Showing 126001 words to 129000 words out of 153569 words
Chapter 43 - A Duniyata Book 1 Complete Hausa Novel
Kamar kowanne lokaci tayi masa sallama wadda shikam ba kasafai yake iya tunawa da ita ba. Sai yadan daburce kadan kafin ya amsa sallamar ya dora da fadin
"Good morning queen....nayi kira nayi kira har na gaji anqi a dagamin waya.... Kwatsam sai gashi na tsinci wani abu da ban taba kawowa zai faru ba".
Murmushi ta saki kadan wanda ko kusa da gefen zuciyarta bai kai ba,yayin da shi kuma kunnuwansa yaji kaman zasu narke da fitar sautin sassanyan murmushin nata. Kowanne tsiga na jikinsa sai ta shiga tashi
"Ka sani ko yanayin alaqa da dangantakarmu ne suka dauko hanyar sauyawa?"
"Da gaske!" Ya fada da wani irin murna daya kasa boyuwa yana fidda idanunsa waje
"Eh mana....." Ta amsa masa a taqaice.
"Yes!" Ya sake fadi da wani irin dadi yana mamayarsa
"Indai haka ne kiyimin proving mana......"
"Kamar?" Ta jefa masa tambayar da zazzaqar muryartan nan,don wajen da takeso azo kenan tana tunanin kuma ana gab da zuwa din,saidai ita ba zata iya requesting ba har sai ya nema da kanshi
"Mu hadu yau.......don Allah kada kicemin aah". Shuru tayi cikin salon jan aji,kaman bataso
"Please mana.....please,kice to" Ya fadi murya a raunane cike da fatan samun amincewarta
"Shikenan"
"Oh god......" Ya sake fadi yana dukan kujera da hannunsa,yana kuma ji duk duniya ba wani d'a namiji da yakaishi sa'a yau dai a duniya. Yana nashi bidirin amma nata qasan zuciyar a quntace. Wani mugun tsanarshi take ji da haushinsa. Da gaske wannan din dabi'arsa ce bazai kuma taba canzawa ba,ko shin mata nawa ya lalata da kalar wannan mummunar dabi'ar tasa?.
"Bansan da wanne irin yare zan gode miki ba....amma zakiga godiya a aikace har saikin rasa da meye zaki maye min gurbin hidimata a gareki......tabbas zan ninka darajarki.....zan daukaka martabarki a idanun duniya......zan maidake tauraruwa cikin mata....zan miki ado da gold irin adon da sai 'yar gata...."
"Thank you......thanks" Kawai tace dashi don tanaso ya dakata daga zubo wannan dogon sharhin nasa. Tana tausaya masa a daren yau irin barnar da zatayi masa,ta tabbatar wadannan maganganun da yake jerowa a yanzu saisun koma sumbatu.
"Zan shiga company akwai lissafin da zamuyi da boss dina.....duk inda la'asar yayi koda bamu gama ba zan dauki excuse......zan kama mana daki a Bristol,zan tura miki details da komai da komai".
Baki ta tabe tana jin wani haushi yana cikata. A daren yau bashi ba,hatta da boss din nasa saita sakasu a lissafin da babu fita. Tanaji a jikinsa ma shi da boss din basa zaiyi wahala idan ba zamuje ta tadda muje mu ba. A yadda yakan bata labarinsa lokaci bayan lokaci......irin kudaden da yake wasa dasu da kuma shekarunsa talatin da bakwai a duniya amma ace ba macen aure?,to idan ba sheqe ayarsa yakeyi ba me yakeyi kenan?.
Ture wannan tunanin tayi daga zuciyarta don a halin yanzu bashi da amfani,abu guda daya ta sani ba sassauci,kuma a yau din takeso mika'il ya zama tarihi cikin rayuwarta,shi kuma ta bashi darasin da zai sanya rayuwarsa tayi laushi da kyau.
"Ba laifi...." Ta amsa mass,bata kuma jira cewarsa ba ta dora
"Ina fata kasan rule din.....zaka rigani isa gurin da wasu mintuna......kuma bana buqatar kowa yasan muna tare ne da kai"
"Dukka dokoki da qa'idojinki kisa a ranki an gamasu......ranki ya dade.....da zaki bani dama da kin fadi inda zan aiko driver ya daukomin ke.....don bana buqatar kiyi wahala" . Wani sirrintaccen murmushi ta saki
"Na maka uzuri saboda baka jima cikin rayuwata ba bare ka fahimci wacece ni......zanzo da kaina,bana buqatar kowanne driver"
"As you wish.....saidai zan saka kudin transportation.......please karkice min aah" Idanunta ta lumshe sannan ta budesu,har ta fara gajiya da dogon hirarsa
"Alright....byee" Ta furta a taqaice tana tsinke wayar.
Ajiyeta tayi gefe tana furzar da iska daga bakinta. Inda ace dukka haka mazan aure suke ba shakka a jiya da kunnuwanta basu jiye mata abinda taji ba saman dogon layin masu lalurar ciwon zuciya dake dakon ganin likita......tabbas da idanunta basu gane matan auren da hawan jinin bacin rai da baqincikin d'a namiji ya jefa musu hawan jinin daya juye musu zuwa ciwon zuciya ba......da bataga matar data yanke jiki a wajen ta fadi ba......wadda daga qarshenta gawarta aka fitar a asibitin 'yaruwata na kuka dukka sanadin baqinciki namiji.
Ita kuwa me zatayi da aure?......wanne tsautsayi ne zai kaita damqa rayuwarta hannun d'a namiji guda daya yayita hajijiya da rayuwarta ba gaira ba dalili?.
Abubuwan data gani din dasu ta kwana,su suka yita yiwa kunnuwa da idanuwanta gizo,kuma suka hanata komawa duba ayshatu.....suka kuma sanyata jin ta matsu ta kora mika'il mashkur harma da ya'aqoub din daga rayuwarta gaba daya.
Kafin tabar wajen taji alamun shigowar saqo. Koda ta duba alert ne daga banki da sunan mika'il wanda ya sanya mata 1mil a matsayin kudin mota kawai. Ta juya wayar a hannunta,ta sake juyata,sai kuma ta saki siririn tsaki tana ajeta a gefe.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 67
Kamar kowanne lokaci,yakanyi breakfast dinsa ne a sassansa,saboda duk wani abu da zaiyi breakfast dashi yasha banban da cimar mutanen gidan. Wannan ya sanya ya aje cook dinsa daban wanda yasan tsare tsare na cimarsa. Koda a ranar baida ra'ayin cin abincin cikin gidan,nashi cook din zai masa irin abincin da yayi dai dai da ra'ayinsa,zai shiga ne kawai ya taya anni zaman cin abincin.
Yau din ranar litinin ne daya tsara abubuwa da yawa da zaiyin. Bakwai da mituna goma sha shida ya murza handle na bedroom dinsa ya soma takowa a nutse zuwa ainihin parlor dinsa.
Yayi wani sassanyan kyau cikin tsadajjen yadin Qiviut fabric me tsananin taushi da kuma rashin nauyi,daya daga cikin favourite yadiddikansa duk da tsadar da suke dashi amma baya jin wannan. Metro blue ne da yayi matuqar haska fatarshi,ya kuma fidda sura haiba da cikar kamalarshi.
Fuskan nan a dinke kaman ko yaushe,wanda kusan duka safiya anni ko abba ne ke jefa murmushi a kanta,sai kuma fitinannenshi farouq musamman idan a sassan ya kwana,to fa kafin su rabu kowa ya wuce wajen aikinsa sai ya addabeshi har ya zare wannan yanayin daga kan fuskarsa din..
Yau din budadden takalmi ya sanya,abinda ya bawa zara zaran yatsunsa daman fitowa kenan cif da cif cikin takalmin da ya soma zareshi daga qafansa sanda ya iso dining area dinsa.
"Good morning sir" Cook din nasa daya kasance yaren igala ya furta cikin girmamawa yana rusunawa
"Morning ameh.....how are you?" Yana jan kujera zai zauna
"Fine sir...." Ya amsa masa yana matsowa da sauri gami da kama aikinsa na serving nasa komai. Wannan kuma shine ya bashi daman duba wayarsa da yaji tana vibration,wanda kusan koda yaushe idan zai kwanta bacci yana barinta ne a hakan gudun takura.
Sunan daya gani ya sakashi dan furzar da iska kadan daga bakinsa. Duk da cewa a yadda suka rabu jiya bayajin yau zata kira ta assasa wata matsalar ko damuwar,shidai baisan me yasa duk sanda zaiga kiranta hakanan ba sai wani abu ya tsirga masa ba.
Daidai sanda Ameh yake barin gurin ya daga wayar,ya ajeta daga gefansa bayan ya sakata a handsfree yana jawo mug din da ya zuba masa dafaffiyar madarar da aka watsa mata turmeric guda guda,wannan yadan sauya mata kala zuwa yellow kadan.
"Barka da asuba" Ya fadi cikin nutsuwar nan tasa. Murmushi ta saki daga daya sashen,cikin son nuna zallar kulawa tace masa
"Barka kadai.....kira nayi naji lafiyar d'ana ya ya tashi?,na kira dan uwanka wayarshi a kashe,ina fatan komai lafiya?" Kaman ko yaushe,duk wani motsi nata yana masa banbarakwai,yanzun ma haka ne,sai ya aje mug din yana hade hannayensa waje daya
"Mun tashi lpy alhmdlh.....da fatan kema haka......musaddiq ban fita cikin gidan ba tukunna,bamu hadu dashi ba". Fuska tadan yamutse,amma bata bari sautin muryarta ya canza ba
"To yayi ba damuwa.....amma ya kamata dai ace kasan kwananshi da tashinsa......banason yadda kuke nesa nesa da juna fa?".
Sai yaji maganar kamar ta saukar da murmushi cikin zuciyarsa,murmushin dake nannade da mamaki,amma sai ya basar
"In sha Allah"
"To hakan yayi.....nace ba?" Ta fada don janyo hankalinsa
"Ina tare dake maamah" Ya amsa mata tana duba agogon hannunsa da kuma qaramar wayar dake ajiye a gefe,wanda kiran saddiq yake shigowa
"Cewa nayi bari nayi muku tuni,dinner by 8pm yau......ina fatan zaku cikamin burina na kasancewa tare daku duk dare?". Idanunsa ya sake lumshewa,tsananin rashin gamsuwa da tsarij yana tsarga masa. Da can da waye da waye taci gaba da kasancewa duk daren a sanda ta tattarasu ta baiwa duniya kyautarsu?. Bayajin a stage din da ake kai yanzun zai yarda da ita ko ya gasgatata. Furucinta da kuma alaqarta da hajja harira ba zasu taba barin zuciyarsa ta nutsu da ita ba
"Okay.....we will be there in sha Allah"
"To yayi na gode.....sai na ganku" Ta fadi tana yanke kiran. Wayar yabi da kallo,har tayi maganar da tafi damunta,ta fadi kuma dalilin da ya sanya ta kirashi suka kammala wayar baiji addu'a guda daya daga bakinta ba.
Yaja numfashi me nauyi yakaishi xuwa cikinsa,ya tabbatar babu yadda za'ayi anni ta kirashi......walau yana qasar nan ko yana wata qasa su kammala maganar su bata bishi da kyawawan addu'o'in da ko yaushe yake jinsu har cikin tsakiyar zuciyarsa ba. Addu'a da tsaftaccen niyya da kuma manufa na alkhairi.
Hasken wayar ya sanyashi maida dubansa gareta,sai ya daga itama ya sakata a handsfree yana sake janyo mug dinsa yaci gaba da kurba
"Saura mintuna goma lokaci ya cika hamma"
"Gani nan......Moses ya qaraso?" Ya tambayeshi yana bude daya plate din dake gabansa
"Muna tare dashi"
"Okay.....get ready" Ya fada yana katse kiran tun kafin saddiq din ya katse nasa.
Kamar kowacce safiya,ya shiga wajen annin cikin nutsuwa mutuntawa da kuma qaunar daya tabbatar daga ubangiji take....irin qaunar da yayi imanin Allah ne ke sanyata cikin zukatan bayinsa aduk sanda yakeso. Ta gyara lullubin laffayarta tana masa addu'a,addu'ar data sanya rauni me yawa a zuciyarsa,raunin da yaso nunawa har sanda yake cikin motar da dagashi sai saddiq sai driver,sauran guards suna gabansa wasu a bayansa cikin wata motar ta daban.
Wacce irin rayuwa ce hakan wai?,wanda zai hafoka daban?,wanda zai gina maka rayuwa da kyakkyawan fata da kuma addu'o'i daban?. Wannan shine abinda ya dinga yi masa yawo akai,har daga qarshe ya samu ya yakice komai a ransa kafin su isa kamfanin.
Kamar kowanne lokaci isowarsa cikin kamfanin kadai yakan sanya kowa shiga hankalinsa. Hakan kuma yana da nasaba da rashin daukan wasansa da yadda yake daukan komai da muhimmanci. Wannan ya sanya duk wanda ke aiki dashi yake shiga taitayinsa yake ajiye komai a gefe sai idan ka fita wajen kamfanin.
Babban office ne dake dauke da kusan sashe biyu a cikinsa,wanda kusan kowanne sashe zaman kansa yakeyi. An qawatashi cikin tsari da nau'in kalolin da yafiso ya kuma fi ta'ammali dasu. Komai cikin tsari yake da tsananin tsafta tamkar wankewa da gyarawa kawai akeyi ba tare da ana shiga ba.
Yadda mamallakin office din ya zama na daban,haka office din nasa ya zama na musamman.
Hularsa ya zare ya ajiye su saman mulmulallen table din yana hadawa da wayoyinsa da system dinsa daya karba daga hannun ahmad,wanda shike jigilarsa tun daga sanda zai shigo kamfanin har ya fita.
Idanunsa na ga wasu files daya tarar saman table din,amma kunnuwansa na sauraren bayanin taheer.
Baice komai ba sai da ya gama sannan ya kalleshi
"Ina mika'il?" Yayi tambayar hankali kwance yana daga wasu takardu dake gefe
"Bai qaraso ba tukunna" Saddiq dake qoqarin kashe tab din hannunsa ya bawa fu'ad amsa.
"Alright.....trading manager da laboratory technician.....su da sauran staffs dake qasansu dukka ka shirya mana meeting.....one hour thirty minutes kawai,akwai meeting da zanyi da sababbin ma'aikatan da muka dauka kafin nayi wannan tafiyar"
"Done" Ya fadi cikin rusunawa da girmamawa.
Daya bayan daya yake duba duka aikin daya bari da wanda suke zaman jiransa. Wadanda yake buqatar qarin haske ya turawa saddiq komai ta email nashi,don shine yake da alhakin kula da komai daya shafeshi,kaman yadda komai din sai ya biyo ta hannun saddiq din kafin ya iso gareshi.
Duk da cewa yasan shi din mutum ne da baya saba lokaci ko karya magana,amma hakanan ya samu kansa da duba agogonsa.
Yau din gaba daya hankalinsa baya a jikinsa,yana jin cewa yau zata kasance babbar rana a gareshi wadda zata kafa tarihi cikin rayuwarsa da kyakkyawar yarinyar da ya tabbatar koda cikin bariki samun irinta abune me wahala.
Duk da 'yar hira da tattaunawa dake gudana tsakanin ma'aikatan hankalinsa shi ba'a wajen yake ba yayi nisa wajen wassafa yadda zai rayu da ita,yayi nisa wajen tsara yadda zai more rayuwarta da kyau.....ya kuma yi nisa wajen tsara yadda zai jiqata da kudi.....yadda zai sake maidata tauraruwa.....da kuma yadda zai maisheta abar kallo.
Muddin ya sameta yayi imanin zaiyi zarra cikin duniyar bariki,zai kuma tayar da hankulan abokan adawa da yawa,hakanan zai zama wani na daban daya mallaki babe din da baijin akwai sauran irinta.
Miqewar da ma'aikatan sukayi daga saman kujerun zamansu dake zagaye da kyakkyawan table ya sanyashi dawowa hayyacinsa. Miqewa ce taban girma ga CEO din nasu,wanda yake takowa cikin hall din cike da takunsa dake sake nuna zallar kamala da nutsuwar da Allah S W T ya hore masa.
Lafiyayyen kwarjinin nasa dake sake saka kowa shiga taitayinsa yana kwance saman fuskarsa. Basu zauna ba har sai daya basu izinin zama sannan shma ya zauna din.
Yadda suka saba gabatar da meeting irin wannan haka suka fara yanzun ma. Mataki bayan mataki,matsayi bayan matsayi. Yana biye da bayanan kowa ta sigar da idan ka kalleshi a haka zata tsammaci kaman baya fahimtar bayanan,don babu system ko abun rubutu ko daya a hannunsa,illama yatsun hannunsa daya sarqe cikin juna yana kallon duk wanda bayani yazo kansa.
A gaban mika'il din akwai mutane da sai sun kammala miqa nasu bayanan kafin azo kanshi. Duk sai yaji ya matsu,tamkar ya nemi a daga masa qafa tukunna ya fara gabatar da nasa bayanan. To amma ko giyar wake yasha yasan hakan bame yuwuwa bane,don waje ne da ba'a daukan irin wannan wargin.
"Ina neman afuwa,lokacin da na tsara zamu zauna din ina ganin kamar sai mun wuceshi.....zamu sake qara awa daya zuwa biyu......akwai me wani uzuri kaman na abinci?,shiga bayan gida da sauransu?". Yayi maganar cikin harshen turanci da wani irin daddadan accent,karyewa da lanqwashewar halshensa kawai ya isa ya gaya maka gwani ne wajen iya yaren.
Cikin rashin jin dadi mika'il din ke rarraba dubansa akan fuskokin staff's din,yana cike da fata da burin samun wanda zaice yana da uzuri shima ya zama na biyu da zai furta haka. Saidai kaman yadda zuciyarsa ke raya masa ba wanda ya nemi wannan excuse din,hasalima daya daga cikinsu cewa yayi
"Koda duka awanninmu na yau zaka qarar sir mun sadaukar maka dasu" Sauran suka shiga gyada kai. Kowannensu da wani irin qawa zuci da qauna ta gaske yake zaune dashi,duk da ba'a rasa qananu matsaloli da kowacce tafiya bata rabo dashi,amma ya gina wani irin qaunarshi a zukatansu da sadaukarwa me tarin gaske,wanda shi kansa baisan ya gina din ba. Saidai kuma abune sananne,duk wajen da ake samun kulawa tausayi da kyautatawa dole qauna ta biyo baya. Fada ce ta ma'aiki,an gina zukata abisa son wanda ke kyautata musu da qin wanda ke munana musu.
"Alright.....na gode" Ya fada da salon daya sake sanyawa kowa nutsuwa da qaunarsa a zuciya.