Showing 63001 words to 66000 words out of 174346 words
nake, can sai ga Sadauki yana kutso kai ta cikin mutanen yana tahowa inda nake amma yawan mutanen da suke gurin ya saka yakasa karasowa sai ya tsaya daga nesa yana miko min hannu, kawai sai na zubar da babies din hannuna na kama hannunsa amma ina kamawa sai ya bace ya barni ni kadai a tsakiyar mutane. Na kwalla masa kira "Sadauki! Sadauki!! Sadauki!!!" Amma bai dawo ba.
Ji nayi ana rirrike ni ana ƙoƙarin kwantar dani yayinda ni kuma nake ta yunkuri ina kiran Sadauki. Na bude idona naga nurses suna tura ni akan gadon marasa lafiya, ga Inna tana biye dasu a baya zani a hannu har suka tura ni wani daki suka rufe kofa, sai kuma naji shigar allura a hannu na, daga nan na koma baccin ko suman ne ban sani ba.
Sanda na kuma farkawa I was feeling much better, dan a hankali na bude idona na sauke su akan ledar ruwan da take sakale a jikin karfe sannan nabi tube din da ya taho daga kasanta da kallo har zuwa inda ruwan yake shiga jikina. Na fara karewa dakin kallo ina kokarin recalling abinda ya kawo ni nan. Idona ya sauka akan Inna da take zaune rashe rashe a dandaryar kasa duk kuwa da cewa akwai kujera a dakin. Kuka take da iyakacin karfinta, sai na tambayi kaina "kukan me take yi?". Abinda na fara tunawa shine kyakykyawar fuskar jarirai na, sai naji wani relief yazo min cewa ban mutu ba at least zan sake ganin su, zan dauko su in rungume su a jikina. Sai naji xewa yanzu na sami wani source of happiness din bayan Sadauki.
Nace "Inna" sai naga ta juyo da sauri gurina tana share hawayenta da gyalenta, tazo ta zauna a kusa dani ta rike hannuna wanda babu ruwan a jiki "sannu Diyam" na gyada mata kai kawai, zuciyata tana so ta tambayeta ina jarirai na amma sai baki na ya kasa furtawa. Ta tambaye ni "menene yake miki ciwo yanzu?" Na rasa me zance mata saboda duk ilahirin jikina ciwo yake yi tun daga kaina har yan yatsun kafata. Na tuna irin wahalar da nasha dan ko a mafarki ban taba tsammanin haka haihuwa take da azaba ba, na tuna mafarki na, sai naji ina jin haushin Sadauki me yasa ya rabu dani in the first place, mai yasa duk sanda nake bukatar sa nake samun bayanan?
Inna ta tashi da sauri ta fita, sai gasu sun dawo tare da wata nurse da tazo tana yi min sannu sannan ta auna bp na ta duba idona da hannuna tace da Inna "har yanzu mijin nata bai zo dawo ba? Yarinyar nan fa in ba'a kara mata jini ba za'a iya rasata, gashi har ta fara kumbura. It is a miracle ma da take a raye wallahi" Inna ta karkata kai "nayi ta kiransa wayar bata shiga wallahi, nayi ta kiran mahaifiyarsa ita ma bata dauka ba, yanzu babu wani abu da za'a iya yi mata kafin kanwata tazo? Tayi tafiya zuwa Abuja ne amma tace min yanzu zasu taho ita da mijinta" nurse din ta girgiza kai tace "gaskiya babu wani abu da zan iya yi mata ni dai, jinin nan dai shi za'a kara mata kamar leda uku first sannan kuma muga yadda za'ayi" Inna ta gyara mayafinta tace "bara in fita in je gidan da kaina" har ta kai bakin kofa kuma sai ta juyo "babu komai idan na tafi na barta ita kadai?" Nurse din tace "babu komai, allurar baccin ma zan sake yi mata. Amma kiyi sauri, in babu kudin ma ki samo maza wadanda za'a iya dauka a jikin su" Inna ta sake kallo na sannan ta fita da sauri. Nurse din tazo kaina tana zuko allura tace "ki godewa Allah yarinya, you are very lucky" tana yi min allurar na tambayeta "ina babies din dana haifa?" Ta girgiza kai tace "ban sani ba gaskiya, ke kadai aka kawo ki nan tun cikin daren jiya" daga nan bacci ya dauke ni ina wandering ina babies dina?.
Sanda ma kuma farkawa Inna na gani tana waya tana kuka "wallahi Hafsa babu ko dari a hannuna a yanzu, gashi suna ta tsorata ni da yana yin jikin nata. Naje gidan babu wanda ma na samu duk sun tafi asibiti gurin Alhaji" naji kamar kaina ya kara nauyi,nayi kokarin daga hannuna naji shi kamar ba a jikina yake ba, eyelids dina ma kansu sunyi nauyi. Na sake cewa "Inna" ta ajiye wayar da take yi ta taho gurina da sauri ta rike hannuna "sannu Diyam, Allah zai dube mu kinji? Allah zai dubi maraicinki ya bamu yadda zamuyi".
Kamar amsa maganar ta sai ga wani doctor sun shigo shida nurse, hannunta dauke da ledojin jini guda biyu tazo da sauri ta fara kokarin dauka min. Inna ta mike "jini? A ina aka samu jini" kana jin muryar ta zaka fahimci wani relief a ciki. Doctor ya juyo yana kallonta yace "ba ke kika kirawo wani dan uwanku ba?" Tayi saurin girgiza kai, "ni ban kira kowa ba, ban samu kowa ba da naje gidan" doctor yace "but baki dade da fita ba wani yazo yace dan uwanku ne, mun dauka ke kika turo shi, yace a debi jininsa, kuma muna aunawa muka ga yayi matching, shi leda ukun ma yaso bayarwa mu muka ce kar ya zama affected shi kuma. Ya biya dukkan bills dinku na gado da kudin magunguna duk mun rubuta masa ya biya har da kari wai ko wani abin zai taso" Inna ta koma ta zauna akan kujera "to waye wannan kuwa?"
Nurse din tace "Halima Usman Kollere dai yace yana nema. Ya shigo nan ma ya tarar tana bacci sai ya fita". Inna ta rasa bakin magana.
Nurse ta gama daura min jinin ta juya suka gama rubuce rubuce ita da doctor sannan suka fita yayin da Inna ta zauna tana ta jera addu'a zuwa ga savior dina. "Allah ya bashi abinda yake so duniya da lahira. Yadda ya bude mu Allah ka bude shi shida zuri'arsa, Allah ya biya shi da gidan aljanna" na gyara kwanciya ta ina kallon window, dare ne, meaning na kwana na wuni kenan da haihuwa. Ina 'ya'ya na?
Washegari sanda na farka naji muryar Mama suna magana da Inna, sai kuma hayaniyar su Asma'u da Muhsina. Na bude ido ina kwallon su, they looked like twins, ina twins dina? A tare suka taho gurina suna rige rigen rije hannuna, nayi musu murmushi ina shafa kawunansu, Mama ta taso itama "sannu Diyam, ya jikin naki?" Nayi gyaran murya nace "da sauki Mama" tayi murmushi tace "naji dadin yadda na ganki, da duk hankali na ya tashi, ai mun auna arziki sosai" Inna tace "gashi kinga har ta fara sabewa, amma jiyan nan duk a kunbure take. Wannan mutumin Allah ya biya shi da aljanna" Mama tace "ni nafi tunanin irin masu bin asibitin nan ne suna taimaka wa mutane, maybe ya tarar ana zancenta shine ya nuna kamar dan uwane, tunda dai kinga yanuwan duk mun tambaya sunce basu bane ba". Ni dai ina jinsu ina jiran inji sunyi hirar jarirai na amma shiru. Tare suka kamani suka tashe ni tsaye, na tashi da kyar ina cije lebe, sannan Mama ta hada min ruwan zafi sosai ta kaini toilet da kanta ta gasa min jikina ta kuma saka na shiga ciki. Muna fitowa take ce da Inna "ashe bata karu ba" inna tace "eh fa, haka nurse tace min. To ai yaran ne baki gansu ba yan kanana dasu, ni ko a bakwaini ban taba ganin masu kankantar wadannan ba" Mama tace "Allah sarki. Allah yasa masu ceton ta ne" gabana ya fadi, na juya ina kallon Mama sai naga duk jikinta yayi sanyi, na saki cup din tean data miko min na rufe fuskata da hannayena. Tayi sauri tazo ta rungume ni a jikinta tana jijjiga ni kamar yarinya "kiyi hakuri Diyam, Allahn da ya baki su shi zai baki wadansu. Kuma yayi alƙawarin aljanna ga duk iyayen da ya karbi ran yayansu suka yi hakuri" na kifa kaina a kafadarta nayi ta kuka, sai naji duk ciwon jikin da naje ji ya barni dan wanda nake ji a raina yafi na jikin ciwo. Sai naji muryar da naji jiya ta cewa ban mutu ba ta koma, naji tamkar rayuwa bata da amfani a gare ni. Na rufe idona ina tuno their cute little faces.
Sai da suka samu na tsagaita da kukan sannan suka saka ni a gaba na basu duk labarin abinda ya faru. Gabaki daya suka dauki salati. Inna tace "amma dai Saghir ya cika makaryaci, cewa fa yayi ita ce ta shiga daki ta rufe kofa sai daya ji shiru ya balla kofar ya shiga ya same ta a haka" na matso hawayen idona nace "wallahi karya yake yi. Shi ya kashe min yara na. Ta sanadiyyar shaye shayensa suka rasa rayuwarsu, bazan taba yafe masa ba wallahi". Mama tace "duniya ce Diyam, ki barshi da duniya ta ishe shi darasi shi da iyayen nasa dukka. Tun yanzu ba gashi nan sun fara gani ba" Nace "me ya faru?" Mama tace "ai daya gama mayen nasa ya farka ya ganku shine ya dauko ku babies din ko cibiya ba'a yanke ba ya taho daku gida a gigice, a nan aka jere wa Alhaji Babba su a gabansa innarki kuma Saghir din ya dauko ta tare dake ya kawo ku nan, dan wulakanci kuma babu wanda yayi kara ya biyo ku su ta yayan da suka riga suka mutu suke yi. Sai gashi Saghir yana kawo ku nan aka kira shi wai kuma gobara ta tashi a kantin kwari, shagunan Alhaji Babba gabaki daya sun kone kurmus babu abinda aka fitar, yanzu dai Alhaji ya yanke jiki ya fadi, hawan jini ya tashi, har yanzu yana asibiti unconscious".
Na karbi tean da Inna ta sake hado min na kurba ina jin zafinsa yana kona min bakina. A raina sai nayi wani tunanin irin hikimar ubangiji da take cikin haihuwar wadannan yaran, sannan kuma na saka a raina cewa mutuwar su tamkar wata sabuwar jarabawa ce a gareni, kuma nayi niyyar yin iyakacin kokarina wajen cinta. Twins dina sunzo sun tafi, ko picture dinsu bani dashi sai wanda nayi saving a memory na, kuma bazan taba mantawa dasu ba har in tafi inda suka tafi.
Kwana na biyar a asibitin na warware sai abinda ba'a rasa ba, sai dai something is bothering me deep inside sai dai na kasa magana a kansa. Ina zaune ina cin abincin da Inna ta zuba min ne ina tunanin yadda rayuwata take, kaddara upon kaddara haka take samu na and I wondered wacce kaddarar ce kuma next.
[2/4, 11:21 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman maama
Episode Thirty Five : A Glimpse
Yan uwa da yawa sunzo sun duba ni kuma sunyi min gaisuwar twins dina. Aunty Fatima tazo har sau biyu ita da yaranta, Adda zubaida tazo itama, sai daga baya sai ga kawu Isa nan yazo shida iyalinsa, sai a lokacin yake tambayar inna nawa ne kudin asibitin? Tace masa kawai an biya shikenan sai ya bar maganar ba tare da yaji yadda aka yi aka biya din ba ko kuma waye ya biya ba.
Da dare sai ga Hajiya Babba ita da wannan sister din tata, amma babu Saghir babu alamarsa, su inna suka karbe su babu yabo babu fallasa sannan suka tambayesu jikin Alhaji. Sunce yana asibiti har lokacin amma yana samun sauki sosai. Suka kawo min maltina da fruits. Na gaishe su sai Hajiya Babba tace "Diyam, banji dadin abinda kika yi ba ko kadan wallahi, kinga abinda ya jawo ko? Garin kiyayyar Saghir an kusa a rasa rayuka har hudu" Mama da dama kamar jira take yi tace "me Diyam din tayi" Hajiya Babba tace "innarta bata gaya miki ba? Saboda bata son Saghir bata son haihuwa dashi shine ta shiga daki ta rufe kanta wai gwara ta mutu ita da yayan baki daya, gashi nan yanzu yaran da basu ji ba ba su gani ba sun rasa ransu, ga kakansu can kuma rai a hannun Allah. Dan ma Saghir mai taurin zuciya ne da har dashi zamu hada muyi jinya" naji raina yana min zafi, hawaye masu zafi suka kawo a idona, na yunkura zanyi magana Inna ta dakatar dani tace "kar kice komai" ta juya gurin Hajiya Babba tace "wannan magana ce da Saghir ya fada, ita kuma Diyam ba haka ta gaya mana ba tace a gaban Saghir ta haife yara guda biyu yana sheka uban bacci, babu irin tashin da bata yi masa ba amma ko motsawa baiyi ba" sai sukayi dariya duk su biyun, yar uwar Hajiya tace "kuma yanzu ku da hankalin ku sai kuka yadda da wannan maganar? Wanne irin bacci ne mutum zaiyi har a haihu a gabansa bai san anayi ba?" Mama tace "baccin wadanda suka sha suka bugu mana? Wadannan kam aiko yanka su zakayi sai dai su farka su gansu a lahira" sai kuma suka daina dariyar, Hajiya Babba tace "Hafsa? Wacce irin mummunar magana ce kike jifan dan dan'uwanki da ita?" Inna tace "ba mummunar magana bace ba, gaskiyar magana kenan. Saghir shayeshaye yake yi, kuma wannan shayeshayen shi yayi sanadiyar mutuwar wadannan yaran. Wannan shine gaskiyar magana" Hajiya Babba ta juyo kaina, fuskarta babu annuri ta nuna ni tace "Diyam sakayyar soyayyar mu gare ki kenan? Sharrin da zaki yiwa dan uwanki kenan?" Na girgiza kai na nace "ba sharri bane Hajiya, in baku yarda da magana ta ba ku je gidan ku bincika, ku duba dakinsa na tabbatar ba zaku rasa kayan maye ba, ku duba motarsa ba zaku rasa kwalbar giya ba, in still baku yarda ba ku tambayi uwani ta baku labarin yadda ta kwace ni rannan a hannunsa wanda shine dalilin fara nakuda ta ba tare da lokacin haihuwa yayi ba, in still baku yarda ba ku tambayi mai gadin gidan, ai yana ganin dawowarsa gida kullum a buge yake shigowa" sai suka hada baki suna tafa hannaye suna salati "kuji yarinyar nan yar karama da ita amma ta iya shirya magana irin wannan? Ku kuma iyayen ta kuka hau kai kuka zauna dan kun zama butulu ko? Duk kun manta irin alkhairin da Alhaji yayi muku amma shine yanzu saboda abinda ya same shi har zaku juya masa baya ku dorawa tilon dansa sharrin shayeshaye? Dan kunga Alhaji iftila'i ya fada masa shine zaku juya mana baya?"
Sai ta kama kuka yar uwarta tana rarrashinta. Mama da Inna duk suka tsaya suka saki baki suna kallonta. Sannan Mama tace "Hajiya saratu in kika ce haka baki kyauta mana ba, da Diyam da Saghir duk yayan mu ne amma dole a cikin su in wani ya kauce hanya zamu fada dan gyaransa ba wai dan bata masa suna ba. Bincike ya kamata ayi kamar yadda Diyam tace, wanda duk aka samu da laifi a cikin su sai ayi masa fada dan ya gyara laifukan sa" sai suka tashi cikin fushi suka fice daga dakin. Mama tazo ta zauna kusa dani ta goge min hawayen fuskata tace "kiyi hakuri Diyam, in dai shayeshaye halin Saghir ne wata rana zai yi ne a gaban jama'a yadda babu wanda zai musa". Ni kam zuciyata zafi take yi min, an jima ba'ayi min abinda ya kona min rai kamar wannan ba, ya Saghir zai kala min wannan sharrin? How can they accused me of killing my own babies?
Washegari da safe Hajiya Yalwati tazo itama, tayi ta bawa inna hakuri wai abubuwa ne suka sha kanta ga Alhaji a kwance ga yara ga gida babu kudi. Sai Inna ta bata labarin yadda mukayi dasu Hajiya Babba jiya, sai tace "dalla rabu dasu, waye baisan Saghir yana shaye shaye ba? Amma su kullum sai su ke nuna kamar ba'a sani ba. Yanzu shima uban da ace lafiyar sa kalau kuna gaya masa zai musa". Da daddare muna zaune Inna tana ta mitar cewa tunda muka zo asibitin Saghir bai ko kira waya ya tambayi jikina ba, bai bada ko kwandala ta magani ba bai kuma nemi yaji inda muka sami kudin maganin ba. Tace "wannan wanne irin aure ne?" Na dauke kaina dan bani da amsar da zan bata. Bayan mun kwanta na yi mata tambayar da take raina. "Inna Sadauki kuwa ko yasan bani da lafiya? Yanzu shi ko duba ni ba zai zo yayi ba ballantana yayi min gaisuwar wadannan yaran? In babu aure tsakanin mu ai akwai shakuwa ko? Shi din tamkar yaya yake a gare ni" sai tayi shiru kamar bata jini ba, sai can tace "Diyam bansan inda Sadauki yake ba. Yaya ladi ma da naje nemanta gidan Alhaji Bukar ance min ta tashi kuma basu gaya min inda ta koma ba" na mike zaune nace "nemanta kikaje yi inna?" Tace "eh, naje nemanta da niyyar in bata gadon zainabu na gidan ku kamar yadda kika bani shawara amma ban same ta ba. Bansan ya zanyi ba yanzu". Nayi ajjiyar zuciya kawai ina wondering what happened? Ina Sadauki? Ko yana bornon? Ya samu admission din kuwa ko bai samu ba? Is he doing well? Na lumshe idona ina hangen fuskarsa a cikin kaina.
Washegari bayan an gama duk tests din da za'a yi suka sallamemu, muna shirin tafiya sai ga mutanen gidan Alhaji Babba nan sunzo, har da saghir, a lokacin ne suka fada mana an sallami Alhajin shima jiya, Hajiya Babba tana ta wani yayyatsina tana bata fuska, shi ogan ma a bakin kofa ya tsaya ya gaishe da Inna sannan yace min "sannu" na tattara shi na bawa iska ajjiyarsa. Budar bakin Hajiya sai cewa tayi "amma Diyam gidan ta za'a mayar da ita ba ko?" Inna ta tsaya tana kallon ta tace "ban gane ba" Hajiya tace "ina ganin abinda yafi shine ta zauna a gidanta, sai a tura wata matar haka take kula da ita kafin jikinta yayi kwari saboda kinga shi Saghir kinga babu dadi a barshi shi kadai a gida ba mace" Inna tace "haka ne" sai ta yafa mayafinta ta kama hannuna muka mike, ranta ya baci sosai.