Showing 105001 words to 108000 words out of 174346 words

Chapter 36 - Diyam Book 1 Hausa Complete

07 Jan 2025

1120

wani makokon takaici ya tokare ni. It really does hurt to be ignored, especially by someone da kuka saba sosai.

Sai kawai na kara volume din kallo na a raina ina fatan karar zata dame shi ya tashi ya fita amma sai ma naga sun dauko takardu shida Asma'u suna dubawa suna ta magana, kallo nake amma hankali na yana kansu sai na fahimci maganar ssce suke yi tana cewa "ni dai dan Allah hamma ka cire ni daga makarantar mu ka saka ni a government school in yi exams dina a can, wallahi government anfi ci, private basa bayarda da amsa" yarike baki "au kenan amsa kike so a baki? Maimakon kiyi karatu kici da kanki?" Tace "chaf, wadanda ma suka fini kokari basa ci ballantana ni? Yanzu kuma kaga in banci ssce din nan ba jamb dina ta tashi a banza kenan fa sai na sake wata" yayi dariya yace "kinsan kuwa sau nawa na zana jamb? Kuma a karshen karshe dai ban samu admission din dana ke nema ba" sai ta juyo ta kalle ni tace "Adda kema da kin sani kin cike form din jamb din. Kinga sai muyi tare in ba haka ba sai next year kuma" nayi kamar ban jita ba sai naji yace "in kina so sai a kawo miki gobe" na juyo na kalle shi naga yana kallona sai na kalli sides dina kamar me neman wani abu sannan na nuna kaina nace "are you talking to me?"

Sai yayi kamar zaiyi dariya amma ya wani maxe ya dauke kai yace "kina so ko ba kya so?" Nace "ina so, amma karka wahalar da kanka gurin kawo min, zan kira yaya Mukhtar ince ya siyo ya kawo min" ya daga kafada yace "duk daya. Tunda kinci waec dinki ba sai kin sake ba" sai na kalle shi da mamaki, I don't remember telling him cewa nayi waec ballantana zancen naci, nace "ya akayi kasan naci waec?". Sai kawai ya zauna yana kallona. And then all of a sudden sai ganin Saghir mukayi ya shigo palon hannunsa rike da Subay'a. He looked at me then at Sadauki and then at me again. Subay'a ta saki hannunsa ta taho gurina da gudu na bude hannuna na rungume ta ina jin dadi har cikin raina.

Saghir yace "what the f....." Sai nayi sauri na mike nace "Asma'u dauki Subay'a ku fita" dan nasan halin Saghir zai iya fadin komai ko yin komai a gaban Subay'a shi babu ruwansa. Ai kuwa tun kafin su fita ya fara "wato na matsa na baku dama ko? Shine wato zaku cigaba daga inda kuka tsaya? Ba kwajin kunyar duniya ba kuma kwajin ta Allah ko?" Sai Sadauki ya gyara zamansa ya dora kafa daya akan daya yayi folding hannunsa yana kallon Saghir. Ni kuma sai na mike, gabaki dayan su basa gabana dan haka baxan tsaya su bata min raina a banza ba. Nazo zan wuce Saghir ya kamo hannuna "ina zaki je? Munafuka kina wani saka hijabi kamar mumina" nayi kokarin kwace hannuna nace "don't touch me" ya maimaita "don't touch me, don't touch me kullum don't touch me." Sai ya juya yana kallon Sadauki yace "but I did touched her. Dan haka gwanjo nace. Duk inda zaka shiga babu inda ban shiga na fita ba and I left my foot print there" raina ya kai kololuwar baci, ban ma san me zance ba sai ji nayi Sadauki ya danyi dariya yace "are you sure about that?" Na kama kokawar kwace hannuna daga rikon Saghir zuciyata tana tafasa, zan so ace na fisu karfi in hada su duk su biyun inyi ta duka, how dare they talked about me like that.

Saghir yace "of cause am sure kasan a ledarta na bare ta. Sabuwa fil aka kawo min ita and I took her virginity" I froze. What? Ba zan ma iya kallon side din da Sadauki yake ba amma sai naji yace "ita nake so, not her virginity so...." Na kwace hannuna da sauri nayi bakin kofa hawaye yana bin fuskata, kafin in fita Saghir ya finciko hijab dina ya dawo dani cikin palon, ya hada ni da jikinsa muna facing Sadauki, Sadauki ya mike tsaye, Saghir yace "me yasa zaki gudu ne? Dan ke fa ake wannan taron ai ya kamata ki tsaya ki saurara kema ki tofa albarkacin bakinki a ciki. For example, tell him about our first night, tunda yace bai damu ba tell him how I did it maybe zai damu" na fara girgiza kaina da sauri. It is either Saghir is drunk ko kuma kwakwalwar sa ta fara tabuwa. And he said it. "I raped her" and then I saw a flash of fire a idon Sadauki. Saghir ya sake maimaita wa "I raped her the first night da aka kai min ita gida na. That was how she got pregnant for me har ta haifa min twins".

Sadauki took one step sai nayi saurin kwace jikina daga Saghir na tari gaban Sadauki na daga masa hannu "don't. Kar kace wani abu kar kayi wani abu just go" Saghir yace "yeah. Just go. But before you go, listen to this. Na mayar da ita dakinta." Na juyo da sauri ina kallonsa zuciyata tana bugawa kamar zata bar kirjina nace "no, no" yace "yes. Na mayar dake tunda dama saki daya nayi miki kuma shima bada son raina ba. Na mayar dake saboda ina son ki sannan kuma saboda I want him to think of you every night of every day when laying on his empty bed har zuwa ranar da zaki bar duniya ko kuma shi zai bar duniya. Sai inga karshen soyayya".

Inna ce ta shigo dakin da sauri, daga alama taga motocinsu a waje kuma tayi sensing something is wrong. Tana zuwa bata ce komai ba sai ta kama hannun Sadauki ta ja shi da sauri ta fitar dashi daga palon. Kafin su fita ya juyo ya kalleni and I saw a look on his face similar to wanda na gani ranar da zamu rabu a gidan Alhaji Babba. Na juya da gudu na shige bedroom din Inna na rufe kofa.
[2/24, 9:25 AM] +234 814 177 3102: ?? DIYAM ??

By

Maman Maama

Episode Fifty One : The Will

A jikin kofar na zame na zauna ina jin zuciyata tana wani irin bugawa, ji nake yi kamar zan mutu, kaina yayi wani irin zafi kuma hawaye ya tsaya a ido na. Ban taba tunanin it's possible ka tsani mutum kamar yadda naji na tsani Saghir a lokacin ba. Na fara girgiza kaina ina cewa "no no no" kamar mahaukaciya. I can't even imagine komawa gidan Saghir a matsayin mijina, I can't imagine him touching me again. I would rather die. Ina jiyo maganganu a palo kamar muryar inna amma bana gane me take cewa, sai naji ta taba kofar amma da yake ina jikin kofar sai ta kasa bude wa sai naji tana kiran Asma'u. Sai kuma naji ana knocking kofar. Da kyar na bude idona na matsa daga jikin kofar sai suka bude suka shigo su biyu sannan Subay'a ta shigo itama tana kallo na sai naga Asma'u tayi sauri ta dauke ta sun sake fita.

Inna ta durkusa gabana tana taba wuyana tana magana a hankali amma ni bana jin ma me take cewa. Sai kuma naga ta kama ni ta mayar dani kan gado ta kwantar dani ta juya na riko rigarta sannan cikin muryar da naji kamar ba tawa ba nace "Inna bazan koma ba. In na koma mutuwa zanyi" ta juyo tana kallona sai ta zauna tace "komawa ina?" Sai kawai na bita da kallo, wato Saghir saboda bai daraja ta ba bai ma gaya mata cewa ya mayar dani ba? Sai ta gane me nake nufi tace "cewa yayi ya mayar dake?" Ban iya bata amsa ba sai kuka, sai ta mike tsaye "wannan wanne irin abu ne? Wanne irin ya mayar dake kuma? Suzo nan su kare mana cin mutumci sannan kuma ya mayar dake bayan babu wani mataki da aka dauka? To babu inda zaki koma. Yanzu fa Hafsa take bani labarin wai kawun ku Isa ya bashi Suwaiba" Suwaiba yar kawu Isa ce itama kuma kusan set din mu ce, mun dan girme ta kadan. Lokacin muna yara ita da Rumaisa ne suke crushing on hamma Saghir, murja tana yawan gayamin cewa har yanzu suwaiba tana son Saghir amma ni ban taba ko saka abin a raina ba.

Inna tace "wato su suna can suna kokarin yi masa huce haushi shine shi kuma zai zo nan yace ya mayar dake? To ku biyu yake so ya hada a gida daya ko kuma ya yake so ayi? Ai indai kinga kin koma gidansa to ki tabbatar an zauna ne an hada ku anyi muku fada kowa an bashi laifin sa bawai kullum ace kece da laifi ba" tayi ta fadanta ni dai ina jinta kawai. Amma ni a raina nasan ko anyi mana fadan bana jin zan iya sake zama da Saghir, not after what he did today, not after what he said a gaban Sadauki.

Tuni da Sadauki da nayi sai naji wata irin fargaba ta shige ni. Tsoro nake ji sosai, tsoron abinda Sadauki zai iya yi akan furucin da Saghir yayi a gaban sa. Ina tsoron zuciyar Sadauki, ina tsoron zafin sa, ina tsoron rashin tafiyar sa, considering abinda yaji da kuma yanayin da ya fita a ciki, bansan hukuncin da zai dauka ba. Sai na samu kaina dayi masa addu'ar Allah ya taushi zuciyarsa Allah ya hane shi ga aikata abinda zaizo yayi nadama.

Sai magrib na tashi. Nayi alwala nayi sallah nayi kuka sosai a cikin sujjada ta na roki Allah ya kawo haske a cikin al'amura na. A lokacin ne Asma'u suka dawo ita da Subay'a. Subay'a ta taho gurina da gudu ta fada jikina tana kallona tace "Mommy kin daina kukan? Dazu naga kina kuka" nace mata "na daina subis" sai tayi dariya tace "Daddy ya tafi ko? Dama cewa yayi zai kawo ni gurinki in kwana biyu sai mu koma gidan mu tare" bance komai da akan wannan sai tace "Mommy kullum sai nayi kuka nace da Hajiya ta kawo ni gurinki ita kuma taki. Mommy dan Allah ni kar a mayar dani can gidan gwara in zauna a gurin ko kuma mj koma gidan Daddy na tare" sai na daga ta nace taje tayo alwala tayi sallah.

Na lura ta rame, ta fada sosai tayi baki. Kamar ba'a kula da tsaftarta sosai sannan idonta ya nuna alamar damuwa. Sai na yanke wata shawarar, bawai ni kadai ce bazan koma gidan Saghir ba har da Subay'a ma ba zata koma ba, tazo kenan.

Da dare ina jin Inna tana cewa Asma'u ta kira mata Sadauki, kamar tasan ina son in tabbayda lafiyar sa. Asma'u ta kira switched off, a raina nace nasan za'a rina, amma ban furta komai ba nayi shiru kawai. Nan fa hankalin Inna ya tashi tace "wai me ya faru ne mai zafi a tsakanin su? Ni sam banji dadin yadda naga Sadauki ba tunda kuma ya fita hankalina yana kansa wallahi" ta juyo tana kallona tace "me Saghir din ya gaya masa me zafi haka?" Na sunkuyar da kaina kawai, ni ba zan iya gaya mata kalaman Saghir ba. Jin nayi shiru sai tayi ajjiyar zuciya tace "Allah ya kyauta".

Washegari babu kunya babu tsoron Allah sai ga Aunty Fatima nan da Hajiya Yalwati da kanwar Hajiya Babba wai Alhaji Babba ya turo su su gaya wa Inna cewa Saghir ya mayar dani, a gaya min in shirya sai mu saka rana ni da Saghir din sai yazo ya dauke ni. Ni kawai kallon su na tsaya ina yi cike da mamaki. Inna tace "yanzu Fatima har da ke? Har dake za'a ci amanar marigayi dan bashi da rai?" Aunty Fatima tace "me akayi Amina? Yanzu mayar da auren shine cin amana?" Inna tace "ba mayar da aure ne cin amana ba, rashin kulawa da nuna son kai shine cin amana" sai ta lissafa musu dukkan laifuffukan Saghir wanda ni na gaya mata tace "ni ba wai goyon bayan Diyam nake yi ba ko kuma bana so ta koma dakinta ba, a'a, so nake a zaunar da Saghir shima ta fadi laifin Diyam din sai a hada su kowa ayi masa fada a bashi laifin sa. A ja masa kunne akan dukanta dan ni abinda yafi komai daga min hankali kenan" sai Aunty Fatima ta nuna itama bata ji dadin abin ba tace "ni duk fa bansan wannan ba, ni cemin sukayi Diyam tana kula Sadauki shi kuma Saghir yaji haushi ya saketa. Kema yadda muke dake ai kamata yayi duk abinda ya faru ki kira ni ki gaya min. Da Diyam da Saghir duk yayana ne ai". Amma ita kanwar Hajiya sai ta kama fada, ita wai lallai nayi wa Saghir sharri "babu wani shayeshaye da yake yi balle neman mata" sukayi ta bugawa da inna har tayi zuciya ta tashi ta tafi Aunty Fatima ma ta tafi sai Hajiya Yalwati ta zauna tace sai anjima zata taho. Daga jin haka nasan tsegumi ta zauna yi.

Tace "wallahi Amina karki mayar da yarinyar nan. Yaron nan fa bawai gyaruwa yayi ba. To yaron da baiji kan iyayensa ba ina zaiji kan wani. Shaye shayen nan fa munsan yanayi amma sai a rufe ido ace bayayi. Neman matan nan kuwa yinsa yake yi kamar babu gobe. Ita kanta Fatima da take wannan maganar rannan a gaba na naji tanayiwa Minal yarta fadan kar ta kuma kula shi. Dama Suwaiba ce tasa kuma yanzu sunce sun bashi dan haka ku rabu dasu, in dai abinda Diyam ta fadi gaskiya ne in ya auri Suwaiban ai zasu gani" Inna tace "za kuwa su gani. Ai ni zanso ayi auren nan ma ko dan gaskiya ta bayyana" Hajiya Yalwati tace "gaskiya kam zata bayyana. Tun yanzu ba gashi nan muna gani yana zuwa yana daukan ta a mota ba? Ahau, lokaci kadai muke jira".

Har tana shirin tafiya kuma sai cewa tayi "ni Diyam kuma ta wani zubin banji dadin tahowar nan taki ba. Dama ke ce mai dan saka shi yana dan kawo mana abinci gidan. Yanzu kuwa shiru. Rannan har ya fara zancen aurar dasu murja yanzu kuwa yadda yake a rikicen nan nasan ba lallai ne yayi ba". Inna ta dauki yan kudade ta bata tace ta siyawa yara sabulu.

Da dare sai ga wayar Saghir. Na kalli wayar kawai na dauke kai. Yayi ta kira sai na saka a silent sai ya turo min message "ki shirya. Rana ita yau zan zo mu tafi". Sai na kashe wayar gaba-daya na ajiye.

Washegari wai dan rashin kunya sai ga Hajiya Babba da kanta. Ina ganin ta nayi wa Asma'u text. "Ki dauki Subay'a ku bar gidan nan, sai na kira ki zaku dawo". Ina kallon su suka fice. Tazo ta saka inna a gaba "yanzu ya za'ayi ace kince ba zata koma gidan taba? Yanzu zumuncin kenan? Koma menene ya faru a tsakanin su shi ya hakura ita me yasa ba zata hakura ba?" Inna tace "tace ba zata koma ba. Ni kuma baxan matsa mata ba, matsantawar da nayi mata a wancan karon ma da ace zan iya dawo da hannun agogo baya da banyi ba".

Sai ta kama hannuna ta jani daki muka zauna a bakin gado tace "yanzu Diyam ke kinsan halin Saghir. Kinsan cewa ya chanja sosai saboda ke kuma ya chanja din. Yanzu da kika barshi Diyam Saghir duk ya koma yadda yake da koma fiye da haka. Me yasa ba zaki je ki karasa abinda kika fara ba? Ko dan saboda Subay'a" nace "Hajiya Saghir fa ba wai chanzawa yayi ba. Indai har da gaske ya chanza bai kamata ya koma ruwa ba dan bana tare da shi. Hakan yana nufin saboda ni ya chanza kenan ba wai saboda kansa ya chanza ba. To yanzu kuma in mutuwa nayi fa?" Tace "a hankali ai yake gyaruwar, in kin koma zai cigaba da gyaruwa ne" nace "Hajiya tun farko ba kwa ganin kamar akwai son zuciya da zalunci a cikin dora mim alhakin gyaran Saghir? Ku da kuka haife shi baku gyara shi ba tun yana danyensa ta yaya zaku bani shi bayan ya bushe kuma ku saka ran in kare rayuwata gurin gyaransa?" Tace "saboda munsan zaki iya. Kin fara kuma zaki iya karasawa" na girgiza kaina nace "bazan koma ba Hajiya" tace "saboda me?" Nace "saboda bana son shi Hajiya" sai ta tsaya tana kallona. Sai na tuno da ranar da Saghir yazo gaban inna yace baya son aure na. Hajiya tace "ba kya son sa fa kika ce min Diyam. Yanzu har idonki yayi budewar da zaki kalle ni kice ba kya son Saghir? Koma dai menene Saghir din nan, koma da gaske ne maganganun da kike fada still Saghir dai danuwan ki ne kuma duk kin da kike masa ba zaki taba cire jinin ki daga nasa ba. Mijinki ne kuma, tunda dai yace ya mayar dake Sannan uban yarki ne, ba zaki taba chanja mata uba ba" nace "Allah zai raya ta ko ba a gidan sa ba" sai ta mike da fushi ta fita, ina jinta tana cewa da Inna ina Subay'a zata tafi da ita, sai inna tace "Diyam tace Subay'a ba zata koma ba. Zata rike yarta" nan tayi ta bala'i "wallahi bata isa ba, ita tace ba zata koma ba sannan yar tasa ma ta hana shi?

Da dare inna ta kuma saka Asma'u ta gwada number din Sadauki but still bata shiga. Inna ta kalleni tace "ke baki san inda yake zaune ba?" Na girgiza kai nace "ban sani ba Inna. Sai dai office dinsa na sani" Asma'u tace "ni dai nasan kamar a hotel yake zaune. Amma bansan wanne hotel din ba" Inna tace "to ko Asma'u zan tura office din nasa gobe ta gani? Ni duk zuciyata bata min dadi wallahi".

Washegari Asma'u tana dawowa daga school sai gashi ya kirata. Tace "Inna ga hamma yana kira" Inna tace "to kiyi sauri ki dauka mana kar ta katse

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login