Showing 108001 words to 111000 words out of 153569 words
Chapter 37 - A Duniyata Book 1 Complete Hausa Novel
zurfi a kansu,kuma tafi hangen samun nasara da wuri akan mika'il da mashkur,don shi ya'aqoub a yanzu tunaninsa yafi karkata kan yadda zai shawo hankalinta ta aminta ta aureshi,abinda kuma bataga ranar yiwuwarsa ba. Wai mema zata tsinta ne a auren?,bayan tana ganin yadda su mazan suke?,tana ganin kuma yadda matan ke komawa?,ko hanyan aure yanzu mutum yayi mata ai bai qaunarta ballantana ace mata tayi. Duka tsari da halayyar mazan baiyi mata ba ballantana ta cusa kanta a sabgarsu da nufin zama tsakaninta da waninsu zama na din din din?.
Miqewa tayi a dole tana duban haneefa,sai haneefa din ta miqo mata takarda tana cewa
"Wani ne wai a waje yace a baki...." Da sauri ta fiddo mata idanunta waje sanda muryar sabreen wadda ke amsa waya take dosowa cikin dakin. Yadda suka daga kai suka kalleta duka su biyun ya sanyata janye wayar daga kunnenta tana kallonsu
"Lafiya?" Tayi tambayar tana sauya yanayin fuskarta. Wani faduwa gabanta yayi,cikin tsoro tsoro ta girgiza kanta tana qaqalo murmushi tace
"Ba komai.....ina kwance haneefa ta tsoratani,na dauka wani abune da naji tanata tashina". Idanu ta sake zuba mata na daqiqu sannan ta amsata tana zama gefan nata gadon
" Ko bata tsorataki ba dama ai yaci ace kin tashi,an kusa kiran sallah.....uniform dinku nadra ta wanke tunda kin koyi laziness......kije kiyi alwala ki dawo ki kwashe abincin tukunya a flask a wanke sauran abinda ya rage".
"Tom" Ta fadi tana matse takardar a tsakiyar hannunta tare da tunanin yadda zata miqe da takardar ba tare data lura da ita ba,to amma kuma ci gaba da zama dinma tunanin mafita tamkar tana bata damar dora ayar tambaya ne a kanta.
Aljihun skirt dinta ta tuna dashi,cikin dabara ta cusa a ciki,sannan ta zame ta sauko tana gyara inda ta kwanta din,ta daura dankwali saman doguwar sumarta ta juya tana fita a dakin. Dauke idonta tayi daga kan tab dinta ta bita da kallo. Haka kawai ta gagara samun nutsuwa kwanaki biyun nan,duk motsinsu a kan idanunta yake,kuma da gaske tana ganin dan sirkawar wani abu kadan tattare da huda din.
Bandaki kawai ta wuce kai tsaye tana fata da zumudin budewa taga meye a takardar?.
Sai data samu guri cikin toilet din ta zauna sannan ta ciro takardar ta kuma warwareta.
Kaman yadda ta zata shi dinne,sunansa kawai data gani sai bugun zuciyarta ya qaru da kaso hamsin cikin dari.
Yau kwanaki uku kenan,ya rakota daga hanyar makaranta har dab da gidansu kamar yadda ya saba a kowacce rana......tun tana gocewa har ya fara zame mata sabo ba tare da sanin nadra ko haneefa ba wadda yanxun aka banbanta musu lokutan tashi qarfi da yaji ba tare da kowa yasan dalili ba. Ya zame mata kamar abokin rakiya a yanzun.....tun tana dari dari da tsoro har hakan ya fara gushewa daga zuciyarta.
A ranar alhamis tayi matuqar mamaki yadda ya tsaya suna tsaka da tafiya,ya kuma kafeta da idanu
"Lafiya kake?" Ta tambayeshi da mamaki
"Ke kyakkyawa ce" Ya fadi yana jin wutar sha'awarta na ruruwa a ransa tamkar yadda ya dinga jin ta 'yar uwarta. Yana jin kamar ya dauketa a yanzun ya wuce da ita ya aikata abinda ya tanadi aikatawa,saidai kuma bazaiyi haka ba,yanason komai ya kasance a daidai sanda zatafi jin ciwo da radadin da zai iya zama ajalinta,ya kuma tarwatsa farincikin da take musu tattali. Yanason idan ya tashi ya tarwatsata tarwatsewar da ba zata taba dawowa ta gyaru ba ballantans ta koma yadda take.
Idanu ta waro tana dubansa,yadda yake yawan kambata da kurantata ya sanya kusan kullum sai ta kalli madubi......kusan kullum sai ta kalli kanta da kanta taga wannan kyan da yake magana a kai......wannan budurwar da yake yawan kiranta dashi. Tun bata ganin abinda yake fada din har ta fara ganin,amma tana ganin kaman bata ca canci kowacce rayuwa ba a yanzun......karatu shine yafi da cewa dasu kamar yadda yaa sabreen ke gaya musu
"Ina sonki huda.......ina tsananin qaunarki tun daga ranar dana fara ganinki.......zuciyata tana miki wani mahaukacin so da bansan iya adadinsa ba......wallahi inaji a zuciyata tamkar zanyi hauka saboda ke huda......ki soni don Allah......ko baki sona ni zan koya miki yadda zaki soni din". Kalaman da suka tsoratata suka kuma razanata kenan. Kalaman kuma da Naseer din ya shiryasu ne kawai don ya soma wasa da tunaninta da qwaqwalwarta,plan na biyu kenan daga cikin tsarikansa.
Baya taja tana girgiza kai,tana jin tsoro yana shigarta. Wacce irin soyayya a shekarunta?,duka duka nawa take?,koda yaa sabreen bataga ta kawo kowa tace shi zata aura ba,bataga wani yazo qofar gidan da sunan zance wajenta ba.....koda abinda ake maganarshi a kanta da nasu idanun basu taba ganinta cikin motar wani ko tsaye da wani ba har zuwa yanzun da take tsaye a gabansa. Ko rakota da yakeyi kullum kwanan duniya a tsorace take......wani lokaci zuciyarta tana raya mata idan sukayi kacibus da yaa sabreen fa?,sai kuma zaqin bakinsa da daddadar hirarsa ta yaudare tunaninta da kunnuwanta.
Tayi mugun tsoratar data dinga ja da baya da baya tana girgiza kai. Yana tsaye ya kafeta da idanu,abun yana masa sugar sosai. Irin hakan yafi buqata don ta haka ne sabreen din zata fuskanci girman nasa aikin. Ya samu sabon ruhi sabon gangar jiki da baisan komai ba game da rayuwa......zai hurewa zuciyar kunne,sannan ya mori gangar jikin yadda yaso ya kuma watsar da ita tamkar wani yasashen abu maras amfani. Yana tsaye harta gudu a layin ta bacewa ganinsa,sai ya bushe da dariya.
Hakan da tayi ya tabbatar masa qwaila ce,ya kuma bashi tabbacin baa taba gaya mata kalmar so ba sai a kansa
"Allah sarki......gashi baki fara da jin kalmar ba a sa'a......anyway......ko mene ya faru dake 'yar uwarki ce taja miki" Ya fada yana juyawa don barin layin ya qarasa inda yaransa ke cikin mota suna jiransa.
Hannunta har rawa yake sanda take warware takardar. Tsakanin alhamis jumaa asabar da kuma yau lahadi ba wasu mintuna biyar kyawawa da suka wuce ba tare da tunanin abinda ya faru tsakaninsu ya dawo kanta ba. Duk juyin da zatayi sai kalamansa sun dawo mata,kallonsa murmushinsa da kambamawarsa. Fuskarta kam ta kalleta yafi sau adadi tana sake duba kyawun surarta da yake yawan jaddadawa. A yadda take gani ba mace me kyan yaa sabreen dinsu......ashe itama to tana da kyau dinne da gaske?,ko kuma yana fada ne kawai?.
*_Hello me kyau,fadin azabtuwar da idanuna da zuciyata sukayi saboda rashin tozali dake ba abu bane me sauqi......ina fata zaki daure a gobe ki barni naga wannan kyawawan idanun da zuciyata ta mutu a kansu.....idan ba haka ba.....zan iya rasa numfashina_*
Da sauri ta duqunqune takardar ta kuma jefa a toilet ta bita da flushing zuciyarta na bugawa sosai. Tsoro zumudi fargaba da mamaki dukka suka hade mata har ta rasa wanne tunani ma zatayi.
Bugun qofar bandakin da akayi ana jiranta ya sake rudata,sai kawai taja qofar ta bude ta fito ba tare da tayi komai ba,taja burki bakin famfo ta daura alwala tayo dakin nasu.
Gaba daya tunaninta ya karkata ga saqon,har ta mance da batun kwashe abinci tayi zaune saman kujera tana bitar saqon da ya riga ya rubuta kansa da kansa a kwanyarta. Fitowar sabreen din ya sanyata tunawa,ta miqe da hanzari ta nufi kitchen.
Yanzunma da kallo sabreen ta bita har ta shige kitchen din. To wai me yake samun huda take wasu wasi haka?. Bata sani ba,sai ta girgiza kai ta taka hannun kujerar tana dauko babbar dardumar da sukan shimfida suyi magariba da ishai akai suyi bitar karatun makaranta ta taimaka musu da wanda zata iya.
Da ruwan zafi sosai tayi wanka bayan wucewar hajja saboda ciwo da jikinta yake mata sakamakon zaman mota data jima batayishi kaman haka ba. Ta shirya kanta cikin fafi indian abaya me laushi,ta yane kanta da mayafin abayar daya kasance medium cotton kaman yadda jikin dogon rigar yake.
Cikin falon tayi zaune bayan ta kirayi me aikinta ta canza mata channel. Qafafunta a miqe saman side glass table din,hannunta dauke da glass cup dake cike da lemon raspberry tatacce me asalin tsadar. Babu wani abu da zata ci ko tayi amfani dashi cikin gidan da yake da qaramin kudi. Komai nata me tsada take zaba,hatta da ruwan da zata sha kuwa ballantana akai ga sutura ko wayar hannunta.
Ko a yanzun haka ta gaya masa tana buqatar ya sauya mata iPhones din hannunta guda biyu. Iphone 15 da wata tsaddadiyar waya sabuwar qira da kamfanin Samsung's. Duka duka wayoyin ba wadda tayi wata uku,to amma garin gane ganenta ta hangi wasu sabbin fitar,su kuma takeso ta riqe.
A komai tafison ta zama cikin sahun mutane na farko da ake ganin komai sabo a wajensu. Inda tana da iko komai zai zamana ana ganinsa ne ta wajenta,sanda zai soma zagayawa hannun masu kudi irinta ita ta dade da cin zamaninta. Ta sani,a dukiyar da d'anta yake dashi yana da qarfin kudi da mulkin da zai iya sanyawa a qera mata duk abinda take buqatar ya kasance nata ita kadai daga kowanne kamfani a fadin duniya,to amma ta fahimci rayuwarsa baya daidaitata dai dai data sauran masu kudin irinsa. Ba kuma haka takeso ba.....ba haka take muradi ba......tanaso ta gansu suna rayuwa daidai da matakin arziqinsa. Ta fahimci yana cikin sawun mutanen da ba kasafai suke bayyana arziqinsu ba,sai abinda ya riga ya bayyana ba yadda zasuyi dashi.
Aka idar da magariba akayi ishai shuru. Tun tana tattalin maganganun da zatayi dashi har wasu suka fara bace mata. Ta daga kai ta kalli agogon dake shirye saman tv din falon takwas da rabi na dare,to shin sai yaushe zai shigo?,sai yaushe wannan abun zaizo qarshe?.
Sannu a sannu sanda taga an doshi tara na dare babu alamunsa,wayoyinsa dukka a kashe shida musaddiq din da zata sanya ya kira mata shi a duk inda yake.
A ranta ta dinga jin cewa hadin baki ne......a ranta kuma ta dinga ji aminatu ce ta hanasu.....a yanxun haka qila suna can gabanta......ta zaunar dasu sai abinda tace musu.
Wannan tunanin ya dugunxuma mata zuciya,har taji bata da wani sauran zama cikin gidan. Dakinta ta wuce kawai bayan ta ajiye kofin lemon,ta shiga zaro takalmi cikin jerin takalman alfarma dake adane a shoe rack dinta. Cikin zuciyarta takeji yau din Alhaji hamzan zata tunkara......tanaso taji shine yayi mata cikin yaran ko ubansu?,tana so taji da ita dasu wai waye ahaqqu dasu?.
"Nazo muje ne?" Zuwaira ta tambayeta sanda taga tana dosar qofar fita daga falon
"Zauna basai kinje ba" Ta amsa mata a gaggauce tana fita a gidan.
Mugun bugun da takewa tafekeken gate din gidan ya fusata securities din gidan,saidai kuma lokacin da suka duba wadda ke bugun ta na'uarar tsaro dole kowannensu fusatarsa tayi nata guri.
Basusan ainihih matsayinta ko ita wacece ba......amma yadda suka fahimci girmamawar da take samu daga mazauna gidan ya basu alamar cewa tana da nata matsayin na daban.
Ko kallo security din daya bude mata qofar bai isheta ba ballantana tabi takan welcoming nata da yakeyi tare da bude mata qofa ta biyu da zata sadaka da farfajiyar gidan. Daga nan wasu security din su sake marabtarka kashi na uku kenan kafin kakai ga ainihin cikin gidan ka zarge qofar da zata sadaka da babban falon anni na farko.
Bata taba tunanin zata sake takowa cikin gidan ba karo na biyu.......don duk lokacin data tako din alatun gidan yakan zame ma idanu da zuciyarta barazana. Tana jin kamar kowanne abu idan ta kalla a gidan yana mata izgili ne tare da gaya mata da dukiyar danki aka samar dani......baki kuma da wata izza ko power ta mallakata.
Kowanne taku daya idan tayi cikin gidan ranta quna yake......sak fasalin yadda takeso gidan da zata rayu ya kasance sai gashi kacokam a yau din irin wannan dream house din nata mallakin aminatu ne.. Wasu mutane da basu da masaniyar sanda ta dauki cikin fuad har ta haifeshi.
Qofa ta qarshe da zata bata daman shiga falon annin nanma sai data jinkirtawa na'ura sannan ta bata izinin shiga,ta dauke kanta ranta yana suya da wani irin fushi. Tafi qarfin ta tako gidan alhaji hamza har abada.....inda sun bata girma da martabarta da a yanzun ba shakka ita ake zuwarma haka neman gindin zama.
Tana sane da yadda mabuqata ke yawan ziyartar gidan karbar taimako a duk sati......taimakon da ta tabbatar daga fuad ake rabashi.......sai gashi ita duk yadda taso ta dinga cina farfajiyar nata gidan da mabuqata,tana raba musu kudi a envelope yadda taso abun bai samu yadda takeso ba. Bai hana taimako,amma saidai ta rubuta list na mabuqatan ya hadasu dana gidan alhaji hamza a raba musu taimakon tare.
Bata samu yin sallama ba,sai Allah ya sanya tana sanya qafafunta a falon idanun anni dake kashingide cikin lausasan sofa ya sauka a kanta.
"Ikon Allah" Anni ta furta tana miqewa daga kashingidar da tayin tana sauke qafafunta qasa idanunta akan maamah
"Da kinyi zamanki ma.....don ni ba wajenki nazo ba kaman yadda na alqawarta zuwa na na qarshe gidan nan......wajen hamza nazo" Maganar tata tazo qarshe dai dai sanda amna ke fitowa daga kitchen ta zuba abincin dare,don tace yau zaman cin abincin abban yayi dare da yawa,ba zata iya jiransa ba da wuri takeso ta kwanta.
Kallon kallo sukayi tsakanin maamah din da amna. A kallon farko ta fahimci wacece duk da wannan shine karon farko da ta fara ganin yarinyar ido da ido. Autar alhaji hamza kenan,yarinyar da ake gaya mata irin sabon dake tsakaninta da fuad......yadda take ji dashi da yadda shima yake ji da ita
"Idan har kikayi da wasa kina zaune zakiji ance 'yar gida akayi.....wannan matar zata aura masa autarta..... Kinga shikenan komai ya qarasa watsewa" Muryar hajja ta dawo mata akai cikin tattaunawar da sukayi da hajjan a dazu dazu kan hanyarsu ta dawowa gida.
"Ke amna......dubamin abbanku idan ya kammala,kice maza maza yayi baquwa"
"To" Ta fada tana ajiye plate din sannan ta miqe tana nufar qofar da zata sadata da sassan abban nasu ba tare da tabi ta ainihin farfajiyar gidan ba. Tana tafe tana waiwayen maamah,itama ta lura da hakan,sai taja wani tsaki me matuqar qarfi abinda ya sanya amna din maida kanta tana yin gaba.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 58
___________________________
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
Assalamualaikum
Yar uwa kinason kiga kitchen dinki a cike da kayan amfani masu kyau da inganci amma Kuma kina tunanin chake kudi kisaya a dunkule??
Koda yarinyace Dake da takusa aure kinason kifara Tara mata kayan kitchen??
To damuwarki tazo karshe Yar uwa kinzo inda za'a share Miki hawayenki *ALFAT KITCHENUTENSILS* (Adashen Yar gata), sun shirya tsaf dan ganin sun sama Miki ingantattu Kuma masu kargo Yan zamanin kayan kitchen.
Zaki dinga tura kudinki idan yakai wani minzali saiki karba duk abunda kikeso daide kudinki.
Ba iya nan muka tsayaba, farashin kayanmu daban yake a ko ina.
Dannan link dinnan domin kisamu damar shiga group dinmu don zabar kayanda kikeso da Kuma ganin yadda abubuwan suke kasancewa. Nagode
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
_________________________
Farfajiyar gidan ba kowa sai qofar dakin malam saidu da yake iya hangowa wanda yake a bude. Juyawa yayi zuwa sassan da spare din famfo dake bawa shukokin gidan ruwa yake,ya xame takalminsa,ya kuma xare agogon hannunsa ya jefa aljihu sannan ya matsa ya kunnashi. Dukkan hannayensa ya tara yana kallon saukar ruwan,sai yaji wasu kalamai suna dawo masa a