Showing 78001 words to 81000 words out of 174346 words

Chapter 27 - Diyam Book 1 Hausa Complete

07 Jan 2025

1105

a duniya. Kinga a office dinmu tun daga dawowar oga yadda ake ta rububi ana shishshige masa kowa yana so ya kafa kansa, ni kuwa babu abinda ya dame ni dasu aikin gaba na kawai nake yi. Amma kinsan ina daki kawai yayi kirana a waya, wai dan Allah in an jima inje airport in dauko shi zai dawo daga Maiduguri, kinsan dan can ne ai, babarbare ne" na cigaba da harkokin gabana looking uninterested, Amma kirjina lugude kawai yake yi nace "hmmm, Allah ya taimaka" ya danyi shiru sai kuma yace "I have an idea, tunda kowa neman shiga yake a gurin oga why not me? Nima ai ina son promotion din. Idan na dauko shi daga airport nan gidan zan kawo shi, you prepare dinner for him tunda dama bashi da aure kuma bashi da gida a hotel yake zama, nasan zaiji dadi, in ya ci abinci anan sai in kaishi hotel din da take zama" na yi saurin juyo wa ina kallon sa, sai na samu kaina da girgiza kaina nace "no" no matter how much zuciyata take son ganin Sadauki nasan ba dai dai bane ba, shigowar sa cikin gidan aure na ba abu ne mai alfanu ba "Please ka zarce dashi inda zai sauka kar ka kawo shi nan" ya mike tsaye yana kwantar da Subay'a da tayi bacci a hannunsa yace "yes, nan zan kawo shi first. Zan fita in yo miki cefane and you cook something nice for him, abincin da kika san mutane irin sa zasu ci" kafin in sake retaliating ya fita. Na zauna a gurin na dafe kaina kirjina yana bugawa da karfi, wata zuciyar tana gaya min cewa in gaya wa Saghir waye ogan sa wata kuma tana hanani har sai na samu Sadauki munyi magana na fahimci inda yasa gaba tukunna. But yaushe zan same shi? Ni a matsayina na matar ma'aikacin sa? Ni a matsayina na wadda yayi addressing as Madam?

Ina nan zaune har Saghir ya dawo da ledoji niki niki ya shiga kitchen ya ajiye, ya fito yace "ga nama can da kayan miya da fruits, akwai wani abu da kike bukata kuma?" Na langwabar da kai "ni yanzu mai zan dafa masa?" Yace "think of something, nima ban sani ba". Daga haka ya fita ya barni.

Sai dana kai Subay'a islamiyya sannan na dawo na shiga kitchen, na saka ledojin a gaba ina kallo, me zan dafa? Kuma wai Sadauki zan dafa wa abinci a matsayin sa na ogan mijina. Lallai life is full of twists and turns.

Sai na tuno da tuwon Ummah da take yi mana muna yara ni da Sadauki. Tuwon laushi miyar yauki sai ta dagargaza kaza a ciki ta cire kashin gaba daya. Sadauki yana so sosai dan har cewa yake yi ayi dan haka na nutsu na fara shirya masa. Na gyara fruit din nayi smoothie na saka a fridge. Zuwa magrib na gama na shirya komai a dining table sannan na fita na dauko Subay'a sai kuma na sake gyara gidan na saka turaren wuta naja subay'a muka hau sama.

A sama nayi wanka nayi mata wanka itama muka yi sallah tare sannan ta kwanta ina yi mata kitson da taki tsayawa ayi dazu, a haka har tayi bacci sannan naji shigowar mota, gabana ya yanke ya fadi na kalli window amma wani barin na zuciyata yace "kul kika leka kallon haramun" sai na kwanta na dunkule a guri daya kamar mai zazzaɓi, naji an tsayar da motar an kuma bude an fito sai dai ba'a rufe ba, naji ina son in san me yasa ba'a rufe din ba. Na jawo pillow na dora a kaina na danne da hannayena amma the next second sai gani na nayi a bakin window a bayan labule ina leka waje.

Saghir na hango a tsaye a bakin mota yana magana dana cikin motar wanda shi bai fito ba, sun jima suna magana a haka, kamar na cikin baya son fito wa yayin da Saghir yake ta insisting akan sai ya fito. Sai kuma naga ya zuro kafafuwansa ya fito Saghir ya rufe masa kofar sai suka jero a tare suka doso cikin gida, yayinda fitilar gaban gidan ta haske min su.

Two men; one fair and the other one dark, fair one din shine mijina amma ni zuciyata dark one din take so; one taller than the other ni kuma tall one din nake so, one younger than the other ni kuma younger one din nake so, one frowning the other one smiling ni kuma me frowning din nake so, one employer the other one employee ni kuma employer din nake so. But the other one is my husband. That was how cruel my was.

For a split second, Sadauki smiled, a smile that went straight to my heart, nayi saurin sakin labulen naja da baya kamar wadda ta taba wuta. Ji nayi kamar an debo wani tarin sonsa cikin trailer an zuba min a zuciyata sai naji tayi min nauyi dan haka na ruke kirjina na zauna akan gado ina ambaton sunan Allah da niyyar ya kawo min dauki a cikin lamari na tun kafin inyi tabewar da zata kaini ga halaka.

Waya ta ta fara ringing, da kyar nayi karfin halin dauka na kara a kunnena Saghir yace ina whisper "mun shigo. Ki zo ki kawo masa abinci" nace "dan Allah Saghir ka bashi kawai, bana jin dadi wallahi" nasan banyi rantsuwa akan karya ba saboda yadda nake jin jikina tabbas nasan akwai zazzaɓi a tare dani, yayi tsaki ya katse wayar. Na koma na kwanta na jawo Subay'a jikina na lullube mu, amma muna fikin kunnena sai yake kokarin zuko min maganganun da ake a palo, wishing to hear muryar Sadauki.

Ina nan kwance kawai naji an hawo saman sai aka bude dakin, Saghir ya shigo fuskarsa kamar zaiyi kuka "Diyam? Me yasa ne wai ke kullum burinki kiga na tozarta a duniya, why?" Na tashi zaune ina girgiza kaina nace "me nayi kuma?" Yace "tuwo. For God's sake tuwo Diyam zaki yi wa wannan mutumin da bana jin ya taba cin sa? Ko ni ba cin tuwo nake yi ba kuma kin sani" nace "cewa yayi ba zai ci ba?" Yace "to ni ina zan iya bashi? Kin san da yadda nayi convincing dinsa ya shigo kuwa kuma kawai sai inkai masa tuwo?" Na tashi na zura jihab dina na fita ya biyo ni a baya.

Yana facing stairs, wannan yasa ina fara sauka na ganshi amma shi kansa yana kasa yana daddanna wayar hannunsa. Na dauke ido na daga fuskarta ina kallon gefe nace cikin wata muryar da naji kamar ba tawa ba "Barka da zuwa" ya dago kai, kallo daya sannan ya mayar da ganinsa kan wayarsa yace "Barka kadai Madam. Ya gida?" Still with the Madam, na fada a raina and my heart hurts. Ban amsa ba na mike naje dining na duba na tabbatar komai yana nan yadda ya kamata sannan na dawo na tsaya ina kallon Saghir da yake ta kokarin yi masa hira nace "ga abinci a table Ko nan za'a kawo muku?" Sadauki ya mike da sauri yace "thank you, zamu ci a can din. Ni am fine ma really, maigidan ki yace sai nazo naci, so I guess I will just have a taste and go" sai kuma ya tafi dining area da sauri Saghir ya bishi a baya, yana zuwa ya dauki plate zaiyi serving kansa sai plate din ya zame daga hannunsa ya fado ya tarwatse, and I noticed that his hand was shaking. Saghir ya kwalla min kira "zo da sauri ki gyara gurin nan" amma kafin in karasa Sadauki ya bar gurin da sauri yayi hanyar waje, Saghir ya kalleni da alamar tambaya na daga masa kafada, sai kuma ya bishi wajen.

Na tsaya da tarin abinci a gaba na ina kallon kofa, so the mask has fallen, my Sadauki is still in there kawai duk pretence ne.

Ina tsaye Saghir ya dawo yace "get a basket ki zuva warmers din a ciki, he is taking it away" naje na dauko na hada masa komai har drink din na rufe, Saghir ya karba yana cewa "Allah yasa ma yaci, wannan mutumi kamar aljanu ne dashi".
[2/12, 6:05 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty One: A Stranger in the Dark

Ina jinsu suka fita daga gidan, and some parts of me went with them.

A juya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na koma sama nayi alwala na gabatar da sallar isha sannan na kai kuka na gurin ubangiji na. Bayan na gama nayi shirin bacci na zauna akan gado ina jujjuya waya ta a hannuna, I wish zan iya sanin halin da Sadauki yake ciki, I can't even begin to imagine in dai har son da yake yi min ya kai wanda nake ji a raina a game dashi to kuma tabbas da nice zuciyata bugawa zata yi in fadi in mutu. It hurts so much to meet him bayan shekaru da yawa and not be able to talk to him, to ina ga shi kuma da yake kallona a matsayin matar wani?

Ina nan zaune naji shigowar Saghir, ya jima a kasa sannan ya hawo sama, nayi tsammanin dakinsa zai wuce kamar kullum amma sai naji ya turo kofar dakina ya shigo da tray a hannunsa ya ajiye akan side table ya zauna a kusa dani yana janyo table din gaban mu. "Sarkin yan tuwo gashi nan na debo miki, ko ba zaki ci ba?" Na zuba a plate ina cewa "Nagode" sai naga ya dauko chokali shima nace "au zakaci ne? Bayan baka cin tuwo?" Yace "albarka ta zan saka miki" murmushi kawai nayi zuciyata tana ayyana min abinda yake ransa. Sai da muka gama ci na kwashe kayan na mayar kasa na taho da ruwa da zuba masa a cup na mika masa ni kuma na zauna ina sha a robar ruwan. Sai dana gama na juya naga ya tsatstsare ni da ido kuma nasan irin wannan kallon but not today, I just can't.

Sai na mike zan bar gurin yasa hannu da yawo dani kan gadon, ya jawo ni jikinsa yana mammatsa min kafadu na amma sai nayi saurin ture hannunsa dan ji nake kamar wanda yake doramin garwashin wuta a jiki, kafin in matsa ya saka hannunsa biyu ya juyo dani ina facing dinsa ya jawo fuskata dai dai tasa yana kokarin hada bakin mu, nayi saurin juyar da kaina nace "Please stop, bana so" amma yaki hakura, na fara ture shi kuma yana jawo ni kamar dai yadda muka saba yi duk sanda yazo da bukatar sa, ganin yafi karfina yasa na fara kuka shabe shabe da hawaye ina rokonsa akan ya kyaleni amma yaki, can kuma sai ya sake ni da karfi ya hankada ni baya ya mike tsaye yana kallona da idonsa da fuskarsa da duk suka yi ja saboda bacin rai yace "nagaji, nagaji, nagaji Diyam nagaji. Yaushe ne wai zaki daina guduna? Yaushe ne zamu mori auren mu ni da ke? Tunda akayi auren nan shekara bakwai Diyam in na zauna zan iya lissafa miki adadin lokutan da kika bari na kusance ki suma kuma babu wanda kika kawo kanki kuma babu wanda kika karbe ni cikin son ranki. Ni fa mutum ne, inada jini da tsoka a jikina ina bukatar kulawar matata amma ke na fahimci da dutse akayi taki halittar. Kullum ina bawa kaina hakuri ina ganin kamar zaki dawo hayyacinki amma kin ki, ni Saghir ni da mata suke rubibi na a waje har kawo min kansu suke yi amma ni ne matata take guduna. Na gaji wallahi. Hakuri na ya kai bango" na sauko daga gadon ina goge hawaye na nace "then let me go, mu daina daukan alhakin juna haka nan, auren nan tun farko da aka yi shi ni da kai bama so, igiyar nan a hannunka take, ka saki igiyar ni da kai mu huta da kunan zuciya" sai ya tsaya yana kallo na yace "haka kika ce? To tsaya kiji, lokacin da akayi auren nan ni kaina banyi niyyar zama dake ba wallahi, after what happened on our first night I thought in na sake ki ban kyauta miki ba, nayi niyyar in rufa miki asiri in cigaba da zama dake a haka ina tunanin with time zaki soni. Amma har yanzu kinki sona, kina ganin kamar ban isa ba ko something like that, ni kuma nasan babu macen da ta isa tace bata sona, in na sake ki Diyam kamar kinyi winning a kaina kin nuna min ban isa ba, which is something I won't agree to. Kin san me? Nasan maganin ki. Aure zanyi. I will let you watch as a lady wadda bata kaiki komai ba take away your husband ta marar dani dan lelenta nima in mayar da ita yar lelena a gaban ki, maybe wannan shi zai nuna miki worth dina ki dawo cikin sense dinki" na mike na rike rigarsa cikin rarraunar murya nace "Saghir, ni ban hana ka aure ba, ni ba zan ma damu dan kayi aure ba ka auri duk matar da kake so Saghir but please ni ma ka barni in koma gurin wanda nake so" yace "ohh, wai dama har yanzu baki hakura da yaron nan ba, dama a saboda shi ne kike tayi min wannan wulakancin? Yaron da aka ce min babu wanda yasan inda yake watakila ma ya zama dan shaye shaye ko dan fashi amma ke shi kike so when you already have me?" Nace "so guda daya ne Saghir, kuma Sadauki naje yi wa shi" ya warce rigarsa daga hannuna yace "then you will rot here. Ke da Sadauki sai a mafarki" ya juya ya fita ya barni. Na jingina kaina da jikin bango ina jujjuya kan, sai kuma na zame na kwanta a gurin akan dandaryar tiles. Ina ji hadari ya hado aka fara ruwan sama mai karfi, tiles din dana ke kai ya dauki sanyi amma na kasa tashi ballantana in koma gado in lulluba, ji nake jikin nawa bashi da wani amfani dan haka lullube shima bashi da amfani. Anan assuba ta same ni, sai da akayi assalatu sannan na tashi da jan kafa na shiga toilet na dauro alwala na gabatar da sallah ina kara kai kuka na a gurin ubangiji na dan nasan shi kadai ne zai iya yi min magani, nasan yana gani na yana kuma jina kuma nasan bai manta dani ba dan yafi kowa sona.

A ranar na tashi da mummunar mura da tari, kuma nasan hakan yana da dangantaka da kwanan da nayi akan tiles. Na shirya Subay'a da kyar, na sha magani na kwanta daga nan kuma sai zazzaɓi ya rufe ni. Daga nan sai ciwo, zazzaɓi ciwon kai mura da tari amma Saghir ko leko inda nake baiyi ba ballantana yaga halin da nake ciki duk kuwa da cewa na tura subay'a ta gaya masa yafi a kirga. A haka nayi ta ciwo na, da kansa yake shirya subay'a ya kaita school kuma ya dauko ta yasiyo musu abinci suci kayansu. Ni kuwa sai naji yunwa tana neman illata ni zan tashi insha tea in koma. Har na kwana biyar a haka.

Ranar Thursday na kira Inna na roke ta ta turo min Asma'u tayi min weekend dan ta dan taya ni wasu abubuwan, na gaya mata bani da lafiya ne. Friday sai gasu sunzo har da Inna, wannan shine zuwan inna gidana na uku tunda nayi aure kuma duk duba ni take zuwa yi in bani da lafiya. A kasa muka zauna dan bata taba hawa sama in tazo, tana tayi min mitar yadda duk nabi na kara ramewa tana cewa me yasa banje asibiti ba? Ni kuma sai nayi shiru kawai dan ina ganin fada mata cewa Saghir ba zai kaini ba bashi da amfani tunda nasan ko tayi masa magana ba zai ji ba sai dai kawai ranta ya baci. Sai kuma nayi tunanin ko ingaya mata zancen Sadauki? Sai dai bani da tabbas din yanzu menene ra'ayinta akan Sadaukin bansan yadda zata dauki kasancewar sa a matsayin ogan Saghir ba. Na dai san tana nemansa akan gadon Ummah na gida dan haka dole zan gaya mata amma ba yanzu ba, sai na samu damar magana dashi tukunna first.

Asma'u ce ta tashi ta gyara min gidana tsaf, har dasu turaren wuta, sannan ta shiga kitchen tayi mana girki muka hadu muka ci tare harda Subay'a. Sai naji dadi sosai, maybe ciwon nawa harda rashin wanda zanyi wa magana da kuma yunwa. Ana yin la'asar Inna tayi sallah sai ta tashi ta fara shirin tafiya. Na fara mita "Inna daga yin la'asar? Ki bari mana sai kamar karfe biyar haka sai ki tafi" tace "uhm uhm, wannan gari na damina yanzu sai kiji ruwa ya sauko. Bana son mijinki yazo ya same ni a gidan nan" muka yi tayi mata dariya ni da Asma'u dan mu a gurin mu kamar babu komai dan sun hadu, ita kuma al kunya ce irin ta fulani.

Ai kuwa kamar ta fada da bakin mala'iku sai ga ruwan sama ya sauko, da yake muma daki babu wanda yasan ma da hadarin sai kawai zubar ruwa mukaji. Inna ta fara salati mu kuma muna dariya "yau kwana ya kama Inna a gidan Adda" inji Asma'u, Inna tace "kwana bai kama ni ba, ai komai dare ruwan nan in ya dauke sai na tafi gida, balle ma ba lallai ne ya kai daren ba". Wasa wasa ruwa har magrib, har isha yin sa ake kamar da bakin kwarya, Inna ta shiga dakin kasa inda Asma'u ta gyara dan anan take zama duk sanda tazo gidan saboda basu fiya shiri da Saghir ba, anan tayi sallolinta duk muka zauna muna hira ita dai tana ta bacin rai. Nace "Inna ki bari idan Saghir ya dawo sai ya kai ki a mota tunda ba kya son kwana" ta girgiza kai "ni da bana son ma yasan nazo? Bazan shiga motarsa ba. Allah ya tashe mu lafiya sai in tafi da safen".

Na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login