Showing 132001 words to 135000 words out of 153569 words
Chapter 45 - A Duniyata Book 1 Complete Hausa Novel
takawa sai kuma ta tsaya cak tana wurga idanunta sassa sassa na qawataccen office din da aka narka kudi akayi masa wani irin lafiyayyen tsari me daukan hankali. Tabbas tasan babu yadda za'ayi guri irin wannan ya rasa CCTV camera,indai kuma hakanne ta yaya zata iya gudanar da komai ba tare data samu wata matsala ba?.
Dan wani abu cikin kunnenta ta matsa,muryar JIB ta bayyana,sai ta danja da baya kadan ta raba qafa tsakanin office din da veranda din da jerin gwanon office din yake don bataso ta fito gaba daya ko ta shiga gaba daya don kada camera din ya samu damar nunata
"Ni dakai duka bamuyi tunanin CCTV ba jib?".
"Ya salam" Ya fadi yana aje wani numfashi
"Haka ne......wasu lokuta dama kece ke mana hasshen irin wadannan abubuwan......ba matsala bane,manyan kamfanoni irin wadannan akwai irin cameras din da suke amfani dasu,katseshi ba zaiyi wahala ba nasan takan irinsu sosai......yanzu ki tsaya daga nan inda kike...kafin ki shiga ki gano mana daga wanne saiti camera din yake shikenan kawai"
"Okay....."
"....karki datse connection daga nan har mu gama aikin"
"So kaji komai tsakaninmu kenan bayan sirri ne?" Ta fada cikin dan salon zolaya da wani lokaci takeyi masa. Dariya ya qyalqyale da ita kadan yana fadin
"Tuba nake....Allah yabar soyayya". Sai kawai ta saki murmushi kadan tana tura qofar hadi da sake qarewa office din kallon tsaf.
Cikin qasa da minti goma ta gano komai suka kuma katse sadarwa da tsaida aikin camera din. Da dan hanzari ta ajjiye hand bag dinta. Tanaso tayi komai ne ta gama kada damar ta subuce mata yazo ya shigo.
Sai data tattara dukka hankalinta da nutsuwarta ta karanci inda komai yake ajiye a office din,gudun kada ta taba wani abu ta kasa maidashi daidai inda yake hakan ya nuna masa alamar tayi masa bincike. Hatta da biro dake ajiye qwaya daya tal saman teburin sai data karanci a yadda yake ajiye din,ta dauka ta kuma gwada maidawa ta tabbatar ya zauna kaman yadda aka ajiyeshi. Wayarta ta fidda,ta sake yiwa office din qaramin video komai da komai sannan ta maida wayar jakar,ta kuma shiga aikin bincika komai daki daki.
Baya ga abinda suke nema taga abubuwa da yawa cikin office din,irinsu condom dake nuna mata lallai riqqaqqen dan bin mata ne,taaba irin masu tsadar nan da sauran abubuwan maye. Abinda ya sake darsa mata mugun tsanarsa kenan,wutar kuma ta tabashin ta hanyar kwakwashe masa komai tana sake ruruwa cikin ranta. Ya zama dole ta durqusar dashi,durqusarwar da bazai sake tashi ba.
Maida komai tayi kaman ba wani abu daya faru a office din,ta tattare duk abubuwan da take nema din tayi musu ajiya ta musamman cikin jakarta. Hatta da wani qaramin ledar cake da akaci aka barshi sai data tabbatar ta maidashi yadda yake,ta gyara rolling dinta da kyau tana sauke numfashin samun nasarar kammala komai ba tare daya dawo ba.
Maqoshinta taji ya bushe tana da buqatar ruwa,sai ta taka tana nufar kyakkyawan fridge din dake girke waje daya.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 70
Turus tayi tana kallon yadda aka maqare gidan farko na fridge din da wasu kalan kwalabe da bata saba ganin irinsu ba. A hankali take dubasu har ta fahimci kwalaben na meye?.
Kwalaben giya ne tabbas,ta maida idanunta ta lumshe tana furta
"Innalillahi" Can qasan harshenta. Sai kuma taja jikinta baya a hankali tana matsawa daga jikin fridge din don batajin zata iya shan wani abun sha daya fito daga fridge din komai halascinsa.
Zuciyarta ke qara bugawa da tsanarsa haushi da kuma takaici. Shikam mikail dame zaiji?,abubuwan ai sunyi masa yawa,sun masa yawan da batasan wanne a ciki zai iya dauka ba. Kaman ana son bata amsar tambayarta sai qofar tayi qaramar qara alamun ana budeta ne,ba jimawa ya bayyana cikin office din yana dubanta da murmushi
"Am so sorry dear......ina fata banyi keeping naki da yawa ba......boss ne idan ya tashi aikinsa tamkar engine.......baya gajiya,na samu na kubota da qyar".
Idanunta ta dauke daga kan files din da yake rungume dasu,wanda ta tabbatar a cikinsa sauran bayanan da take nema suke. Ta kalato dukkan dauriyarta ta jefeshi da qaramin murmushi
"You deserve it ai....."
"Wow......serious?" Ya fada da wani irin zumudi da zakwadi yana qarasowa gabanta dab da ita ya zauna har yana neman hade gwiwoyinsu guri guda. A dabarance ta miqe da sauri,sai ya bita da kallo. Taji a jikinta yana kallonta ne don haka ba tare data juyo ba tace
"Bari nayi fitsari kadan"
"Oh....okay to dear" Ya fada yana dora files din saman table din cikin ransa yana qissima yadda a yau din zai gwangwaje,a yau din zai kashe duk wata qishirwa tasa dake damunshi a rai.....a yau zaiyi morewar da bayajin ko daren amarcinsa zaiyi wannan.
Gaban madubij toilet din ta tsaya tana sauke numfashi idanunta akan fuskartata. Muryarta can qasa tace
"Please jib.....muyi komai mu gama da sauri......banason ganin fuskarshi kwata kwata"
"I know.....zanyi iya qoqarina......amma please kada kice zakiyi halin hawainiyar nan taki" Dan murmushi ta saki,yasan halinta sarai,koda nawa aikin zai basu idan ta motsa mata tana iya cancel dinsa
"Zanyi qoqarin nima" Ta amsa masa tana kunna famfo sai ta bige da daura alwala.
Mutum hudu ke biye dashi sanda yake takowa cikin veranda din idanunsa saman takardar dake hannunsa yana sake karanta abinda take dauke dashi. Can qasan zuciyarsa akwai wani kokwanto da mamaki,kusan zaman yau da suka fara yi da mikail wanda ba'a qarqareshi ba saboda quracewar lokaci ya karanci kamar hankalinsa ba gurin yake ba sam sam. Yana karance da kuma bibiye da motsinsa. Duk muhimmanci da girman takardar a wajen kamfanin gaba daya amma har ya iya mantota cikin dakin taron,wannan ya sanya ya yanke biyoshi da kanshi ya kawo masa don ya sake alamta masa muhimmancin takardar.
"Wait here" Ya fadi a nutse ga mutanen dake bayanshi yana sanya code na qofar office din Mikhail din ta bude ya murza handle din yana turawa can qasan ransa yana jin kamar bai kamata yayi hakan ba ba tare daya nema izinin shigar ba. Duk da kowanne office a qarqashinsa yake amma bai shiga office din kowa,hakanan baya taba bada damar a bude maka office muddin baka nan,amma haka kawai yau din yaji yayi hakan.
Sanda ya murda handle din yake shigowa da sallama cikin husky and deep voice nashin nan,dai dai sannan itama ta bude qofar toilet din ta fito tana qoqarin maida rolling na mayafinta.
Idanunsa kan mikail daya miqe a rude cike da tsananin mamakin ganin boss din nasa yau da kanshi a office dinsa gabansa yana faduwa,yayin da nata idanun suke kan fu'ad fuskar fu'ad din tana dubansa qasan ranta tana jin kamar tasan wannan fuskar.
Baikai ga lura da ita ba ya miqa masa takardar
"Keep it......." Ya furta da wani irin yanayi idanunsa cikin tsakiyar qwayar idanun mikail wanda hakan kadai ya isa ya gaya masa wani gargadi yake aika masa da kuma muhimmancin da takardar ke dashi
"In sha Allah sir" Ya amsa yana karbarta da hannu biyu. Juyawa yayi da zummar ficewa a office din,dai dai sannan idonsa ya sauka a kanta. Idanunasu suka gauraya waje daya,sai tayi saurin zare dubanta daga kan fuskar tashi gabanta yayi wani irin faduwar da batasan meye dalili ba.
Dan zuba mata ido yayi na sakanni tamkar zaiyi magana,sai kuma ya fasa,ya juya ya kalli mikail sannan ya maida dubansa kanta sai kuma ya juya yana ficewa a nutse daga office din.
Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke. Allah ya sanya ba zuwa yayi ya samesu cikin wani yanayi ba da dukka sauran gaskiyarsa da yakeson tabbatarwa boos din a yau babu ita.
Yasan an jima ana kai masa tsegumin halinsa,amma kasancewar shi din ba mutum bane me daukan qananun maganganu ya sanya abun bai wani tasiri ba.
A yadda yake jinsa a dan rude sai yaji yana buqatar giya don daidaita nutsuwarsa. Ya tafi zuwa fridge din yana fadin
"Boss......bashi da sauqi kwata kwata,idan har wani kuskure ya faru tsaf zaka rasa aikinka,a wajensa wannan din ba wani abu bane me wahala".
Batace dashi komai ba kaman yadda bata kula da abinda ya dauko yakw sha ba,ta qarasa wani sashe na dakin ta tayar da sallah kawai don lokacinta ya shiga.
Tunda ta tayar da sallar har ta idar yaba zubawa cikinsa barasa. Sanda ta sallame din saita kafeshi da idanu kawai. Ranta cike fal da mamakin yadda dan adam da hannunsa zai dinga durawa cikinsa abinda yasan zai cutar dashi?.
Waiwayowa yayi sai suka hada ido. Ta hade fuska da kyau tana miqewa
"Banason wannan abar sam... Muddin kanason mu kasance tare kuwa saidai ka rabu da ita" Tayi maganar duka tana jin wani iri har cikin ranta
"Am sorry dear.......indai wannna ne kada ki damu na ajiye".
Tana maida takalmin qafarta tana tunanin yadda zata samu ta duba takardar da boos din nasa ya kawo masa yanzu?.
Ta kalleshi tana gyara zamanta bayan ta gama saka takalmin
"No water no drinks?" Murmushi ya sake mata
"Akwai mana.....gasucan a fridge sai kalan wanda kikeso" Kai ta girgiza
"Ba wani abu da zai fita a fridge dinnan na sha shi"
"Why?" Ya tambayeta yana zare ido
"Na tsani shaye shaye" Ta bashi amsa kai tsaye,amsar data sakashi sake zaro idanu
"Duk kyan nan naki babe?,kinsan yanzun macen bariki bata gama cika ba sai ta hada da cakewa?". Ido ta dan rufe kadan tana budesu,kalmar MACEN BARIKI da yayi amfani da ita a kanta tana mata quna sosai cikin rai
"Cikar wannan kyan naki babe ki dinga taba wani abun da zai sanya ki dinga jin kanki very high......Ni zan dauki nauyin baki komai mai tsada wanda ba kowacce yarinya ce ta isa ta samesu ba......sai irinku matan da kuke da gata a wajen partner dinsu......like kaman wannan giyar.....bata bugar dani,saidai nayi bacci na awa daya shikenan idan na farka zan jini fresh......please ki koya sha ko kadanne akwai dadi,saikin gwada zaki gayamin" Yayi maganar yana qoqarin sake zuba wata a cup da alama kuma ita yake da niyyar baiwa idan ya zuba din.
Tsam ta miqe tana jawo jakarta dake a gefanta tana ratayawa
"Ya haka kuma?" Ya tambaya yana dubanta
"Zan wuce gida" Da sauri ya diro daga saman kujerar da yake kai
"Haba babe.....me yayi zafi?,bayan baki cikan alqawari na ba......kinsan dakin nawa na kama mana a Bristol kawai saboda yau?" Idanunta ta juya tana ajiye numfashi
"Banga alamun ka dauko wannan hanyar ba......kana yimin maganar abinda babu shi a tsarina.......baka iya saukar baqo ba sam......na nema abun sha kana min sharhin da lokacinka yake ci maka......idan lokacin dana diba ya cika zan tafi koda ba komai daka samu"
"Ba za'ayi haka ba" Ya fada da hautsine jin zaiyi asaran abinda ya qwallafa rai a kai,ya ajjiye komai na hannunsa ciki harda takardar da yanzu yanzu aka jaddada masa muhimmancinta yayi hanyar fita daga office din.
Wannan shine ya bata cikakkiyar damar qarasawa,ta fidda wayarta tayi snapping takardar ta turawa JIB kai tsaye ta share komai ta koma mazauninta tana jiran dawowarsa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 71
Kai tsaye ya wuce saman sofan dake ajiye bangare daban na office din yana zame takalman qafarsa. Already sunyi sallan azahar bayan fitowarsu daga hall din,don haka ya maida bayansa kadan ya jingina da sofa din.
So yake ya huta kadan kafin ya fita yaje yaga baqinsa,to amma tunani ya hanashi hutawar,don maamah ce ta fado a ransa,sai ya fidda waya yana kiran musaddiq idanunsa akan agogo yana qirga yawan awannin da suka rage da zasu maidasu gida su duka. Ko kadan bazai bari musaddiq yaci gaba da mu'amala da gidan maamah haka kai tsaye ba,ko mu'amala da dukkan wani abu daya shafi gidan game da abinci ko abun sha ba. Don sam hankalinsa bai kwanta ba bazai kuma taba kwanciya ba,don ta kashe dukkan wani abu da zai bashi nutsuwa tattare da ita.
Bugu daya ya daga,muryarshi ta fita cikin girmamawa.
"Qarfe nawa zaku bar company yau din?".
"Zamu dan jima yau,saboda akwai sabbin fertilizer da aka muka fitar,zamu gabatar dashi ga manoma"
"Yayi kyau,idan kun kammala kafin ka fita a company din ka sanarmin"
"In sha Allah" Ya fada a girmame.
Katse wayar yayi yana sanya hannu zai jawo file din daya shigo dashi sai kuma abun ya fado masa. Ya tsaya cak yana juya ganin da yayi mata. Daga toilet ta fito,jikinta duk damshi da lema da yake nuna ta taba ruwa,to me yakai mace office din mikail?.
Ya jima yana jin maganganu iri iri akan mikail din,to amma shi din ba mutum bane ke daukan qananun maganganu shi yasa bai taba bi takai ba. Hakanan bai fiya zafafa bincike da bin al'aurar mutum ba. Amma yau haka kawai yaji maganganun da yakeji a kanshi din yana dawo masa.
Muqamin da Mikhail yake dashi a company din bashi da alaqa sam da hada hadar jama'a karbar baqi ko mu'amala dasu ballantana yace harkar kasuwanci ne ya kawota wajensa.
Qaramin tsaki yaja yana qoqarin watsar da maganar. Ta iya yiwuwa irin watsatsun 'yammatan nan ne dake yawon bin maza office office dinsu don kawai son abun duniya. Muddin ko haka ne shi bazai bari wannan ta faru cikin kamfaninsa ba. Dukiya yake nema ta halal me cike da albarka,dole duk wanda yake qasansa ya kiyaye dokar Allah lokacin mu'amalarsu,bayan kuma mutum ya fita daga kamfanin saura ya rage nashi.
Zancen ya maqale a ransa duk da ya bude file yana dubawa,qananun shekarun daya fuskanta tana dasu su sukafi tsaye masa a ido duk da ba qare mata kallo yayi ba,yana tsoron kada ya zamana yaudarota yayi ya kawota office dinsa?. Wayarsa ya zaro ya laluba number saddiq da ya baro a first floor yana ganin ma'aikatan da suke da buqatar dauka kafin shi ya gansu yayi final interview dasu.
Ringing biyu ya daga,sai ya zauna sosai ya sake tambayarsa inda yake duk da yasan a inda yake din
"Muna qasa.....na kusa kammalawa dasu"
"Alright......kasan me nakeso da kai?" Ya tambayeshi yana shafa baqar kwantacciyar sumar dake gefan fuskarsa zuwa habarsa
"Aah hamma"
"Mikail......ina buqatar kowanne motsi nasa daga yanzu ya zama ana min monitoring nasa"
"Done hamma" Saddiq din ya fada cikin qwarin gwiwa.
Sosai wannan aikin da hamman ya bashi yayi masa dadi,don ya jima yana ganin abubuwan zargi masu yawa tattare da mika'il din,to amma baida cikakkiyar hujja da zai gabatarwa da hamma,shi kuma hamma koda kana da hujja sanda zaka gaya masa magana sai ya bincika ya tabbatar da gaskiyar maganarka.
Minti talatin ya sake duba agogonsa. Yana shirin miqewa saddiq din ya shigo,ya gabatar masa da komai ya ajiye masa duka takaddun
"Well done" Fu'ad ya fadi bayan ya tabbatar da komai ya tafi daidai.
"Kira me sunan malam.....wanne time ya bawa mutanen nan?" Ya gayawa saddiq daya kasance executive assistant dinsa wani lokaci ya juya ya zama P.A dinsa,har muqamin me sunan malam dinma yana hawa wato scheduling coordinator ma gaba daya.
Hularsa ya dauka da agogonsa daya