Showing 12001 words to 15000 words out of 61846 words

Chapter 5 - Nakasa B Kasawaba Book 2 Complete Hausa Novel

maida bacci.

Washe gari.
Kamar yanda takeyi tun da tazo gidan haka yauma tayi, tana gama idar da sallah tatafi ɓangaren Ummi inda tagaisheta.
Yau ɗinma Ummi cikin so da ƙauna ta amsa mata gaisuwarta,
a falo ta haɗu da Saifudddeen da Hayatuddeen bisa dukkan alamu daga masallaci suke,
cikin sakin fuska Hayatuddeen yace,
"Barka da safiya Aunty Zaleeha."
ɗan tsayawa tayi fuska a sake tace.
"Barka dai autan Ummi."
murmushi yayi tare da cewa.
"Ya amarci da gajiyan biki."
hararansho taƴi cikin sanyi ta ratsa gefen Hamma Saifuddeen ɗin harara ta cillamishi, sai kuma tayi wuf ta wuceshi kamar dai tsoro take kar ya cabketa
abinma dariya ya basu kana suka bita da ido.
daga ɓangaren na Ummi kaitsaye part dinsu ta  dawo, komawa tayi tanaɗe akan gado inda tacigaba da baccinta.

Acan gidan su Zaleeha kuwa sai jiya Mama tadawo daga tafiyanta da tayi, Baba Malam dai ko sannu baice da ita ba, koda ya lura cewa Zaheera bata gidan, tana can gidan Zaleeha, sosai ransa ya ɓaci, nanfa yasa Ya Ameenu Habu akan su kwashi kayayyakinta na aure da motocinta su kai maita kana su ɗauko Zahira sannan su ƙara yiwa Zaleehan nasiha inda yaje.
Hakan kuwa akayi, tuni Ya Ameenu da Habu sukatafi dan ɗauko Zaheeran bayan duk sun lodo kayan aurenta a motocintan.
Koda sukaje gidan nasu Saifuddeen sai Ya Aminun ya bawa Habu kuɗi yacewa Habu ya hau keke napep ya koma ya ɗauko motarshi su samu wacce zasu koma da ita tunda duk motoci biyun da suka zo dasu na Zaleehan ne ɗaya na cikin kayan aurenta ɗaya kuma wacce Ya Ahmad ɗinta ya saya mata,
Ya Aminu na fitowa cikin motar ya nufi wurin maigaɗinsu akan yaje ya mishi sallama da masu gidan a nan suka haɗu da Ahmad, inda suka gaisa cikin girmamawa da mutum ta juna, Ahmad ne yayi masa jagora har cikin gidan, saida Ya Ameena yafara zuwa ɓangaren Ummi tukunna, cikin mutum tawa ya gaida ta, sannan yayi mata bayanin cewa yazo ɗaukar Zaheera ne,  sosai Ummi taji daɗin karramata da yayi, nan tasake aminta da tarbiyan gidan Baba Malam ɗin, Ahmad ne yayiwa Ya Ameenu jagora zuwa ɓangaren Zaleehan, don kuwa Saifuddeen bayanan, sun tafi meeting ɗin ƙungiyarsu na Jonapwd shida Ishaq.
Sosai Zaleeha taji daɗin ganin yayan nata, saidai kuma jin cewa Zaheera yazo ɗauka, yasanya taɗan ɓata fuska, saidai kuma bata isa cewa komai ba, sanin cewa Ya Ameenun nada zafi sosai, babu ruwansa yanzu saiya solleta soso da sabulu.
Haka Zaheera ma ranta baiso ba, don dai kawai Ya Ameenun ne yazo da kansa, amma da wanine bazata bisa ba, don ita ke gadin Zaleeha a cewarsu a yadda suka tsara kenan wai ai duk nacinsa bazai zo inda takeba in Zahira nan kuma da ita aketa plant ɗin yadda Zaleeha zata gudu,

Haka dole ta haɗo kayanta, Gyara zama ya Ameenu yayi, cikin kulawa haɗi da kwantar da murya, yashigayiwa Zaleehan nasiha, dayi mata nuni akan tabi mijinta, idan ya umarceta da yinnabu matuƙar bai saɓawa shariya ba yace tayi to koda bataso tayi, domin hakan shine dai-dai domin al'jannarta na ƙarƙashin diga-diginsa .
Itadai Zaleeha jinsa kawai take, amma bata ɗauƙa, koda yazo tafiya har compound ɗin gidan ta rakosu,
nan kuma yasa Hayatuddeen da Imran dasu Zakariyya kwashe kayayyakinta kab suka shigar mata,
sannan ya bata car keys ɗinta duka biyu a hannunta, godiya tayi tare da cewa ya gaishe mata da Ƴar uwarta Maryam.
Haka Ya Ameenu yatasa Zaheera suka bar cikin gidan, shikansa ya yaba da tsarin gidan, musamman ma part ɗin Zaleeha wanda yayi matuƙar kyau, shida kansa ya ƙyasa, ya kuma yabawa Saifuddeen sosai, don bakowani namiji bane zai iya ɓarnatar da dukiyarsa wajen ƙawata gida mai kyau kamar haka ba.

Tafiyan Zaheera yasa Zaleeha duk taji gidan bayayi mata daɗi, hakanan taji komai ya tsaya mata, batasan dacewa motsin Zaheeran na ɗebe mata kewa ba, sai ayanzu da Zaheeran tatafi, haka ta koma ɗaki ta kwanta, zuciyarta cike da saƙe-saƙe kala-kala.
Tananan ƙule aɗaki har akayi sallan isha,
Nanfa wani irin tsoro yashiga diro mata, take fargaba ta cika zuciyarta, sam batajin zata iya kwana itakaɗai aɗakin batare da wani nata ba, sosai tsoron sa yashiga zuciyarta, tabbas ayanda taga cikin idanunsa jiya to idan tayi wasa komai zai iya aikata mata, abanza saiya rabata da virginty ɗinta, shikenan kuma daganan yagama cutanta, dan tasa aranta cewa bamakawa daga ranan daya yayi disvirgin ɗinta tofa shikenan itakam ta sallama rai da rayuwa, don baƙinciki ne zaiyi ajalinta tabbas.
Tashi tayi daga kan sallayan tare da kai dubanta jikin ƙofar ɗakin, ganin babu key ajikin ƙofar yasa gaba ɗaya hankalinta ya ƙara tashi,  atsorace tashiga neman key ɗin amma bata gani ba.
Ƙirjintane yatsananta bugu alokacin da taji motsin mutum a falonta.

Shikuwa Saifuddeen lokacin dawowansa kenan daga masallaci, kaitsaye ɗakinsa ya wuce, dan yanaso yaɗan watsa ruwa, kafun ya ya ɗa ci abinci.
Jin motsin buɗe kofar falonsa, dakuma rufewa yasanya taɗanji zuciyarta tayi sanyi, cikin hanzari ta ɗauki blanket da pillow, saikuma phone ɗinta, saɗab-saɗab tafito daga cikin ɗakin, ahanzarce tayi hanyar fita daga cikin falon, tana samun kanta aɗan compound ɗin shashin nata kuwa ta saki ajiyar zuciya,  kaitsaye garden ɗin dake cikin part ɗin nata ta nufa wanda yake cike da sanyi da sauraye, kan wata kujera dake ɗan cikin garden din ta kwanta, tare da jawo blanket ta rufa jikinta, ɗaura kanta tayi akan pillow tare da sauƙe ajiyar zuciya, ta dai gwammace kwana awajen da dai ta tsaya aciki ya illata mata rayuwa, zata jure komai amma bazata iya jure abinda zai iya mata ba, hakanan bata tsaya wani mugu yayi disvirgin ɗinta ba tunda ta duba ɗaya ɗakinma babu key sai tayi zaton shine ya zaresu dan karta rufe ƙofa ya samu damar shigowa ya mata fyaɗe injita da faɗi.

Raliya kuwa wacce tazo rufe window'n ɗakinta dake abu ɗe ne taga kaman wulgawan mutum ya shiga cikin garden, kanta tasake zurowa ta cikin window'n, nan idanunta suka gane mata Zaleeha dake ƙoƙarin kwanciya akan wata kujeran ƙarfe.
Mamakine yakusan  kasheta awajen, sosai abun ya ɗaure mata kai, komawa cikin ɗakin nata tayi ta zauna tare dayin jigum, me hakan yake nufi kenan? tsanar da Zaleeha tayiwa ɗan uwanta har yakai wanda zataƙi haɗa shumfuɗa dashi? har ta gwammaci kwana acikin sauro da ciyawi da sanyi a kan kujerar ƙarfe akan ta kwana dashi.
Kanta ta jinjina tare da rumtse idanunta wanda suka ciko da ƙwalla, sam bahaka ta ke wa ɗan uwannata fata ba, babban burinta shine yasamu ingantaccen kulawa daga wajen matar tasa amma meyasa Zaleeha ke gudunsa?
kwaffa tayi tare da cewa.
"Ko ya zakiyi wlh in sha Allah sai dai ya raɓi jikinki in Allah ya yarda duk iskancinki kin shiga hannu kenan mutu ka raba, ato sai yaci sadakinshi."
Tana faɗin haka sai kuma ta miƙe da sauri ta nufi.....!





Littafina na kune in kin ganshi a wojema na satane, turo ɗari 300 ta wannan no 09097853276 ko ka/kiyi min transfer'n 300 ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.




Wanda ya karanta na sata Yaseeeen doguwa.

By
*GARKUWAR FULANI*
[9/9, 9:05 PM] +234 806 222 4030: Murmushi Baba Malam yayi irin nasu na manya, kana ya ɗanyi jim, haƙiƙa fasa auren Zaleeha bazai rage komai ba face mutuncinsa da kimarshi, mutuƙar kuwa aka fasa auren to tabbas ita da mahaifiyarta sun samu abun da suke so, sam shikuma bazai lamunci hakan ba, gyara zamansa yayi tare da kai dubansa ga su Baffa Ali da Malam Ashiru.
Cikin nutsuwa haɗi da kamala yace.
"Haƙiƙa nafahimci me kukeji agame da wannan auren, saidai kada ku manta mu daku ɗin kamar ƴan uwa muke,  dukanmu tsofaffine masu dattako da sanin ya kamata,  amatsayina kuma na mahaifi ga Zaleeha zan ƙirata na zaunar da ita nayi mata nasiha, insha Allah nasan zata fahimta, dan Allah kuyi haƙuri, rashin tunanine kawai irin na yaran zamani!."
Ajiyar zuciya su Baffa Ali suka sauƙe, cikin sanyin murya haɗi da fahimtar Baba Malam ɗin, Baffa Ali yace, "shikenan Malam Basheer babu komai, Allah yasa auren ya zama al'khairi agaresu, Allah kuma ya sawa Zaleeha so da ƙaunar Saifuddeen acikin zuciyarta, don shikam yana sonta sosai, fatan mu shine auren nasu yayi al'barka!."
Da "Ameen Ameen!." suka amsa su dukansu,  inda Baba Malam ya sauƙe ajiyar zuciya, sosai yaji girman na iyayen Saifuddeen ya ƙaru acikin idanunsa, nan suka ɗan tattauna maganganu masu muhimmanci, daga nan kuwa su Baffa Ali sukayiwa Baba Malam ɗin sallama,  har bakin motarsu Baba Malam ya rakosu, inda bai dawo cikin gida ba saida yaga tafiyarsu.
Zama yayi akan ɗaya daga cikin tausassun royal chairs ɗin da suka ƙawata haɗaɗɗen falon nasa, bayansa ya jingina da jikin kujeran tare da lumshe idanunsa,  cikin ransa haka yakejin ba daɗi, tunda yake baitaɓa sanya ranan auren ɗansa ko ƴarsa daga baya kuma akazo da maganar fasawa ba sai akan Zaleeha! duk kuma a dalilin taurin kai irin nata, tabbas Zaleeha tanason sashi yaji kunya a idanun mutanen da suke matuƙar ganin ƙimansa, amma babu komai zaiyi abun tubkar hanci tunda wuri,  wayarsa dake cikin al'jihun rigarsa ya laluɓo inda ya dannawa nombern Mama ƙira, bugu uku ana huɗu Mama ta ɗauki ƙiran, batare daya jira komai daga gareta ba yace.
"Kituromin Zaleeha." kitt ya kashe wayan, don sam baison abun dazai ɓata ransa da daren nan.
Bayan kamar minti shida dai-dai Mama tashigo cikin falon hannunta ɗauke da ɗan madaidaicin tray wanda samansa ke ɗauke da flask da kuma ƙananan cup guda biyu,  bakinta ɗauke da sallama ta ƙaraso cikin falon, inda ta jawo wani babban table dake tsakiyan falon ta kawosa har gaban Baba Malam ɗin, nan ta ɗaura ɗan ƙaramin tray din akan table ɗin,  duban Baba Malam tayi fuska ɗauke da Murmushi tace.
"Barka da hutawa!."
Shima Baba Malam ɗin fuskarsa ɗauke da murmushi, ya jinjina mata kai alaman ya amsa.

Su Baffa Ali kuwa koda suka isa gidan nasu Saifudden kai tsaye ɓangaren Ummi suka nufa,  zaune suka isketa ababban falon nata, gefenta kuwa Hayatudeen ne wanda keta faman buga game ɗin Drok Stack Ball awayarsa.
ganinsu yasa Hayatuddeen ya gaishesu cikin ladabi, don kuwa hadda Dirankadi akazo,  nan ya miƙe ya haura sama zuwa ɗakinsa.
Ummi kuwa tashi tayi ta kawo musu drinks masu ɗan sanyi,   nan ta zauna suka shiga ɗan gaisawa, musamman da Dirankaɗi wanda suka jima basu haɗu ba.
Bayan sungama gaisawa ne, Dirankaɗi ya gyara zamansa tare da fuskantar Ummi'n, sanin cewa ita ɗin mai yawan haƙuri da sauƙin kai ne yasanyasa tausasa lafuzansa, tayanda zata fahimcesa sosai, ahankali yace.
"Kamar yanda kika buƙata da muje gidan su Zaleeha, munje munkuma sanar musu cewar mun janye batun auren!.".
Ajiyan zuciya sauƙe a hankali tare da cewa.
"Alhamdulillah".
murmushi suka ɗanyi, sai kuma Dirankadi ya ɗan numfasa tare da cewa.
"Kiyi haƙuri Hajiya..  kisa aranki cewa auren Saifuddeen da Zaleeha haɗine na Allah bawai yin kanmu ba, sannan kada ki manta ance matar mutum kabarinsa, sannan idan Allah Ya nufa cewa Saifuddeen sai ya auri Zaleeha bamu isa hanawa ba."
shiru tayi jiki a mace taci gaba da sauraronshi.
"Tabbas nasan mekikeji nakuma fahimci irin fargaban da kike ciki, ƙwarai kowacce uwa bazata taɓa son wani abu dazai cutar mata da ɗanta ba, nasan kina gujewa Saifuddeen auren Zaleeha ne badon komai ba saidan, kina jin tsoron abunda kaje kazo, da kuma irin tsananin ƙiyayyar da Zaleehan ke nuna masa,  ƙwarai hakan abun tsorone to amma kada ki manta, babu wani abu dazai samu bawa me kyau ko akasinsa,  face dama tuntuni anrubuta acikin littafin ƙaddaransa."
Kai ta gyaɗa tare da cewa .
"Haƙƙun".
Cikin jin daɗin tana gamsuwa yaci ga da cewa.
"Wani baya taɓa iya cutar da wani harsai Allah Ne ya tsara hakan,  saboda haka inaso ki kwantar da hankalinki, munyi magana ta fahimta da mahaifin yarinyar, mutum ne shi mai tsananin dattako da kamala, kema kinsan hakan tuntuni, ya ƙasƙantar da kansa ya bamu haƙuri, ya haɗamu da Allah cewa kada a fasa auren! yakuma taushemu da lafuzza masu daɗi, saboda haka mu dai mun aminta cewa Saifuddeen zai auri Zaleeha, saboda haka yana ɗaya daga cikin ƙaddaransa, komai zai wuce kuma watarana sai labari, kema inaso
kisa aranki cewa Insha Allah auren Saifuddeen da Zaleeha al'khairine mai tarin yawa, wanda zaisa dukkanmu farinciki anan gaba,   mudai addu'an al'khairi yadace munayi musu ako da yaushe!."

Baffa Aline yaɗan nisa tare da amsawa da cewa.
"Ƙwarai kuwa, abun da Dirankaɗi ya faɗa gaskiyace, haƙiƙa dukanmu nan munsan cewa ke uwa ta gari ce,  munsanki da haƙuri Ummi, dan Allah inaso ki ƙara akan nada, ki-kumayi duba da irin tarin soyayyar da Saifuddeen keyiwa yarinyarnan tunfa suna ƙanana, kuma rauninki zaisa Saifuddeen fasa auren nan!."

Malam Ashiru ne yace. "Ƙwarai kuwa, ayanzu dai fatan al'khairi da sa al'barka kawai suke buƙata daga garemu."
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare dayin ƙasa da kanta, sosai taji zuciyarta tayi mata nauyi, yayinda matsanancin rauni ya bayyana acikin idanunta, haƙiƙa ita abu ɗaya take gujewa Saifuddeen shine halin dazai faɗa bayan aurensa da Zaleeha, matuƙar bata sanja hali ba, tasan Saifuddeen bazaiji daɗin zaman auren ba, wanda ita kuma duk wani fata da burinta baiwuce Saifuddeen ɗinta ya samu mace tagari, mai share hawayensa.
Hawayen dake ƙoƙarin cika idanunta ta shanye tare da ɗan sakin murmushi, cikin sanyi tace.
"Babu komai, duk yanda kukace shikenan, dama ni baƙin Zaleeha nake ba kawai dai munanan kalamai da ƙudurinta akan Saifuddeen shine ke bani tsoro, amma zantayi musu addu'a Allah yasa auren yazama alkhairi, wanda kowa zai amfana dashi!."
Cikin jin daɗin sauƙin kai irin na Ummin dukansu suka amsa da "Ameen Ameen."
Nan Dirankadi yace acigaba da shirye shiryen biki kada afasa komai da akayi niya, baiwani jima agidan ba yashiga motarsa inda ya nufi gida, su kuwa su Baffa Ali can cikin BQ suka sauƙa, saboda dare yayi babu yiyuwar komawarsu Dukku aranan, saidai gobe da safe zasu kama hanya.

Jin ƙiran da Baban nata keyi mata yasanya taji gabanta ya faɗi, take tsoro ya shigeta saidai kuma babu yanda ta iya dolenta ta amsa ƙiran nasa, zumbuleliyar hijab ɗinta ta zura, kana tanufi ɓangaren mahaifin nasu.
Da sallama ɗauke abakinta ta kutsa kanta cikin falon,   cikin sanyi Baba Malam ya amsa mata,   ƙarasowa tayi inda ta zauna akan lallausan carpet ɗin dake malale bisa tsakiyan falon, duƙunƙune jikinta tayi acikin hijabin, cikin ƴar siririyar muryarta dake rawa tace.
"Barka da dare Baba Malam!."
Kansa kawai ya jinjina mata alamar "Yauwa."
Aƙalla ta ɗau sama da mintuna 5 baice da ita komai ba, nanfa bugawar zuciyarta ya tsananta, don amatuƙar tsorace take.
Gyara zama Baba Malam yayi tare da fuskantar ta,  cikin kulawa yaƙira sunanta.
Ɗagowa tayi ta kalleshi tare da amsa masa murya na rawa jiki asanyaye.
Ajiyar zuciya Baba Malam ya sauƙe tare da yi mata duban tsab, cikin son tausasa lafuzansa agareta dan yi mta nasihar da wala Allah imaninta zai sabunta cikin kula yace.
"Haƙiƙa kowani uba yana al'fahari da ƴarsa ko ɗansa matuƙar sukayi masa biyayya,."
Sosai lafazinshi ya ratsa jikinta,
Shi kuwa cigaba yayi da cewa.
  "Bazance bana al'fahari dake ba Zaleeha saboda ke jininace, sannan kuma ko ba komai kin amshi zaɓin dana baki, kin kuma yi na am, saidai kuma labari yazo kunnena akan cewar kina rubuta saƙo irin na ɓaƙaƙen maganganu da kuma gargaɗi da barazana da kisan kai kina turawa Saifuddeen".
Tuni jikinta yake tsuma.
  "Kada ki watsamin ƙasa a ido Zaleeha! Dan in kikamin haka ,wallahi Allah zan barranta dake, kada kimin fuska biyu.
tabbas nasan cewa rashin sanin wanene Saifuddeen agareki shiyasa kike wulaƙantasa, yanunamiki ƙauna da gata tun kina ƴar ƙanƙanuwan yarinya, haka kuma har kawo yanzu bai janye ƙaunarsa daga gareki ba,  Saifuddeen maganarci ne wanda nayi imani samun kamarsa nada matuƙar wahala, ba'akowani gida ne ake haihuwar irin Saifuddeen ba haka kuma irinsu basu da yawa acikin al'umma, nazaɓa miki Saifuddeen amatsayin mijine saboda nasan bazaki taɓa danasanin aurensa ba, Saifuddeen bazai barki kiyi baƙinciki ba Zaleeha."
Tuni hawaye ke kwaranyo mata a ranta take faɗin.
"Wannan musakin wanne farin ciki zai samar min,mutun da bashi da bakin da zai furta min kalaman so, mutumin dake kamar dutse duk daɗin kalmar da zan masa ba ji zaiba,
haka zan rayu dashi babu so bare soyayya da ƙauna! muryar baban natane ya katse mata hasashenta. "Zaleeha kina ganin nakasasshe ne ko, to Saifuddeen da kike gani shi zai zame miki GARKUWA sannan bongo majingina na rayuwarki,  shin Zaleeha menene aibun Saifuddeen dan yakasance Nakasashshe? saboda shi nakasashshene shiyasa kawai kike gudunsa? Baki san cewa Nakasa Ba Kasawa Bace Zaleeha, kuma babu nakasasshe sai kasasshe musamman nakasa irin ta Saifuddeen da bata shafi lafiyarsa ba, sannan nakasar zuci itace nakasa ba wai ta gangar jiki ba,  Saifuddeen yana da kyakkyawar zuciya, kyawawan ɗabi'u, kyawawan halayya, ga  wadatan zuci  duk ya haɗa in kuma kyau ne tako ina Allah ya mishi kyau da haiba, haƙiƙa amatsayina na uba mahaifinki, ina matuƙar yi miki kwaɗayin samun managarcin miji kamar Saifuddeen, sanin cewa miƙa aurenki ga Saifuddeen danayi bazaisa nayi dana sani ba, shiya zuciyata ta aminta da shi sosai,  dan Allah Zaleeha, ki nutsu ki dawo cikin hankalinki, ki watsar da duk wani buri ki rungumi auren Saifuddeen amatsayin ƙaddarar rayuwarki,  kin kuma san idan kikayi haka Allah bazai bari ki taɓe ba,  ni mahaifinki ne Zaleeha, idan ban nusar dake ba, babu wani wanda zai nusar dake, saboda haka maganan tura ɓaƙaƙen maganganu ga Saifuddeen banasonshi dan Allah ki daina kinji ko Mamana?."
A hankali ta gyaɗa kanta alamar to yayinda cikin zuciyarta kamar ta mutu dan baƙin ciki.
"Saura ƴan kwanaki kaɗan yazamanto miji agareki saboda haka yazama dole ki girmamasa kamar yanda kike girmamani harma fiye da haka domin shi mijinki ne kuma al'jannarki tana ƙarkashi diga-diginshi ,sai ya ɗaga zaki shiga".
A ranta take cewa.
"Wannan gurgun kam ai ɗaga ƙafarma ba iyawa zaiba." hannu tasa tana share hawayenta jin Baba malam ɗiɓ yaci gaba da cewa. "Saboda matsayinsa na miji agareki yazama dole kiyi masa biyayya da ɗa'a, koda wasa kada kice zaki bijirewa umarninsa, ƙin bin umarninsa tamkar saɓawa Allah Ne saboda haka ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login