Showing 111001 words to 114000 words out of 174346 words

Chapter 38 - Diyam Book 1 Hausa Complete

07 Jan 2025

1110

taho mata dasu suna mota sai ta cigaba da amfani dasu" sai ya dora ta akan cinyarta tana ta zuba masa surutu yana dariya, ina jinsu ya fada mata zaiyi tafiya ita kuma ta fara lissafo masa kayan da zai siyo mata. Sannan tace "Daddy dan Allah ka dawo da wuri mu koma gidan mu ni nafi son zama tarr da kai da Mommy" yayi pecking dinta a cheeks yace "ina dawowa zamu koma kinji princess? It is going to be sabuwar rayuwa for us".

Sai naji a raina cewa tunda har yanzu ni matarsa ce then it is my responsibility inji source din kudinsa. Sai nace "kudi ka samu ne masu yawa haka? A ina?" Sai ya watso min wani mugun kallo yace "matse ni sai in gaya miki, kinsan dai tunda kika sanni da arziki na kika san ni ko? Ko kin taba gani na ina gyaran matattun motoci? Wanda ya samu dukiya sama ta ka shi ake yiwa tambayar inda ya samu dan zata iya yiwuwa yankan kai ko fashi da makami yake yi".

Sai da yasa na raka shi har bakin kofa, ya fito da kayan Subay'a jaka guda ya mika min sannan yace "I will be seeing you soon, sweet pie".

Washegari jirginsu ya daga shi da Fauziyya, I didn't even know ina suka tafi sai ya suka sauka ya kira ni yace min sun sauka a Miami, yace in ajiye number din saboda zai ke kira na da ita.

Bayan tafiyar Saghir ne Asma'u ta kammala jarabawarta, tayi candy, sannan kuma hakan yazo dai dai dayin saukar Alqur'anin ta. Wannan yasa ta shirya walima a nan gidan mu ita da kawayenta. Inna ta aika wa duk yan'uwa aka gayyato su kuma ga mamakin mu sai gasu sunzo, sai dai abinda muka lura dashi shine babu jituwa tsakanin iyalin Alhaji Babba da kawu Isa. Aka gabatar musu da abinci iri iri wanda su kansu sai da sukayi mamaki, daga abincin da aka ci har zuwa sutturar da muka saka daga mu har Inna duk sun nuna cewa ba a cikin kunci muke ba. Su Murja sai tambayata suke yi "yaushe zaki koma gidan hamma?" Murja ta jani gefe "dan Allah Diyam in baki koma bama kiyi masa magana ko zaiji maganar ki. Kinga maganar auren nan fa ta tsaya duk uban kudin da yake samu kwanan nan amma yace ba zaiyi ba. Shi kuma kawu isa da muke tunanin tura masa samarin mu shi kuma gashi yanzu ko magana basa yi da Alhaji" nace "wai me ya hadasu ne?" Ta rufe baki tace "ba za'aji a baki na ba".

Kwana biyu da yin walimar Asma'u sai ga Kawu Isa a gidan mu. Mamaki ya ishe ni na tuna ranar da yace sun cire mu a cikin zuri'a ranar da sagjir ya sake ni a gabansu amma yanzu gashi few months after ya dawo da kafafuwansa. Muka gaishe shi ni da Asma'u muka fita muka basu guri da inna. Sun jima suna maganganu kafin muji ya fita sannan muka dawo dakin. Asma'u ta saka Inna a gaba da tambaya "me yace? Me ya faru" Inna tace "ina ruwanki? Suda mai bakin magana"

Sai da Asma'u ta tafi islamiyya sannan inna ta bani labari. "Zuwa yayi yace min wai dan Allah duk yadda za'ayi kar mu mayar dake gidan Saghir. Ashe abinda Yalwati take fada min rannan gaskiya ne, Suwaiba dai har da cikin Saghir a jikinta. Alhaji Babba yace shi lallai sharri aka yiwa dansa, shi ma kuma Saghir din yace ba nashi vane ba kuma yama fasa aurenta ke zai mayar. Shine shi kuma hamma Isa yazo yace kar mu mayar masa da ke in yaso yayi biyu babu kenan. Su yanzu likitan da zai cire cikin suke nema". Nayi shiru ina jin hawaye yana bin fuskata. Na tuno zafin da naji sanda Saghir yayi min sharri a gaban yan'uwan mahaifina amma duk babu wanda yayi komai a kai. Ga zina nan ta kare a gabansu, yanzu sai su ware ni da Saghir waye mazinaci.

Bayan sati ya kuma zagayowa sai ga malam iliya maigadin gidan Saghir ya kirani hankali a tashe. Na tambayeshi sai yace "yan NDLE ne suka zo gidan, sun yi filla filla da komai na gidan wai suna neman kayan maye" cikin tashin hankali na tambayeshi sun samu sai yace "sun samu, a dakin mai gidan sukayi ta fitowa dasu sannan suka samu wasu kuma a motarsa. Yanzu tafiyarsu kenan nima guduwa nayi da ina jin dani zasu hada. Shine na kira ki tunda su basa nan in gaya miki halin da ake ciki" nayi masa godiya na kashe wayar, ina kokarin bawa inna labari sai ga kira ya shigo wayarta daga Hajiya Yalwati tana ta kuka "Amina mun shiga uku. Wai yan drugs ne suka zo zasu tafi da Alhaji. Alhaji Babba fa? Me ya hada shi da shaye shaye?". Nan take Inna ta rikirkice ta saka mu muka shirya muka tafi gidan gaba daya, muna zuwa muka tarar har an tafi dashi ga yan gidan nan sun fito sunyi chirko cirko masu kuka nayi masu salati nayi, yan unguwa kuma ana tsaye ana kallo. Mukayi ta basu baki muna mayar dasu cikin gida har muka samu suka koma ciki sannan aka fara tunanin ta inda za'a bullowa lamarin. Ni dai na fada musu abinda mai gadin gidan Saghir ya fada, dan haka sai muka fahimci cewa neman Saghir suke yi shi yasa suka kama Alhaji. Aka kira Kawu Isa aka gaya masa amma yace shi babu ruwansa "tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka".

Dan abin kunya sai surukan gidan aka nema, ciki harda wanda yake neman auren Murja, su sukayi ta zirga zirga Inna kuma ta saka Asma'u taje ta ciro kudi a account a bawa wancan cin hanci a bawa wancan amma sai da Alhaji Babba ya kwana biyu a garkame sannan suka sake shi da yarjejeniyar Saghir yana shigowa kasar zai danka musu shi a hannun su.

Ranar da Alhaji ya dawo gida haka ya zauna yana ta kuka kamar karamin yaro "ban taba ganin cin mutumci irin wannan ba, wannan yaro mai ya janyo min haka ni Muhammadu. Ankwa hannu da kafa haka aka saka min ana jana a titi kamar wanda yayi kisan kai" sai kuma ya fara yiwa Inna godiya a kan kokarin ta da karfin ta da kudinta gurin ganin an fito dashi. Yana ta kuka har ciwonsa yana kokarin tashi dan haka akayi masa allurar bacci mu kuma muka tafi gida.

What remains a mystery shine yadda akayi yan drugs suka yi suspecting Saghir yana ta'ammali da kayan maye har suka kaiwa gidansa ziyara.

Two weeks after tafiyar Saghir sadauki ya dawo. A gurin Asma'u naji zancen dawowar tasa sai kuwa gashi nan yazo gidan. Ina jin shigowarsa na shige cikin daki na lulluba kamar mai bacci. Ina jin su suna ta hirar su a palo, ya kawowa Asma'u graduation gift na wata desighner handbag da takalmi, ya kawo wa Subay'a yar karamar computer ta yara mai kyau. Ta shigo da murna tana nuna min "Mommy kinga abinda wannan yayan naki ya kawo min, amma ke yace bai siyo miki komai ba" na karba ina dubawa nace "to kije kice kin gode madallah" ta fita na koma na kwanta.

Ina ta so dai inyi masa maganar kudin companyn sa, amma bana son ganinsa dan haka bayan ya bar gidan sai na kara dauko waya ta ban kirashi ba dan nasan ba shiga zata yi ba amma sai na rubuta masa message. "Ka sa ido a kudaden kamfanin ka. I might be wrong. Just taking precautions". Na tura masa. Na zauna da wayar a hannu ina jiran reply, shiru shiru babu. Har na gaji na ajiye ta na tashi na cigaba da harkoki na. Aka jima na sake dubawa babu reply, nayi tsaki a raina nace "ku kuka sani" Sai kuma nake jin haushin kaina for caring a inda ni ba'a damu dani ba.

Saghir yakan kira ni sometimes, in ya kira sai in bawa Subay'a suyi magana. Ko da wasa ban bashi labarin case din drugs ba dan nasan ba karamin aikinsa bane ba yaki dawowa dan ba damuwa yayi da abinda za'ayiwa Alhaji in bai dawo din ba. Ranar nan ya kira na bawa Subay'a suka gama maganganun su sai yace ta bani, na karba yace min "jibi zamu dawo. Ina son ki kawo Subay'a airport ta tare mu. Tace tana son zuwa" nace "okay Allah ya kaimu jibin. Allah ya kawo ku lfy" yace "ameen. Hope kin gama shiryawa dan daga airport sabon gidazamu zarce" na sake cewa "Allah ya kaimu" na kashe. I didn't have the energy or the patient to argue.

Muna gama wayar sai naga Asma'u ta dauki tata wayar tayi kira sannan tace "jibi zai dawo" ta kashe. Ta kalleta nace "what was that?" Tace "Hamma yace in gaya masa ranar da Saghir zai dawo" na saki baki kawai ina kallonta. What was that about?

Ranar dawowarsu na shirya Subay'a tana ta murna muka tafi malam Aminu Kano international airport. Muka tsaya a gurin da aka tanada dan taryar matafiya. Subay'a tana ta tsalle ta kasa tsayawa a guri daya yayin da ni kuma nake ta lissafe lissafen halin da nake ciki. Ni har yanzu ban gama fahimtar kudurin Sadauki na mayar da Saghir aiki sannan da kuma hanani gaya masa cewa ni ba zan koma gidansa ba. Na fahimci kamar yana buying time ne but for what? Me yasa kuma yake son jin lokacin dawowar Saghir?

Muna tsaye akayi announcing saukar jirgin su Saghir, muna tsaye kuma har suka gama checking out suka fito. Na hango shi, as handsome as ever, hannunsa cikin na Fauziyya suna fitowa daga revolving door din gurin. Subay'a ta fara murna "Daddy, Daddy" ya dago mata hannu yana murmushi.

And then as he steps his feet out of the door, police surrounded him. Police, not NDLE officers. Fauziyya ta matsa baya da sauri tana ihu, Subay'a ma ta fara ihun kiran Daddy yayinda shi kuma ya fara demanding dalilin kamashi. Na daga Subay'a na rungume ta a kirjina, muna kallo daga inda muke tsaye aka garkamawa Saghir ankwa a hannayensa aka wuce dashi police car da take gefe tana jira.

Subay'a ta fara jera min tambayoyi "me yasa yan sanda suka tafi da Daddy na? Ina zasu kai shi?" A lokacin naji karar shigowar text cikin wayata. Na dauko ta na duba naga number din Sadauki. Sai yanzu yayi replying message dina. Na karanta "check up" it said.

?? DIYAM ??

By

Maman Maama

Episode Fifty Four & Five : The Games We Play

"Check up" na maimaita a fili. Nasan wannan kalmar amma a ina? Sai mind dina ta koma baya, back in time lokacin muna yara a gida muna playing game of cards ni da Sadauki a incomplete benen Baffa a lokacin da nake gudun islamiyya ya rama min duka ance in na koma sai an zane ni. A cikin game din ana cewa check up. And it means game over.

Amma wanne game din ne over bayan ni bansan sanda game din ya fara ba? Ya akayi ya turo min wannan text din a dai dai wannan lokacin? Ko dai Sadauki yana da hannu ne gurin kama Saghir?

Kamar ance min in juya baya sai na juya. And I saw him. Yana tsaye ya jingina da jikin motarsa with dark glasses a idonsa and a broad smile on his face yana kallon motar police din da aka saka Saghir a ciki, sai da yaga sun ja sun tafi sannan ya bude motarsa shima ya shiga shima ya tafi.

Da sauri na koma taxi din da nayo shutter nace masa mubi bayan police car din data fita. A hanya drivern yake ta surutai "ai haka police suke yiwa irin wadannan bata garin, in sunyi abu sai su gudu su bar kasar sai a shammace su ranar da zasu dawo azo ayi gaba dasu. Ai wannan commissioner din baya wasa" jin ban kula shiba sai yayi shiru kuma muka cigaba da bin su a baya har na tabbatar cewa bompai zasu tafi dashi sannan nace da drivern ya kaini badawa layout, gidan Mama, muna zuwa na ajiye Subay'a na gayawa Mama briefly abinda ya faru, naci sa'a yaya Sadiq yana gida sai ta hadani dashi muka koma police station din dan muji takamaiman abinda ya faru, for what charges aka kama Saghir.

But ni already jiki na ya gama bani charges din ina dai so ne in tabbatar da zargi na. Ina kuma bukatar wasu amsoshin daga Saghir. Da kyar muka samu desk officer din ya kula mu, amma da muka nemi ganin Saghir Muhammad da aka shigo dashi yanzu sai kawai yayi mana dariya irin mun ma bashi dariya din nan, yace "wannan ai ko uwarsa ce take son ganinsa sai dai ta hakura. Ku koma gida kuyi taja masa charbi dan yau ne za'ayi masa tambayar kabari ta duniya" ya fada yana dariyar mugunta.

Nace "to zamu iya sanin dalilin da yasa aka kama shi?" Yace "ke wacece a gurinsa?" Nace "matarsa" yace "kinsan inda yake aiki?" Na hadiye wani abu a kirjina Nace "eh. Abatcha Motors" yace "to can zaki je ki tambayi abinda yayi, zasu yi miki bayani dalla dalla".

Haka muka hakura muka fito. Yaya Sadiq yana jan motar mama ni kuma ina gaba nayi shiru ina juta lamarin a raina. My deepest fear have come true, wannan case din bana drugs bane ba kuma wani ne daban, case din Sadauki ne, Saghir ya debi kudin companyn Sadauki yayi facaka dasu Sadauki kuma ya saka an kama shi. But what was Saghir thinking?

Gidan Alhaji Babba nace Yaya Sadiq ya kaini, dole inje in fada musu halin da dansu yake ciki in yaso a hadu a san yadda za'ayi tackling lamarin. Ga kuma wancan case din NDLEA da yake jiran Saghir. Sai kawai naji ina jin tausayin iyaye da yan uwan Saghir.

I also needed to talk with Sadauki. Bana ko raba daya da biyu nasan tarko ne Sadauki ya dana wa Saghir shi kuma ya fada head over heels. Wato wannan shine time din daya nema in yi masa buying kenan. Sai kuma na sake tambayar kaina "menene hadin Sadauki da case din NDLEA? I really do hope bashi da hannu a ciki.

Da muka je gidan kuma sai na kasa gaya musu, musamman ganin da nayi suna ta fama da kansu, an dafa wake da shinkafa ana ta lissafin yadda za'a samu kudin mai, sai da naje na bayar aka siyo musu. Sai na ja Hajiya Yalwati gefe na labarta mata. Ta rike baki tana salati tace "gurin aikin sa kuma? Ba companyn Sadauki bane yake aikin ji nake ya kore shi?" Nace "bai kore shi ba, ga kuma abinda ya faru. Yanzu yana bompai. Naje an ma hanani ganinsa" haka na tafi na barta da jimami nace ta gayawa Alhaji da Hajiya. Ni ba zan iya ganin wannan heart break din ba.

Daga nan gida yaya Sadiq ya kaini, na bar Subay'a gidan Mama in yaso gobe in na koma station din sai in biya in taho da ita saboda nasan yanzu in muka he gida ta saka ni a gaba kenan da tambayar ina daddyn ta? Ina police suka kai shi?. Ina shiga gidan Inna tana sallamar wani yaro da yazo siyan kankara ta gane something is wrong, sai data sallame shi tace min "lafiya? Ina Subay'a? Rigima kuka sake yi da Saghir?" na zauna ina cire hijab dina nace "inna Saghir yana bompai" ta saka salati tana tafa hannu tace "masu neman nasa ne suka kama shi? Dama sun san yau zai dawo?" Nace "basu bane ba Inna. Wani case din ne daban, basu gaya min menene ba amma sunce case ne daga gurin aikinsa" na fada ina kallonta cikin ido, nan da nan sai naga ta fahimta tace "Sadauki? Me ya kuma hada su kuma?" Na daga kafada nace "ban sani ba. Sai gobe zan sake komawa inji ko zasu yi min bayani" tace "to ki kira Sadaukin mana ki tambayeshi shi?" Na kwanta a kujera ina cewa "ba zai dauka ba Inna. Dama can baya daukar waya ta ballantana yanzu".

Na jima kwance da idanuna a rufe har aka fara kiran magrib. Ni dai va bacci nake ba kawai ina ta lissafe lissafe ne, Sadauki should have just let me take Saghir to court shikenan a wuce gurin. In na rabu dashi ba dai shikenan ba?

Ina ji da dare Inna ta saka Asma'u tana ta bugawa Sadauki waya amma yaki dauka, daga baya ma sai ya kashe wayar gabaki daya. A raina nace dai dai kenan.

Washegari tun da wuri na tashi na shirya inna ma ta shirya tace gwara muje tare, muka bar Asma'u a gida muka tafi bompai amma muna zuwa muka tarar Hajiya Babba ta riga mu zuwa ita da wani kaninta. Idanunta sun kumbura alamar tayi kuka harta gode wa Allah. Muna shiga ta taho gurina da sauri "Diyam sharri yake masa wallahi, wallahi sharri yake yi masa ina yaron nan zai kai wadannan uban kudade?" Inna ta rike ta tana lallashinta ni kuma na karasa gurin desk officer din da yake on duty. Ya miko min wata takarda wacce take dauke da case statement na case din Saghir, a jiki naga bayanin cewa ya yi transfer din kudi ne daga account din company zuwa private account dinsa. Amount din dana gani sai daya saka kaina ya sara naji kamar zan fadi, mai Saghir yake tunani ne wai? A jiki kuma naga cewa Saghir din ya karbi laifinsa tun a jiyan da aka kawo shi dan haka har an fara shirin tura shi court. Na ajiye takardar nace da officer din "can I see him please" ya kalle ni da mamaki yace "are you sure? He went through some questioning so an dan sassama shi kadan" ya karasa yana grinning. Na juya na kalli inda Hajiya har yanzu take zaune tana kuka Inna tana rarrashinta. Nace "zan ganshi, amma ni kadai" sai ya miko min wani form yace in cike. Na karba na tafi gurin su Hajiya nace musu "sun hana ganinsa, gwara ku tafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login