Inna tace masa tana son ganin sa sai yace zai zo watarana" na tambayeta "ya tambaye ki ni?" Tace "a'a" na lumshe ido ina jin hawaye yana taho min. Idan ni ce na hadu da yaya ladi misali nasan abinda zan fara tambayarta shine Sadauki. Ko dai Sadauki ya daina so nane? Duk da dai Saghir yace min baiyi aure ba amma for all I know maybe yana da budurwa yanzu, maybe ma an kusa bikin. Maybe ma yaruwarsa zai aura a Maiduguri.
Nace da Asma'u ta kira Mama ta gaya mata abinda ya faru, ni ba zan iya zuwa in lallashi Inna ba saboda Saghir ya rufe ni a gida. Na san kuma yanzu inna tana bukatar wanda zasuyi magana dashi, musamman wanda yasan abinda tayi wa Sadauki da shi kuma sakayyar da yayi mata.
Ta barshi a titi a lokacin da yafi bukatar gida, shi kuma sai ya dauko ta daga titi ya kai ta gida a lokacin da tafi bukatar hakan.
Washegari Sunday, Saghir ya fita sai gashi ya dawo yana washe baki, ko kula shi banyi ba dan ban damu da insan me ya saka shi farin ciki ba amma sai ya zauna yana cewa "subay'a daddyn ki zai tafi kasar waje, me kike so in siyo miki?" Ta mike da murna tana tsalle tana yi masa list din kaya, shi kuma yana ta dariya, sai ya kalle ni yace "ki hada min kaya, gobe zan tafi oga ya tura ni zanyi signing contract da wani company a can" na dauke kai kamar ban ji shi ba sai yace "dama nan da two months ne tafiyar nan tazo, da da amarya ta zan tafi. Ohh ban fada miki ba ko? Nan da wata biyu ne aure na fa" nace "to ka daga tafiyar mana sai anyi bikin? Ohh na manta, ashe bada kudinka zaka yi tafiyar ba da kudin oga ne kuma dole sai abinda oga yace sannan zakayi tunda kudin sa ne. Mtsww i pity you" da naga dai neman magana yake yi sai na tashi na bashi guri saboda ni bana son rigima dashi a gaban Subay'a, amma kuma sai na samu zuciya ta da jin haushin Sadauki na budawa Saghir da yake yi.
Shi ya hada kayan tafiyar sa da kansa, da safe ya turo Subay'a ta kira ni naje na tsaya a bakin kofa yace "rashin kunyar ki, da rashin biyayyar ki shi yasa har yanzu auren mu yaki daidaita, da ace kin kwantar da kai, kin bini yadda nake so da ba karamin jin dadi zakiyi tare da ni ba. Kinga wannan tafiyar ma oga mu biyu ya biya wa, ni dake, yace in tafi da matata saboda wata daya zanyi kar in zauna gwauro a can, kinga da sai muyi tafiyar mu ni da ke da Subay'a but I guess I will have to go alone" ya ajiye kudi a kan mirror "ga kudin cefane nan, kinsan ni ina tsoron Allah dan haka ina kokarin sauke hakkin ki da yake kaina. Ban yafe ba, in kika fita ko da kofar gida ne indai ba abinda ya shafi makarantar Subay'a bane ba, sai kuma rashin lafiya, Allah yana kallonki in kika ci amana ta in bana nan" nayi murmushin takaici kawai, akwai amsoshi da yawa a raina wanda nake so in bashi amma ganin Subay'a yasa nayi shiru har ya dauki jakarsa ya fita yana cewa "gwara mutum ma ya dan bar kasar ya sarara na kwana biyu".
Tafiyar Saghir da kwana biyu Alhaji Babba ya kira ni a waya, I can't remember last sanda ya kira ni. Na dauka na gaishe shi sai naji muryarsa wani iri yace min "Diyam ki zo gida ina nemanki dan Allah" sai naji wani iri da yace min dan Allah, duk da dai Alhaji Babba yayi sanyi sosai tunda yanzu kusan hannu baka hannu kwarya suke zaune a gidan, bashi da komai sai yan abokai da suke taimaka masa da kuma kawu isa shima da yake dan bashi wani abu, duk sana'ar daya kama sai ta rushe, kullum muka je gidan yana ta cewa makiya ne suka sako shi a gaba ni kuwa deep down nasan inda matsalar dukiyar Alhaji Babba take, kudin mune da yaci, dukiyar marayu daya handame ya hada da tasa dukiyar da yasha wahala