Showing 33001 words to 36000 words out of 61846 words
Chapter 12 - Nakasa B Kasawaba Book 2 Complete Hausa Novel
dake kanta, al'ƙawarine saita wulaƙanta aurensa, sam bazata zauna da nakasashshe ba!.
Cike da tsananin tausayinta Maryam ta kamo hannunta, cikin yanayin sanyinta tace.
"Zaleeha ke ƙanwatace, jini ɗayane ke yawo ajikinmu, tabbas inason duk wani abun da kikeso, haka kuma inaƙin abunda kike ƙi, saidai kuma Saifuddeen ba abun ƙi bane, irin Saifuddeen mata da yawa ke fata da burin samu amatsayin miji, kada ki taɓa dubansa da nakasarsa, domin NAKASA BA KASAWA BACE, haka kuma nakasa bata zama ciwo matuƙar ba nakasar zuciya bace, tabbas ina tayaki farincikin samun Saifuddeen, saboda inaji ajikina ko anan gaba koda bayan raina nasan cewa ƙanwata tasamu managarcin mijin dazai zame mata garkuwa, na tabbata koda ace yau kowa namu zai ƙare abarki ke ɗaya, bani da kokonto akan saifuddeen saboda nasan zai riƙeki da amana, bakuma zai taɓa bari ki wulaƙanta ba, nasan ayanzu kina ganin laifin Baba dama su Ya Ahmad da Ya Ameenu saboda sun aura miki wanda bakyaso."
Ɗan tsagaitawa da maganan maryam tayi tare da sakin murmushi, ahankali ta cigaba inda tace.
"Watarana zakiyi alfahari da Baba Malam Zaleeha, zakuma kiji cewa yayi miki zaɓi irin wanda kowani uba ke fatan yiwa ƴarsa, tabbas nasani komin jimawa saikinyi al'fahari da zaɓin Baba Malam, sannan kuma kada kimanta cewar duk wanda yayi biyayya ga Iyayensa to har abada baya taɓa taɓewa."
Duk wannan maganganun da Maryam keyi Zaleeha bata buɗe idanunta ba haka kuma hawaye basu bar tsiyaya daga cikin idanun nata ba, zuciyarta tayi tauri, ɓacin rai ya cikata, tsana ƙiyayya masu tsanani, sun riga da sunyi tasiri acikin jikinta da ƙarfin sirin da Ruda ke zuƙa Mama suna banka mata, saboda haka babu wani magana daza a faɗa don atausasata da zaiyi aiki acikin ƙwaƙwalwa da zuciyarta, hasalima ji take kamar ana ƙara mata yawan tsanar Saifuddeen ɗinne.
Duban Rasheeda Aunty Lubna tayi cikin kulawa tace, "Rasheeda kiyi abun daya dace, tasamu tayi wanka bari naje nakawo kayan da zata sa."
"To" Rashida ta amsa zuciyarta cike da tausayin Zaleeha, saidai kuma ta wani ɓangare wautan Zaleeha kawai take gani.
Su Aunty lubna na fita, Rasheeda ta kamo Zaleeha, da ƙarfi Zaleeha ta fusge hannunta daga na Rashida, cikin yanayi na faɗa-faɗa zaleeha tace.
"kada ma kice zaki faɗamin komai Rashida, babu abun da zaki faɗa min wanda zan fahimta, sannan kowani kalma zaki faɗa, zakiyi asaran yawun bakinki ne kawai, dan koda wasa bazan taɓa ɗauka ba."
Murmushi Rashida tayi tabbas tasan Zaleehan tana cikin ɓacin rai da baƙinciki, hakan yasama bazata biyeta ba, tasan tanajin haushinta ne saboda tabawa Saifuddeen da abokansa haɗin kai wajen ganin antsara abubuwan biki sun tafi dai-dai.
Dawowar Aunty Lubna ne ta lallaɓa Zaleehan inda ta haɗa mata ruwan wanka, ko acikin toilet ɗin da ƙyar Zaleehan ta iyayin wanka, domin gaba ɗaya jikinta babu kuzari, tana fitowa daga wankan aunty lubna ta kamata inda ta zaunar da ita akan stull, da ƙyar ta iya shafawa jikinta mai, aunty lubna dakanta taɗanyi mata light meckup akan fuskarta kasancewar tasan ba isashshen lafiya bane da ita, yimata meckup me yawa kaman takurata ne, doguwar rigar bababar atamfar chiganvy me kalan ja aunty lubna ta bata tace ta sanya, kanta yafara ciwo sosai hakan yasa batayi musuba ta amsa, ta zura ajikinta, sosai ɗinkin rigar tayi kyau yayinda tabi jikinta ta lafe, rigar irin A shape dinnan ne me faffaɗan hannu, an ɗameta daga ƙirji zuwa ciki yayinda daga ƙasa kuma aka faɗaɗata, haka hannun rigar akayishi mai faɗi, sosai yayi wa Zaleehan kyau musamman ma idan ka haɗa da kalan atamfar da takasance ja mai ratsin green colour, dogon gashinta da akullum yake cikin gyara aunty lubna ta tubke mata shi akusan wuyanta, jan ribbom aka maƙala ajikin gashin, aunty lubna dakanta tayi mata ɗaurin ɗan kwali mai kyau, hakannema ya ƙara ƙawata shiganta, kama daga kan sarƙa ɗankunne, harma da awarwaro.duka na gold aka samata masu kyaun gaske, aunty lubna naƙoƙarin yafa mata mayafi ajikinta ta shagwaɓe fuska tare da turo baki, hawayene suka cika idanunta, ganin haka yasa Aunty lubna sakin murmushi tare da kamata ta kwantar da'ita akan gado, komawa aunty lubna tayi tasanarwa da ya Ahmad halin da Zaleehan ke ciki, nan take Ahmad yayiwa family doctor ɗinsu waya, babu ɓata lokaci kuwa sai gashi yazo, sanin cewa batason allura ne yasanya likitan bata magunguna bayan ya auna yanayin jikinnata, magunguna masu ƙarfi ya bata, tare da ɗaura mata drip, don kuwa shima zai taimaka wajen bata ƙarfin jiki da kuzari.
Ko mintuna 20 ba ayi da samata drip ɗinba bacci ya ɗauketa.
Acan gidansu Saifuddeen kuwa receiption aka gabatar me rai da lafiya inda akayi ɓarin nairori wajen ƙawata haɗaɗɗen abinci da drinks ɗin da akasha, bayan anci ansha ne kuma aka bawa kowa takeaway wanda ke ɗauke da kayan ciye ciye dana shaye-shaye, kowani ledan takeaway kaza ne guda aciki anyi raping ɗinta da poil paper abun dai sai wanda ya gani, nan fa Saifuddeen da abokansa suka shiga ɗaukan hotuna kala-kala, haka sukayita bidiri basu suka samu kansuba saida aka ƙira sallan azahar nanfa masu tafiya masallaci suka tafi masu tafiya gidama suka tafi, inda wasu sun koma gidane don suɗan huta kafun lokacin ɗauko amarya da kuma diner.
Gaba ɗaya gidan nasu Saifuddeen babu masaka tsinke, jama'ane takota ina, hatta ɓangaren saifuddeen dinma mutanene acikinsa maƙil.
Su Ahmad da ishaq ne suke zaune afalon sunata hiransu, wasu kuwa na kallo, kowadai da abunda yakeyi, Saifuddeen na cikinsu inda gaba ɗaya hankalinsa kekan laptop ɗinsa, da alamun wani aiki mai tsananin mahimmanci yakeyi, dan gaba ɗaya hankalinshi na kan System ɗin gaba ɗaya idanunshi sai yawo sukeyi a jikin fuskar laptop ɗin, ganin hayaninyar abokan nashi yayi yawa ne suna katse mishi hamzarine ya sashi sarrafa kekenshin ya shiga bedroom ɗinshi.
Abuja.
Kuka sosae Amina keyi hakan tatashi yau batajin daɗi wani irin abune takeji ya toshe mata maƙoshi, tabbas babu makawa tasan kishin Saifuddeen ne ke ɗawainiya da zuciyarta, har wani zafi zafi takeji aƙirjinta, tanason Saifuddeen so mai tarin yawa tana kuma kishinsa sosai, bata san dacewa soyayyar Saifuddeen yayi ƙarfi azuciyarta ba sai yau daya kasance ya auri wata ba'ita ba, ahankali take fitar da sautin kukanta, wayarta ta ɗaga tare da kunnawa, take hoton Saifuddeen wanda akayi masa ɗazu inda Hayatuddeen ya ɗaura a status ɗinsa ya bayyana akan fuskarta, don tuni ta sauƙe hoton zuwa wayanta, sosai yayi mata masifar kyau acikin farar shaddan dake jikinsa, fuskarsa ta ƙurawa ido, tabbas kowa yagansa yasan yanacikin matsanancin farinciki, rumtse idanunta tayi tare da sakin wasu zafafan hawaye, tabbas ta barwa Allah itakam, ta fawwala masa dukanin lamuranta, tasan zaiyi mata jagora, idan tana darai da kuma rabo tabbas tasan watarana zata mallaki saifuddeen amatsayin mijinta.
Kaduna, Asma'u Ahmad matawalle kuwa tun jinya da taga batun auren Saifuddeen sosai hankalinta ya tashi sai dai tasa a ranta babu wani na ƴa macen da zata hanata mallakar Saifuddeen a matsayin mijin aurenta, shiyasa daren jiya harda mafarkinta wai auren da ita aka ɗaura.
Ahmad ne yabi bayan Ishaq da ya shiga bedroom ɗin Saifuddeen, akan gado suka sameshi, yana zaune kana abokinshi Aziz Wanda ya kasance babban SS shima yana zaune gefenshi duk sun zubawa laptop ɗin idanu bisa dukkan alamu wani abun Saifuddeen ke nuna mishi, kana da alamun tashin hankali a fuskarsu.
Ahmad ne ya kalleshi da kyau kana ya zauna kan durowar gefen gadon,
ganin hakanne yasa Saifuddeen gyara zamanshi kana ya jingina bayanshi da kan allon gadon. Wayarshi ya ɗauka text ya turawa Umminshi cewa yana jin yunwa kuma ya gaji.
yana turawa ya ajiye wayar sannan ya ɗan miƙawa ishaq hannu suka yi irin gausuwarsu sanna ya kuma kalli Ahmad daketa mishi kallon tuhuma.
Da Sallama Ummi da Adda Rahma suka shigo falonshi dake cike da abokanshi gaisawa sukayi sannan suka wuce cikin uwar ɗakan,
yana ganin Umminshi ya ɗan kwaɓe fuska tare tanƙwashe kanshi bisa kafaɗunshi yayi rau-rau da manyan idanunshi da suke cike da tashin hankali da tarin gajiya,
da sauri Ummi ta zauna gefenshi,
murmushin jin daɗi yayi tare da raɓawa jikinta,
hannnta tasa kan goshinsa sai kuma tayi saurin sunkuyiwa ta leƙa fuskarsa tare da cewa.
"Meke damunka?." rumtse idonsa yayi da ƙarfi, sanna ya buɗesu,
Adda Rahma kuwa murmushi kawai taketayi a ranta take cewa.
"Hmmm shaleleln Ummi wannan ɗan shagwaɓan inaga randa duk ya kusanci matarma sai anyi jinya biyu mutun sam shi baya son wahala abu kaɗan sai yazo yayi ta narkewa Umminshi yana shogoɓa."
a fili kuwa ajiye kulolin abincin da suka kawo mishi tayi tare da zama ƙasa kan carpet ta kamo hannunshi alamun tausasawa,
sai kuma ta ɗan leƙo fuskar wayarshi da yake nunawa Ummi inda ya rubuta,
"Ummi sacemin ita akeson ayi, meyasa? me tayi musu? wayake shirya sacemin matata ranar da za'a kawo min ita gidana? me nayi musu?."
cikin kaɗuwa da tsoro Rahma ta mike tsaye tare da cewa.
"Su waye ne Saifuddeen meyasa zasu saceta?."
Ummi kuwa wani irin fargabane da tsoro ya rufeta jiki a mace ta kalli Ahmad da ishaq da Aziz ta musu bayanin abinda ya rubuta mata sosai Ishaq da Ahmad suka shiga ruɗani Aziz kuwa kai ya jinjina tare da cewa.
"To ai da sauƙi tunda mun gano shirinsu,
tun a zuwa ɗaurin aure Saifuddeen ya gano akwai baƙin ayarin motocin da suka shiga sahunmu kana ya ɗauki numbers ɗin motocin ya kuma bi diddigin inda aka sai motocin ashema a kamfanin Salisu ne, to yanzu bincike yazo mana da sauƙi dan Salisu ya bamu komai na masayin motocin harma da number wayarsa, shine ya bawa Saifuddeen damar bibibiyar kiran wayar dama motsinsu munji shirinsu na son sace Zaleeha."
wasu siraran hawayenesu ka zubowa Ummi murya a raunace tace .
"Aziz ku nemo hukuma a lamarin."
kai Saifuddeen ya jujjuya mata alamun a a,
shi kuwa aziz gyara zama yayi tare da cewa.
"Uhmmm Ummi kenan to ai su kansu Hukumar Saifuddeen ne idonsu, tunda duk wani tantirin daya gagaresu gane inda yake Saifuddeen suke miƙawa aikin bin diddiginshi ta na'ura mai ƙwoƙwalwa yake gano musu komai, to yake binciko tantiran da basu shafeshi bama bare wannan dake son sace mishi amarya, yanzu haka ya tsara komai ya kuma haɗe kiran wayar waɗancan da wayata, yanzu haka hatta motar da ya saya dan ɗauko amaryarshi suma sun sayi irinta, dan su samu damar sacetan, rashin sanin Saifuddeen yana ɗaya daga cikin tawagar UPSC, ne ya sasuyin wannan gangancin."
Adda Rahma kam gaba ɗaya hankaƙinta ya tashi, sai dai ganin yadda Saifuddeen ke basu ƙarfin guiwa yasa hankalinsu ya ɗan konta, Adda Rahman ne ta kalli Aziz tare da cewa.
"Wacce tawaga ce kuma UPSC?."
Cikin fidda nufashi yace.
"Ma'ana tawagar Union public service commission! sai dai sirrance yake musu aikin, ƙarƙashin jagorancin DSS."
Jinjina kai Adda Rahma tayi dan ta fahimci sirri Saifuddeen ke yi wanda ba'a cika son mutane su saniba, duk da sunsan yana tare da DSS amman basuyi zaton matsayin aikinshi ya kai nan ba.
nan suka ɗan sashi yaci abinci sannan suka fita suka tafi.
Ƙarfe 4 dai-dai kamar yanda al'adan gombawa takasance da yamma suke ɗauko aure kuma hakan ya samu asaline tun lokacin da ƙungiyar ƴan kalare suka fare da sace amare in za'a kaisu gidajen aurensu da dare shiyasa aka dawo da al'adar garin kai amarya gidanta da yamma ido na ganin idop.
Hakan yasa gaba ɗaya abokan saifuddeen sun shirya tsab don zuwa ɗauko amaryarsu, motoci ne masu uban yawa suka tanada don zuwa ɗauko auren, tuni su Ahmad, Ishaq, Salisu, Wareesu, Saminu, Mudassir, Jabeer, Hisham, ibrahim, Rabi'u, Aziz, Aryan, Gaddafi,duk sun kammala komai, kowa yasanja shiga irin ta alfarma.
Ahankali Saifuddeen yake tuƙa kekensa, har ya ƙaraso harabar gidan, sanye yake da ɗanyar shadda blue mai masifar kyau, sai shinning take yayi kyau matuƙa, saidai awannna karon baisanya gareba, hasalima rigar half jumper ce, su Adda Rahama da suka fito don zuwa ɗauko aure tana ganin ƙaninnata taƙarasa garesa da sauri, yanaganinta ya sakar mata murmushi tare da shagwaɓe mata fuska kaman wanda zaiyi kuka, murmushi Adda Rahama tayi tare da ƙarasowa ta shafa gefen fuskarsa, cike da ƙaunarsa tace.
"To sakalallen Ummi na farko yanda naga ka shagwaɓe fuskarnan so kake kace kagaji ko? ehem ai duk wata shagwaɓa Hayatuddeen awajenka ya koyota."
Murmushin daya bayyana fararen haƙwaransa yayi tare da ɗan lumshe idanunsa, hannunta ya kama inda ya ɗaura adai-dai saitin heart ɗinsa, dariya me haɗe da murmushi tayi, cikin jin daɗi ta dubesa inda tace.
"Kamar yanda kake cikin farinciki Saifuddeen haka muma muke, farincikinmu nayau bazai misaltuba angon Zaleeha!."
Yanzunkam dariya sosai Saifuddeen ɗin keyi saidai babu sauti, sosai maganan addan nasa tafaranta ransa, ganin yanda yake dariya yasa Adda Rahama lumshe idanunta tana mejin daɗi acikin ranta, ita da kanta takoma bayansa inda ahankali take ɗan tura kekennasa, harsuka ƙarasa gaban wata hamshaƙiyar ƙatuwar mercedess benz 2019 mai azabar kyau da tsada, sabuwace dal sai shinning take tana ɗauke ido, shida kansa ya shiga motar kamar yanda ya saba, inda Ahmad ya naɗe kekensa ya tura masa cikin both, nanfa kowa yashiga mota, inda ƴan ɗauko amarya ma suka shiga tasu motar, ajere haka motoci ashirin da shidan ke tafiyan gwano akan babban titin, kasancewar Gombe akwai manyan tituna sannan kokusa babu ƙazanta akan gaba ɗaya titunansu, cikin motoci ashirin da shidan nan tsakiyarsu ta Saifuddeen take wanda cikintane za a ɗauko amarya.
Tunda ta kwanta bacci ba ita ta tashiba sai 3:40 cikin ikon Allah kuwa jikinnata yayi sauƙi sosai don koda tatashi babu abun da takeji, don taɗan samu kuzari ajikinta, still Aunty Lubna da Maryam da Aunty Shatu ne suka tsaya kaida fata inda sukaga tasake sabon wanka, to fa yanzukam meckup aka tsantsara afuskartata ta musamman, kayan da tasa kuwa ya banbanta dana ɗazu, duk da kasancewarsu duka dogin riguna ne, saidai wannan na wani tsadadden shadda lace ne me matsifar kyau, shima ɗindai akwai ratsin ja ajikinsa, sosai yayi bala'in yi mata kyau, ɗauri ɗankwali aka zizara mata tare da yane mata jiki da babban mayafi, wasu tsadaddun sarka da ɗan kunne aka sanya mata, turare kuwa kusan ma wanka akayi mata dashi, don wani irin masifaffen ƙamshi take.
Gefe kuwa Rashida da Balkeesu ne zaune, balkeesu sai washe haƙoran munafurci take, yayinda take ta saƙa sharri acikin zuciyarta, bakomai yasama tazo ɗaukan auren ba face matsanancin gulma dake cinta tana son taje taga gidan kurma gurgun tunda Mama ta hanasu ganin kayan auren kam.
Cikin nutsuwa tarin motocin suka ƙaraso ƙofar gidan nasu Zaleeha, su Adda Rahama waƴanda sune zasu shiga gidan don fito da amarya suka fiffito, kaitsaye suka nufi cikin gidan.
Shi kuwa Saifuddeen ido ya ɗan lumshe tare da yin murmushi ganin wata benzz irin tasa tazo kusa dashi ta tsaya kana yaga a ƙalla yanzu motocin sun kai talatin banda guda biyar wanda sukazo suka samu a cikin ƙaton harabar gidan duk da girman wurin saida ya tsuke ya musu kaɗan wata motar har tana gogar wata, lips ɗinshi ya ɗan lasa gano harda motocin masu sun sace Zaleeha ne a wurin.
A cikin gida kuwa Aunty Lubna ce ta shiryata tsab inda ta rufe mata fuskarta da mayafin laffaya mai tsananin tsada da ƙyalli dake jikinta, Goggo Maryama ƙanwar Baba malam da Aunty Aisha ƙanwar Mama ce suka kamata harzuwa falon Baba Malam, inda Ya Ahamd, Ya Aminu, Malam Adam harma da Mamy ke zaune, nasiha sosai Baba Malam da yayunnata sukayi mata, inda suka gargaɗeta sosai akan zaman auren nata, nasiha sukayi mata irin mai ratsa zuciya da jiki, nasihace irin wanda ke nutsar da duk wata ƴa mace, saidai kuma ko kaɗan Zaleeha babu abu ɗaya data ɗauka daga cikin nasihartasu, hasalima kukan baƙinciki kawai takeyi, sukuma take suka cika da tausayinta domin kuwa duk atunaninsu nasihar tasuce ta tsumata har take kuka.
Ganin kukan nata yaƙarune yasanya Aunty Aisha da goggonta ƙanwar Baba Malam suka kamata, domin kuwa tuni Maryam itama tasa kukan rabuwa da ƴar uwartata, haka Zaleeha take kuka sosai, yayinda ayanzu take kukan mai dalilai biyu, dalilin farko shine auren ta da aka ɗaura da wanda bataso, dalili na biyu kuwa shine dalilin dake sa ko wacce amarya kuka da zubda ƙolla tanajin bege da kewa da zafin barin gidannasu da zatayi, tabbas tasan zatayi matsanancin kewar yayu da ƴan uwanta, hakanan takejin duk ba daɗi, haka Aunty Lubna da Goggo suka riƙota har zuwa compound ɗin gidan, kuka take sosai, tanamejin tsananin baƙinciki aranta don kuwa kowani taku ɗaya da zatayi zuciyarta tafasa takeyi, yayinda wani irin malolon baƙin ciki ke cika zuciyarta, sosai takejin takaicin kaita gidan Saifuddeen da za'ayi.
Haka suka nufi wajen motocin tare da tarin zugar ƴan rakiyar amarya wanda dama tuntuni su ake jira, Balkisu da Rasheeda ne tafe wanda dama mota ɗaya sukeson shiga da amarya, babuma kamar balkeesu don ita da biyu ma takeson zama kusa da Zaleehan, dan so take taƙara zugata sosae.
a cikin motocin kuwa text Saifuddeen ya turawa Aziz na numbers ɗin motocin da suke zargi,
amsa ya tura mishi da cewa.
"Ba matsala duk nabisu na sace iskar tayun bayansu, sai ta motar dake kusa damu nan na barta amman naja tamu mutar na matsesu basuma da damar motsawa, na kuma gayawa Ahmad ya fito cikin motar taku yayiwa amarya jagora ,zakaga gefen hagu da daman ku akwai mata uku uku sojojine cikin farin kaya."
murmushi mai cike da nasara Saifuddeen yayi.
Shi kuwa Ahmad yana ganin fitowarsu yayi saurin ƙarasawa garesu, shiyayi musu jagora zuwa motar da za'a sanya amarya wato wanda Saifuddeen ke ciki, shida kansa Ahmad ya buɗe mata ƙofar motar, Aunty Lubna ne ta sata cikin motar, ganin Saifuddeen zaune acikin motar yayinda hankalinsa gaba ɗaya kekan laptop ɗinsa, yasanyata sakin murmushi, lallai tajinjinawa ƙauna irin na Saifuddeen da sauri ta kamo hannun goggo Maryama dake shirin shiga tace.
"Tsaya Goggo angon yana ciki, shi yazo ɗaukan amaryarshi da kanshi."
Ahmad ne ya ɗanyi murmushi tare da cewa.
"Sabida tsarone babbar yaya ba don tsoro ba."
dariya sukayi cikin happy Balkeesu ne tay kamar bata jisuba tasoma ƙoƙarin shiga motar, da sauri ta ɗan dawo da baya ganin Saifuddeen hakimce acikin motar haibarsa da kimarsa da kwarjinta sun bugi zuciyarta shakkarshi mai yawa ta rufeta, bisa ɗole taja da baya,
Ya Ahmad da Adda Maryam ma dake gefensu murmushin jin daɗi