Showing 93001 words to 96000 words out of 153569 words
Chapter 32 - A Duniyata Book 1 Complete Hausa Novel
a Kunnensa,
Cikin jin isa da izzar cewa ta haihu.....cikin isa da jin izzar ita din a yanxu wata abace cikin duniyar.....cikin jin izzar ta isa takai qololuwar gata a cikin jerin iyaye mata ta amsa sallamarsa.
"Barka da dare.....an wuni lafiya?". Maimakon ta amsa masa saita sake daidaita kanta,a dake take masa magana
"Yanzun ace bankai kima da martabar da a kullum zaka kirani kaji ya na kwana ya na tashi ba?" Ta maida masa gaisuwar da qorafin abinda me masa suya a qirji.
"Afwan.....kiyi haquri" Ya zabi furtawan. Har cikin zuciyarsa,har kuma tsakaninsa da Allah kirantan kaman yadda take buqata wani baqon abune cikin rayuwarsa dama lokutansa. Yadda ta zamewa rayuwarsu baquwa haka dukkan wata mu'amala da zaiyi da ita take zama baquwa a wajensa. Koda yayi niyyan yin hakan saboda sauke nauyi da haqqin haihuwa dake wuyansa sai ya manta sam sam,tunda abune da aka fareshi bada dadewa ba,sabo dashi kuwa zai dauki lokaci kafin ya shiga jiki da zuciya,bayan haka ma......kwata kwata mu'amalar dake a tsakaninsu wata irin tattaurar mu'amala ce da babu taushi a jikinta bare ta shiga zuciya da kyau ta tsayema tunani.
"Koda baka nemeni ba ni bazan zubewa duniya ku ba.....ku zama inuwar giginya na nesa kasha dadi...." Ta fadi tana watsa hannuwa ba tare data tuna da kuskuren rayuwarta na farko ba.
Numfashi ya aje,maganartata ta zama tamkar wani tuni ne daya dace ace kanta da kanta ta yiwa shi
"Ba zata zubewa duniya su ba....." Baisan zubewa ta nawa ya rage tayi musi ba,kalamanta a kullum sake haska masa ita yake,yayi imani yana kuma sake samun gamsuwa da dalilai masu tarin yawa dake bayyana masa lallai AKWAI DALILIN dawowarta cikin rayuwarsu......lallai ta dawo ne bawai da sunan nadama ba ko gyaran kuskure......AKWAI DALILI AKWAI KUMA HUJJA.
Wasu yana kallonsu shimfide a zanen tafin hannun qaddararsa,wasu kuma baisan daga inda zasu soma bullo musu ba.
"Ba'a canzawa tuwo suna Muhammad,kuma ko ma meye ka zama sai dana haifeka sannan ka zama din......mahaifiya daya ce kuma ni dince dai". Idanunsa ya lumshe na wasu sakanni kafin ya samu budesu. Ba abinda maganganunsa ke haddasa masa sai sake jagula duk wata qanqanuwar nutsuwa tasa da yake qoqarin samarwa kansa.
"Kiyi haquri" Ya sake maimaita mata kalaman da ta dade da haddacesu daga bakinsa.
"Yaushe zaku dawo?,idan ba nan kusa bane dawowar taka ka sanarmin......don nasan sai yadda akayi dakai,sai kuma abinda aka shimfida maka".
Yaji saukar kalamanta sosai har saman zuciyarsa. BATA SON AHALIN ALHAJI HAMZA KIBIYA ya dade dayin wannan karatun a qanqanin lokacin data duro cikin rayuwarsu......ya kuma san halinta tun daga sanda ya fara rarrabe abubuwa har zuwa sanda ta fice daga rayuwarsu. Idan batason abu bata sonshi kenan......dadi ko wahala basa sauyata akan abun. Idan taqi taqi kenan.....hakanan idan taso taso kenan......bata ja da baya akan duk abinda ta sanya a gaba......bata rasa ABUN HARINTA komai dadewar lokaci.
Wadannan abubuwan ya sanya ya sanya dukkan wata nutsuwa da karatu nasa a kanta......ya sanya duk wani nazari da dogon hange da tsinkayensa a kanta,yasan wacece......sanin da ita kanta batasan bata kuma yi zaton yakai zurfin haka ba.
"Ba zamu wuce satin nan ba in sha Allah" Ya amsa mata kamar yadda ya amsawa anni a dazun.
"Har sai ankai sati?" Ta masa tambayar a zaqe,har abun yadan so bashi mamaki,don sam salon tambayar nata baiyi kama da ta zaqu ko tsahon kwanakin sun mata yawa da zasu bayu ga ganinsa ba,tabbas yasan akwai dalilin tambayar a qasa.
"In sha Allah" Ya bata tabbaci yana jiran dalili na gaba
"Kudi nake buqata ka turamin ta account dina akwai amfanin da zanyi dasu......kada suyi qasa da million daya" Tayi maganar kanta tsaye cike da karsashi da qwarin gwiwa kaman yadda hajja ta kwatanta mata.
Mamaki kadan ya kamashi.....saidai ya ajeshi a gefe
"Akwai abinda baki dashi?,cikin gidan ko sutura ko wani abu makamancin haka?,ko akwai wanda kike da buqatar ayi masa wani abun?"
"Duka babu ko daya.......shin waima sai ina da wannan buqatun zan buqaci kudi daga wajenka?,yarinya ce ni qarama ko kuwa?,ko banyi isar da zaa dauki tsabar kudi a bani ba har sai akwai dalili ko hujja?"
"A'ah......"
"To dakata......ba sharhi nakeso ba......kayi abinda nace daga yau zuwa gobe". Sai yaji alamun yanke kiran,abinda ya tilasta masa sauke wayar daga Kunnensa yana binta da kallo.
Yatsunsa kawai ya dora saman goshinsa yana murzasu a hankali,kadan kadan yake furzar da iska me zafi daga bakinsa. Tabbas yasan da akwai wani abu......akwai wata a qasa......
Wanzuwar kudi a hannunta kwata kwata ba alkhairi bane,kuma ko yanzun bayajin alkhairi ne ya sanya ta nema.
Cikin lokaci qanqani yaji jijiyoyin kansa sun qara adadin gudunsu da kuma harbawarsu,abinda ya haifar masa da fara jin alamun ciwon kai. Bayason hayaniya......bayason matsala kwata kwata,wannan ya sanya yake nesa da mutane da al'amuransu,banda kasuwanci daya daukoshi tsundum ya jefa cikin mu'amalantar mutane qarfi da yaji.
Ba wani karsashi ko qwarin gwiwa ya dauki dukan abinda yasan yana da buqata,a maimakon tattare takardun nasa gaba daya da yayi niyyar yi ya kuma shiryasu kamar yadda ya saba. Yana da wani irin tsafta da duk abinda yayi amfani dashi zai wahala ka sameshi ba'a killace ba.
Kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka ya tura qofar dakinsa idanunsa akan dakunan abba da saddiq daya tabbatar zuwa lokacin sun jima da yin bacci,wani lokacin sai ya dinga ji kamar su kadai ne basuyi sa'ar rayuwa ba.....sai ya dinga ganin kamar kowa ya dace da rayuwa me kyau amma banda su. Duk sanda irin wannan tunanin ya fado masa yakanyi qoqarin korar shaidanne daga ransa.
A gefan gadon ya zauna,ya miqa hannu ya kunna bedside lamp,dan siririn hasken da baida takura da yawa ya bayyana. Hannunsa ya zura qasan drawer din da fitilan take kai,ya ciro wani mini wallet dinsa,ya bude ya sake zaro wani qaramin hoton dake ciki.
Duk da hoton baida cikakkiyar kala amma fuskar mutumin ta fita sosai,kamannin nan nasa da murmushinsan nan da idan ya kalla sai yaji kaman idan ya kirashi zai amsa.
Wani abu ya tsaya masa a wuya,yayin da idanunsa suka sauya launi,gefe daya wani qaqarfan abu da ya jima yana kokawa dashi akan maamah din ya fara taso masa,sai ya fara hadiyar zuciya kadan kadan yana qoqarin hadiye bacin ranshi,tamkar me hadiyar lomar abinci,don daga inda inda kake kana iya hangen Adams Apple dinsa daya zamewa wuyansa dama fuskarsa ado yana kaikawo daga sama zuwa qasa.
A duk sanda ya kalli fuskarsa cikin hoton sai yaji duk duniya ba wanda ya kaisu maraici......a duk sa'ilin da zai kalli wannan jarumar fuskar sai yaji zuciyarsa ta cika da qiyayyar kowacce d'iya mace a duniya idan ka debe anni da manal......wata irin wuta ce take ruruwa a zuciyarsa a kanta......har yakanji kamar bazai iya sake kusantar muhallin da take bama ballantana yaci gaba da accepting nata ko kyautata mata a matsayin uwa.
Fuskar abban wata fuska ce da a kullum take tunasar dashi gwagwarmaya da ainihin ma'anarta.....fuskar tasa fuska ce dake karanta masa tare dayi masa bitar cusgunawa....uzzurawa da azabtarwa irin ta diya mace. Kowanne hoto nasa da abinda yake karanta masa.....hakanan da abinda yake tunasar dashi. Ko kusa ko alama....ko sau daya.....hakanan koda wasa bai taba sha'awar aure ba ballantana wata diya mace. Yana kallonsu a wasu halittu ne na daban da babu imani ko tausayawa cikin lamuransu.
Sanadin ciwon abban....da silar data sanya ya dinga ci gaba abune da bayason tunawa,abune dake dake tilasta zuciyarsa juyawa MAAMAH baya da dukkan abinda ya danganceta. Koda ya tuna da abin a sanda take daura dashi yakanji baya buqatar kallon fuskarta ko kuma sauraren muryarta,yanaji cewa ba abinda zai bashi sukuni face yayi nesa da ita.
*_AKWAI WANI SIRRI.....AKWAI WANI BOYAYYEN SIRRI CIKIN DUNIYARSA_*
*******Sannu a hankali take tafiya cikin daya daga cikin layukan da suke zame musu turba kuma hanya ta isarsu gida a duk sanda suka rasa samun abun hawa ko kuma kawai jin rikici irin na dalibin dakan qirqirarwa kansa tafiyar qafa haka siddan.
Ita daya a hanya amma tanata mamakin yadda yau aka raba musu lokacin tashi daga makarantar alhalin tunda suka fara tsahon shekarun tare ake tashinsu. Ta cika tayi fam akan yadda nadra din da haneefa sukayi gaban kansu suka taho gida abinsu ba kamar yadda suka saba ba abinda basu taba yi ba.
Gefe daya kuma na zuciyarta ya cika da saqe saqe tare da tunanin yadda zata qarqare haddace ayoyin qarshe na shafin da a yau zata bada haddarsa a islamiyya. Kaman daga sama,babu zato kuma ba tsammani taji an finciki qaramar jakar da take dan cillata a hannunta wadda ke dauke da muhimman abubuwa da dama. Sanda ta daga kai kuwa a firgice barawon ya soma nisa da ita yana gaya mata
"Idan kina da gata,ko kina da me qwatoshi ki turo shi" Sai ya juya cilla sassarfa ya fada wani lokon dake daura dasu.
Ko wanne sashe na jikinta rawa yake,tayi wata irin tsorata da bata taba yin irinta ba.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 51
Abune da bai taba faruwa da ita ba koda wasa,ta waiga gabas da yamma kudu da arewa,ba kowa a layin,babu gicci ko wulqawar kowa,ko cutas da ita zayayi zaiyi ne hankali kwance,abinda ya sake kada mata hankali kenan,ta soma yunqurin tattara dukkan qoqarinta wajen ganin tabar layin.
Taku uku tayi ya shawo kwana. Hannunsa riqe da jakartata da yanzu yanzu aka wafceta. Birki taja ta tsaya,gudun zuciyarta yana sake qaruwa kaman zuciyarta zata fito ta bakinta. Ta qura masa idanu tana kallonsa kaman yadda shima ita yake kallon. Guduwa takeson tayi amma ta kasa kaman an kafeta a wajen.
Duk taku daya da zaiyi yana sake ganin kamanni na jini da kuma yanayinta da SABREEN din. Yana mamakin yadda ta iya boye komai nata,yadda ta iya bad da bami,ta iya nutsewa da narkewa cikin sararin duniya ba tare da ka iya gano daga ina take fitowa ba ina kuma take komawa?.
"Karkiji tsoro......ni ba cutar dake zanyi ba.....jakarki na karbo miki,nazo wucewa naga abinda ya faru,karbi jakarki" Baya taja kadan,bata jin aminta dashi sam sam a zuciyarta. Wani irin raino da horo sabreen ta yiwa kowannensu na rashin yarda da baquwar FUSKA muddin sunanka NAMIJI.
"Da gaske nake miki.....ba cutar dake zanyi ba,idan kuma baki yarda ba ga jakarki nan" Ya fada yana ajiyeta a tsakaninsu sannna ya juya ya fara takawa yana barin wajen fuskarsa shimfide da murmushi,qasan zuciyarsa kuma fes cike da murnar samun CIKAKKIYAR NASARA da kuma tabbacin DAUKAN FASA mafi ciwo a gareta.
Sai data tabbatar ya bada tazarar da koda ya juyo zuwa gareta zaiyi wahala ya cimmata sannan ta taka ta isa ga jakar,ta tsugunna ta dauka,ba tare data damu da datti da qurar data debo daga qasa ba ta rataya tana maida idanunta kansa.
Tafiyarshi yakeyi baiko waiwayota ba,ta kalli jakar ta kuma kalleshi,sai ta buda bakinta a hankali tana furta
"Na gode". Cak ya tsaya tamkar dama yana dakon martaninta ne,sai ya waiwayo yana sake fadada fara'ar fuskarsa
"Nima na gode.....sunana....." Dakatawa yayi kadan saboda tuna wani abu da yayi
_"Tana da wayo,tana da hadari.....da alama kuma akwai abinda ta taka_ kalaman suka dawo masa kai fes
"Sunana BASSAM....kefa?" Ya furta yana murmushi tare da samun gamsuwar lallai sunan zaifi saurin isar da saqo a maimakon ainihin sunansa na NASEER. Bashi da buri baya kuma fatanbta fahimci komai har sai zuwa sanda komai din ya kammala......har sai zuwa sanda shi da kansa zai mata bayanin komai. A lokacin da yake buri da kwadayin jin sheshsheqar kukanta......a yanayin qunci baqinciki da kuma tarin damuwa da yake fatan ta hallakata......koda bata hallakata ba yana fatan tayi mata mummunar illar da koda gaba ba zata qara gigi kasada ko gangancin shiga shingen mutane irinsa ba.
"Kefa 'yammata?" Ya tambayeta cikin lanqwasa murya da tausasa harshe gami da sanya wani amo me sanya nutsuwa ga duk me saurare.
Lokaci daya ta danji ta samu nutsuwa kadan,sai ta sauke boyayyar ajiyar zuciya sannan ta bashi amsa
"Huda" Ta furta a nutse tana jin wani iri da kiranta da sunan 'YAMMATA da yayi,karo na farko cikin rayuwarta da wani ya taba kiranta da wannan sunan.
Murmushi ya sakar mata yana gyada kanshi gami da lumshe ido yakuma budesu a lokaci guda
"Nice name.....duk wanda ya baki wannan sunan ya iya zaben suna". Maganar tasa ta sanya fitar murmushin dole a saman fuskarta. Tadan murmusa kadan,abinda ya sake sanyashi ganin kamanninta muraran da sabreen. Wutar daukan fansanshi ta sake ruruwa cikin ransa.
Kai ta jinjina a nutse tana dan sadda kanta qasa kadan
"Autyna ce" Ta samu kanta da bashi amsa
"Antynkin nan tana ja da yawa.....ta iya zaben sunaye" Ta fada da ma'ana biyu,a zahirance kuma da harshen da ba kowane zai fahimci boyayyen sirrin dake qasan zuciya ba.
Dagowa tayi a karo na biyu ta sake kallonsa,sai taji wani dadi zuciyarta tana saki kadan. Duk wanda zaya so sabreen a wajensu basu da kamarshi......kaman yadda suke nisantar wanda zai kawo suka a kanta ko wanene.
"Nadan rakaki kadan ko?,ki fita daga layin nan,don har yanzu ban gamsu da sahihancinsa" Ya fadi yana duban gefe da gefansa bayan ya zube dukka hannayensa cikin aljihu.
Tayashi duban itama tayi gabanta yana dan faduwa,ta yaya zata iya jerawa dashi wai?. Amma ko kafin tace komai ya fara takowa zuwa inda take tsayen yana jifanta da murmushi,tadan ja baya kadan dole ta fara takawa ya rufa mata baya
"Kada ki damu,bawai zamu jera bane,ba wanda zaisan tare muke......kawai dai zanyi gadinki har ki aminta" Kalmar aminci daga bakinsa ta sanya taji ta sake,sai taci gaba da tafiya,shi kuma yana biye da ita da 'yar nisan tazara a tsakaninsu.
Duk wani taku nata guda daya yana lasafta yadda komai zai wakana......a yanzu bayan wutar daukan fansa dake ransa,wata wutar daban ta soma rura kanta da kanta a zuciyarsa.......bayajin koda ba komai tsakaninsa da sabreen zai iya qyale wannan danyar 'yar shilar ta wuceshi. Duk da bata qarasa 'yar uwarta ba a komai.......amma zata sama masa nutsuwa yayi yaqinin hakan ko yaya take kaman yadda ya dade yana tsara zai samu daga yayartata.
Bai tsaya ba har sai da qafafunta suka isa babban qofar gidan nasu,sai ya samu waje nesa kadan saboda gudun bacin rana da bacin aiki,ya tsaya kawai yana jifanta da wani mayataccen kallo tamkar mayunwacin zaki.
Har ta sanya qafafunta sai ta dakata ta waiwayo,suka hada idanu abinda ya bashi damat jifanta da wani shu'umin murmushi. Itama murmushin ne ya subuce daga bakinta tana jin cewa ya kyautata mata matuqa,abinda ba kasafai suke samunsa daga wajen al'ummar da suke kewaye dasu ba,don haka wannan din ya qawatar da ita. Bakinta ta bude a hankali ta furta kalmar
"Na gode sosai". Duk da tasan ba lallai ya iyajinta ba,amma zai karanci bakinta. Ya kuma karanta din,sai ya daga mata kai don haka ta juya tana shigewa cikin gidan.
Haka kawai murmushi ke fita a fuskarta tana tuna yadda komai ya kasance. Badan shi ba Allah ne kadai yasan abinda zai faru da ita a wannan qonannen layin da babu kowa. Ba yadda kuma zatayi,nan dinne dai hanyar wucewarsu tilo guda daya,inda da wata hanyar tabbas ba abinda zai sanyata ta sake bi ta nan wajen.
"Ke dawa kike murmushi ke daya?" Sabreen dake tsaye gaban fridge dinsu tana duba adadin pure water da lemon daya rage musu a ciki ta fada hannunta dafe da murfin fridge din. Cikin sauri ta gyara