Showing 135001 words to 138000 words out of 153569 words
Chapter 46 - A Duniyata Book 1 Complete Hausa Novel
jiye a gefe,ya qarasa ya sanya takalmansa daidai sanda executive Porter dinsa ya shigo
Shi ya dauki sauran kayan da yasan zai iya fita dasu din,yabi bayansa,yayin da musaddiq ya tsaya don ya qarasa killace komai ya kashe sauran electronics dake kunne,don yasan ba lallai su sake dawowa ta kamfanin sai kuma gobe.
Yana fita suka hadu dame sunan malam din,sai yabi bayansa suna takawa a nutse yana gaya masa sauran schedule dinsa na yau duka
"Amma sir.....sai nakega kaman abubuwan sunyi yawa.....ko akwai abinda zaa rage ko a sauyashi a kaishi gobe?".
Kansa ya girgiza sanda saddiq ya matso yana scanning keycard jikin designated elevator din da shi daya yake amfani dashi cikin company din.
"Kada ayi cancel komai.....zamu kammala in sha Allah komin dare.....make sure kowanne ka sanar masa da exact time da zamu hadun"
"Yes sir" Me sunan malam ya fada yana bawa guards dinsa waje,daya daga cikinsu yayi gaba don tabbatar da lafiyar elevator din duk da anyi keeping nata waje daya kuma don saboda shi,muhammad jadda yabi bayansa sauran guards din suka shiga hadi da saddiq.
Cikin ransa ya shirya sake maida kanshi busy fiye da kima,bama wai shi kadai ba,hadda musaddiq don kaucema duk wani tsari da plan na maamah har sai yaga iya inda gudun ruwanta zai kaisu. Ya shirya sadaukar da dukka lokacinsa ya tafi dashi a aiki fiye da yadda yakeyi a baya,duk da ko a bayan shi din ba wani cikakken lokaci gareshi ba. Sau tari anni tana yawan yi masa fadan yana tsaurarawa rayuwarsa da yawa,ya kamata ya fiddawa kansa lokaci da zai dinga hutawa. Bashi da wani time qwaqwara daya ware don yaje hutu,idan ka ganshi yana hutawa to tabbas umra yaje wadda duka duka baya haura sati daya yake dawowa.
Suna yawan ware qarshen kowacce shekara suje dukansu suyi umra,daga nan abban ya zaba musu qasashe guda biyu dake da wani tarihi cikin addini ko rayuwa suje su qarashe qarshen shekararsu a can. Sau tari shi din baya tafiya tare dasu,saidai ya biyosu daga baya,wanda ana kammala umra dinsa yake dawowa kan kamfaninsa,bai fiya binsu tafiye tafiyensu da suka tsara ba.
Direct suka nufi private parking garage dinsa wanda aka tanada kawai saboda ajiye motocin da yake kai kawo da kuma hidima dasu. Wajene da yasha banban da sauran duka parking lot na company din,wanda aka qawatashi aka kuma cikashi da tsaro na cctv da kai kawon security.
Dukka sauran guard nashi suna tsaye suna jiran qarasowarsa. Isowar nashi yasa da sauri CSO dinsa ya qaraso ya bude motor din da zai tafi a cikin ta ya matsa yana bashi guri,ya shiga saddiq yabi bayansa.
Sanda motocin ke motsawa suna barin wajen zuwa ainihin hanyar da zata sadasu da gate na farko na kamfanin,daidai lokacin ya gyara zamanshi yana bude wani guri a side na kujerar da yake kai don ciro earpiece da zaiyi using nasa wajen amsa kiran daya shigo wayarsa.
Kaman fitar kibiya idanunshi suka fada parking lot na sauran staff da suke da matsayi na biyu cikin kamfanin. Kan mikail idanunshi suka fada,ya bude mata murfin motar yana jifanta da wani mayen murmushi,yayin da nata fuskar yake kadaran kadaham tana sanya jikinta cikin motar
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 72
Zare Idanunshi yayi daga kansu yana jin wani quna a ransa.
"Tun yaushe mikail yake irin wannan abun?" Yayi maganar a hankali ba tare da yayi tunanin saddiq zai jishi ba. Dan dubansa sadiq din yayi kafin ya rusunar da idanunsa
"Hamma yana dan taba harkokinsa dama,amma kuma banajin a cikin company,yanayin komai ne a wajen company"
"Idan har a wajen company yakeyi in zanyi wani abun bazai wuce tunasar dashi kawai da gyara masa kuskurensa da take wuyan kowanne musulmi,ya kuma wajaba a kansa ya zama dole a addini da wajen ubangiji yayi akan dan uwansa musulmi a sanda ya fahimci kuskure ko gyara cikin al'amarinsa.....amma kuma muddin yana shigo min da wasu abubuwa da basu dace ba muhallin neman halal dina.....lallai lallai zan dauki mummunan mataki ne a kansa". Yayi maganar da sound din da zai nuna maka da gasken gaske yake.
Tunda suka shiga motar take jifanta da wani irin narkakken kallo. Yanaji jikinsa yana macewa kasala yana saukar masa kamar ko yaushe idan yasha barasa,shi yasa yaso ta bashi hadin kai ko hannunshi yadan fara kaiwa jikinta guraren da suka tsone masa idanu amma ta qiya. Yana kuma tsoron suna isa Bristol zaiyi wahala baiyi baccin nan nasa ba na wajibi,wanda muddin baiyishi ba bazai iya hasala komai ba yadda ya kamata.
Ta gaya masa tana da qa'ida da kuma dokokin da dole ya kiyayesu muddin yanason rakiyarsu tayi tsaho. To sai yaga hanzarin ma na meye?,ya qyaleta mana?,don dai jiran awa daya kacal me zai cishi?,shi da ta tabbatar masa a yau din wuni guda tana tare dashi?.
"Babe......muddin a yau kika bani hadin kai yadda na jima ina mafarki.....zan baki fara sheet da ba komai a ciki ki rubuta komai da yazo kanki kike burin mallaka......idan nace komai ina nufin komai fa,komai tsadarsa ko yawansa.....ina tare da lalitar jadda diamondchore" Ya fadi yana sakin qaramin shu'umin murmushi,don ya hango irin barnar da ganimar da kwasa cikin account din.
Kadan tadan dubeshi sai ta dauke kai,tana maimaita sunan kamfanin da tun shigarta ta tabbatar ba qaramin kamfani bane gama gari da kowa ya saba gani ba......to amma sai taji ba abinda ya burgeta tattare dashi. Ta tabbatar tunda har mamallakin kamfanin zai danqawa mutum irin mika'il ragamae tasarrufi da dukiyar kamfanin duk kanwar ja ce,ba yadda za'ayi mikail din ya dinga irin wannan fantamawar yana wasa da kudadensa ba tare da masaniya ko daurin gindinsa ba.
Ta yaya ma cikakken namiji kamar wannan daya mallaki dukiya ke dimbij yawa,kadarori kala daban daban ciki harda private jet amma ya gagara aure?,bayan a shika shikan aure bai rasa komai ba?.
Qaramin tsaki taja qasan ranta hoton fuskarsa yana dawo mata tana jin kimarsa da haushinsa suna kwaranyewa daga idanunta,saboda haka batajin daga shi har mika'il sun cancanci tausayawa.
Saidai ta sani,kudaden da suke da zummar kwasa din ba qananun kudade bane.....kudade ne da ta tabbatar ita kanta sunfi qarfinta dama duk wanda yake tare dasu,saidai kuma yawan masu buqatan kudi da muke dasu suke kuma kewaye da idanunta sun isa su lashe komai cikin zama mawadata da zasuci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin salama,ta soma hango wasu daga cikinsu suna rayuwa irin rayuwar da takeson ganinsu sunayi,wannan tunanin ya sanyaya sakin sassanyar ajiyar zuciya.
"Bakice komai ba" Mikail ya fadi yana dan waiwayowa ya dubeta kadan,don tsananin rudewa da firgicewa cikin farinciki da dimuwa da yake ganin wasu matan a ciki idan ya musu irin wannan albishir din sam sam baiga koda kamannin haka a wajenta ba
"Idan kuma hakan baiyi miki ba ki zabi kome kikeso a rayuwa......indai zaki bani rayuwarki zan baki komai da kike da buri" Ya sake fada cikin qoqarinsa nason gamsar da ita kalamansa.
"Baka da damuwa" Ta amsa masa cikin salon miskilancin nan nata,don maganganunsa sun fara isarta,bata fiya son doguwar magana ba.
Juya kalmar ta bashi rayuwarta takeyi cikin ranta. Har yanzu ta kasa sabawa da kalaman maza 'yan bariki,har yanzu mamakin wannan halittar ta d'a namiji ta kasa sakinta,su koda yaushe kansu sukeso?,kansu suka sani?,ko yaushe yaya zasuyi su samu jin dadinsu daga wajen 'ya mace?,ba tare da sun damu da yadda tata rayuwar zata kasance ba?. Basu da wannan asarar,suna iya sanya qafa suyi fatali dake duk sanda wannan halin nasu ya motsa na BUTULCI,aurenki sukeyi ko zaman bariki kuke?.
Tayi imanin halin D'A NAMIJI A JININSA YAKE,dan kunama ne shi da gaske,tana kyautata zaton babu wani d'a namiji da bashi da wannan halayyar,saidai na wani ne ya d'ara na wani kamar yadda take gani take kuma kan gani din. Wannan hasashe da karatun da tayi musu shike nesanta zuciyarta kullum daduniyarsu,takejin ba abinda yafi dadi a wajen mace irin ta rayu ita kadai ba tare data raba kowanne namiji cikin rayuwarta ba bare ta bashi wani matsayi da zai zameta lalura qunci ko quna nan gaba cikin rayuwa.......gwara ta rayu ita daya shine zata zama me cikakken 'yancin da bata dame bata mata rai.
Nisa da zurfin da tayi a tunani ya sanya har suka iso Bristol bata sani ba. Yayi parking na motar ya fito yana takawa da qyar saboda yadda jikinsa yake qara nauyaya,ya zagaya side din da take zaune ya bude mata qofar sai ya miqa mata hannu alamun ta taho.
Hannun nasa ta kalla sannan ta kalli fuskarsa. Ta gama ganin zallar mayen giyar da yasha yana narkewa a jikinsa
"No need" Ta fada tana girgiza kai sannan ta dauke dubanta daga kanshi.
Baya yaja kadan yana furzar da iska daga bakinsa. Gulmarta yakeyi a ranshi,jin kanta yayi yawa,tana da wata izza da wani irin jan aji da kamewar da bai taba gani a wajen matan titi ba sai a kanta,amma ba komai,yaci alwashin a yau dinnan sai ya banbance mata aya da tsakuwa,dukka wannan jan ajin garawar da wahalar dashi data dinga yi sai ya fansheshi a yau.
Tana gaba yana bayanta kamar ma ba tare suke ba har suka wuce ciki. Bata sake gasgata da gaske yayi booking ba......da gaske lamarin namiji abune me bada mamaki da daure kai ba sai da suka shiga babban dakin daya kama musu,wanda duk kwana daya a yadda ta gani cikin jadawalinsu naira dubu tari takwas da hamsinne. Komai an jere na kayan abinci,isowarsu kawai ake jira. Ya fada saman lafiyayyen gadon da yafi kama da gadon da ake shirin cin amarci a kai yana dubanta qasa qasa.
"Komai da kike buqata akwai an tanadeshi.....amma inajin sai kinyimin alfarma na matse baccin nan ko na awa daya ne cakal.....kiji dadinki yadda kikeso.....idanma akwai wani abu da kike da buqata ga waya can ki musu magana zasu kawo miki" Yayi maganar muryarsa tana maye ita kanta,da alama baccin yayi mugun cin qarfinsa.
Sanda ya miqe yana shirin sabule wandonsa da riga sai ta kau da kanta tana jin yadda zuciyarta tayi wani irin bugawa. Irin wadannan abubuwan take gudu shi yasa bata taba yarda ta biyo kowa wani kebantaccen waje ba,sai gashi haka kawai jib ya takura mata sai tabi mutum biyu don samun cikar aikinsu.
Yif taji ya koma ya fada saman gadon,koda ta maida dubanta sai taga bai iya cire komai a jikin nasa ba,kawai kokawar banza ya gama yi ya koma ya fadi cikin bacci.
Minti goma qwarara ta bashi sannan ta taka ta isa gabansa. Yayi sadidan a baccinsa,taja da baya a hankali tana jin faduwar gaba tace
"JIB yayi bacci"
"Good" Ya fada yana jawo dukka kayan aikinsa.
"Stay tuned.....minti talatin ya wadatar......ki kula da duk abinda zanyi requesting"
"Okay" Ta fada tana jin sanyin jiki da faduwar gaban da batasan dalilinsu ba.
Ganin mintuna arba'in suna niyyar shudewa ba wani labarin nasara,ga mikail yana motsawa lokaci bayan lokaci ya sanyata magantuwa
"Jib.....ya ake ciki?"
"Wannan aikin yayi tsauri da yawa adda.....akwai tsauraran matakai da shinguna masu zafi a kai,yanxun haka abinda na soma fahimta kamar wani abu ya fara alerting nasu anason musu kutse cikin asusun nasu" Ya fadi shi kansa kamar yanajin qarfin gwiwarsa yana son sarewa. Duk inda ya zaci zai samu nasarar balla account din nasu da dukkan hanyoyi da dabaru amma sai yaga abun kamar ya wuce nan.
Daidai lokacin da yake tsaka da meeting da investors din da suka jima suna da shaawar sanya hannun jarinsu a kamfaninsa na jadda diamondchore resources da yake a lagos da kano.....da kuma sabon kamfanin da yakeson yabude din a yanzu na jewelry da sauran dangin kayan ado da qawa na mata.
Daga saman system dinsa wani abu ya fara harbawa. Alamace da take nuna masa DANGER. Sosai ya zubawa alamar idanu,sannan da hanzari ya jawo system din gabansa ya soma bibiyar abun
"What?,scammers?" Ya furta qasan ransa,sai ya kalli baqin nasa yana miqewa tsaye gami da daukan wayarsa
"Excuse me" Yana daga musu hannu tare da takawa a hankali yana matsawa nesa dasu. Sadiq dake can nesa dashi ya kira
"Call the security team na kamfani......ka gaya musu akwai alamun shirin yin kutse su kula".
"Done" Ya fada kaman yadda ya saba gaya masa. Juyawa yayi yana komawa wajen baqinsa,ya koma mazauninsa ya zauna yana jawo system din gabansa.
Hankalinsa ya raba biyu,yana saurarensu yana kuma duba yadda suke samun progress na sake kutsa musu. Alama ta qarshe daya gani ta sanyashi lumshe idanunsa hadi da ture system din gefe kadan ya maida dukka hankalinsa dari bisa dari akan baqinsa.
"Done adda!......done,millions of naira sunyo dropping" JIB ya fadi da wani irin sautin farinciki,yana jin sukuni yana ratsashi na samun cikar mafarkin mutanen da suke rayuwa ruhinsu a jikkunansu.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
Page 73
"Zan iya tafiya?" Shine abu na farko data tambayeshi ba tare da tabi takan adadin kudin da suka samu cira ba
"Yes adda.... Zaki samu me napep a corner farko na street din yana jiranki gudun samun delay". Katse kiran kawai tayi,ta miqe tana daukar jakarta ta jefa wayar hannunta da sauri tana dan duban yadda mikail yaketa motsawa,alamar koda kowanne lokaci yana iya farkawa,saita wuce kai tsaye ta bude qofar ta fice.
Sai data tsaya da lobby din ta daidaita nutsuwarta da kyau gudun zama suspect a idanun security na hotel din,sannan ta fara takawa a nutse tana qarasa ficewa.
Hankalinsa a tashe yake dawowa wajen fuad din,yama gaza kiransa a waya kaman yadda shi ya kirashi a daxun.
Ta bayansa ya qaraso,yadan rusuna don sanar dashi halin da ake ciki
"Na sani.....jeka jirani mu qarasa mu wuce gida" Ya dakatar dashi ba tare da ya barshi yace komai ba. Da dan mamaki sadiq yake dubansa ganinsa zaune hankali kwance. Duk da yasan yafi gaban hakan amma wannan din ba qaramin abu bane da ya kamata ya ganshi haka a zaune calmly ba yana tattaunawa da investors,to amma bashi da sauran zabi illa juyawa ya tafi din kamar yadda ya buqata.
Tana tafe a hanya tunane tunane cinkus cikin kanta da qwaqwalwarta. Haka kawai taji ta kasa isa gida,sai kawai ta bawa me napep din umarnin suna da wajen da take so ya kaita.
Guri ne very quite,ba cikar jamaa,kuma kowa sabgan gabanshi yakeyi. Hakanan gurin yana da yalwa da fadin da zaka zauna a guri wani ma da yake nemanka bai ganka ba. Order din lemo da ruwa kawai tayi don batajin zata iya cin komai. Batasan me yasa ba.....ba yaune karon farko da haka ta fara faruwa ba amma wannan din yanason tsaye mata gami da sanyayar mata da jiki.
"Eh ba shine na farko ba......amma kuma yafi kowanne nauyi da girma......baki taba samun kudade masu tsananin kauri da yawan wadannan ba,sannan kamar an shiga lalitar wadanda baki taba koda magana dasu ba.....kaman akwai nasu haqqin a ciki". Wani sashe na zuciyarta ya fara tunasar da ita. Wanda qarar ring na wayarta ya katse mata tunanin.
Sunan titi data gani shi ya dauke hankalinta daga dukkan tunanin komai,ba jinkiri ta daga wayar suka fara magana
"Da sauqi.....amma sumanta biyu yau"
"Komai ya qare in sha Allah" Ta bawa titi amsa a taqaice saita katse kiran. Dukka karsashinta taso dawo dashi,ta fara lalubar wata number da jib ya bata.
Ayyuka biyu tayi a wajen da suka qara kashe mata kusan awa daya da rabi. Ta tura dukkan abinda mutumin ya buqata don yiwa titi