Showing 162001 words to 165000 words out of 174346 words

Chapter 55 - Diyam Book 1 Hausa Complete

07 Jan 2025

1103

cikin nasa "kai ba kayi wanka bane ba?" Yace da dasashshiyar murya "ban fita ba, wani wankan zan sake". Sai da kuwa ya sake din. Yana tayar da sallah ta mike ta nannade jikinta da bedsheet sannan ta fita da sauri ta tafi dakinta.
Toilet ta zarce tayi wanka a gaggauce sannan ta fito ta saka doguwar riga da hijab tayi sallah. Tana son ta koma bacci amma kuma yunwa take ji sosai dan jin cikinta take yi kamar anyi mata yasa. Ta duba agogo taga karfe bakwai, a lokacin kira ya shigo wayarta daga Murjanatu. Ta dauka da sallama Murjanatu tace "amarya, wannan saurin daukan waya haka kamar wadda ta kwana ba tayi bacci ba?" Sai kuma ta kyalkyale da dariya. Diyam tayi rolling eyes dinta tace "kina da abin cewa ne ko kuma kirana kikayi saboda credit yayi miki yawa?" Murjanatu ta daina dariyar tace "Mama ce tace in kira ki in tuna miki cewa karfe goma jirgin mu zai tashi, ki shirya zamu biyo mu dauke ki" Diyam ta dafe kanta, shaf ta manta akwai mother's eve da Maman su Murjanatu ta shirya musu yau a Maiduguri. Lallai Sadauki ba karamin formatting kwakwalwar ta yayi ba. Murjanatu tace "kin manta ko?" Diyam tayi saurin cewa "no no no, ban manta ba, baki ji har na tashi na fara shiryawa ba?"........

Ta cire rigar da tayi sallah da ita ta mayar da wata doguwar rigar wadda bata karasa har kasa ba amma ta kama ta tsam-tsam like a second skin. Yadin rigar mai layi layi ne na kalolin black, dark ash, ligh ash da white. Wuyan rigar ya bude sosai har Diyam tayi tunanin ya zama too reveling, wannan yasa maimakon ta daura dan kwalin sai ta nade shi a wuyanta stylishly yadda ya rufe kirjinta. Ta bude kofa ta fito daga dakinta a dai dai lokacin da taji kara kamar ta faduwar wani abu, followed by another sound kamar ana ?ari. Ta dan kara sauri zuwa inda take jiyo sound din sai ta ga daga mini kitchen dinsu ne da yake a sama.

Ta tsaya a bakin kofa leka ciki, abinda ta gani shi ya saka ta rufe bakinta tana hana dariya fitowa. Sadauki ne daga shi sai singlet da short, kusan duk cabinet din kitchen din a bude su ke ga kasan tiles kaca kaca da egg shells da kuma ?awon dankali, ga mai cikin kasko a kan wuta shi kuma yana tsaye like three meters away from kaskon hannunsa da spatula yana leka cikin man. Sai kuma taga ya dauko wasu bowls guda biyu, daya ruwan kwai ne a ciki kusan rabin crete, dayan kuma danyan dankali ne guda gudan sa. Sai taga ya dauko dankali guda daya ya saka a cikin ruwan kwan sannan ya dauka da spatula ya jefa a cikin man daya riga yayi over heating.

Dariyar da take rikewa ce ta kwace mata lokacin da yayi wani tsalle zuwa karshen kitchen din. Dariyar ta ce ta juyo hankalinsa gurinta. Yayi kamar zai yar da bowl din kwan da take hannunsa amma sai yayi saurin ajiyewa ya taho gurinta yana kallon ta tun daga kasa har zuwa sama. Ta rufe fuskarta cikin jin kunya sannan ta juya masa baya, not realizing cewa ta juyo masa daya daga cikin abinda yake so a jikinta.

Yana zuwa inda take sai ya jawo ta ya hada bayanta da jikinsa, ya saka fuskarsa a wuyanta yana shakar kamshinta mai dadi sannan yace "good morning Sadiyam" bata amsa ba sai yace "wai kunyar ce har yanzu? I tot na cire ta tun jiya ashe da akwai sauranta. Ki gayawa kunyar nan ko ta rabu dake ko kuma inyi maganin ta" ta kara narkewa a jikinsa tana lumshe idonta. Ya kai baki dai dai kunnenta yace "na dauka kunyar ta tafi lokacin da naji kina cewa 'sadauki more please" ya fada yana kwaikwayon muryar ta. Tayi saurin kokarin janye jikinta daga nasa tana bubbuga kafa tace "lahh! Ni wallahi ban fadi haka ba" yana dariya yace "nayi recording fa, in baki yarda ba mu koma dakina in kunna miki kiji" kamar zata yi kuka tace "ni bana son ji, ni ban fada ba" ya dawo da ita jikinsa yace "I had the greatest night of my life yesterday. And I had the greatest birthday gift. Yanzu wish dina guda daya a rayuwa shine every night na sauran rayuwa ta ya cigaba da kasance wa like yesterday night" ta juyo tana facing dinsa tace "lallai ma. To yau ma ba anan zan kwana ba" ya bata rai yace "ban gane ba" ta saka hannu tana gyara masa hannun rigarsa tace "biki zanje" ya sake bata rai "biki kuma? Bikin wa?" Tana murmushin fahimtar ba ita kadai ta manta ba tace "bikin mu ni da kai. Ka manta yau za'ayi event a Maiduguri? Mama har ta saka a kira ni a tuna min karfe goma jirgin mu zai tashi. Kuma nasan ba zan dawo yau ba, maybe sai jibi". Ta fada da yanayin tsokana. Ya kife kansa a kafadarta yace "bara inje in hada kayana nima" ta ture shi tace "ba fa a gayyace ka ba" yace "duk wanda ya gayyaci matata to kuwa tabbas ya gayyace ni. Anywhere you go I will also go".

Ta kalli kaskon da yake kan wuta tace "me kake dafa mana ne?" Ya kalli kaskon shima, har ya manta ma da cewa girki yake yi, sai yace "dankali da kwai" tayi murmushi kawai sai ya dan ja da baya yana kara kallon shigar jikinta, ya daga gira yace "if you want to wear a dress like this, wear it with confidence" sai ya saka hannu ya zare dakwalin da ta rufe wuyanta da kirjinta da shi. Ta danji kunya ta sunne kai a kirjinsa sai shi kuma ya daga ta chak ya dora akan worktop, ta karbi dankwalin a hannun sa ta nada masa shi a nasa wuyan tana dariya, yace "ki zauna anan. Let me cook for you" sai ya koma ya leka cikin man sa, ya juyo yana kallon ta fuskarsa abin tausayi yace "ya kone" tayi dariya shi kuma ya harare ta ya dauko dankalin da ya zama kamar gawayi ya jefa a waste basket ya dawo gurinta ya zagaye ta da hannayensa ya dora kansa a kirjinta yace "ban iya girkin ba. I wanted to cook for you" tace "ka iya mana. Let me tell you what to do. Shi wannan dankalin you boil it first with a little bit of salt, sai ka yayyanka shi a kwance yayi shape din circles, shi kuma kwan sai ka zuba masa attaruhu da albasa da spices, sai ka juye dankalin a cikin kwan ka juya su sosai sannan ka dora frying pan akan wuta ka zuba mai kadan sannan ka juye dankalin da kwan ka soya su together on a very low heat, in side daya yayi ka juya dayan side din shima yayi, shikenan" sai ta sauko taje ta kashe wutar da har yanzu man yake kanta yana konewa. Tace "yanzu bara in hada mana, in ka gani yadda nayi kaga watarana kai ma sai kayi mana" sai ya sake daukanta ya mayar da ita kan worktop yace "you seat here, ni zanyi mana, ai na gane".

Har ya koma gaban cooker din sai kuma ya dawo gurinta yana langwabe kai yace "energy na ya kare. I need a refill" ta turo baki tana magana kasa kasa, yace "me kike cewa?" Tace "bayan yunwa nake ji tun jiya banci komai ba kuma kazar ma baka barni naci ba" yace "to ba nace zan biya ki ba, please" ya fara koma mata Sadaukin jiya, tayi kokarin ture shi "kitchen ne fa" yace "kitchen din waye? Gidan waye? Matar waye?" Ta sake makale kafada sai yace "okay, just a kiss then" ya fada yana kawo fuskarsa kusa da tata, ta saka fingers dinta tana tracing gashin girarsa ta zagayo har zuwa sajen sa, ya lumshe ido sai tayi sauri ta juya fuskarsa side tayi kissing cheek dinsa. Ya bude idonsa ya bata rai ita kuma tana dariya yace "gaskiya ban yarda ba. Ni bana son wannan" ta miko hannunta tace "bani kaya na to tunda baka so" yayi mata murmushin mugunta yace "with pleasure" sannan ya dora lips dinsa akan nata.

Hmmmm. Naga wadannan ba yunwar suke ji da gaske ba, kuma na fahimci basu da niyyar zuwa Maiduguri. Gwara in tafi kar jirgi ya tafi ya barni.

?? DIYAM ??

By

Maman Maama

Episode Seventy Five : Maiduguri
Diyam bata samu shiryawa ba har sai data ji horn din mota a waje, sannan ta ruga daki da gudu tayi refreshing. Tana cikin saka kaya Murjanatu ta shigo dakin tana kallon ta tace "wai sai yanzu kike shiryawa?" Diyam tace "da wannan complain din da kike yi dama jakar da zan tafi da ita kika dauko min a closet. Na riga na hada kayan da zanyi amfani dasu tun a gida" Murjanatu ta shiga ta fito da karamar jaka a hannun ta, lokacin Diyam har ya dauko hijab dinta tana checking contents din handbag dinta sannan ta kara abinda zata kara tayi zipping dinta ta rataya. Suna saukowa Murjanatu tace "baku da abinci a gidan nan? Ki zubo min dan Allah ko a mota ne sai inci yunwa nake ji" Diyam tace "nima yunwar nake ji, in kin samu nima ina so".

A waje Sadauki ne a tsaye tare da Al-mustapha wanda yake cousin din su Sadauki kuma daya daga cikin maneman Murjanatu suna magana, ya dora jallabiya akan shorts din dake jikinsa. Su Diyam suna fitowa Al-mustapha yazo ya karbi jakar hannun Murjanatu ya je ya saka a mota, Murjanatu tana kallon Sadauki tayi wa Diyam rada tace "baiwar Allah me kika yiwa yaya na? Na ga ya zama fari cikin dare daya. Ko dai man bleaching kika shafa masa?" Diyam tana dariya tace "kakan bleaching ba bleaching ba" amma ita ma sai ta lura fatar Sadaukin tayi haske sosai, wani annuri a kwance a fuskarsa and he seems kamar ya kasa daina murmushi.

Al-mustapha ya dawo suka gaisa da Diyam yana kallon Sadauki, Sadauki ya lura tsokanar sa yake son yi sai yace "to ya isa haka, shiga mota" ya nuna Murjanatu yace "kema shiga, ko a gaban ku zanyi sallama da mata ta?" Almustapha yace "kaji masu mata, muma dai mun kusa zuwa gurin" Sadauki yace "kun kusa, amma baku zo ba. Ka bari sai kazo gurin sannan sai kazo mu jera, amma yanzu kana baya na" duk suka yi dariya, sannan su biyun suka shiga mota.

Ya karaso gaban Diyam yana kallon ta, kanta a kasa tana wasa da fingers dinta, sai ya mika hannu ya kama nata, tace "zamu tafi" yace "Allah ya kiyaye hanya. I will be on the next flight insha Allah. Take care of yourself for me kinji? Sai nazo anjima" tayi murmushi tana gyada kai, sai kuma tayi ?age on her toes tayi kissing beard dinsa. Ya bude mata kofa, ta shiga sannan ya gyara mata hijab dinta ya manna mata kiss a palm dinta sannan ya rufe mata kofa.

Suna jan mota Murjanatu tace "I will pretend kamar banga komai ba" Diyam ta harare ta tace "to ai dama babu abinda kika gani yarinya. Ni yunwa nake ji wallahi". Suna zuwa airport suka wuce VIP lounge. A can suka tarar dasu Mama already har sun isa, sai a nan Diyam ta samu tayi breakfast kafin su tafi. A lokacin ne kuma ta yi studying maman su Murjanatu sosai, sai ta ga cewa akwai tsantsar ilimi da wayewa a tare da ita wanda Diyam ta fahimci cewa shine dalilin da yasa bata daukan Sadauki a matsayin abin ki sai dai abin so, dan jahilci da rashin aikin yi suna playing role sosai akan wadannan abubuwa.

Kafin 11 na safe sun sauka a Maiduguri. Tun daga yadda akayi musu a airport, tun daga motocin da Diyam taga sun zo daukan su harda motar security, Diyam ta kara tabbatar wa lallai ?an Umar Mustapha Abatcha ta aura. Gidan da suka je kuwa ba gida bane ba, Diyam ta fahimci kamar wani estate ne amma family estate mai dauke da gidajen kakanni, iyaye da ya'ya. Gidan baban Sadauki a ciki yake, uncles uncles dinsa duk suna ciki, da kuma cousins dinsa da sukayi aure. Ko wanne gida ka gani a cikin estate din abin kallo ne, amma babban abin kallon shine gidan Umar Abatcha, tsarin gidan, motocin da suke gidan, kayan alatun da aka kawata gidan dasu, su suka saka Diyam ta fahimci dalilin da yasa Sadauki baya jin fitar kudi daga aljihunsa dan akwai su din.

Yadda ake tayi mata ya saka take ta jin kunya, abincin da aka sauke su dashi ma takasa ci sai da Murjanatu ta ja ta suka tafi part dinsu su yammatan gidan wanda shi a kansa ma gida guda ne. Murjanatu tana ta tsokanar ta "wallahi in kika ce kunya zaki ringa ji ko? To wallahi a gidan nan sai an kusa mayar dake tababbiya" Diyam tayi murmushi, amma ita tasan ba zata iya cire kunya daga ranta ba kamar yadda ba zata iya cire jini daga jijiyoyin ta ba.

Anan ta samu taci abinci sosai tare da sauran yammatan, sai kuma duk suka yi wanka har ita suka fara shiryawa, ta jawo jakar kayanta zata saka sai Sa'adatu tace "Mama fa ta bayar anyi miki dinkin da zaki saka yau, sai dai ki gwada abinda baiyi ba aje yanzu ayi miki adjusting" Diyam tayi godiya, amma kuma ta so saka nata kayan data tanada musamman saboda yau din sai dai kuma hausawa sunce yaba kyauta tukuici, in bata saka kayan ba Mama ba zata ji dadi ba. Dan haka sai ta yanke shawarar zata saka yanzu in yaso in an jima sai ta saka nata. Aka kawo mata kayan ta saka, komai yayi mata sai hips ne da za'a dan buda mata. Nan take Sa'adatu tayi waya aka zo aka karba kuma suna cikin yin kwalliya sai gashi an dawo dashi. Farar shadda ce da akayi mata wani irin stone work da golden brown stones a gaban rigar da kuma hannayenta, in ka gani zaka dauka aikin sirfani ne amma stones ne kawai aka jera su, Falmata tayi mata dauri mai kyau da dankwalin shaddar sannan ta saka bungles na danyen gold wanda ta dauko daga kayan lefenta, ta saka takalmi ta rike clutch golden brown nan take ta fito a matsayin Mrs Aliyu Abatcha. Bayan suma su Murjanatu sun gama shiryawa sai suka fita babban palon gidan, aka zaunar da Diyam a kan kujera kusa da Mama wadda Diyam tana zama ta rike hannunta tana yaba kyawun da Diyam din tayi.

Already mutane sun fara zuwa gidan, yanuwan Sadauki, kannen babansa mata da matan kawun nan sa, matan abokan babansa, abokan arziki da sauran matan manyan gari. Duk wadda tazo zata zo su gaisa da Mama sannan Diyam ta gaishe ta, Mama kuma tayi introducing dinsu, kuma duk sai sun yaba kyawun Diyam sannan suyi mata wasa saboda kasancewar su barebari ita kuma sai dai tayi murmushi kawai dan ba zata iya mayarwa ba.

Wasa wasa gida ya fara cika, duk girman palon sai Diyam taga mutane suna neman cika shi. Kowa kuma tazo zata kawo mata gift ta karba tayi godiya sannan sai Mama ta saka a shiga dashi ciki. Sai a lokacin ta fahimci ma ashe ba wai anan ne za'ayi taron ba, akwai hall da suke dashi a gidan wanda suke amfani dashi dan gudanar da tarurruka ko kuma family meetings. Sai da akayi la'asar sannan aka fara kai mutane can gurin taron, Diyam kuma ta koma daki dan shiryawa. Tana shiga sallah ta fara yi sannan ta dauko kayan da ta taho dasu ta ajiye akan gado a lokacin da Sa'adatu ta shigo dakin tana kallon kayan tace "wow" Diyam tayi murmushi. Kayan Fulani ne na saki complete set din da abin wuya da hannu da kafa da komai. A gaggauce tayi wanka, sannan ta danci abinci kadan kafin ta shirya tsaf ta fito a cikakkiyar bafulatanar ta. Nan take ta dauki kanta a hoto ta turawa Sadauki wanda tun dazu da suka tare da su Mama yake ta kiranta a waya amma ta kasa daukan wayarsa a gabansu. Yana gani yayo reply
"Diyam, na taba gaya miki kuwa cewa ke din kyakykyawa ce?"
"Really? Ba zan iya tunawa ba. Maybe ka taba fada but not directly"
"To yanzu zan fada directly din. You are very beautiful Halima. Kina da beauty na fuska, na jiki dana zuciya. Ki godewa Allah Diyam dan yayi miki komai"
"Anya kuwa na kaika kyau Aliyu? Ni in ina kallonka har mamakin kyawunka nake yi. Komai naka tamkar kai ka zabar wa kanka. Komai ya dace da komai a fuskarka wadda ita kuma ta dace da jikin ka. Jikinka kuma ya dace da sunanka, Aliyu Sadauki. Strong in the heart and the body.
Imojin heart mai beating
"I love you so much my husband"
"I love you more, my wife".

Dakin taron ya cika sosai da manyan mata, ga makada nan suna ta aikin su mata ana ta cashewa ana barin kudi. Diyam tana zuwa aka saka ta a tsakiyar fage aka fara yi mata ruwan kudin da har sai da ta fara tunanin anya wannan ba almubazzaranci bane ba? Ba'a tashi daga event din ba sai daaka fara kiran magrib.

Karshen gajiya Diyam ta gaji, jikinta gabaki daya ciwo yake yi mata dan haka akan sallayar da tayi magrib anan ta zame ta kwanta sai bacci. Cikin baccin aka zo aka tasheta wai taje su gaisa da matar governor wadda bata samu zuwa dazu ba sai yanzu. Can palon Mama aka kaita ta tarar dasu suna ta hirar su suna dariya, ta gaishe su suka amsa mata da fara'a suka yi ta tsokanar ta tana rufe fuska sannan matar ta dauko wani set din scent burner mai kyau ta bata a matsayin gift sannan tayi musu sallama Mama ta tafi ta raka ta. Bayan Mama ta dawo ne sai kuma ta zauna tana ta yiwa Diyam nasiha da kuma dabaru irin na zaman aure, wadansu maganar sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login