Showing 90001 words to 93000 words out of 153569 words
Chapter 31 - A Duniyata Book 1 Complete Hausa Novel
da tsafta. Ba kowa a filin gidan sai hayaqi dake fitowa daga kitchen da alamu ana gab da kammala tuwon dare. Yaransu bakwai da malam,maza hudu mata uku kuma dukkansu sun aurar dasu,don haka inna ce kadai ke rayuwa cikin gidan,sai babbar jikarta da aka kawo mata don ta tayata zama.
Sake sallamar tayi,kusan lokaci daya aka amsa mata daga kitchen din da kuma rumfar dakin inna. Cikin qasa da second daya wadda ke kitchen din ta fito. Matashiya ce da duka duka bata wuce sa'ar huda ba,murmushi sosai take saki,ta baro cikin kitchen din tana goge hawayen fuskarta da hayaqi ya sanya mata tana takowa
"Adda sabreen.....kece yau a gari?" Miskilin murmushin nan nata ta saki
"Inji maqi baqo ko rumasa'u?" Sai ta saki 'yar dariya tana kamo haneefa
"Muje yau inna taga su auta,tanata zancanku tace kwana biyu shuru,gashi batasan muhallinku ba bare ta binciki ko lafiya?,layinki Kuma kwata kwata baya shiga" Ta qarasa maganar tana riqe da hannun haneefa wanda tuni sukayi gaba zuwa dakin innar.
Sai a sannan da rumasa'u tayi zancan layinta baya shiga ma ta tuna yana daya daga cikin layukanta da suka tafi hutu,sai ta taka a hankali tana bin bayansu zuwa ainihin falon innar.
Dare dare ta samu haneefa gefan cinyar inna. A duniya gidan yana daga cikin gidan dasu haneefa din keson azo,don sai ya kasance musu kamar wani gida daya qwaya tak na 'yan uwansu da suke iya ziyarta su kuma sake,sakewar da basa iyayinta cikin ainihin gidan mahaifinsu.
Da murmushin tambayar da taji innar na yiwa haneefa ta qarasa shigowa ciki
"Wa'alaikumussslam.... .ina nan ina tuhumar amaryata me takeci naga tana ta tsaho?,kunyi nisan zango wannan karon AMEENATU(real name dinta kenan)". Murmushi ta kuma saki,a duk sanda innan ko malam sukayi kiranta da sunan ba wanda ke fado mata a rai sai mahaifinta. Shike yawaita kiranta da sunan,sunan da ya kasance na qanwa ga mahaifinsu guda daya tak da aka haifa a tsakanin su maza su uku,tazo kuma ta rigasu rasuwa a wajen haihuwa tabar nata yaran mata duka su uku.
"Kuna raina inna....abubuwa ne suka sha kaina" Ta fada tana zama itama.
Gaisawa sukayi sosai ta tambayeta malam
"Malam yau duka bai zauna ba,ya tafi kasuwar qauye,amma yana hanya nasan in sha Allahu".
Kamar kusan kowanne lokaci idan sunzo gidan,komawa take 'yar kallo,nadra haneefa harma da hudan suke sabgoginsu.
Lumshe idanunta tayi tana sauke boyayyar ajiyar zuciya. Ta tabbatar yau ta faranta musu ta kuma rage musu kewa qunci da takurar zama waje daya. Tana so ta dinga kaisu guraren da zasu dan sha iska,amma tana tsoron koda da kuskure suga wani abu da zai iya affecting tunaninsu.
Suna matuqar son a zo gidan,amma kuma duk dadewar da za'ayi ba'azo din ba ba zasu taba tada mata zancan ko suyi qorafi koda kuwa sau daya ba,har sai ranar da sukazo din.
A nan sukayi sallar magariba,sukaci kuma tuwon dare. Suna haramar tafiya malam din ya dawo.
Sosai shima yaji dadin ganinsu,ya bude kuma duk abinda yazo dashi din kama daga rake,gyada,quli kabewa,dinya da sauransu ya diba musu. Walwalarsu ta dadu sosai a sannan,duk sai da suka fice da zummar zasu tafi ya rage saura Sabreen din,ta xuge jakarta ta fiddo kudi ta aje gaban malam
"Malam ayimin sadaka,sannan ayi mana addu'a". Kudin ya kalla sannan ya kalleta.
"Zan miki addu'a aminatu koda baki bada komai ba....."
"Malam bakai na bawa ba,yaran malam na bawa"
"Idan kin fita waje ki raba musu da kanki kamar yadda aka saba" Ya tareta
"Malam don Allah kayimin alfarma ko rumasa'u ta raba musu,tabbas don dare yayi ne da bazan karya maka tsarinka ba,malam kai kemin fadan kaiwa dare a waje" Ta fada murya a karye. Tanason masa ihsani,amma mutumin yana da wani irin kamewa da gudun duniyar data tabbatar bazai karbi komai nata ba
"Shikenan,Allah ya karba.....kici gaba da kula da qannenki da kanki"
"In sha Allah malam" Ta fada tana yin qasa da kanta kunya da nauyinsa suna kamata. Tana jin kamar inna ta gaya masa wani abu a kanta ko zata gaya masa,saidai ta sani ko daya innar nada cikakkiyar kamalar da bazata taba fadin sirrin wani ba
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 49
Tunani ne kala daban daban cikin kanta sanda suke abun hawa har suka isa gida.
Banda hadiyya data samu tana zance a farfajiyar gidan nasu bata hadu da wani babba ba sai yara dake dan kai kawo a tsakar gidan nasu. Zuciyarta a karye take bude musu qofar dakin. Wannan shine tabbacin basu da wani sauran gata.....ba wani wanda ke tsaye yana jiran dawowarsu......babu wani da zai tambayi ina sukaje?,me yasa suka dade wuni sur a waje?,ba wani me musu barka da dawowa,dasu dawo da kada su dawo duk daya.....ire iren wadannan abubuwa ke qara mata wata qaqqarfar zuciya tare da jin cewa.....ZATA SADAUKAR DA TATA RAYUWAR don samarwa rayuwar qannenta gobe me kyau.....zata zame musu makwafin uwa da uba,dukkan wuya da dadi.....zata hanasu dandanar duk wani kalar baqinciki na rashin gata dama rashin abun kulawa da rayuwarsu.
Dukansu a qoshe suke kuma a gajiye,don haka basu jima ba kowacce ta nema wajen kwanciya,don dama ita haneefa suna shigowa ta bingire a wajen.
Sau biyu tana yaye labulen tana duban tsakar gidan nasu. Wanka takeso ta fita tayi saboda yadda gajiya kebin jikinta,uwa uba ma kuma ita din tun asali mutum ce data saba da yin wanka da dare kafin ta kwanta,saidai kuma daga baya abun ya zame mata qalubale babba,saboda kallon da ake mata da wasu idanu na daban.
Yadda ta fita dinnan ta wuni a waje ba zata iya kwanciya haka ba,don haka taci gaba da dabuwa. Akwai daukewar qafafu sosai,wanann ya bata daman cire kayan jikinta ta daura zani ta kuma lullube sassalkan gashinta da babban towel,ta dauki kayan wankanta.
Tana shirin fita nepa suka kawo wuta,don haka ta tsaya ta kashe solar din dakin ta maida musu nepa sannan ta fito.
Ta tsaya daga bakin famfonsu tana tarar ruwa. Tsakar gidan tarwai da haske,kuma tsaf tsaf dashi,dabiar gidan qwaya daya tal dake burgeta,wanda idan ka dauke wannan babu wani abu dake burgeta cikin gidan dama jama'ar gidan gaba daya.
Allah yasa har ta gama tarar ta wuce wankan ba wanda ya fito. Ta kammala ta nade jikinta da zanin ta dauro towel din a sama ta fito.
Tana duqe baqin famfon tana daura alwala. Bude toilet din wankan da akayi ya sanyata daga kai. Sukayi idanu hudu da ita,saita miqe sosai ta tsaya maimakon dazun da take duqe tana daura alwala.
Kallon bibo din takeyi kamar yadda itama ita take kalla,tun daga qafafunta har zuwa kanta da yake lullube da towel.
"Ha'illallahu.....mahammadurrasulillahi......ke duniya ina zaki damu?,aah?yanzu wankan ma sai kinzo gida?" Bibo taja qaramin salati sannan ta kama haba tana sake qarewa sabreen kallo.
Wani abune yazo ya yiwa sabreen tsaye a wuya,ta lumshe idanun takaici. Ta gama fahimtar zahirin abinda bibo ke nufi......ta kuma gama fahimtar abinda inda ta dosa,saidai kafin ma ta sake daga qafarta ta sake jin muryarta
"Kiji tsoron Allah 'yar nan......ki daina sanyawa mala'iku suna tsaida iyayenki cak cikin kabarinsu......yanzu wannan wankan....." A fusace da kuma wani irin zafin nama ta waiwaya tana duban bibo,abinda ya sanya towel din kanta zamewa sumarta ta fito.
Bata qarasa ba itama sai tabi kan nata da kallo. A bushe yake ba kuma alamun damshi ko lema,hasalima ta nannade doguwar sumar tata da tayi gado ta uwa da uba a tsakiyar kanta ta cusata guri guda,wannan ya sanya bibo din hadiye abinda taso fada din.
"Ke zaa cewa kiji tsoron Allah,kuma zan maimaita miki kiji tsoron Allahn" Ta fadi da ita a nutse sannan ta fara takawa tana dosar dakinsu.
Idanma tace zata riqe zafin da qirjinta yakeyi da suya to tabbas ta yiwa kanta qarya,don haka ta sulale saman kujerar falon ta saki wani marayan kuka.
Bibo na daya daga cikin qalubalen rayuwarta,bibo na daya daga cikin mutane na gaba gaba da suke mata wata irin adawa mara fasali ba tare da tasan meye ne ta tsare musu ba. Ta jima a wajen tana kuka har sai da fuskarta tayi wani pink pink,sannan ta samu ta sauya kaya taja jikinta zuwa kan gadonta ta kwanta tana rufe idanunta tare da sauraron bugawar jini daga kanta wanda keson komawa ciwon kai.
Sassanyan ringing dinnan shine ya sakata bude idanunta. Shaf ta mance da batun wayar sai yanzu da tayi kuka. Tunawa tayi tayi alqawarin kai wayar a yau,kada ma su tsammaci ko ta gudu da sune,wannan ya sanya ta miqa hannunta qasan pillow din data ajeta dazu ta dauko da nufin dagawa ta basu uzurin gobe in sha Allah aje a karba.
Bata wani tsaya bata lokacin duba me kiran ba,tunda tasan koma waye zai kira a irin wannan lokacin tabbas makusanci ne,don haka ta shafa ta daga ta kuma Kara a kunnenta.
"Assalamu alaikum anni?" Ya furta cikin husky voice dinsa dake cakude da wani irin nannauyan sauti dake nuna izza da zatin mamallakin muryar. Yayi sallamar a sanda yake tsakiyar system da kuma tarin tarkacen takardun dake dauke da plan na ginin sabon kamfanin samar da kayan qyale qyale na mata mafi tsafa da daraja da za'a dinga qawatashi d wani yanki na diamond d gold.
Wani yankewa gabanta yayi ya fadi,zuciyarta kuma ta buga sosai har tana jin sautin bugun cikin kunnuwanta. Batasan dalili ba batasan kuma me yasa taji hakan ba,sai ta buda bakinta a hankali da muryarta da tayi nauyi saboda nauyin dake cike a qirjinta
"Ba ita bace". Shuru ne ya biyo bayan fitar sautin nata. Ita tana bawa kanta tabbacin wancan mutumin ne daya kira duba da shurun da aka sakeyi mata kaman dazu,shi kuma kwanyarsa tana son alaqanta sautin da muryar mara kunyar yarinyar nan data dag masa waya.
Kusan a tare suka daga wayar daga kunnuwansu. Ta samu tabbacinne ta hanyar karanta sunan dake yawo saman screen din.
Sauke wayar yayi daga idanunsa,yaja siririn tsaki yana kashe wayar. Sautin tsakin yakai mata har kunnenta,wani mummunan baci taji ranta yayi. To ita meye nata a ciki da har zai bita da tsaki?,waye wannan daya cika izza haka?,wanne irin mutum ne me izgili da rashin sanin daraja da martabar dan adam?,don kawai a bisa kuskure wayarsu ta fado cikin kayanta sai ta zama abar wulaqantawa?. Samun kanta tayi da latse wayar kawai ta kasheta gaba daya ranta yana suya,cikin ranta kuma tana yiwa kanta alqawarin a gobe wayar ba zatakai sha biyu na rana ba a hannunta zata kira busari yakai musu duk inda suke.
"Wanne irin wulaqanci ne da rashin sanin abinda kukeyi da zaku ci gaba da barin wayar anni a wani wajen?" Fuad din ya furta daidai sanda ya kira musaddiq.
"Kayi haquri hamma,ta fadi inda za'a karba anje ba'a samu ba,anyita kiran wayar kuma ba'a dagawa".
"Koma meye banason na sake kira naji muryarta.....kuyi magana da ita idan wayar takeso ta sauke layin daga kai,ka sanya ayima annin swapping a dauki wata wayar a hada mata".
" Ka kwantar da hankalinka me babban suna,banjin yarinyar tana da niyya ko nufin riqe wayar nan,akasi kawai dai aka samu da ajizanci irin na dam adam......tana da kirki qwarai,ita ta kaini asibiti ta kuma zauna dani har sai da musaddiq ya iso". Wata sassanyar iska ya saki daga bakinsa,sai yanzu ya tuna inda yasan muryar
"Itace mara kunyar yarinyar nan data tsaya tana yiwa mutane fada akai don ta kaisu asibiti?" Ya jefawa anni tambayar da nutsatsiyar muryarsan nan.
Murmushi ne ya subucewa annin. Tasan halin fu'ad qwarai da gaske. Yana da tsananin kamewa da rashin son shiga sabgar kowa
"Ba rashin kunya tayi ba muhammadu......fada ta yiwa musaddiq,kuma ai ta fadi gaskiya ne,ta kuma yi daidai,sun tafi yawonsu sun barni,a jikina kuma babu inhaler kwata kwata,a nata ganin indai hakan taci gaba da kasancewa komai ma yana iya faruwa". Shuru ya ratsa tsakanin bayanin anni,yana ji kawai annin tana son bata kariya ne saboda halinta na bawa kowa uzuri komai girman laifin da ya aikata mata
"Is okay....." Ya fada yana sauke siririyar ajiyar zuciya a qoqarinsa na fesar da bacin da ranshi yayi
"Ya jikin naki anni?"
"Jiki alhamdulillah na warware"
"Suna kula dake kuwa?" Ya sake tambayarta da wannan seriousness din nashi. Murmushi ta saki kadan
"Qannenka suna qoqari sosai,ina samun kulawa tamkar kana nan.....saidai kewarku,ina fatan komai yana tafiya kaman yadda aka zata?,kowa kuma yana lafiya?" Murmushi ya saki,wanda mutum uku keda wannan baiwar sakashi murmushin koda baiyi niyya ba,anni abba da farouq kada ma farouq din yaji labari. Abune me wahala ka tsinci murmushi akan fuskarsa,akwai mutane da yawa dake da tambayoyi da yawa a kansa
Anya kuwa ya taba dariya?
Wannan kuwa yana murmushi?.
Wasu tambayoyin na isa kunnensa ta harshen farouq,wasuma kam baisan ana yinsu ba.
"Ba zamu wuce kwanaki hudu ba anni in sha Allah". Farinciki ya wadaci fuska da zuciyarta
"To ma sha Allah.....amma baka shaidamin ba me babban suna?,banda na tambayeka da ba zaka gayamin ba ko?".
"Aah anni......banason na sanyaki wannan hidimar me yawa" Murmushi ta sake saki
"Hidima ai bata qarewa Muhammadu muddin akwai rai a jikina.....fatan da zakuci gaba da yi mana shine Allah ya qara mana lafiya....."
"......da nisan kwana me amfani" Ya qarashe fadi. Qaramar dariya ya sanyata a wannan karon
"To da nisan kwana me amfanin mu daku gaba daya".
Koda suka gama wayar baiko motsa ba a wajen,yayi zaune da wayar kawai a hannu yana juyata. Duk yadda zai fasalta anni a rayuwarsa da zuciyarsa bazai kwatantu ba. Ita din uwa ce data amsa sunanta na uwa. Wadda tayi sadaukarwa da yawa cikin rayuwarsu,sadaukarwar da tayi musu ba qarama bace,sadaukarwa ce da UWA kadai ke iyayi wa danta.
Asthma dinta bata taba hanata taba ruwa saboda su,asthma dinta bata taba hanata sammakon tashi koda da sassafe ne a lokacin da hazo da sanyi suka lullube sararin samaniya......a yanayin da kuma yafi zama barazana ga masu lalurar......asthma dinta bata hanata tsaftace musu muhallin kwanansu......bata hanata dafa musu abinda zasuci
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 50
koda ita din bataci ba,bata kuma hanata kulawa da lafiyarsu koda ita din bata da cikakkiyar lafiya. Har tsakiyar zuciyarsa yana jin wata qauna me girma tana tabashi game da anni,tayi musu abinda baki bazai iya fadi ba,zuciya da ruhi ba zasu iya mancewa ba. Ta musu hidima da jikinta da kudinta da lokacinta harma da lafiyarta,irin hidimar da ya debe tsammanin zasu sameta,irin hidimar da suka buqaceta a yunwace daga wajen wadda tayi silar zuwansu duniya amma ta gagaresu.....kulawar da baiyi tsammanin zasu sameta ba daga gurin kowacce mace a duniya. Baiga abinda zai samu a duniya ba da zai manta da anni.....baya tunanin akwai abinda anni zata nema daga gareshi ta rasa.
Yana shirin sauke wayar tasa don ya tattara tarkacensa ya wuce daki ya samu bacci koda na awa biyu ne kafin zuwan lokacin sallar asuba sai kiranta ya shigo.
Kamar ko yaushe ya zubawa kiran idanu,a duk sanda zata kirashin sai ta tuna masa da abubuwa masu yawa. Aduk sanda kiranta zai shigo wayarsa saita tada masa wani abu daga can qasan zuciyarsa.
Bashi da wani zabi da ya wuce ya daga din,sai ya sake zama sosai ya ya dauki wayar yana karawa