Showing 42001 words to 45000 words out of 61846 words

Chapter 15 - Nakasa B Kasawaba Book 2 Complete Hausa Novel

da dare, hannu tasa ta share hawayenta wanda bata san dalilin zubowarduba a hankali tace.
"Ya Allah kasa kada Babana yayi fushi sani".
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.
"Hmmmm Allah na godema daka tsere tar dani daga hannun wannan mutumin, na sani tabbas da na ƙara kwana a gidan shi, haka zai ta lallatseni kamar maggoro yayi ta tsotsini kamar tom-tom daga nan zai gwada min ƙarfin yace zai farkeni, dole nema in gudu daga komarshi mugu kawai."
haka dai taci gaba tuƙi.

Daga cikin garin na Numan, kai tsaye anguwar bakin kogi ta nufa, don acanne uncle solomon ɗin yake, a bakin kogi nan sukeyin rayuwa,  da ƙyarma ta iya ƙarasawa wajen, don kafun ma ta isa tuni tayi laushi, amatuƙar gajiye takejin kanta,  a ƙofar ɗan madaidaicin gidan wanda gininsa yayi masifar tsufa ta dai-dai-ta parking ɗin motar, buɗe murfin motar tayi inda tafito kai tsaye tanufi cikin gidan, ko damuwa da mutanen dake kallonta batayi ba.
Sanincewar su ɗin ba musulmai bane yasa, kanta tsaye ta kutsa kanta cikin gidan.

Elizabet  matar Solomon dake zaune atsakar gida tana tatan markaɗen dawan burkutunsu, jin motsin shigowan mutum yasa ta ɗago kanta ta dubi ƙofar shigowa gidan, ganin Zaleeha tsaye yasanya taɗan saki fuskarta, cikin ɗaga murya Elizabet ɗin tace.
"Solo oya come out ga baƙuwarka ta iso."
Solomon dake cikin ɗaki jin abun da Elizabet ɗin ke faɗa yasan yashi fitowa, hannunsa riƙe da fartanya, da'alama dama gona zashi, kasancewarsa manomi kayyakin marmari na bakin kogi.
Ganin Zaleeha yasashi washe haƙoransa.
Cikin gurɓatacciyar hausarsa yace.
"Aa Zali'a kin iso kenan, your wellcome, shigo ciki  mana."
Ɗan guntun murmushi Zaleeha tayi tare da ƙarasowa cikin ɗan ƙaramin gidan,  tana wucewa Elizabet ta bita da kallo ƙasa-ƙasa ta taɓe baki.

Nan Zaleeha tabi Uncle ɗin nata zuwa cikin ɗaki, inda yace da Elizabet ta kawo mawa Zaleehan ruwan sha.

Abakin wata katifa wanda ta fara lashewa Zaleehan ta zauna, nan shima Uncle ɗin nata ya zauna.
Dubansa tayi tare da cewa.
"Good evining uncle, haw was the day?."
"Am very fine my daughter, how are you, i hope are you okay, right?."
Murmushi ta ɗanyi tare da jinjina masa kai, ahankali tace.
"Yeah."
Dai-dai lokacin Elizabet ta shigo hannunta ɗauke da kofin ruwa wanda ta tara a bakin fomfonsu dake ɗan tsakar gidan nasu, aje kofin tayi agaban Zaleeha, ɗauke kai Zaleeha tayi domin sam batason jin ƙamshi ne ko warinsu zata ce ne oho, cikin ƙasa da murya tace.
"Aunty good evining."

"Evining, how are you?."
Elizabet tafa ɗa tana me kallon Zaleeha'n, wanda take ta faman ƙarewa ɗakin kallo.

"Am fine!" Zaleeha tafaɗa tana me ƙarewa kofin da aka kawo mata ruwa aciki kallo, Allah Yasani itakam ƙyanƙyaminsu takeji, hakanan take ganin komai nasu yafita daban, komai nasu ba irin na sauran mutane ba, shiyasa ma kwata kwata bata fiye shiri da dangin mahaifiyarta ta ba, domin ita sam batason zama da su, saboda zama da waƴanda hasken addinin musulunci bai cimmusu ba, sai ahankali, zakaga kwaɓa da kuma shirme kala-kala.

Duk da kasancewar tanajin ƙishin ruwa, amma kasa shan ruwan tayi, don sam bata yarda ma da tsabtan gidan ba.
Hira kaɗan suka ɗan taɓa da Uncle din nata, nan yace da ita zai tafi gona, yana tafiya ta jawo akwatunanta, zanin gadon dake kan katifan da take kai ta yaye, nan taciro wani bedsheet mai ɗan taushi wanda baida nauyi ta shumfuɗa, kimtsa akwatunanta tayi agefe kana ta fito da sallayanta da komai na buƙatan musulmi ta a dana,
hand bag ɗinta ta zuge, nan ta ciro wasu diary milk chocolate guda biyu, tare da wani cake, nan ta kwanta tare da jawo wayarta, power bank dinta ta ɗauko inda ta saƙala wayarta a charge, kwanciya tayi tana mecin chocolate ɗin ahankali, hakanan dai ta gwammace gwara zaman nan dana gidan SAIFUDDEEN dake cike da jin daɗin daular duniya.

Acan Gombe kuwa, Haka su Ya Ameenu suka ƙare yawonsu har suka gaji, dawowa gida sukayi inda sukayi jigum jigum.
Baba Malam ma haka ya dawo daga Dukku zuciyarsa duk ba daɗi.

Ganin yanda gaba ɗaya dangin suka tashi hankalinsu ne yasanya wani tunani ya faɗowa Ahmad, nan yaƙira Ya Ameenu yasanar masa cewa, lokacin da Zaleeha zata tafi, tabbas yaga Zaheera tazo a napep inda ta bata wani abu a jaka, sannan ita Zaleehan tatafi, ita kuwa Zaheera ta shiga napep din daya kawota, saboda haka atambayi Zahira ko tasan inda Zaleehan taje.
Habawa ae Ya Ameenu kaman kububuwa haka yaji ransa ya ɓaci, atake ya gayawa Baba Malam, nan Baba Malam yace da Zakariyya wanda tun safe yake gidan, cewa yaje ya ƙira masa Zahira, Zakariyya na zuwa ƙiranta, Mama ta buga tsalle inda ta kama hannun Zahira, tare da cewa tare zasu je, nan Mama tace da Zahiran ko kasheta zasuyi, kada ta sake tafaɗi inda Zaleeha take, dayake Zahiran ma zuciyar arna gareta, take ta kafe kan cewa bazata faɗa ba.
Atare suka shiga falon ita da Mama, cikin zafin nama Ya Ameenu ya damƙo Zahira, wani lafiyayyen mari ya sauƙe mata akan fuskarta, take tafasa wani uban ƙara, tare da buga tsalle tasoma yayyarfa hannuwanta, cikin zafin zuciya yace.
"Ina Zaleeeha ta tafi?." Bata iya basa amasa ba saboda marin ya matuƙar gigitata.
Cikin fushi haɗi da ɓacin rai Mama tace.
"Maganar banza ma kenan, wannan ai kora kunya da hauka kuke ƙoƙarin yi min, ku da kanku kuka salwantar min da rayuwar ƴata, sannan yanzu kuzo kuna tambayan Zahira, wallahi Ameenu kakiyaye ni kada kasake ka ƙara kai hannunka jikin Zahira tam!!."
Mama tafaɗa ranta amatuƙar ɓace, zuciyarta kuwa cike da fargaban kada zafin mari yasa Zahira faɗin gaskiyan inda Zaleeha take.

Ran Baba Malam a ɓace ya dakawa Mama tsawa, cikin faɗa yace.
"Ina ki ka kai Zaleeha?."
Afusace Mama tace.
"Bansan inda takeba!!."
Cikin ɓacin rai Baba Malam yace.
"Na baki nanda kafun gari ya waye, duk inda Zaleeha tashiga ki tabbatar kin dawo da ita ɗakin mijinta, idan kuwa ba haka ba, ki tattara komai naki kibarmin gidana, kuma sannan idan kin tashi tafiya ki haɗa da Zahira karkiyi kuskuren barmin ita agidana, don bana ƙaunar zama da munafuki!, kada ki manta koki ƙira Zaleeha ta dawo ko kuma kibarmin gidana ayu basai gobe ba!!!." Yana gama faɗin haka ya wuce ɗakinsa, amatuƙar fusace.
Wani irin masifeffen tsorone ya rufe Mama kadafa Baba Malam ya saketa ta koma ƙauyensu noma, wani sashin na zuciyarta kuwa zugar ruda ce ta ratsota haka yasa ta ɗan ja tsaki tare da kamo hannun Zahira, cikin ɓacin rai tace.
"Mu tafi ai nima inada gidan uba, saboda haka kwana ɗaya bazamu ƙara ba, Zaleeha ne kuma bamusan inda take ba, kuma ko sama da ƙasa zasu haɗe, aurenta da nakasashshen gurgu ya ƙare kenan har gaban abadan."





Littafina na kuɗine in kin gashi a wojema na satane. Turo katin Mtn na ɗari 300 kacal ta wannan number 09097853276 ko ka/koyi min transfer ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa kana ki turo min shaidar biyan ki.

   By
*GARKUWAR FULANI*
[9/9, 9:05 PM] +234 806 222 4030:     
                       


"Wai Duk wannan haɗe fuskan na memene wai? dan ance za'a ƙara maka aure?." kanshi ya sunkuyar ba tare da yace komaiba.
Ahmad ne ya gyara zama tare da duban Saifuddeen ɗin, cikin zolaya yace.
"Manya kenan angon mata biyu, gaskiya bakowani namiji bane zai taki sa'a irin wanda ka taka, auren mata biyu awata ɗaya kacal, lallai Saifuddeen kai ɗan gata ne."
Harara Saifuddeen ya watsa Ahmad ɗin tare da haɗe fusks, wani irin abu yakeji a maƙoshinsa, sam shi atsarinsa babu auren mace wanda ta wuce sama da ɗaya a rayuwarsa.
Ummi ne ta ɗan saki murmushi tare da duban Ahmad, cikin kulawa tace.
"Ni kaina naji na gamsu da batun ƙarin auren Saifuddeen, amma kuma sai-dai bansan wace kalar matar kuma zai ƙara samowa ba, musamman ma yanzu da yace babu wata wacce ya keso."
Murmushi Ahmad yayi cikin nutsuwa yace.
"Saifuddeen ai mai farin jini ne, muna nan zaune zamuga wata santaleliyar budurwa ta bayyana, don neman aurensa! In wata ta gudu wata zata zo. Ita kuwa ɗiyar taki Zaleeha in taga dama tafi ruwa gudu."
ya ƙare maganar yana  gimtse dariyarsa, don sosai yakejin wani irin farin ciki yau ɗin, don yasan ta hanyar ƙarin auren Saifuddeen ɗinne kaɗai Zaleeha zata shiga cikin sense ɗinta kuma tanannne Saifuddeen zai samu nitsuwa.
Cin ƙufula Saifuddeen ya ɗauki ɗaya daga cikin pillow kujerun falon, nan ya wurgawa Ahmad ɗin, da sauri Ahmad ya kauce yana dariya,   duban Raliya dake zaune Ahmad yayi, cikin son ƙara tsokar Saifuddeen ɗin yace.
"Nikam zan fita, idan na fita kuwa sai inda mai na ya ƙare, saboda zan zaga gari, ko Allah ma zai sa na samawa ɗan bazawarin abokina mata ta biyu!."
Yanzun kam harta Ummi saida tayi dariya, shikuwa Saifuddeen sake kwaɓe fuska yayi nan yasake wurgawa Ahmad ɗin pillow, da sauri Ahmad ya kauce kana ya fice daga cikin falon yana murmushi.
Ahankali ya danna madannin wheelchair ɗinsa, inda ya ƙaraso har gaban Ummi dake zaune,  Raliya kuwa miƙewa tayi inda tabi bayan mijinta.
Hannun Ummin Saifuddeen ya kamo, karyar da wuyansa yayi, tare da shagwaɓe fuska, narai-narai yayi da idanunsa, tare da ɗan yaɓe lips ɗinsa, hakan yasa yanayinsa ya koma kamar na ƙaramin yaro,  ganin yanda yayi da fuskar ne yasa Ummi fuskantar me yake nufi, cikin yanayin lallashi ta kama hannunsa, tausasa murya tayi tare da cewa.
"Nasan bakaso amma haƙuri zakayi ka ƙara auren nan Saifuddeen, tun da dai kaga shi baban Zaleehan da kansa ya faɗa, kuma ai dai nasan kafahimci me yace, tun da dai yace akan maganar ƙarin auren,  ba shawara yake ba ka ba, umarni ne."
Kai Saifuddeen ya ɗan girgiza, tare da ɗan lumshe idanunsa, kana ya buɗe su alokaci guda, duban Ummin nasa yayi, cikin body language ɗinsa yake yi mata alaman cewa.
"Bashi da ra'ayin ƙarin aure, sam babu auren mata biyu atsarinsa, idan ma ya ƙara auren ya zaiyi da matar?."
Kanshi ta shafa cikin bashi ƙarfin guiwa tace.
"Je kasha maganinka, daga gobe zamuyi mgnar, kana Kayita Addu'ar Allah ya tabbatar maka da al'khairi a cikin lamarin."
Kanshi ya gyaɗa mata cikin bin umarninta ya juya ya nufi side ɗinshi.
Ita kuwa ta koma cikin ɗakinta zuciyarta fal farin ciki,
Adda Rahama ta kira ta sanarwa abinda ke faruwa, abinda yayi matuƙar faran ta mata rai, nan tace.
"In sha Allah zanzo in ya Adnan ya barni."
"Allah ya kaimu." cewar Amin Amin ta amsa kana sukayi sallama.

Washe gari da yamma, Saifuddeen na zaune gaban Umminshi cikin nitsuwa yake mata tambayar meyasa zata bari aƙara mishi aure bayan tasan shi mai raunine.
Wani irin yalwataccen murmushi Ummin tayi tare kamo hannunshi, bata kai ga basa amsa ba.
Adda Rahama wanda tun ɗazun ta shiga kitchine haɗo wa kanta abun da zata ci, ta dawo cikin falon, zama tayi tare da duban su Ummi'n.
Nan Ummi ta sauƙe ajiyar zuciya tare da duban Adda Rahama'n, cikin kulawa tace.
"Kinjisa wai shi bayason wani ƙarin aure, waishi mai raunine."
Dubansa Adda Rahama tayi cikin kula tare da ɗan nutsuwa, cikin son fahimtar dashi tace.
"Akan maganar ƙarin auren nan, ba wai zaɓinka aka nema bafa, zaɓin da aka baka dai kawai shine ka fito da wata, wanda kake ganin ta kwanta maka arai, amma ƙarin aure kasa aranka cewa in sha Allah babu fashi, ita wanda kake mutuwar so ɗin ba guduwa tayi daga gareka ba, saboda haka nidai ina goyon bayan da kasakeyin wani auren, don gaskiya bazamu barka kaci gaba da zama ahaka ba."
Fuskarsa ya haɗe tare da dubansu su duka biyun, cikin body language ɗinsa, yayi musu alaman cewa.
"Ahakanne zai ƙara aure bayan ko yaushe bisa keke yake, kodai sun manta cewa shi ba cikakken lafiyayye bane, ko kuwa sun manta da cewar shiɗin mai rauni ne, ayanda yake ma gaskiya baijin zai iya zama da mata biyu."

Murmushi Adda Rahama tayi tare da tasowa, ta ƙaraso inda yake, hannunta ta sanya inda ta dafa kafaɗunsa, cikin ƙauna haɗi da tausayinsa tace.
"Ni na tabbatar kai ba rago bane, nasan zaka iya rayuwa da mata huɗu ma ba biyu ba,  kai jajirtaccen Namiji ne Saifuddeen, saboda haka kada kabari rauni ya ziyarci tunanin ka, tun ada kai jarumi ne, haka ayanzu ma kai ɗin, you are the super hero, sannan kafi kowa sanin nakasa bata taɓa zama kasawa, sai-dai ga wanda ya bari zuciya da kuma tunaninsa suka mace, saboda haka ako yaushe kasa azuciyarka cewa, kai ɗin jarumi ne!! Sai dai kuma in salon tirjiyarka ce hakan".
Taƙare maganar tana me ɗan bubbuga kafaɗunsa tana murmshin zanca wai shi mai raunine kaji yaro da wayo wato ace bazai iya jure mu'amala da mata biyu ba.
Shiru yayi tare da lumshe idanunsa,  hakan na nufin cewa kenan bashida wani zaɓi? ko kuwa dai ƙaddaransa ne take ƙoƙarin canzawa?
Ganin yayi shiru ne yasa Adda Rahama komawa kan kujera ta zauna, nan ta shiga cin abincinta hankali kwance.

Da sallama Hayatuddeen ya shigo cikin falon Ummi, ganin su azaune ga kuma Hammansa daya haɗe fuska, yasan yashi ƙarasowa cikin falon, jakar makaranta da kuma littatafan dake hannunsa ya watsa akan kujera, zama yayi daɓas akan sofa, tare da miƙe ƙafafunsa, cikin shagwaɓa haɗi da kasala ya ɗago indo ya dubi Ummi, asangarce yace.
"Ummi am so tired, ƙafana bayana kaina idona kunennena ɗuwawuna kai ko'ina ɗina ma ciwo suke min!."
Murmushi Ummi tayi, tare da cewa.
"To sannu auta na, ae dai ku kam gaba ɗayan ku haka kuke, abu kaɗan ke gajiyar daku, sai kace ba gwaraza ba."
Sake shagwaɓe fuska yayi, cikin salon sakalci yace.
"Wallahi Ummi makaranta ba daɗi, duk acika ku da lectures, yau fa ko ɗan hutu bamu samu ba."
Ƙare maganar yayi yana me ɗago kansa, inda ya kalli Saifuddeen, wanda ya haɗe fuska, inda ya kawar da kansa gefe, da'alamu cewa ba ya cikin yanayi me daɗi, cikin kulawa haɗi da faɗuwar gaba, asanyaye Hayatuddeen ɗin yace.
"Hamma!."
Kasancewar Saifuddeen ɗin ya juyar da fuskarsa, zuwa wani ɓangare na daban hakan yasa baiji ƙiran da Hayatuddeen ɗin yayi masa ba, don dama sai yana kallon ka ne, sannan yake karantar abun da kake faɗa, ta hanyar kallon yanayin motsin bakinka shiyasa yake da yawan kallon ammanfa ga wanda yake son ya gane abinda zai faɗa.
Ganin Hamman nasa baisan da cewa yanayi ba, hakan yasa ya taso da sauri ya, ƙarasowa gaban Hamman shi hannunshi ya ɗaura a akan kafaɗan Hamman nasa, ahankali Saifuddeen ya ɗago da kansa, duban Hayatuddeen ɗin yayi, sai kuma ya kau da kansa gefe.
Hakanne yasa jikin Hayatuddeen yayi sanyi sosai.
A take kuma yaji gabansa ya faɗi, ƙirjinsa ne ya shiga duka, cikin zuciyarsa yace.
"Nashiga uku badai Hamma na yasamu labarin cewa, yau na fita amakaranta, na bi Khamis muntafi yawo ba?."
Cikin ɗari-ɗari da fargaba ya kalli Ummi, wanda ke ƙoƙarin tashi, don komawa ɗaki, da sauri ya rufa mata baya, jin mutum abayanta yasata juyowa, kafe Hayatuddeen ɗin tayi da ido, tare da cewa.
"Lafiyanka ƙalau kuwa kake biye dani, sai kace wani ƙaramin jariri, kodai ka aikata wani rashin gaskiya ne?."
Ummi tafaɗa tana me ƙare masa kallo, don tsab tasan yaranta, da zaran sunyi wani abun da ba dai-dai ba, takan saurin ganewa, ko daga halin rashin nutsuwa da zata gansu aciki, kamar dai yadda ta fara zargin yanayin canji nitsuwar Hayatuddeen.
Ƙifi-ƙifi Hayatuddeen ɗin yayi da idanunshi tare da cewa.
"A'a babu abun danayi, kawai dai naga ran Hamma Saifuddeen ne kamar aɓace yake."
Ajiyar zuciya Ummi tayi tare da cewa.
"Hmm rabu da Hammanku, gata ake son a mishi shi kuma wai baya so."
Da sauri yace.
"Ummi wanne irin gatane?."
murmushi tayi tare da cewa.
"Wai fushi yake don ance masa ya ƙara aure, shine yake ta faman haɗa rai sai kace wanda akace yayi wani abun, wanda ba dai-dai ba."
Cikin zaro ido Hayatuddeen yace.
"Haaah Ummi to kuce ni inyi auren mana, tunda shi baya son gatan ni kuyi mini."
Cikin mamaki da al'ajabi da zazzaro ido Ummi tayi kana tayi kasake tana kallonshi da nazartanshi.
Shi kuwa da sauri ya dawo nitsuwarsa gudun karta ramfoshi.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Hayatuddeen ya sauƙe, ya godewa Allah da yasa, ba asirinsa bane ya tonu, domin yasan tabbas idan Hamman nasa, ya gane irin abubuwan da yake yi, to fa kashinsa ya bushe, yasan sai anrabasa da duk wani abu nasa najin daɗi.
Gyara tsayuwarsa yayi tare da cewa.
"To Ummi me yasa zai ƙara aure, yaushe ma yayi auren?."
Harara Ummi ta watsa masa, tare da cewa.
"To kai mekasani acikin aure da kake tsoma baki cikin abun  da babu ruwanka?."
Kanshi ya jujjuya tare da cewa.
"Wallahi ba abinda na sani, kawai a auro mishi mai sonshi tunda hegiyar nan taƙi zama."
haɗe fuska Ummi tayi tare da cewa.
"Hayatu baka da kunya fa ba yayarka bace kake ce mata hegiya, to a kul wlh kada in sake jin ka zagarmin ƴata dan mu dai Zaleeha bata ƙi muba bata mana wani laifiba ita dai auren ne da bata so."
Murmushi yayi tare da ɗan shafa kansa yace.
"Afwan ya Ummi bazan sakeba, nima nasan Zaleeha na sonmu amman dai ina jin haushinta in na tuno wai bata son Hamma nane yasa ta gudu."
ya ƙarishe mgnar tare da, juyawa ya inda ya fice daga cikin ɗaki, a falo ya samu Adda Rahama, har yanzun Saifuddeen na zaune afalon,   komawa kan sofa yayi ya zauna, inda ya matso kusa da Adda Rahama wanda kecin abinci,  dubansa Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Bafa zanci dakai ahaka ba, jeka wanko hannunka."
Ɗan shagwaɓe fuska yayi tare da cewa.
"Dan Allah Adda Rahama, muyi karɓe-karɓe, don nagaji, dama kafun na zauna ne kikace na wanko hannun nawa."
Kai Adda Rahama ta girgiza tare da cewa.
"Allah ya shiryeka, sarkin lalaci kawai, da ace kai mace ne, tabbas da anyi uwar son jiki."
Murmushi kawai yayi tare da amsan spoon ɗin dake hannunta, haka suka shigayin karɓe-karɓe, idan tayi loma guda, ta bashi spoon ɗin shima yayi, duk wai saboda tsananin ganda, ɗauko spoon kaɗai ya gagaresa.
Ummi ce tafito ɗaga cikin ɗaki, hannunta ɗauke da wayarta, duban Saifuddeen tayi tare da cewa.
"Bappa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login