Showing 36001 words to 39000 words out of 61846 words
Chapter 13 - Nakasa B Kasawaba Book 2 Complete Hausa Novel
sukayi sabida sunga tarin so da kulawar Saifuddeen a kan ƙanwar tasi, dan ya gayawa ya Ahmad duk abinda ke faruwa na son sace amarya, ya faɗa mishine da kashedin karfa wasu suzo su basu amarya su jira sai sunzo da kansu
.Su Bilkeesu kuwa bisa dolensu suka shiga wata mota ta daban.
Ahankali duka motocin ke tafiya a jere a jere.
Sosai hankalin yaran Dalla yayi matuƙar tashi ganin duk motocin sun fice sun barsu sai nasu kawai ,nasun kuma duk sunyi faci, sai ƙwaya ɗayar nan,
koda suka shaidawa Dalla hankalinshi yayi masifar tashi to waya gano shirinsu, waya ɓata mishi tsarin sace matar wannan gurgun kurman,
dole a tsorace suka fita da motocin a haka suka lallaɓa suka isa wurin mai sa iska,
yayinda duk abinda sukeyi Saifuddeen na ganinsu a system ɗinshi ta sanadin na'urar bibiya da ya bawa Hayatuddeen ya liƙa musu a jikin motar da take irin tasa.
Tunda tashiga cikin motar ta cusa kanta atsakankanun cinyoyinta kuka take sosai har kaman zata shide, samma batasan dawa take tare ba acikin motarba, ta gefen ido yake kallonta, hakan ne ya tabbatar mishi kuka takeyi.
Sosai yakejin kukan nata na taɓa masa zuciya da jiki dan jikinshi ya bashi kuka take ga kuma alamu yana ganin yadda ta takure tana shessheƙa, saidai kuma tun shigowarta motar ko ɗago kansa baiyi ba, gaba ɗaya ya maida idanunsa akan system na laptop ɗinsa, saidai kuma duka hankalinsa na gareta, ɗan ɗagowa yayi tare da numfasawa, cikin nutsuwa ya rufe laptop ɗin bayan ya saita abinda zai naɗe mishi diddigin yaran Dalla sai dai akasi kaɗan da aka samu lokacin da yasa yayi ƙarancin binsu har inda zasu isa,
ido ya zuba mata cikin jin tausayinta yasan halinda mata kan shiga lokacin da suke barin gidan iyayensu zuwa gidan mazansu, dan bai mance auren Raihana ba da Adda Rahma ke badu labarin daga cikin gombe har suka isa Kaduna Raihana bata bar kukaba sai ta ɗanyi shiru sai kuma taci gaba har suna mata dariya wai hutawa takeyi bare da dama sun san Raihana saurin kuka gareta,
ido ya lumshe tare da buɗesu ya zuba mata su, ahankali ya sanya duka hannuwansa akan kafaɗunta, ɗan ɗagota yayi kaɗan,
ita kuwa Zaleeha jin anriƙe kafaɗunta ne yasanyata yin tunanin Aunty Lubna ce, hakan yasa batare data buɗe idanunta ba, haka bata yaye mayafin dake kanta ba, tafaɗa jikinsa, sakin sabon kuka tayi tare da sanya hannuwanta duka ta zagaye cikinsa, cikin kukan fitar hayyaci tace.
"Dan Allah Aunty Lubna ku maidani gida, wallahi bana son barin gida,karku kaini cikin bare ban sansuba basu sanniba, wlh bana sonsa, natsanesa, ko ganinsa banason yi, mutuwa zanyi matuƙar kuka kaini gidansa, dan Allah Aunty ki taimakeni, taƙare maganar tana me cusa kanta cikin ajikinsa.
Ahankali ya lumshe idanunsa, tare da sanya duka hannuwansa ya ƙara jawota jikinsa, wasu irin tagwayen ajiyar zuciya ya rinƙa sauƙewa take wani irin zazzafan shauƙi ya shiga ratsa zuciyarsa da jikinsa.
Jin wani masifaffen ƙamshi mai azabar daɗin ji da shaƙa wanda bata taɓa jin irinsa ba na shiga cikin hancinta wanda ba ƙamshin Aunty Lubna bane yasanyata ɗan jan jikinta baya, ahankali ta ɗago kanta, azabure tawani irin jan jikinta baya, kallon fuskarsa da yayi masifar kyau wanda ita da kanta sauda ta ganshi kamar balarabe, ganin shinne yasanya komai ya ƙwace mata, wani irin baƙin ciki ne ya cika zuciyarta take tasaki kuka tare da maida kanta ƙasa, wani irin tafasa zuciyarta keyi mata.
Ƙawataccen murmushi Saifuddeen yayi tare da maida bayansa ya jingina da jikin kujeran, lumshe idanunsa yayi yayinda yake shaƙan dadaaɗan ƙamshinta, runguman da tayi masa yasanya yaji wani abu na tsargawa ta cikin jikinsa, sam baiyi yunƙurin sake taɓa ta ba, haka kuma bai hanata kukan da takeyi ba, ahaka har suka iso cikin katafaren gidannasu.
Nan fa ƴan kawo amarya kowa yacika da mamakin haɗuwar gida, masu son auren sai masha Allah kawai suketa cewa,
Goggo Maryama ce ta riƙeta inda tace tashiga gidan da ƙafar dama haɗi da bismillah, ranta aƙuntace haka tayi bismillah duk da cewa bawai ganin gabanta takeyi ba, zuwa yanzu tama daina kukan, jira kawai take Saifuddeen yace da ita wani abu ta sauƙe masa kwandon bala'i.
Baƙaramin mamaki kyan ɓanagaren na Zaleeha ƴan uwanta sukayi ba, don kuwa komai yayi harma ya zarcewa tunaninsu, koda Balkeesu taga uwar dukiyar da aka kashewa Zaleeha, dakuma irin tsaruwan gidan al'afarma part ɗin nata, saida taji wani abu kaman mashi ya caki zuciyarta, sam bata ɗauka haɗuwar wajen zaikai har haka ba.
Acan cikin ɗaki aka zaunar da Zaleeha.
Sannu ahankali jama'a ke watsewa don nan da wasu awanni za a gudanar da diner, Rasheda ma tatafi don zuwa taho da me meckup ɗin da zatayiwa amarya, hakanne yabawa Balkeesu daman ƙara hurewa Zaleehan kunne, sam tace da ita tadaina asaran hawayenta, tabari idan hidiman biki ya kammala plant ɗinsu da suka haɗa sai ya fara aiki, sosai Zaleeha kuwa tahau kan maganan na Balkeesu ta zauna wanda zugan bilkeesu da asirin mma yazo iri ɗaya.
Kamar yanda al'adan Gombawa yake aduk sanda aka kawo amarya gidansu ango, to fa akan tarbesu da kayan ciye ciye dana shaye shaye, hakance takasance agidansu Saifuddeen dan kuwa sosai aka cikawa su Zaleeha kayan ciye ciye, komai cikin wadata akayisa, abun ma har mamaki yake bawa wasu daga cikin dangin Zaleeha don kuwa kuɗi sosae gidan su Saifuddeen ɗin ke kashewa wajen ƙawata komai nasu, kamar basajin ciwon kuɗin.
Ya Habu kuwa da ya Aminu har cikin ɗakin suka shigo suka gargaɗeta akan batun diner muddin tayi abinda zai kunya tasu Habu yace.
"Wlh rabaki gida biyu zanyi kin sanni ba mutun cine da niba, ni ba irin ya Ahmad bane."
Dolenta ta nitsu koda suka tafi ko motsin kirki bata kuma yiba.
Kasancewar ƙarfe 8:00 pm dai-dai za a fara gudanar da diner'n hakan yasa amarya Zaleeha tana idar da sallan isha aka soma tsantsara mata meckup akan fuskarta, musamman aka ɗauko ƙwararriyar meyin meckup inda tazo ta baje basirarta akan fuskar Zaleeha, wani irin haɗaɗɗen meckup aka tsantsara akan fuskar Zaleeha wanda yayi bala'in fito da kyawun fuskarta,
dakanta ta zura wata haɗaɗɗiyar fitted weeding gown mai azabar kyau, jifa jifa aka sanya ratsin fari ajikin rigar, rigace irin doguwa ɗinnan wanda har sharan ƙasa take, sosai rigan takama jikinta tazauna ɗas, inda gefe da gefen waist ɗin rigar aka sanya wani irin yadi mai sharara wanda yake da masifar tsawo, haɗuwar rigar ya zarce misali, musamman ma yanda ya zauna ajikinta yayi ɗas, tabbas ko ba a faɗaba kallo ɗaya zakaiwa rigar kasan da cewa taja maƙudan kuɗaɗe wajen tsarata,
haɗaɗɗen ɗaurin ɗan kwali irin na amare aka kafa mata akanta, bayan anyi parking dogon gashinta atsakiyar kanta, inda aka sanya mata wani haɗaɗɗen sarƙan gold mai tsananin kyau da tsada, dagakan ɗankunne har zoben dake hannunta duka na gold ne, masu masifar tsada da kyau, wani irin takalmi mai masifar tsini ta sanya aƙafafunta, bakaɗanba tayi kyau nafitar hankali, harwani ɗauke ido take, turare kuwa kamar ɓarinsa akayi ajikinta, sosai Zaleeha tayi kyau cikin shigarta ta diner, inda kowa ke yabawa da tsantsar kyawun da Allah yayiwa Zaleeha, ita kanta Zaleeha tasan cewa ayau ɗin tayi kyau.
Gombe International Hotel
Sosai aka ƙawata babban falon wanda ananne za a gudanar da diner ɗin, anyiwa wajen ƙawa naban mamaki tare da haɗaɗɗen decoration na peach and white, sannan kuma daga sama adon decoration blue akayi mai masifar kyau, gurin acike yake da jama'a , inda kowani team da kalan shigarsu, gabaki ɗaya abokan Saifuddeen shigar shadda blue colour ce ajikinsu, inda gefe guda kuwa su Hayatuddeen ke sanye da peach colour ɗin shadda, daga gefe kuwa su Adda Rahama suka tsantsara ado cikin wani tsadadden farin lace mai adon blue, gurin tuni yacika da jama'a zuwan ango da amarya kawai ake jira.
Ɓangaren Zaleeha kuwa ana gama tsantsara mata kwalliya Rasheeda ta sanar dasu zuwan ango, hakan yasa aka ƙara ƙawata mata adon nata, Balkeesu da Rasheeda na riƙe da ƙasan rigarta dake jan ƙasa suka nufi compound ɗin gidan.
Saifuddeen ne zaune acikin wata rantsatstsiyar mota yabala'in yin kyau acikin farar shadda mai peach colour ɗin aiki dake jikinsa, yayi kyau fiye daduk wani tunani mai tunani, idanunsane suka sauƙa akan tauraruwar amaryarsa wanda tsananin kyawun da tayi yaso zautar dashi.
A hankali suke taku tamkar wahainiyoyi, suna isa gab ɓakin motar Saifuddeen ya...!
Littafin nan na kuɗine in kika ganshi a woje to na satane kuma yaseeen doguwa aradu in kina buƙata turo katin mtn na 300 kacal ta wannan number 09097853276 ko kuma kimin transfer ta 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.
By
*GARKUWAR FULANI*
[9/9, 9:05 PM] +234 806 222 4030: *INAH ZAKI DAMU!!!* daga jin sunan labarin ba saikun tambaya ba kunsan labarine daya kunshi al'amuran da suke faruwa a cikin duniyar nan tamu wanda tunani ko zato bai taba kawowa ba, ban tausayi al'ajabi soyayya fad'akarwa da ilimantar wa duk zaku samu a cikin littafin nan da naira 200 kacal littafin marubuciyar nan da kuke nishad'antuwa da rubutun ta *SISIN MAMA* kada ku bari a baku labari dan samun mallakar littafin ku nemeta a wannan number d'in 08107499249.
Aisha Aliyu Garkuwa: Sosai ta firgita da tsawan da Baba Malam ɗin ya daka mata, a zatonta zai kai mata dukane a nata banzan tunani kenan dan bashi yiwuwa namiji mai kamala da dottuku da tausayi ya daki matarsa, har sai irin dukan da shariya ta lamunce musu. Duk da Mama taci duka.
Ganin yayi kwaffa ya jinjina kaine yasa ta
Sake gyara tsayuwa ta, cikin rashin tunanin zuciya tace.
"Tun wuri ma ku ƙira ku sanar dashi, ya sakomin ƴata, don wallahi bazan taɓa lamunta, haka nan ya dakar min ƴa ba!."
Cikin matsanancin ɓacin rai da ƙunan zuciya Baba Malam ya kumadaka mata wata gigitacciyar tsawa wacce ta hautsine hanjin cikin Mama, saboda tsabar firgici da kuma yanda tsawan yazomata abazata, saida tayi baya-baya inda ta faɗa kan kujera.
Su Mamy da Ya Aminu kuwa, sosai suka shiga mamakin irin tsawan da Baba Malam ɗin yayiwa Mama wanda yake nuna zallan ɓacin ranshi,
saɗaf-saɗaf Ameenu da Mamy suka fice sukabar cikin falon.
Cikin tsananin ɓacin rai Baba Malam yace da Mama.
"Ya'isa haka, kinyi min ba sau ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba, duk ina ƙyaleki, to kisani ayanzu kin kai matakin da bai yiwuwa na ƙyaleki, sai yaushe zakiyi hankali ne? sai yaushe ne zaki samarwa kanki nutsuwa? sai yaushene ɗabi'ar musulamai da imani zai kama zuciyarki? ako yaushe idan kin tashi yin abunki bakya sa tunani acikinsa, ashe rashin hankalinki har yakai ki tsaya akaina, gaban ɗana, ɗanki kuma surukin ki kina me ɗaga mini murya, to wallahi kisani daga yau na daina ɗaga miki ƙafa akan komai, badai zaman lafiya ne bakyaso ba, to shikenan zanbi dake aduk yanda kikeso.
Sannan batun Zaleeha ki sani ƴata ce, ina da ikon da zansa ahukunta ta, aduk sanda tayi mini laifi, haka kuma Saifuddeen mijinta ne, shima kuma yana da ikon da zai hukunta ta aduk sanda tayi masa laifi."
Gyara zaman babbar rigarsa yayi tare da duban Mama cikin ɓacin rai da kuma tsanan halayenta yace.
"Wallahi namiki rantsuwa Haleema aduk sanda kika sake, wata matsalar ta auku agidan auren Zaleeha, wanda har ya kasance da sa hannunki aciki, tabbas zan shayar dake mamaki, tashi ki ficemin daga falo!!."
Ya ƙare maganar murya a kausashe, kana yana meyi mata nuni da ƙofar fita daga falon.
Cikin hanzari Mama ta-tashi inda ta fice daga cikin falon, duk da cewar tsawan da yayi mata ya tsorata ta sosai, amma hakan baisa ta daina cika da batsewan da takeyi ba, sosai tacika tayi fam, tana ƙarasawa part ɗinta ta saki dogon tsaki, tare da yin ƙwafa, abayyane tace.
"Dani kuke wasan, ai dai nikam nawa ƙuncin kuma ya ƙare saura naku, yanzu ne aka fara buga wasan, sannan yanzu ne kuma tashin hankalinku zai fara, wallahi sai na shayar daku baƙin ciki, fiye da wanda kuka shayar dani".
Tana ƙarasawa ɗaki, wayarta ta ɗauka inda ta dannawa number'n Ruda ƙira, bugu uku kuwa Ruda ta ɗaga wayar, Mama na fitar da huci tayi mawa Ruda bayanin duk wani abu dake faruwa, shewa Ruda tayi tare da cewa.
"Karki wani damu hankalinki badai kinsa ta gudu ba, shikenan ki manta dasu kawai, nan da kwana 2 zaki gansu arana karki damu kinji dai boka ya gaya mana zaisa ta daina jin tsoron ɓacin ran Babanta da son yimishi biyayya, kinji yace mana komai zai tafi yadda mukeso."
Murmushin mugunta Mama tayi tare da aje wayar, kwanciya tayi akan gado, jin ranta takeyi fes, hakanan takejin kamar an rabata da ƙaya, domin kuwa tunda Zaleeha'nta ta auri gurgu, kullum kwanan duniya da baƙin ciki take kwana, yanzu kuwa Allah ya yaye musu, ya rabasu da masifa saboda haka ta gyara kwanciyarta donyin baccin safe, wanda ta ɗan kwana biyu bata yi shi ba.
Can gidan su Saifuddeen kuwa, Ahmad na ganin tashin motar na Zaleeha'n, ya bita da kallo har sai da ta ɓacewa ganinsa, mamakin inda zataje awannan sanyin safiyan yake, yasan dai hakanan bazata fita da sanyin asuba ba kuma dai yasan hukunta bai ƙare ta koma wurin aikinta ba bare yace ko can ta sammakawa.
Koma cikin gidan yayi, inda kai tsaye ya nufi ɓangaren Ummi, da sallama ɗauke abakinsa ya shiga cikin falon, zaune ya iske Ummi akan lallausan darduman dake shumfuɗe tsakiyar ɗakin, gefe kuwa Raliya ce, yayinda ummin ke jan carbin dake hannunta, ƙarasa shigowa cikin falon yayi, nan ya zauna abakin carpet ɗin tare, da ɗagawa Ummi gaisuwa, cikin girmamawa, fuska ɗauke da murmushi Ummi ta amsa masa gaisuwan nasa, duban Ummin yayi tare da cewa.
"Naga Zaleeha tafita yanzu, ko ta faɗa muku inda zata jene?."
Ɗan jim Ummi tayi tare da cewa.
"Tafita kuma, da safen nan?."
Kai Ahmad yajinjina tare da cewa.
"Yanzun naga fitarta."
Girgiza kai Ummi tayi tare da cewa.
"Ɗazun kuma tabar nan, don tazo ta gaisheni, saidai kuma sam bata faɗamin cewa zata fita ba, amma wata ƙila shi Saifuddeen yasan da fitarta."
Kai Ahmad ya jinjina, tare da neman kawar da zancen ta hanyar duban Raliya, cikin kulawa yace.
"Please haɗamin tea mana, yau so nake nafita da wuri."
Da "To." Raliya ta amsa sannan ta tashi ta wuce kitchine, shi kuma kaitsaye ya wuce ɓangarensu don yin wanka.
Can wajen Saifuddeen kuwa fitowarsa daga wanka kenan, cikin nutsuwa ya gama goge jikinsa, inda ya sanya towel ya shiga tsane lallausan sumar kansa, wanda yaji aski irin na zamani, uwa uba yasha gyara sai ƙyalli yake, yana kammala goge jikin nasa, ya ɗauki body lotion ɗinsa mai daɗin ƙamshi, cikin nutsuwa ya shiga shafawa, yana kammala wa, ya shafe jikinsa da wani irin body oil spray mai matuƙar ƙamshi, take gaba ɗaya ɗakin ya gauraye da ƙamshin sa, ahankali ya tura wheellchair ɗinsa har zuwa gaban haɗaɗɗen drawer ɗinsa, buɗe drawer'n nasa dake shaƙe da kaya yayi, hannunsa yakai zuwa ɓangaren da ƙananan kayansa ke jere, wani crazy combat jeans Black colour haɗi da wata D&G t-shirt mai kyaun gaske ya zaro, daga cikin tarin kayan nasa, sosai drawer'n nasa ke cike da kaya, sai kace wani kanti, wani kayan ma har mantawa yake dasu, dan ma duk bayan wani ɗan lokaci yana kyautar da kayayyakin da sosai musamman wa mutanen ƙungiyar su Jonapwd.
Cikin yanayinsa na nutsuwa ya zura kayan ajikinsa, wanda suka matuƙar amsar farar fatarsa, wani silver watch ya sanya ahannunsa, sannan ya buɗe wata ƴar glass drawer dake nan cikinsu yake aje caps ɗinsa, wata baƙar facing cap mai kyau ya zaro, inda ya ɗaura akansa, take yafito yayi wani daban dashi, ga wani irin kyau da yayi, ahankali ya tura wheelchair ɗinsa zuwa inda yake aje takalmansa, wasu flat shoe masu kyaun gaske ya zura acikin fararen ƙafafunsa, wayoyinsa da kuma laptop ɗinsa ya ɗauka, parfumed ya shafa, sannan yanufi hanyar fita daga ɗakin, ahankali yake tafiyar da wheelchair ɗin nasa, har yasamu kansa acikin falon Zaleeha'n, ko ƙofar ɗakinta bai kalla ba haka yafice daga cikin part ɗin nasu gaba ɗaya, direct ɓangaren Umminsa ya nufa.
Kusan karo sukayi da Hayatuddeen wanda ke ƙoƙarin zuwa part ɗin nasu, ƙiransa shida Zaleeha akan cewa suzo suyi break, don su atunaninsu zuwa lokacin ta dawo.
Duban Saifuddeen ɗin Hayatuddeen yayi, cikin ƙaunar Hamman nasa yace.
"Wow Hammana kaga yanda kayi kyau kuwa!."
Murmushi Saifuddeen yayi tare da duban Hayatuddeen, irin duban nan mai ɗauke da yanayin magana, alama yayi masa cewar.
"Uhummm ."
Kai Hayatuddeen yajinjina masa tare da cewa.
"Fiye da kullum ma kuwa, wani lokaci Hamma nakan tambayi kaina, me yasa kai ba mace ba amma kowani kaya kasa saikayi musu kyau, saidai kuma idan na tuna da cewa Hamman nawa Namijin gaske ne, sai naji kaina ya ƙara girma, saboda samun ka amatsayin Hamma yafiyemin komai."
Murmushin daya bayyana tsantsar kyawunsa yayi, cikin ƙaunar ɗan uwan nasa yasanya hannunsa inda yakamo kumatun Hayatuddeen ɗin.
Dariya Hayatuddeen yayi tare da zagawa bayan hamman nasa inda ya turosa zuwa cikin falon, da shigowarsa cikin falon har falon ya ɗauki ƙamshin oud ɗin dake jikinsa.
Har gaban dinning area Hayatuddeen ya tura hamman nasa, inda Raliya da kuma Ahmad ke zaune, Raliya ne ta gaishe da yayan nata, cikin ƙauna da kuma ganin ƙoƙarin ƴar uwar tasa na haɗa musu break fast kullum da takeyi ya amsa mata, yana tunanin gashi tasa an sallami mai akin wai duk a kanshi dan sun san yanada tsantsani.
Dai-dai lokacin Ummi ta fito daga cikin ɗaki, ganin Saifuddeen zaune yasa ta ƙara faɗaɗa fara'arta cikin kulawa tace.
"Kunfito ko, ina Zaleeha'n, nace yau itama tazo cikin mu tayi break dan duk anzama ɗaya."
Ummi taƙare maganar tana me jawo kujera ta zauna.
Kallon Hayatuddeen Saifuddeen yayi, cikin body language yayi masa alama kan cewar yaje ya ƙirawo Zaleeha'n, kai tsaye hayatuddeen ya tafi don ƙiranta.
Koda yaje part ɗin nasu, haka yayita knocking a ƙofarta, amma shiru, jin shiru ne yasashi tura ƙofar ɗakin ahankali, ɗan tsayawa yayi abakin ƙofa, da ɗan ƙarfi