Showing 39001 words to 42000 words out of 61846 words
Chapter 14 - Nakasa B Kasawaba Book 2 Complete Hausa Novel
yace.
"Aunty Zaleeha kizo muyi break, kin san dai bana iya jure yunwa."
Jin shiru ba'a amsa shi bane yasanyashi ƙara kutsa kansa cikin ɗakin, nan yashiga dube dube kozai ganta amma shiru, kasa kunnensa yayi wai ko zaiji motsin ruwa a toilet, nan ma dai shiru, hakan yasashi juyawa kawai yafice daga ɓangaren nasu gaba ɗaya.
Yana komawa yace musu baiganta ba, har ɗakinta ya shiga amma bakowa ciki, fuska ɗauke da mamaki Saifuddeen ke kallonsa, to ina Zaleeha zata je kenan, kallon Ahmad yayi wanda yake ƙoƙarin saving ɗin kanshi, yana cewa.
"Maybe bata dawo daga fitan da tayi bane."
Gane abun da Ahmad ɗin ya faɗa ne, yasa shi ɗan lumshe idanunsa, Ummi ne ta dubesa, cikin kulawa tace.
"Dama kasan da fitarta ne? dan Ahmad yace yaga fitanta tun da sanyin safiya koma ince asuba."
Idanunsa ya rumtse tare da girgizawa Ummi'n kai, alaman "A'a." ɗan jim Ummi tayi take kuma, wani tunani yazo mata inda ta raya aranta cewa ko gida Zaleehan taje, nan dai tace tasan cewa zuwa anjima zata dawo.
Raliya ne tayi saving ɗinsu inda suka soma cin abinci cikin nutsuwa, shidai Ahmad hakanan jikinsa ya basa wani abu daban, yasan babu dalilin da zai kai Zaleeha gida awannan sanyin safiyan, idan da ace akwai dalilin ma to tabbas yasan da zuwa yanzu ansanar dasu.
Haka suka kammala break fast ɗin nasu cikin nutsuwa, Ahmad ne ya miƙe dan yana so yaɗan fita, shikuwa Saifuddeen cikin falon na Umminsa ya koma, inda ya sauƙa daga kan kekensa, kwanciya yayi akan doguwar kujera tare da jawo laptop ɗinsa, ya ɗaura akan cikinsa, nan ya buɗe cikin nutsuwa yashiga yawo a internet, Hayatuddeen ma zama yayi akusa da hamman nasa inda ya jona game a tv plasma ɗin dake cikin falon, hakan yasa kowa da inda ya bada hankalinsa, Ummi kuwa ɗaki ta koma dan tanason kimtsa wasu kayyakin gudumowan biki da aka kawo mata, nan Raliya ta bita inda suka shiga aikin tare.
Sosai yabada hankalinsa akan aikin da yakeyi, hakanne ma yasa har lokuta suka ja batare daya sani ba, inda Hayatuddeen kuwa tuni ya kwanta akan carpet yayinda bacci ya ɗaukesa, da dukkan alama jiya kusan kwana yayi yana chat, don abu ɗaya ne ke saka Hayatuddeen bacci da rana, shine idan bai samu enough bacci da dare ba, to dole da rana zaiyi bacci, wai abun ma yazo masa da sauƙi don yau basu da lectures sai ƙarfe 2:00 pm, shi yasama yaji gwamma yayi baccinsa, kafun time ɗin.
Ummi ne tafito daga cikin ɗakinta, duban Saifuddeen tayi, ganin kaman baisan da zuwanta ba yasa ta shafi gashin kansa, ɗago da kansa yayi inda ya dubeta, ganin Umminsa ya sashi narke fuska, akasalance yayi mata alaman sannu da fitowa, hakanan yake aduk sanda zaiga Umminsa, to fa raki da shagwaɓa kawai zai dinga yi mata, wani lokaci ko Hayatuddeen bai kai Saifuddeen yawan shagwaɓa ba.
Kansa Ummi ta shafa, cikin kulawa tace.
"Inajin gabana yana ɗan faɗuwa tun ɗazu, ya kamata kaje ka duba Zaleeha kota dawo."
Fuskansa yaɗan kwaɓe, tare da tashi zaune miƙa yayi inda yayiwa Ummin alaman cewa ya gaji, murmushi kawai Ummi tayi tare da ƙwala ƙiran Raliya, wanda ta shiga kitchine don ɗaura musu lunch, don a time ɗin kusan ƙarfe ɗaya ake nema.
koda Raliya'n tazo, cewa da ita Ummi tayi, taje ta duba part ɗin nasu Saifuddeen ko Zaleeha ta dawo.
Da "To." Kawai Raliya ta amsa, nan tafice daga cikin falon, koda taje part ɗin, haka tayi ta kwaɗa sallama amma shiru ba amsa, alaman bata dawo ba kenan, haka ta fito daga falon, koda ta kawo compound ɗin gidan, parking space ɗinsu ta duba, nan taga babu motar Zaleeha'n, alaman kenan bata dawo ɗin ba, nan ta koma inda ta faɗawa Ummi cewa "Zaleehan bata dawo ba."
Ɗan jim Ummi tayi nan tace.
"To bari dai zuwa yamma, idan bata dawo ba sai muƙira gidansu mu tambaya, ko wani abunne ya faru."
Shidai Saifuddeen ƙala baice ba, saboda ae Zaleehan bata maidashi miji ba, because da zata fita kanta tsaye ta fita, babu neman izini ba komai, wannan yasa shima bazai shiga cikin shirgin nemanta ba, sauƙa daga kan kujeran ma yayi, inda ya hau kan wheelchair ɗinsa, da kansa ya tashi Hayatuddeen, inda yace yaje ya ɗauro alwala yazo su wuce masallaci, don yin sallan Azahar, part ɗinsu yaje inda yayi alwala, koda yafito yasamu Hayatuddeen tsaye nan suka wuce masallacin dake kusa dasu.
Ummi kam dai hakanan takejin wani abu dangane da tafiyan Zaleehan, sosai take fargaban abun da zuciyarta ke raya mata, aranta tana fatan ma Allah yasa ba hakan bane.
Saifuddeen kuwa koda suka dawo masallaci, part ɗinsu ya nufa, nan ya nufi bedroom ɗinsa, inda ya kwanta ya ɗan huta.
Abu kamar wasa tun ana ƙarfe ɗaya, biyu, uku, har zuwa ƙarfe huɗun yamma babu Zaleeha babu alamarta, sannan daga gidansu ba'a ƙira ance tana can ba, abun da yayi mugun ɗaga hankalin Ummi kenan, nan tatura akayi mata ƙiran Saifuddeen, zuwa yanzu yasake wanka cikin wasu tsadaddun riga da wandon jeans masu kalar navy blue, sosai sukayi masa kyau.
Dubansa Ummi tayi cikin nuna damuwarta afili tace.
"Gabana faɗuwa yake Saifuddeen, har yanzu fa Zaleeha bata dawo ba, kuma kace bata sanar dakai fitan ta ba."
Kansa ya jinjinawa Ummin tare da kamo hannunta, cikin kulawa yayi mata alama da body language ɗinsa, kan cewar.
"Kada ta damu Zaleehan zata dawo ne, wata ƙila tayi nisan zango ne."
Girgiza kai Ummi tayi cikin kulawa tace.
"Bari dai naƙira gidan nasu naji, ace mutum ya fita tun gari bai gama haske ba, kuma ace har yanzu kusan ƙarfe 5 ake nema amma baidawo ba."
Nan Ummi ta ɗauki wayarta, inda ta danna wa number'n Mamy ƙira, don duk gidan number'n mamy kaɗai take dashi.
Bugu biyu aka ɗauki ƙiran, amutunce suka gaisa da Mamyn, cikin nutsuwa Ummi tace.
"Dama cewa zanyi ko Zaleeha na gidan naku ne, tun safe ta fita kuma shine har yanzu munji shiru bata dawo ba."
Gaban Mamy ne ya faɗi, cikin yanayin mamaki tace.
"Tun safe kuma, to ina take kenan don dai kam batazo gidan nan ba yau."
Zuciyar Ummi ne ya tsinke cikin muryar damuwa tace.
"Nima fargaba ne ya isheni shiyasa nace kawai bara naƙira na tambaya, indai ko bata gida to ina taje kenan, tunfa gari baigama haske ba ta fice."
Cikin mamaki haɗi da fargaba Mamy tace.
"Bakomai ku kwantar da hankalin ku, bari na shiga can ɓangaren mahaifiyarta ta saina tambaya kota zo, sannan zan faɗawa Baban nata ma, duk yanda ake ciki zaku jini."
Nan Ummi tayi mata godiya, daga haka ta aje wayar, kallon fuskar Ummi kaɗai Saifuddeen yayi, ya fuskanci cewa akwai damuwa.
Mamy kuwa ko aje wayar batayi ba ta nufi ɓangaren Mama, da sallama ɗauke abakinta ta kutsa cikin falon Mama'n, Zaheera dake kwance tana kallo ne ta amsawa Mamy'n, dubanta Mamy tayi tare da cewa.
"Zaheera ina maman taku."
Zaheera bata kai ga cewa komai ba, saiga Mama tafito daga cikin kitchine, duban Mama Mamy tayi cikin nutsuwa tace.
"Halima yanzun mahaifiyar Saifuddeen taƙirani, wai tun safe Zaleeha tabar gida kuma har yanzu bata koma ba, shine take tambaya ko nan tazo, nace da ita a'a, saidai kuma bansani ba ko tazo yau ɗin, naji ma kamar hankalinsu atashe yake, kuma gashi naga bata nan ɗin ma, ina Zaleeha tashiga kenan?."
Mamy ta tambaya cikin yanayin damuwa.
Tsuka Mama tayi tare da turo ɗan kwalinta gaba, cikin halin ko inkula tace.
"Wani daga cikin ku yabani ajiyar Zaleeha ne da zakizo kina tambaya ta, ko kuwa idan tazo nan ɗin goyata zanyi abayana na kaita ɗaki na ɓoyeta, kwaje can kunemeta nikam banganta ba!." Mama taƙare maganar tana me yatsuna fuska.
Shiru Mamy tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, ahankali tace.
"Allah ya huci zuciyarki."
Bata jirayi me maman zata ce ba, ta juya tabar falon.
Ƙwafa Mama tayi tare da jijjiga kanta, cikin yanayin mugunta tace.
"Gaba ɗayanku zaku sani ne, kuma ku sani, wallahi ƴata tagama zama da nakasashshe ehe."
Daga ɓangaren na Mama kai tsaye Mamy wajen Baba Malam ta nufa, tana shiga kuwa ta iskesa zaune shida Habu da kuma Ameenu, cikin nutsuwa Mamyn ta sanarwa Baba Malam abun dake faruwa, nan take Baba Malam yaji zuciyarsa tayi wani irin bugawa, gyara zamansa yayi tare da fuskantar Mamy'n cikin, nuna damuwa yace.
"Zaleeha bata gidan mijinta kuma, to ina tashiga?."
Rumtse idanunsa yayi, tare da ambatan sunan ALLAH Acikin ransa, haƙiƙa Zaleeha kyautace daga wajen Allah, amma sosai lamuranta ke caza masa ƙwaƙwalwa, sam batajin magana ko kaɗan ta bambanta da Maryam.
Ya Ameenu kuwa wani irin baƙin cikin Zaleehan ne ya turnuƙesa, shikam tun ba yauba ya gane cewa iskanci Zaleehan keji dashi, yayi rantsuwa kuma saiya sauƙe mata, guguwar dake kanta, burinta kullum shine tajawo musu abun faɗa, so take ta ɓata musu suna, ta kuma ɓatawa Baba Malam halin dattakon sa.
Ya Habu ne yace.
"To yanzun ina taje?."
"Sai Allah!." Mamy ta faɗa asanyaye.
Nan take Ya Habu ya ɗauki wayarsa, inda yasoma ƙiran ƴan uwansu na kusa ko Zaleehan taje, amma babu wanda yace tazo.
Ya Ameenu ne ya ƙira Maryam awaya inda ya tambayeta ko Zaleehan tazo bayan fitowan sa daga gida, cikin tsananin tashin hankali Maryam tace masa bata zoba.
Baba Malam da kansa ya ɗauki wayarsa inda ya dannawa ƙanwarsa, wato Goggo Maryama ƙira, nan ma cewa tayi sam Zaleehan bata zoba, haka Ya Habu da Ya Ameenu suka dinga ƙiran layukan ƴan uwa da kuma abokai na kusa, waƴanda suke tsammanin cewa Zaleehan zata iya zuwa, amma babu wanda yace tazo, ko labarinta ma babu wani wanda yace yaji.
Take Ya Ameenu ya danna ƙiran Lambarta, haka wayar tayita ringing har ta katse, no answer, sake dialing yayi, still har ƙiran yasake katsewa ba a ɗauka ba, saida yayi mata 4 missed calls, amma duka no answer, Ya Habu ne shima yaƙira layin nata, nan ma bata ɗauka ba, sau 5 yana ƙira amma shima bata ɗauka, Baba Malam ne dakansa ya laluɓo lambar tata, nan ya danna mata ƙira, saidai shima kamar sauran haka har ya katse no answer, nan fa akeyinta ran Ya Ameenu idan yakai million to saida ya ɓaci, take yasoma sakin huci, yayin da yakejin wani ɗaci aransa, har wacece Zaleeha da baba Malam zaiyi mata 2 missed call amma bazata ɗaga ba, lallai idan ya kama Zaleeha, saiya rabata gida biyu.
Ganin duk bata ɗauki wayansu bane, yasa Mamy ta ƙirata da layinta, duk dai abu ɗayane bata ɗagawa, nan hankalin Mamy yatashi, take tsoro ya shigeta, nan ta fara tunanin ko Zaleehan bata lafiya ne.
Ya Ameenu ne ya kirata da sabon SIM ɗinsa, inda ya sake dialing number'n Zaleeha'n, shi ɗin ma dai batai picking ba, maida wayarsa cikin alj'ihu yayi, inda ransa ke ƙara tsuma yana ɓaci.
Baba Malam ne ya dubi Ya Ameenu, nan yace.
"Yaje gidan su Saifuddeen ɗin, don sanar dasu halin da ake ciki, idan kuma yasamu Zaleehan ta dawo, to ya basa umarni ya tattakata yayi mata duka irin wanda sai ta kasa tashi, sannan kuma ta faɗa masa gidan ubanwa taje."
Nan Ya Ameenu ya miƙe, haka ya fita yana huci don cika umarnin Baba Malam ɗin.
Acan gidan su Saifuddeen kuwa, sosai Ummi ta ɗaga hankalinta, tabbas tasan zuwa yanzu rashin dawowan na Zaleeha ba lafiya ba, ita da Raliya harma da Hayatuddeen gaba ɗaya hankalinsu atashe yake, Adda Rahma wanda itama yanzu zuwanta, jin labarin rashin ganin Zaleeha'n , sosai ya tashi hankalinta.
Saifuddeen kuwa yana zaune afalon, laptop ɗinsa yake ta dannawa, sam baikula da harkan neman Zaleehan ba domin duk wani motsinta afa tafin hannunshi take yasan muddin ya maida na'urarshi kanta bata da mafakar da zata shiga ya gaza ganewa.
Zuwan Ya Ameenu ne ya ƙara tada hankalin su Ummi, nanfa abu kamar wasa ya zama gaske, sosai aka shiga neman Zaleeha amma kamar ɓatan laya babu ita babu alamanta, Ahmad da Ya Ameenu ne suka shiga mota, inda suka soma zaga gari nemanta, har gidansu Rasheeda da Bilkeesu sunje, amma sun shaida cewa basu ganta ba, nan Ya Ameenu yasa Ahmad dake driving suka nufi family hause ɗinsu, wato gidansu Ya Ameenun kenan, nan ma dai bata nan, gaba ɗaya ƙanne da yayyan Ya Ameenun saida yaƙirasu ko Zaleehan tazo amma haka suke cewa bata zoba, sosai hankalin familyn ya tashi, Zakariyya da Ziyada kuwa da labarin neman Zaleehan ya iskesu, haka suka shiga damuwa sosai, Hajja kuwa take tasoma kuka, abunka da tsufa, dama kuka baiwa tsofi wahala.
Gaba ɗaya ran Ya Ameenu yasake ɓaci, domin sosai shida Ahmad sukayi buji-buji dasu wajen neman Zaleehan, gashi yanzu har ƙarfe goman dare kenan amma babu ita babu alamanta, still wani abun baƙin cikin kuma shine idan anƙira wayarta bata picking, koda kuwa za'ai mata ƙira ashirin ne bazata ɗaga ba, wannan dalilin yasa ran Ya Ameenu dana Baba Malam ƙara ɓaci, can gidan su Saifuddeen kuwa, sosai ɓatan Zaleehan ya ƙiɗima Ummi da su Raliya, Saifuddeen kuwa, ganin yanda hankalin Umminsa ya tashi sosai ne, yasan yashi barin sashin na Ummi gaba ɗaya, part ɗinsu ya koma inda ya kwanta yayi shiru, sosai al'amarin Zaleeha ke ƙona masa rai wani lokaci, sai dai yayi rantsuwa bazai taɓa bari sha'anin haukanta ya damesa ba, wani abu can daban bai damesa ba, saboda haka haukan guduwanta bazai taɓa damunsa ba, yasani koma tana inane to ita takai kanta, sannan kuma ita ta zaɓa, abinda dai ya sani yasa a ransa ta boni da aurensa dan babu saki a tsarin rayuwarsa ta gama guje-gujenta aurensu takalmin kazane mutu ka raba ya rantse wa ransa ko shekara 30 zatayi bata dawoba ba saki ta shiga ukunta dashi dan babu ita babu wanda take cewa tana son.
Can gidan Baba Malam kuwa, sawa yayi aka ƙira masa Mama, cikin tsananin ɓacin rai ya dubeta, ransa nayi masa suya yace.
"Zaleeha tabar gidan mijinta tun asuba, sannan har yanzu bata dawo ba, an kuma nemeta an rasa, tabbas nasan cewa kome Zaleeha ta aikata da sa hannunki, saboda haka ina kika kaita kika ɓoyeta?."
Yaƙare maganar murya a kausashe.
Ihu Mama tasanya tare da zamowa ƙasa ta zauna daɓas, hannu tasa aka, cikin ɗaga murya tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! wayyo Allah na, shikenan kun cuceni kun halakarmin da ƴata, shikenan abun danake gudu shiya faru, baƙin cikinku yasa ta gudu, wayyo Allah na!!."
Mama taƙare maganar tana me rushewa da kuka, kuka sosai take tana faɗin,
"Shikenan kun cuceni, kun rabani da ƴata, wayyo Allah Zaleeha na!."
Kallon takaici Baba Malam yayi mata tare da girgiza kansa kawai, nan ya wuce zuwa ɗakinsa, don baida wadataccen lokacin da zai tsaya sauraran ihun Mama'n.
Ganin Baba Malam ya wuce ɗaki, sannan Mamy da Habu sun fice daga falon ne, yasa Mama saurin tashi, cikin matsanancin farinciki tayi juyi, fes takejin zuciyarta, nan ta sake sakin kukan ƙarya, haka tafita daga falon na Baba Malam tana ta faɗin, cewa sun cuceta, tare da cewa lallai su nemo mata ƴarta duk inda ta shiga ta fita.
Awannan rana kuwa har ƙarfe 2 na dare babu wanda ya rumtsa acikin waƴannan gidaje guda biyu, Mama kuwa da gangan tahana idanunta bacci, hakanan taketa kukan cewa ane mo mata Zaleeha'nta.
Saifuddeen kuwa, damuwar dayaga Umminsa aciki ne kawai ya hanasa bacci, sosai yayi ƙoƙari wajen bawa Ummin nasa baki, amma ina Ummi har ƙwalla saida ta zubar, musamman ma idan ta tuna da cewa, basu san wani hali Zaleehan ke ciki ba, shi kuwa Saifuddeen tsab yaga text ɗin da Zaleeha ta turawa ƙawarta Bilkeesu cewa ta gudu, sabida ya haɗe kan wayar Zaleeha da tasa duk abinda zatayi zai gani kuna zaiji, to dai har yanzu baiga ko ji ga inda ta nufaba.
Ɓangaren Baba Malam kuwa, baƙin ciki da ɓacin rai ne suka hanasa bacci, tabbas yaji ajikinsa cewa, ba ƴan kidnappers ko wasu mutanen bane suka kama Zaleehan ba, hakanan yaji ajikinsa cewa, guduwa kawai tayi don nuna masa cewa bai isa da ita ba, sannan tayi hakanne don ƙara masa damuwa, sannan ta kuma watsar masa da mutumcinsa a idanun jama'a.
Ya Ameenu kuwa tsananin takaicin Zaleehan ne ya hanasa bacci, yayinda Maryam kuwa ke kuka wiwi, rarrashin duniya yayi mata amma takasa daina kuka.
Ya Ahmad ma da ba'a gari yake bama, yanacan Abuja saida yakasa rumtsawa, wani irin babban tashin hankali yasamu kansa aciki lokacin da aka faɗa masa, haka ma Aunty Lubna, sosai hankalin Ya Ahmad ya tashi, don yasan cewa Baba Malam zaisanya damuwar acikin ransa, ko kaɗan kuma baya ƙaunar abun da zai taɓa mahaifinsu.
Haka dai gaba ɗaya ahlin gidaje biyun nan sukayi kwanan zaune, dasu da kuma duk wani danginsu na kusa, washe gari kuwa da sassafe Ya Ameenu da Ya Habu suka sake bazama neman Zaleeha.
Inda Ahmad ma yashiga cikinsu,suka shiga nemanta tare.
Baba Malam kuwa da sassafe ya shirya, inda ya nufi Dukku, dan zuciyarsa na raya masa cewa ko can taje.
Haka su Ya Ameenu suka ƙarishe yawonsu amma babu Zaleeha babu alamarta, nan Ya Habu ya shiga motarsa, kai tsaye ya nufi Ɓilliri, wajen dangin mahaifiyarsu, koda zai sameta acan, amma koda yaje haka yagama shan wahala, ko ina yaje, sai suce bata zoba.
Baban Mama kuwa ranshi yayi masifar ɓaci duk da kasan cewarshi kafuri baiji daɗin abinda Zaleeha ta aikataba, koda yake ya zargi ƴarsane a lamarin, dan a zahiri ta nuna mishi bata son auren.
Can Dukku kuwa Baba Malam babu inda baije duba Zaleeha'n ba, kama daga gidajen ƴan uwa da abokan arziki, duk yaje amma babu ita ba labarinta, sosai hankalinsa ya tashi, nan take yaji wani ciwon kai mai zafi ya rufesa, alaman cewa jininsa ne keson hawa, don dama yana da ciwon hawan jini.
Ya Ahmad kuwa tuni ya biyo jirgi shida Aunty Lubna, inda suka dira acikin garin Gombe, sosai hankalinsa ya ƙara tashi ganin cewa har yanzu ba'aga Zaleehan ba, ƙira kuwa yayi mata yafi sau hamsin amma bata ɗagawa ba, wannan abun shiya ƙara jefasa acikin tashin hankali.
Ɓangaren Zaleeha kuwa tun da ta ɗauki hanya bata tsaya ba harsaida tasamu kanta acikin garin Numan na Adamawa yola, gaba ɗaya ƙiran da akeyi mata akan idanunta, amma zuciyarta tayi wani irin nauyi wanda batajin zata iya ɗaga ƙiran kowa, sannan kuma batajin cewa zata kashe wayarta.
Hamdala taketayi a ranta tanaga ta tsira daga farmakin Saifuddeen, dan yayi masifar razanata da bata tsoro jiya