Showing 54001 words to 57000 words out of 61846 words
Chapter 19 - Nakasa B Kasawaba Book 2 Complete Hausa Novel
Dada ma ɗakin Ummi ta wuce don hutawa, shi kuwa Hayatuddeen sama ya haura, yana shiga ɗakinsa ya jawo wayarsa, data ya kunna sannan yashiga cikin Whatsapp ɗinsa. Nan ya iske saƙon Ameena. Inda tace.
"Hey ƙanina." Ganin tana online yasashi sakin murmushi, nan yayi mata reply da cewa.
"Sannu me wayo, wato kinma fara ƙirana da ƙaninki ko, saboda kinsan kinyi nasara, zaki auri handsome ɗin Hammana."
Ameena dake kwance ganin saƙon Hayatuddeen din yasa ta saki murmushi, harda dariya. Cikin kulawa tace.
"Dama na faɗa maka ae watarana insha Allah zan zama auntynka saboda haka biyayya dole."
Koda Hayatuddeen yagama karanta saƙon dariya sosai yayi, nan dai ya tsaya suka ɗan taɓa hira da Ameenan, daga ƙarshe ganin ta sauƙa online, yasashi maida hankalinsa wajen chatting da abokansa.
Yau kwana Uku kenan dakai lefen Ameena, har zuwa yau kuwa ko da sau ɗaya ne Saifuddeen bai taɓa tura mata saƙo ba, harkokin gabansa ma yake, yayinda ya watsar da batun auren acikin ransa. Inda yanzu auren ya kama saura kwana takwas kacal, domin dasa lokacin auren zuwa yanzu anci kwana shida acikin kwanakin bikin.
Adda Rahama da kanta taƙirayi Ummi inda tace ta tambayi Saifuddeen, ko yayi mgna da Ameena'n, sai alokacinne ma Ummi ta farga.
Aikuwa tana aje wayan, ta dubi Hayatuddeen dake kwance akan doguwar kujera yana chat.
Cikin kulawa tace.
"Hayatuddeen ƙiramin Hamma'n ka."
Take kuwa ya miƙe, inda ya nufi part ɗin Hamman nashi.
Koda yaje afalo ya iskesa, zaune akan wheellchair, inda yake sanye da dogon wando da kuma wata farar t shirt, laptop ɗinsa ne agabansa yana ta faman dannawa yana ta murmushin ganin amsar saƙon da ya kai kwana goma da turawa Zaleeha shi da numbarsa ta sirri in da ya nuna mata shi saurayine kuma yana sonta, to bata duba saƙonba sai shekaran jiya, bata kulashiba kuma sai yanzu da ya sake ce mata.
"Hello my love". Koda ta buɗe saƙon sai yaga ta turo mishi amsa.
"Wa iyazubillahi, kai wanne irin mutunne da zaka rasa wanda zaka so da bibiya sai matar aure, nayi block naka tun randa naga saƙonka sai kuma naga ka kuma min mgna ban san kai waye bane dake iya sarrafa na'urar da ba tasaba, na haɗaka da Allah da Manzonsa kada ka sake yimin mgna ni matar aurece, kaji tsoron Allah ka rabu dani!".
Murmushi yaketayi yana mai-maita karanta saƙonta, yasan dole tayi mmkin cewar tayi blocking nashi kuma taga ya sake mata mgna. A ranshi yake cewa.
"Baki san cewa nike sarrafa wayarki ba."
Saƙon Ummin Hayatuddeen yasanar masa, sannan ya juya ya fita.
Bai wani ɓata lokaci ba, ya nufi ɓangaren Ummin nasa bayan ya rufe system ɗin nashi.
Tana nan zaune akan kujera, tana ganinsa taɗan sanja yanayin fuskarta, sarai tasanshi dayaga murmushi akan fuskartata, to tabbas tasan zai ɗauki maganar da zata faɗa masa amazaunin wasa kuma zai samu damar shigar da ƙorafinshi.
Dubansa Ummin tayi bayan ya ƙaraso gabanta.
Cikin kulawa tace.
"Daga ranan dana baka number'n Ameena kawo yau sau nawa katura mata saƙo?."
Gane abun da ta faɗa yasashi kwaɓe fuska, tabbas yasan dama watarana za'ayi haka.
Ganin yanda ya kwaɓe fuska yasa Ummi cewa.
"Au baka tura mata saƙon ba kenan?."
Kansa ya jinjina alaman "Eh." danshi dama kwata-kwata bai iya ƙarya ba, sannan kuma koda wasa baya yiwa Umminsa ƙarya.
Duban sa Ummi tayi tare da cewa.
"To lallai katabbatar da yau katura mata saƙo, ko ka manta cewa aurenta zakayi ne?."
Fuska ya sake kwaɓewa, tare da ɗan ciza kyawawan laɓɓansa, shikam yaga takansa da wannan liƙaƙƙen auren, hakanan an tilastashi auren wata mayyar yarinya, gashi tun ma bata shigo cikin gidan nasu ba, Umminsa ta fara takura masa akanta.
"Kajini dae kam ko?."
Ummi ta katse masa tunanin da yake.
Kansa ya jinjina mata alaman yaji.
Daga haka Ummi batace dashi komai ba, ta juya inda ta wuce ɗakinta, idanunsa yaɗan lumshe tare da buɗesu alokaci guda, kallonsa ya mayar ga Hayatuddeen wanda gaba ɗaya hankalinsa nakan wayarsa, sai murmushi yake yi, da'alama wani abun yake.
Ƙura masa idanu yna ƴan wasu mintuna Saifuddeen yayi, kana ya girgiza kansa, cikin nutsuwa ya tura kekensa inda yabar falon.
Bayan yadawo Sallan Isha ne, yaje part ɗin Ummin coffee ya amso tare da dawowa part ɗinsa, wayarsa ya ɗauka inda ya shiga cikin Whatsapp chat ɗinsa.
Contact ɗinsa yabi inda ya laluɓo numbern Ameenan, da yayi seven ɗinta da sunan *Ta'annabi* a cewarsa wai sadaka za'a kawo misho ita shiyasa ya raɗa mata sunan Ta'annabi.
ido ya ɗan zuwa no tata wanda hoton ta nema akan profile picture ɗinta. View ɗin hoton yayi, inda ya ƙurawa hoton ido.
Sosai tayi kyau a hoton don tasha adone cikin wani jan lace, sannan fuskartan nan tayi fayau, don tana murmushi ne aka ɗauketa hoton, taɓe baki yayi tare da maganar zuci, mayya ko me ya tuno kuma sai yayi murmushi sannan ya rubuta mata saƙo kamar haka.
"Slm".
Ameena wanda kusan always tana online, kwance take akan gado, kamar da wasa kuwa taga numbern Saifuddeen ɗin yayi mata magana, azabure tatashi ta zauna, cikin zumuɗi tace.
"Wayyo Allah ni daɗi kasheni, nakarɓi numbern ka wajen Hayatuddeen inason yi maka magana, sai gashi kai ka rigani."
Cikin sauri ta amsa masa da.
"Wslm".
harma da ƙarin tambayarsa.
"Ya gida."
Yana karanta saƙon nata, yaƙara taɓe laɓɓansa, cikin zuciyarsa yace.
"Su mazari, daga magana sai amsa babu ɗan jan aji kamar ba maceba."
Ɗan jim yayi, cikin rashin sabo ya rubuta.
"Ykk." Sannan ya tura mata.
Lumshe idanu Ameena tayi tsabar daɗi, cikin mamaki tace.
"Wai yau ni Ameena Saifuddeen ke tambaya ya nake?."
Cikin sauri tayi typing.... "Lafiya ƙalau ya aiki, yasu Ummi?."
Saida yayi kusan 3 minute bai buɗe saƙon ba, kafun daga bisani ya buɗe.
Koda ya karanta ataƙaice yace.
"Lfy." Ya amsa ataƙaice.
Sanan ya kuma rubuta.
"Meyasa kika amincewa Aurena, bayan kinsan da cewa, ni kurma ne, sannan kuma bana iya tafiya?."
Ganin tambayar tasa yasa Ameena sakin murmushi, abayyane tace.
"Kaiɗin nakeso Saifudeen ina matuƙar sonka, inasonka fiye ma da yanda nakeson komai."
Arubuce kuwa cewa tayi.
"Nakasa Ba Kasawa Bace, inasonka aduk yanda kake, sannan kuma zan zauna dakai ahaka, aurenka kuma ba kasawa bace."
Koda ya karanta saƙon idanunsa ya lumshe tare dayin shiru, kamar zaice wani abu kuma, ataƙaice ya rubuta.
"Okay saida safe jekiyi bacci."
Daga haka ya kashe data'n sa, tare da aje wayan gaba ɗaya.
Inda ya haurawa saman gado ya kwanta.
A ranshi yake cewa.
"Hmmmm kina dai da abin da kikeso a jikina, fitinanniya kawai mai idon cin maza."
Ameena kuwa ganin ya sauƙa online yasa ta lumshe idanunta, daɗi da farin ciki su suka cika zuciyarta, haka tayita juyi akan gadon, wani irin shauƙinsa ne ke damunta, da haka tayi bacci.
Tabbas akullum kwanaki ƙarewa suke, haka kuma lokaci na shuɗewa, akwana atashi asaran me rai, yau dai ya kama saura kwana uku kacal bikin Ameena da Saifuddeen.
Inda daga ɓangare biyu na gidajen duk shirye shiryen bikin suke.
Babu ma kamar gidansu Ameena, inda Ameena'n ke karɓan gyara na musamman, sosai ake mata gyaran jiki, hakan yasa fatarta tayi fresh.
Ɓangaren gidansu Saifuddeen kuwa, su Ummi ne kaɗai ke kiɗa da rawansu, Saifuddeen iyakacinsa ido, tunkuwa ranan da yayiwa Ameenan magana ta Whatsapp baisake bi ta kanta ba.
Zaune suke su dukansu Afalon Ummi, nan Ahmad ya shigo inda yake ƙara sanar dasu batun tashinsu don dama ya kammala gidansa tuntuni, Nan fa Saifuddeen ya kafe kan cewar Ahmad ɗin babu inda zaije, ae tunda ya saka baki ake ƙoƙarin yi masa auren dole dolensa kuwa ya zauna agidan.
Duk kuwa yanda Ahmad yaso Saifuddeen da Ummi su barshi ya koma gidansa sun ƙiya.
Nandai Saifuddeen yace Hayatuddeen ya dawo ƙasa, su kuma Ahmad ɗin su koma sama.
Hakan kuwa akayi, inda aka gyara duka ɓangare biyun, Raliya ta tattaro kayanta suka dawo sama.
Hayatuddeen kuwa ƙasa ya dawo.
Can ɓangaren su Ahmad ɗin kuwa aka gyarawa Amarya Ameena.
Sannu-sannu bata hana zuwa saide adaɗe ba'a je ba.
Rana kuwa bata ƙarya.
Yau yakasance Alhamis, inda gobe Jumma'a ɗaurin auren Saifuddeen da Ameena.
Acan Abuja yau Ameena ta gudanar da walima, inda aka yi wa'azi mai ratsa jiki, sosai kuwa waliman ya ƙawatar, don Ahmad dakansa ya tura mata kuɗi a account ɗinta, inda yace tayi duk wani hidima da takeso. Kana kuma yaune akaiwa Amarya jere, domin kuwa Babanta da kansa yayiwa kamfanin masu saida furnitures magana, ta online suka sai kayan, wanda Ameenan da kanta ta zaɓi kalan da takeso.
Ma'aikatan kamfanin kuwa suda kansu suka zo har gidan su Saifuddeen ɗin suka jera mata kayanta, sosai kuma yayi kyau.
Washegari.
Jumma'a.
Ranan yau takasance jumma'a, wanda kuma ayau ɗinne za'a ɗaura Auren Saifuddeen da kuma Ameena.
Tun safe kuwa Saifuddeen yaƙi fitowa, inda ya ce bashi da lafiya, sanin cewa Ameenan ba budurwa bace, kana kuma ba agari za'ai ɗaurin auren ba, yasa sam su Bappa Ali basu matsa masa ba.
Ƙarfe tara dai-dai jirginsu zai tashi.
Baba Malam, Bappa Ali, Dirankadi, Malam Adam, Baba Bello, Ishaq, Ahmad, Wareesu, Saleesu, Hayatuddeen, sune waƴanda zasuje ɗaurin auren, sai kuma Adda Rahama da Aunty Meena, wanda sune zasu ɗauko amarya.
Ƙarfe tara acikin jirgi tayi musu, inda suka ɗaga zuwa garin na Abuja.
Sun isa Abuja ƙarfe goma dai-dai, inda kuma za'a ɗaura auren ƙarfe 11 na rana dai-dai.
Ya Ahmad ne yazo ɗaukansu kai tsaye Asokoro gidansu Amarya suka nufa.
Nan suka tarar da ƙofar gidan ɗinke da jama'a, ƴan ɗaurin aure.
Alhaji Naseer da kuma mahaifin Ameena Alhaji Sadam su suka tarbesu cikin mutum tawa, inda su Adda Rahama kuwa suka wuce cikin gidan.
Kamar yanda aka sanya lokaci, ƙarfe sha ɗaya dai-dai jama'an dake wajen suka shaida ɗaurin auren Saifuddeen da Ameena, akan sadaki naira dubu hamsin.
Nan fa jama'a suka dinga sanya alkahiri, da nema musu zaman lafiya.
Acan cikin gida kuwa, amarya Ameena tayi kyau don an tsantsara mata meckup dai-dai misali, inda ta suturce jikinta da shiga ta al'farma, balaifi tayi kyau don kuwa sam bata da muni, saidai kuma bata da azababben kyau.
Jirgin ƙarfe ɗaya zasu biyo don dawowa Gombe, hakan yasa Dady wato Alhaji Naseer da kuma mahaifinta suka jata gefe inda sukayi mata nasiha sosai mai ratsa jiki.
Harma da ɗan guntun ƙwallanta.
Daga haka su Adda Rahama suka kamata, inda aka sanyata a mota, ƴan uwanta biyu ne zasuyi mata rakiya.
Akwai auntynta wanda ake ƙira da Aunty Zubaida, sai kuma ƙanwar mamanta, Aunty Zainab, nan dai suka ɗunguma dukansu zuwa airport.
Ƙarfe ɗaya kuwa dai-dai jirginsu ya tashi, zuciyar Ameena cike da kewar gida.
Sun iso cikin garin Gombe lafiya, inda lafiyayyun motoci har guda shida suka zo ɗaukarsu, Baba Malam dai kaitsaye gidansa aka wuce dashi shida Malam Adam, sai kuma Dirankadi da Ishaq, wanda suma kaitsaye gida suka wuce.
Koda suka ƙaraso, sosai ƴan uwan Ameenan suka yaba da kyaun gidan nasu Saifuddeen, nan dai kaitsaye part ɗin Ummi aka wuce da ita.
Tarba mai kyau Ummi tayi musu, tare da nuna musu ƙauna, haka ta jawo Ameenan jikinta cikin kulawa tayi musu addu'an samun zaman lafiya, da kuma zuri'a ta gari.
Daga nan kuma Adda Rahama tayi musu jagora zuwa ɓangaren Ameenan.
Nan ma sun yaba da tsaruwan part ɗin nata.
Kasancewar waƴanda sukai mata rakiyan ba kwana zasuyi ba, ƙarfe 5 na yammaci dai-dai sukabi jirgi inda suka koma Abuja.
Nan fa akabar Amarya Ameena ita kaɗai aɗakinta.
Yayinda ƴan tsirarun mutanen da sukazo bikin, tuni suma sun koma, domin dama Ummi batayi wani gayya ba, Aunty Mina ma tabi Bappa Ali sun koma dukku.
Haka gidan ya rage, daga Ummi, Adda Rahama, sai Raliya da kuma Hayatuddeen.
Shikuwa Saifuddeen tuni dama yana ƙule acikin ɗakinsa.
Koda akayi sallan Isha kuwa, saiga su Ahmad da Ishaq wai sunzo yi masa rakiya zuwa ɗakin amarya, abun ma dariya ya basa, nan dai ya haɗe gabar da yamma, inda yace.
"Baya buƙatar rakiyan nasu."
Duk yanda sukaso rakasa wajen Amaryar ƙiyawa yayi.
Haka suka tafi suna masa dariya.
Part ɗin Ummi ya nufa inda yasamesu zaune su dukansu afalo.
Cikin salon shagwaɓansa, ya dubi Ummin, gane abun dayake nufi yasa tace da Raliya ta ɗauko masa flask ɗin coffe ɗinsa, don dama tuni ta haɗa masa.
Yana amsa kuwa ya juya inda ya nufi part ɗinsa.
Ta ɓangaren Zaleeha yabi inda yashiga falonsa, kai tsaye ɗaki ya wuce, kayan jikinsa yaɗan rage sannan yasha coffee ɗin, kan gadonsa ya haye tare da rufawa kansa blanket, sam babuma maganar zuwa wajen Ameena acikin ransa, don kuwa ko Zaleeha dayake mutuwar so, ranan farko baije ɗakinta ba balle wata Ameena da yasan jira take ta ganshi ta mishi fyaɗe dan ya dai san abinda take so.
Can ɓangare Ameena kuwa koda tayi sallan isha, komawa tayi ta zauna jigum, kaɗaici ne ya dameta, tun tana zaune harta gaji ta kwanta, take kuwa bacci ya ɗauketa.
Washegari.
Tunda ya fita sallan asuba bai dawo gidan ba, can ya zauna amasallaci inda ya shiga rera karatun alƙur'ani.
Ameena kuwa tana idar da sallah, ɗakinta ta kimtsa, sannan ta zura doguwar hijabinta ta fito.
Nanne ta shiga ƙarewa ɓangaren nata kallo.
Ganin wata ƙofa acikin falon nata yasata buɗewa, nan ta tsinci kanta cikin wani haɗaɗɗen falo wanda haɗuwarsa ya zarce misali, ƙamshinsa kaɗai da taji yasa ta fahimci cewa ɗakinsa ne.
Ƙarewa falon kallo tayi sosai, sannan aɗaɗare ta nufi wata ƙofa dake cikin falon, wanda tana kyautata zaton cewa bedroom ne.
Aɗan ɗaɗare tayo knocking, amma shiru ba'a amsa mata ba, tunowa da tayi cewar bazai jita ba koda yana ciki hakan yasa tatura ƙofar ahankali tare da tura kanta ciki, ni'imtaccen ƙamshin daya daki hancinta ne yasata lumshe ido, ƙara kutsawa cikin ɗakin tayi, baki ta buɗe tana ƙarewa aljannar duniyar ɗakinnasa kallo, komai dake cikin ɗakin ya haɗu, ganin baya cikin ɗakinne yasa taɗan sauƙe ajiyar zuciya.
Komai dake cikin ɗakin nead, kan gadonne kawai dayake aɗan hargitse, cikin nutsuwa ta shiga kimtsa masa gadon nasa, sabon bedsheet ta shumfuɗa masa, kana ta sake share ɗakin.
Nan ta fesa air freshner'n da ta gani asaman mirror'n ɗakin.
Take ɗakin yasake ɗaukan ƙamshi.
Fita tayi daga ɗakin inda kaitsaye ta wuce ɓangaren Ummi don ta gaida ita.
Tana shiga kuwa ta samu Ummin afalo.
Cikin ladabi ta rusuna har ƙasa tagaishe da Ummin, cikin jindaɗi haɗi da ƙaunarta Ummi ta amsa mata, tare da tambayanta ya kwanan baƙunta.
Cikin al'kunya tace.
"Alhamdulillah."
Dai-dai lokacin kuwa saiga Saifuddeen din yashigo wanda dawowansa daga masallaci kenan.
Afakaice Ameena tasaci kallonsa, shikuwa bai kalli inda take bama saima gaishe da Ummi da yayi.
Fuska ɗauke da murmushi Ummin ta amsa.
Cikin matsanancin nuna girmamawa Ameena.
Tayi ƙasa da murya aladafce tace dashi.
"Ina, kwana!."
Muskarshi ya ɗan yamutsa tare da taɓe fuska, a hankali ya ɗan ɗago ida nunshi ya kalli fuskarta, kauda kanshi yayi dasauri kana ya...!
By
*GARKUWAR FULANI*
[9/9, 9:05 PM] +234 806 222 4030:
Sbpett Lumshe idanunta tayi tana mejin wani irin sanyi na shiga jikinta, cikin wani irin tsantsar farin ciki ta samu kanta, hakanan takejin zuciyarta fes, gaba ɗaya duk wani damuwarta ta kau, sake shigewa cikin blanket tayi, cikin zuciyarta tace.
"Tabbas shiɗin na dabanne, duk da cewa namiji ɗaya na taɓa sani kafun shi, amma nasan cewa, samun irinsa abune me matuƙar wahala."
murmushi tayi tare da ɗan cije laɓɓanta, cikin zuciyarta ta kuma cewa.
"Wai ahakan ma don bashi da lafiya, duk lokacin da yasamu lafiya yaya kenan, tabbas ranar zai zautar dani zai sani duniya gajumare."
hannu tasa ta ɗan rufe fuskarta, sakamakon wani irin kunya da taji ya rufeta.
Can cikin toilet kuwa Saifuddeen ne kwance cikin bathtube ɗin wanka, yayinda kansa ne kaɗai ke waje, ya lumshe kyawawan idanunsa, masu matuƙar kyau, ahankali yake fitar da numfashi, wani irin sanyi haɗi da zazzaɓi zazzaɓi yakeji, cikin yanayin dauriya haka yayi wanka, wheelchair dinsa ya jawo, kana ya hau kai, ƙarasawa gaban wani ɗan glass, dake kamar sip yayi, nan ya zaro ɗaya daga cikin bathrobe's ɗin dake cikin glass ɗin, sanyawa yayi ajikinsa, yayinda ya riƙe towel ɗaya ahannunsa yana goge jiƙaƙƙen gashin kansa, madannin wheelchair ɗinsa ya danna, tare da nufan hanyar fita daga bathroom ɗin. Ahankali ya buɗe ƙofar ya fito.
Cikin nutsuwa ya tura kekansa zuwa gaban mirror, handryer ya jona tare da busar da gashin kansa, turarensa mai sanyin ƙamshi ya fesa, nan ya ƙarasa gaban drawer'nsa, dogon wando da t shirt ya zaro, tare da sanyawa ajikinsa.
Nan ya nufi gadon nasa. Wanda har yanzu Ameena ke kananna ɗe akai.
Hannunsa yakai inda yaɗan janye bargon da take rufa dashi, kasancewar duk abun dayakeyi tana jinsa ba bacci take ba, hakan yasa ta ɗago da kanta ta kalleshi.
Ganin cewa ba bacci take ba, yasashi jan kekensa baya, yasake komawa gaban dressing mirror.
Ganin ya juya mata baya, yasa ta tashi daga kwancen da take.
Rigarta dake yashe bisa kan gadon ta ɗauka, nan ta sanya, ahankali ta sauƙo daga kan gadon, cikin yanayin sanyi ta wuce bathroom.
Dukkan abun da take yana lure da ita, dan yana ganinta ta gefen idonsa.
Ganin ta shige bathroom ne yasa shi, ƙarasawa jikin gadon, hannunsa yakai inda ya yaye bedsheet ɗin dake shumfuɗe akan gadon, cikin wani durtsbin wanda yake aje, ƴan kayayyakin da ba a wanke ba, ya jefasa, sannan ya ciro wani sabo acikin drawer ya shumfuɗa, kasancewar sa mutum me tsananin son tsabta, shiyasa baijin zai iya kwana akan wannan bedsheet ɗin, domin idanunsa sun gane masa sperm ya zuba kaɗan ajikin zanin gadon.
Yana gama shumfuɗa zanin gadon, ya sauƙa daga kan wheelchair ɗinsa, hawa kan gadon yayi tare da jawo sabon blanket ya rufa ajikinsa.
Kwanciya yayi tare dayin lub, sannu ahankali yakejin zazzaɓin jikinsa na ƙaruwa.
Can cikin toilet kuwa wanka Ameena tayi, sannan ta ɗauro alwala, itama ɗaya daga cikin bathrobe ɗin nasa ta sanya, nan ta fito daga toilet ɗin tana me goge kanta.
Handryer'n da yayi amfani wajen busar da gashin kansa, itama