Showing 51001 words to 54000 words out of 61846 words
Chapter 18 - Nakasa B Kasawaba Book 2 Complete Hausa Novel
yasa ta sakin murmushi cikin kulawa tace.
"Masha Allah ka fito kenan, yanzu fa nake cewa Hayatuddeen ya gama ya ƙiraka, kazo kayi break fast."
Ummi taƙare maganar tana mejan kujera wanda take facing na Saifuddeen ta zauna, duk dama shi always akan wheellchair ɗinsa yake zama.
Raliya ce tafito daga cikin kitchine, hannunta ɗauke da plate. Ganin Hamman nata yasata sakin murmushi, cikin nutsuwa tace.
"G/N Hamma."
Kansa ya jinjina mata alaman ya amsa, zagayowa ɓangaren da yake tayi, nan ta aje masa plate ɗin da ta fito dashi daga kitchine ɗin, wanda saman sa ke ɗauke da roasted fish, wanda yaji kayan haɗi, hadda lemon tsami. murmushi Saifuddeen yayi tare da dubanta, hannu ya jinjina mata alaman "Thanks." Itama murmushin tayi, don dama tayi hakanne don ta faranta masa, kasancewar tasan yanason roasted fish.
Nan ta zauna, inda suka shiga cin breakfast ɗin cikin nutsuwa, Ya lura dukaninsu suna cikin farinciki, musamman ma Umminsa, wanda duk bayan ƴan mintuna kaɗan take sakin murmushi, haka dai suka kammala break ɗin nasu, nan ya dawo cikin falon Ummin ya kwanta, Hayatuddeen kuwa ɗaki ya koma, inda shima yayi shiga shigen irin ta hamman nasa, nan yafito riƙe da jakarsa ta makaranta, duban Ummi dake zaune afalon yayi, cikin sangarta haɗi da zallan shagwaɓa yace.
"Ummi zan tafi school, 11:30 muke da lecture."
Batare da Ummi ta ɗago kanta ba tace.
"To Autana adawo lafiya."
Jin haka yasashi ɓata fuska ashagwaɓe
yace.
"Ummi kuɗin hannuna fa ya ƙare."
Murmushi Ummi tayi, don dama tasan kwanan zancen.
Dubansa tayi tare da cewa.
"Kullum sai an baka kuɗi Hayatuddeen sai kace ƙaramin yaro."
Cikin tura baki yace.
"Ni ban san ammafin buɗe min ac da Hamma Saifuddeen yayiba, ya tarkata komai ya riƙe ko Atm ɗin ban taɓa riƙewa koda na wuni ɗayaba, sai dai inyi ta ganin Arlet yanata shiga ba sauƙi, ina ganin miliyoyi amman bani da damar taɓasu."
Dariya Ummi tayi hakama Saifuddeen, dan zancen autan nasu ya nuna burinshi na a bashi kuɗi ya fara lalata.
Shi kuwa auta sake shagwaɓe mata yayi, wai adole sai ta bashi kuɗi, saikace ƙaramin yaro, nan Ahmad yashigo ya iske suna maganan, Ahmad ne ya ciro 5k daga cikin aljihunsa, inda ya bawa Hayatuddeen ɗin, nan Hayatuddeen yasaki murmushi sannan yasakai yafice daga cikin falon.
Nan Ahmad ya zauna acikin falon suka shiga ɗan taɓa hira da Ummi, Saifuddeen kuwa, luf yayi tare da lumshe idanunsa, kamar wanda ke bacci.
Abuja Nigeria.
Kwana biyu kenan da zuwan su Baba Malam Abujan, yayinda yau
Tsab Aunty Lubna da kuma wata ƙawarta, mai suna Samira suka shiga cikin shoprite, don haɗo kayan auren, ba laifi kaya masu kyau da kuma tsada suka sayo, duk da cewa ran Aunty Lubna baiso ƙara auren na Saifuddeen ba tanajin taya Zaleeha kishi, tana kuma tausayawa Zaleeha a gaba, to amma tasan cewa koma menene hakan shine dai-dai, don itama guduwan da Zaleehan tayi ya sosa mata zuciya.
Akwatuna goma sha biyu suka saya, kana kuma suka cikasu da kaya, sannan kuma suka saya wasu uku daban wanda ciki aka sanya kayan uwa da na uba.
Haka dai suka dawo gida bayan motarsu cike da kaya.
Aranan kuwa Ya Ahmad ya ƙira Baba Malam, inda yasanar dashi cewa, anagama haɗa kayan auren.
Kasancewar da dare ne Ya Ahmad da Baba Malam ɗin sukai waya, hakan yasa washe gari da safe, Baba Malam yaƙirayi Bappa Ali ya sanar masa, nan Bappa Ali yace.
"Zai sanar da Ummin, sai susa ranan da za'a kai kayan."
Hakan kuwa akayi don bayan sallan Azahar Ummi na zaune akan sallaya, sallame sallan ta kenan, wayarta tasoma ruri, ɗaga ƙiran tayi, bayan sun gaisa da Bappa Ali'n ne kuma, yake shaida mata cewar.
"An kammala haɗa kayan auren, yanzun ita zata sanya ranan da za akai kayan."
Cikin jindaɗi da gamsuwa Ummi tace.
"Masha Allah, amma ni sai nake ga kamar ku ya kamata kutsai da ranan kai lefen, tunda dai auren bawani lokaci mai tsawo aka ɗauka masa ba, yanzu gashi kamar wasa har anci kwana uku acikin ranakun."
Cike da gamsuwa Bappa Ali yace.
"Tunda yau takasance asabar ne, to ranan litinin da safe, sai waƴanda zasu kai lefen su shirya."
Nan Ummi take sanar dashi cewa.
"Goggo dada, Adda Rahama, da kuma Ahmad, sai kuma Hayatuddeen, sune wanda zasuje, amma bawai kai tsaye abujan zasu nufa ba, a Kaduna gidan Raihana zasu sauƙa tukun."
Nan dai tace ya kawo shawaransa. Cikin gamsuwa Bappa Ali yace mata.
"Hakan ma yayi."
Nan akayanke cewa, ranan litinin zasu kai lefen.
Ummi na gama waya da Bappa Ali'n, numbern Adda Rahama ta ƙira, nan take shaida mata duk yanda sukayi da Bappan nasu, sosai itama Adda Rahama tayi na'am da hakan. Nan dai sukayi sallama.
Numan.
Zaman Zaleeha a numan ya miƙa sosai, duk da cewa bawai tanajin daɗin rayuwa acikin ƙauyen bane, amma babu laifi tana ɗan samun abun da take ɗan so, tunda da kuɗi a hannunta, rayuwa take cike da kaɗaici, saidai wani lokaci wayarta da kuma tsohuwar laptop ɗinta suke ɗebe mata kewa.
Sai kuma wata sabuwar ƙawa wacce take ƴar fulani da tayi, inda sun haɗu ne, abakin kogi, don wani lokaci Zaleeha kan zuwa bakin kogin ta zauna, itakuwa sabuwar ƙawar Zaleehan mai suna Aisha, anan cikin wani ɗan ƙaramin rugar fulani dake kusa da Numan ɗin take, wanda yake rugace na zallan fulani sannan kuma dukansu musulmai ne, babu christan ko ɗaya acikinsu, tun Zaleeha bata sake da Aishan ba, har dai zuwa yanzu suka sama, domin kuwa taji daɗin haɗuwa da Aishan, kasancewar sosai Aishan ke ɗebe mata kewa, ta wani ɓangare kuwa mamaki take, kasancewar ansan cewa fulani suna aurar da ƴaƴansu da wuri, sai gashi ita kuma Aishan karatu ma take acikin birni, inda take aji biyu a university, wato level two, duka duka Aishan bazata ɗarawa Zaleehan ba, domin kusan ma kansu ɗaya, haka ma dai shekarunsu, sai-dai Zaleehan tafi Aishan cika dama duk wani abu na gogewa.
Yanzu ma dai tsab ta gama shirinta, cikin wani riga da sket na material masu kyaun gaske, wani babban mayafi ta yafa ajikinta, wanda yazo har ƙasa ya ɓoye duk wani kyawun surarta, waya da kuma power bank ɗinta ta ɗauka, duban Aishan dake zaune tayi.
Aishan ma dubanta tayi, ganin Zaleehan ta kammala shirinta yasa tace.
"Masha Allah, kinga yanda kikayi kyau kuwa, sau dayawa ina mamakin ki, duk da cewa aƙauye kike zaune, amma kuma kullum ƙara kyau kike, yanayin shigarki ta kame kai tana matuƙar yi miki kyau."
Murmushi Zaleeha tayi tare da cewa.
"Uhumm kedai Aisha bakya gajiyawa da surutu, kullum ganin kyauna kike ke bakya ganin naki, dan Allah tashi muje, yau kam naƙosa muje gidanku, kodan ma na huta, da gorin da kikemin, kan cewa da kike, wai kullum ni bana zuwa gidanku, saidai ke kizo."
Miƙewa Aisha tayi tana dariya, nan suka fito daga ɗakin.
Babu kowa atsakar gidan, domin kuwa tun safe Elizabet, da kuma Solomon suka tafi church, kasancewar yau Lahadi.
Suna fita Zaleeha ta jawo ƙofar gidan ta rufe, nan suka ɗauki hanya zuwa cikin rugar su Aisha, wanda yake nan kusa bashi da nisa,
Koda suka shiga cikin rugar sosai Zaleeha taji zuciyarta tayi sanyi, sakamakon ganin yanda jama'ar rugar keta hada hadansu, wanda dukansu musulmai ne kana kuma fulani masu mutunci waɗanda hasken addini ya ratsasu, don da ka kallesu zakaga hasken musulunci agoshinsu, idanu ta lumshe, tare da sauƙe ajiyar zuciya, tabbas akullum tana ƙara godewa Allah daya yita musulma, domin kuwa tabbas duk wani addini da ba na musulunci ba, babu komai acikinsa sai ɓata,
musulunci shi kaɗaine haske.
Koda suka ƙarasa gidan nasu Aisha, cikin girmamawa ta gaishe da Innar na Aisha, haka dai suka ɗan gaggaisa da ɗan sauran jama'ar gidan. Nan suka zauna da Aisha'n, suka shiga ɗan taɓa hira.
Sun ɗan jima suna hira ganin cewa la'asar ta kusa ne, yasa Zaleehan miƙewa, nan tace zata tafi, batason yammaci ya mata awaje, Inna Maman Aishan ne, ta bata pure nono cikin wani babban gora, wanda aka zuba zuma acikinsa, Aisha kuwa da kanta ta gasawa Zaleehan naman ƙatuwar Zabuwa, duk yanda Zaleeha taso kin amsa, saida suka sata ta amsa, nan tayi musu godiya sosai, sannan Aisha ta rakota, har kusan wajen rugar, daga haka sukai sallama, inda Aishan tace da Zaleeha sai tazo.
Batayi wani tafiya mai nisa ba ta iso gida, nan ta iske har zuwa wannan lokacin su kawun nata basu dawo ba, ɗakinta ta shiga inda ta aje nama da kuma nonon da suka bata.
Fitowa tayi donyin alwalan sallan la'asar, dai-dai nan Elizabet ta shigo cikin gidan, kamar an jefota ba sallama duk tayi wujiga-wujiga da ita, ƙafarnan tata tayi futu-futu, idanunta kuwa sunyi tsuru tsuru, alamun gajiya da wahala ya bayyana ƙarara ajikinta.
Dubanta Zaleeha tayi, kana ta kau da kanta gefe, da taso yi mata sannu da dawowa, amma tunowa cewa Elizabet ɗin daga church take, hakan yasa ta fasa, zama tayi akan dakali, tare da jawo ƴar butar ta, ta soma al'wala.
Elizabet kuwa kan wani benci dake tsakar gidan ta baje, nan tashiga maida numfashi akai-akai, saikace wacce tayi wasan tsere, amatuƙar gajiye ta ɗago kai ta dubi Zaleeha, wanda ke gudanar da al'wala cikin nutsuwa, ƙura mata idanu Elizabet ɗin tayi, tana me kallon yanda take alwala'n, cikin ranta tace.
"Oo ni Elizabet kalli yanda suke gudanar da ibadansu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da jin daɗi, batare da wani hayaniya ba da ife-ife da raye-rayeba."
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da ɗan gantsarewa dan azabar ciwon da ƙugunta yakeyi sabida wuni rawan da suka wuni tiƙawa a majami'ar bautar tasu.
Duban ƙafanta wanda sukayi suntum tayi, hakan kuma ya farune sakamakon tiƙar rawa da tayi a church, don kuwa tun safe suke rawan bahutu, gaba ɗaya ta gaji.
Idon dai ta zubawa Zaleeha tana ganin yadda take gudanar da harkar ibadarta a mutunce.
Ita kuwa Zaleeha, tana alwalanne amma gaba ɗaya kewar da begen gida da danginta da Baba Malam ne ya cika zuciyarta, sosai takejin kewar mahaifin nata, tana matuƙar son Baban nata ƙwarai da gaske, tabbas ta wani ɓangare tanajin son komawa gida, tana so da ƙaunar taga tayiwa mahaifinta biyayya tana son farin cikin shi dana Ya Ahmad koda irin al'ƙawarurrukan da ya mata, tana jin ciwo a ranta ace da aure a kanta a kuma bata gidanta ɗakinta damahaifinta ya umarceta data zauna lokuta da dama tamkar tayi zama tsuntsuwa tayi fiffige ta koma cikin iyayenta tayiwa mahaifinta biyayya, koda ko sanadin rasa masoyin nata zaisa ta rasa ranta.
To amma hakanan takeji kaman anɗaure ta da jijiyoyin jikinta, wanda takejin kamar dole akai mata zama anan Numan ɗin tanaji a ranta tana son ta koma amman duk sanda ta aiyana haka sai taji kamar a ɗaureta ne, a garin, haka dai ta kammala al'walanta kai tsaye ta wuce ɗakinta,
a nan tabar Elizabet zaune tana ta faman maida ajiyar zuciya.
Sallah tayi sannan ta jawo goran nonon, nan taɗansha kaɗan sosai kuwa taji daɗinsa, kasancewar bata wani jin yunwa yasa ta ajiye, kan cewar sai zuwa dare taci zabuwan da kuma nono'n....
Gombe State.
Kasancewar yau ya kasance litinin, kuma yaune su Adda Rahama zasu wuce Kaduna, daga nan kuwa Abuja zasu inda zasu ɗau lefen agidan Ya Ahmad, sukai zuwa gidansu Ameena.
Ƙarfe 9 dai-dai dukansu suka hallara afalon na Ummi, Adda Rahama, Goggo Dada, Ahmad da kuma Hayatuddeen, sune wanda zasu tafi, tun ƙarfe 8 Raliya ta gama musu break fast, inda sukaci suka ƙoshi, ƙarfe goma dai-dai jirgin dazai kwashesu zuwa Kaduna zai tashi, hakan yasa tuni suka kammala duk wani shirye-shiryensu, ɓangaren Saifuddeen kuwa, yana can part ɗinsa, baimasan wainar da suke toyawa ba.
Kasan cewar lokacin ana tsaka da gyara Airport ɗin Abuja shine ya basu damar samun jirgin kaduna kai tsaye.
Raliya da kuma Ummi sune sukai musu rakiya, har zuwa airport, kamar yanda yake arubuce kuwa ƙarfe 10 dai-dai jirgin nasu ya tashi.
Kwata kwata tafiyar mintuna 46 jirgin nasu yayi, ya iso cikin airport ɗin garin Kaduna, koda suka sauƙo daga cikin jirgin nan suka iske Saminu najiransu, wanda shi da kansa yazo ɗaukarsu, sunyi farin ciki sosai da ganin juna, nan ya kwashesu cikin motarsa, suka nufi gidansa.
Adda Rahama na shiga cikin gidan, Raihana ta rungumeta cikin tsananin farin ciki, itama Adda Rahaman rungume Raihanan tayi, don kuwa tayi kewarta, Hayatuddeen ne ya zumɓura baki tare da cewa.
"Wayyo Adda Raihana ni bazaki rungumeni bane, kodai bakiyi kewata bane?."
Dariya Raihana tayi tare dajan kumatunsa, cikin tsokana tace.
"Ƙato dakai ne zan rungume ka, kaikam ai saidai ma nasa maka duka, kancewa ka shigomin gida, ƙato dakai, ai da katsaya daga waje."
Dariya suka sanya su duka, Hayatuddeen kuwa, sake tunzura baki yayi, tare da faɗin.
"Ae dama batun yauba nasan Raliya tafiki sona."
Jin haka yasa Adda Raihana'n jawo hannunsa, cikin ƙaunar autan nasu, ta rungumesa, cikin son sanyaya masa zuciya tace.
"Inasonka mana autan Ummi, ai kowa ya soka bayana ne, saboda kai fa yasa na shirya lafiyayyen girki, harma fa ferfesu nayi maka naka kai kaɗai na musamman."
Jin haka yasa Hayatuddeen sakin murmushi mai ɗauke da tsananin farinciki.
Cikin jin dadi yace.
"Yesss shiyasa nake ƙara sonki Adda na, saboda koba komai kinfi su matar o'o kirki."
Yaƙare maganar yana me satan kallon Ahmad.
Dariya suka sanya don sarai sun gane dawa yake.
Ahmad kuwa ƙwafa yayi inda yace.
"Zamu koma ne yaro zakayi bayani agabanta."
Nan dai suka zazzauna inda Raihana ta cika musu gabansu da kayan ciye ciye, haɗi dasu drinks.
Saida sukaci abincin suka ƙoshi sannan, suka kimtsa don kama hanyar Abuja. Inda Ahmad ya ɗauki ɗayar motar Saminu, wanda ya ɗauki Goggo Dada da kuma Adda Rahama acikinsa, sai kuma Saminu wanda ya ɗauki, Hayatuddeen da kuma Matarsa Raihana.
Kasancewar tsakanin Abuja da kuma Kaduna babu wani nisa, hakan yasa suka isa dai-dai an idar da sallan Azahar.
Kaitsaye unguwar Wuse zone 2 suka nufa, wanda anan gidan Ya Ahmad yake.
Koda suka ƙarasa gidan sun samu tarba me kyau daga wajen Aunty Lubna, sunkuwa ji daɗi ƙwarai, nan tafito musu da kayan auren suka gani, sosai suka yaba, don ƙwarai kayan sunyi kyau.
Kimtsawa itama Aunty Lubna'n tayi, inda cikin motarta su Hayatuddeen suka loda akwatunan.
Kaitsaye suka nufi Asokoro wato gidansu Ameena.
Horn sukayi inda maigadi ya wangale musu gate ɗin gidan, suka shigar da motocinsu ciki. Tabbas gidan yayi kyau ba laifi, sannan suma masu kuɗi ne.
Wata matashiyar Mata itace ta fito zuwa compound ɗin gidan, nan tayiwa su Adda Rahama jagora zuwa cikin gidan, yayinda driver da kuma mai bawa flowers ruwa sune suka shiga jidon akwatunan suna shigarwa zuwa falon gidan.
Koda su Adda Rahama suka ƙarasa zuwa cikin gidan, sun samu tarba mai kyau, cikin karramawa matan da suka samu acikin falon suka tarbesu.
Nan dai suka zauna inda suka gaggaisa.
Take kuwa aka cika musu gaba da kayan shaye shaye.
Bayan sun ɗan nutsane.
Adda Rahama ta gabatar musu da kayan, nan suma suka yaba sosai, haka dai suka ɗan taɓa hira cikin mutunta juna.
Koda suka tashi tafiya haka aka cika musu bayan motarsu da kayan ciye ciye.
Nan dai suka rabu cike da ganin mutumcin juna.
Duk wannan wainar da ake toyawa Ameena na kwance aɗaki tayi ƙumus, zuciyarta cike take da ɗanyar farinciki, ji take kaman tafi kowa sa'a aduniya, bazata iya misalta daɗin da takeji ba, tabbas babbar nasarace samun Saifuddeen amatsayin miji.
Su Adda Rahama kuwa, gidan Aunty Lubna suka koma, nan dai suka ɗiba mata kayan ciye ciye dana shaye shayen da aka haɗosu dashi.
Basuwani jima agidannata ba suka kamo hanyar Kaduna.
Can gidan su Ameena kusa, ƙwarai sun yaba da kayan, kasancewar sanin Ameena ba budurwa bace, hakan yasa basui tunanin dangin Saifuddeen din zasuyi mata wannan karamcin ba.
Koda Momma taƙirawo ta akan cewar tazo taga kayan, koda tagani taji daɗi ƙwarai, don harta farincikinta saida ya kasa ɓoyuwa, Allah kawai take ta godewa acikin ranta.
Can Kaduna kuwa, gaba ɗayansu zaune suke afalon Raihanan, inda suke ta hiransu, Hayatuddeen ne yasaka bowl ɗin snacks agaba yanaci kana yana yagan cinyar kaza, sai wani jijjiga kansa yake, yana lashe red lips ɗinsa, wanda suke shige dana Hamma Saifuddeen ɗinsa.
Dubansa Adda Rahama tayi, cikin zolaya tace.
"Aikin ka kenan autan Ummi ci, acici kazar birni, niko da ace halittarka mai ƙiba ne, sannan ci nasa ƙiba, tabbas Hayatuddeen da yanzu girman jikinka ya cika falon nan."
Idanunsa ya zazzaro waje.
Cikin shagwaɓa yace.
"Haba Adda saikace Yaya Saminu."
Dundu Raihana takai masa tare da cewa.
"Mijin nawa?."
Dukansu suka sa dariya.
Ahmad kuwa cewa yayi "Kaɗan ma kika gani indai Hayatuddeen ne."
Shima dariyar yayi kana yace.
"Ya Wareesu fa nake nufi."
Haka dai sukaci gaba da hiransu, har aka ƙirayi sallan magriba.
Saida sukayi sallan Isha kafun suka zauna inda suka sake kafa sabon hira.
Haka dai sukaita hira har kusan goman dare, dagananne kowa ya nemi makwanci, Inda Ahmad da Hayatuddeen suka shiga cikin wani extra ɗakin dake cikin falon, Su Adda Rahama, da goggo Dada ma ɗaki guda aka basu. Domin kuwa gidan na Saminu akwai yalwatattun ɗakuna.
Washegari da safe kuwa, Raihana lafiyayyen break fast ta shirya musu, inda suka cika cikinsu, nan kuma suka soma shirye-shiryen tafiya, don yau ɗinma jirgin ƙarfe 10 zasu bi zuwa Gombe.
Saminu ne ya kaisu airport wanan karon hadda Raihana tayi musu rakiya.
Basu bar airport ɗin ba kuwa saida suka ga tashin jirginsu, sannan suka dawo gida.
Ƙarfe sha ɗayan rana acikin garin Gombe tayi musu, inda Sule driver yazo da babbar motar Saifuddeen har airport ya kwashesu zuwa gida.
Afalon Ummi suka baje, wanda nan suka samu Saifuddeen zaune akan wheellchair dinsa, yana shan yogo fruit wanda Ummi ta haɗa masa, yayinda tasashi agaba sai tarairayarsa takeyi kamar wani ƙaramin yaro, shikuwa dama aikinsa ne shagwaɓa hakan yasa ya narke mata.
Sam abun baya bawa su Adda Rahama mamaki, saboda sun san ƙaunar dake tsakanin Ummi da kuma Saifuddeen mai ƙarfi ce.
Nan dai suka shiga labartawa Ummi, irin tarban mutumcin da suka samu daga wajen dangin Amina.
Jin suna ta yaba kirkin dangin su Ameenan yasanya Saifuddeen kauda fuska, nan yamaida hankalinsa ga tv, don bama yason fahimtar mai suke faɗa.
Anan dai Adda Rahama tayi sallan La'asar kafun Dr Adnan yazo ya ɗauketa.
Goggo