Showing 21001 words to 24000 words out of 61846 words

Chapter 8 - Nakasa B Kasawaba Book 2 Complete Hausa Novel

da shewane ke tashi, domin sosai salon na abokan Saifuddeen ya tafi da kowa, sun bala'in burgewa.
Koda suka gama bidirinsu suka koma, nanfa mc yayi gyaran murya tare da ƙiran masu gayya da aiki, ginshiƙai kuma ƙannen ango.
Hohoho inji hausawa sukace abu namu maganin akwaɓemu.
Su Hayatuddeen da Zakariyya Imran da Sulaiman kana isma'il da Faruq ɗan Adda Rahma.
Manyan ƙanne, yara matasa masuji da ƙarfi ajikinsu, ƴan matasan da suke ji da tashen tasowarsu, salon rawar tasuma ta dabance don kuwa saida ango da kansa yashiga tafa musu, don da wani irin ƙayataccen rawa suka shigo cikin filin, nanfa aka somayi musu ihu ana ƙara zugasu kansu na ƙara girma, harta Isma'el ɗan Alhji Kaburu dayake kurma saida ya taka,  sosai Hayatuddeen da abokansa Imran, Sulaiman, Isma'il da ƙanin amarya Zakariyya rawa irin ta zamani sukeyi mai ɗaukar hankali, hakanan jama'an wajen sukaji kwaɗayin yi musu liƙi, don kuwa rawan nasu yayi kyau sosai, nanfa jama'a suka soma yi musu ɓarin kuɗin.
Ango Saifuddeen kuwa sai wani ƙasaitaccen murmurshi yaketayi hannunshi rike da hannun Zaleeha daketa mutsutsun kwacewa, yayinda hawaye ke zubo mata tabbas taron ya haɗu iya haɗuwa irin haɗuwa na kece raini da nunawa sa'a taso ace da wanda take sone take zaune a yanzu ,domin har tsikar jikinta tashi yakeyi yadda hall ɗin ya ricaɓe aketa ɓarin kuɗi, ita da kanta tasan babu ƙaranta a bikin ta kuma yarda komai na alfarma akeyi ta gamsu da ranta mijinta kuma kekyawane irin kyau na kece raini da nunawa sa'a ta kuma gamsu mai cikekkiyar tsabta ne da gayu, kuma masoyine na gaskiya dan taga salon zazzafar soyayyarshi to amman mijinfa bashi da maraba da ginennen taɓo kuma duk haka tasan yazo a ƙirerren lokacine wlh da yazo kafin haɗuwanta da wanda ya taimaketa tabbas yanada nagartar da dole ta soshi to amman a makere yazo, kuma sai takeji can cikin zuciyarta kamar wani abu ke sarrafa mata zuciya,
bata dawo daga duniyar tunaniba taji sauƙan tattausan yatsunshi kan haɓarta da sauri ta ɗan juyo ta kalleshi sai kuma tayi maza ta lumshe idanunta ganin ya ɗaga mata girarshi ɗaya tare da kashe mata ido kana ya ɗan kaɗa mata harshe alamun,
ya dai, kana ya ɗan nago hannunta dake tsarke da nashi bayan hannun nata ya juya tare da manna mata wani irin sassanyan kiss.
wow nanfa masu hoto suka koma kansu.
Cikin farinciki Hayatuddeen yaƙarasa wajen Hammansa nanfa yasanja salon rawarsa, hannun Hamman nasa ya kamo, ahankali yake juya kujeran Hamma Saifuddeen ɗin nasa, hakan yasa abun yaƙara armashi, murmushin farinciki kawai Saifuddeen ɗin keyi, haƙiƙa ƴan uwa da abokansa sun nuna masa tsananin gata, nanfa Hayatuddeen da abokansa suka ciro kuɗaɗen al'jihunsu suka soma zubawa Saifuddeen da Amarya Zaleeha, Zakariyyane yaƙarasa jikin ƴar uwartasa ahankali ya kamo hannuwanta tare da jawota tsakiyan filin, tayi matuƙar mmkin ganin Ya Aminu Ya Ahmad Ya Habu Aunty Shatu Aunty Lubna da Adda Maryam dasu Amira ƙannen ya Aminu sun mata zobe ita da ango Saifuddeen suna mata yayyafin kuɗi, Zakariyya kuwa nan ya riƙe duka hannuwanta, cikin tsananin ƙaunar ƴar uwartasa yasoma ɗan jijjigata hakanne yasa Zaleeha taɗan saki murmushi, nan taɗan soma ƙafafunta, ganin haka yasa gaba ɗaya su Hayatuddeen suka ke wayeta suna rawa, bisa dole Zaleeha ta biyesu suka ɗan soma takawa,don kuwa ansanya musu wata daddaɗan waƙa, wanda ko baka da niyar yin rawa saika taka, bare ita Zaleeha uwar son waƙa da kiɗi haka yasa taɗan saki jikinta bayan anyi musu ɓarin kuɗi sosai takoma kan kujeran ta zauna tana me maida ajiyar zuciya.
Haka dai akayita shagulgula masu ƙayatarwa yan ƙungiyar jonapwd sunyi matuƙar bada mmkin irin kuɗaɗen da suka liƙawa ango, nairori kam awannan rana sunyi kuka sosai, an ɓarnatar dasu baɗan kaɗan ba, sai wajen ƙarfe 10:00 pm, aka kammala gudanar da diner'n, nan kowa yasoma ƙoƙarin tafiya gida, don dayawan mutane amatuƙar gajiye suke, babuma kamar Saifuddeen, wanda dama shi sam bai iya jure wahala, abu kaɗan ke gajiyar dashi, sai yaji duk yazama very weak bare kuma ga hidimar da yasha, yanzuma babu wani abu dayake buri da fatan gani kamar Umminsa, so kawai yake yaje yayi mata complain ɗin gajiyar dake damunsa, kamar yanda sukazo amota ɗaya haka komawarsu ma takasance amota ɗaya, saidai har suka iso gidan ko ƙala baice mata ba, gaba ɗaya gajiya ke damunsa, itama Zaleehan agajiye take hakan yasa ta lafe jikinta ajikin kujeran motar tare da lumshe idanunta da suke cike da bacci.

Jin isowarsu yasanya dakanta ta buɗe murfin motar ta fice, ko tsayawa batayi ba, riganta na sharan ƙasa haka tanufi ɓangaren nasu, don ta zaƙu da ta cire rigan, sam bata wani iya zama da kaya mai nauyi ba, musamman ma wannan dayake wedding gown.

Shima Saifuddeen saita wheelchair dinsa yayi tare da hawa kai, kaitsaye yanufi cikin gidan nasu.
Kasancewar darene babu wani hayaniya, dayawan mutane bacci suke, waƴanda suka dawo daga wajen diner kuwa tuni kowa ya shige ɗaki don ya ɗan huta,  ahankali yake tura wheelchair ɗinnasa har yaƙaraso cikin falon, idanunsa ne sukayi masa tozali da Umminsa dake zaune acikin falon, yana ganinta yaɗan lumshe idanunsa tare da shagwaɓe fuska, murmushi Ummi tayi tare dayi masa duban tsab, tabbas tasan da cewa Saifuddeen bazai taɓa dawowa har ya kwanta  batare daya neme ta ba, tasan dolene zaizo gareta hakanne ma yasa tazauna afalon zaman jiransa, ahankali ya ƙaraso tare da ɗaura kansa akan kafaɗan Ummin, cikin yanayi na zallan shagwaɓa ya ɓata fuska tare da taɓe red colour lips ɗinsa.
Hannu Ummi tasa tashafi lallausan sumar kansa, cikin kulawa tace.
"Ka gaji ko?."
Kansa yajinjina mata alamar "Eh." Tare da ƙara maida kansa jikinta, tamkar wani yaro ɗan shekara shida haka ya koma mata, sakalci haɗi da shagwaɓa kawai yake zuba mata, komai ta cikin body language ɗinsa yakeyi mata,  sosai Ummin ke lallaɓinsa, sarai dama tasan ɗanta bayason wahala, gashi da ɗanbanzan shagwaɓa, abu kaɗan ke wahalar dashi sai dai jarumtar zuciyarshi na danne sakalcinsa, lallaɓasa Ummi tayi tare da cewa.
Yaje yayi wanka, tun tuni dama tasa anshirya musu abinci akan dinning area.
Da ƙyar Ummi ta iya lallaɓasa yabar part ɗin nata, yana fita yasamu su Ahmad da su Ishaq wai zasuyi masa rakiya zuwa wajen amarya, nanfa yace musu ya gode, ganin cewa dama suma sungaji yasa suma basu matsaba, nan kowa yanemi inda zai huce gajiyarsa, Ahmad da Saminu kuwa kowa matarsa ya kama suka ƙule aɗaki.

Cikin nutsuwa Saifuddeen ya kutsa cikin ɓangaren nasu, babu kowa acikin falon sai daddaɗan ƙamshin turaren wuta, dubansa yakai ga ƙofar bedroom ɗin na Zaleeha, nan yagansa agarƙame, baiwani damu ba yanufi ƙofar dazata kaisa zuwa falonsa, don kuwa  dole sai yabi ta falon Zaleehan kafun yasamu kansa cikin nasa falon.
Yana shiga haɗaɗɗen falon nasa kai tsaye ɗaki ya nufa, kayan jikinsa ya shiga ragewa, saida ya rage dagashi sai gajeren wando sannan ya nufi toilet, shida kansa ya haɗawa kansa hot water acikin bathtube, kwanciya yayi lub aciki tare da lumshe idanunsa, sosai yaji daɗin ruwan don ahankali yaɗanji gajiyan jikinsa naɗan warwarewa,  wanka yayi insa ya fito daga cikin bathroom ɗin bayan ya ɗauro alwala, koda ya fito wata marroon ɗin jallabiya ya sanya, duk da akwai gajiya ajikinsa ko kaɗan hakan bai hanasa yin sallah raka'a biyu ba yana idarwa ya shafa addu'oinsa sannan yabi lafiyar gado, light off na wutan ɗakin yayi tare da jawo blanket ya rufa ajikinsa, lumshe idanunsa yayi, sannu ahankali tunanin matarsa ke mamaye zuciyarsa,  ahaka bacci mai nauyi ya ɗaukesa.

Washegari
Ƙiran sallan asuban fari ya farka, nan yatashi tare da faɗawa bathroom yayi wanka haɗi da ɗauro alwala, koda yafito dogon wandon jeans da kuma white crazy shirt yasanya ajikinsa, sosai kayan sukayi masa kyau, kan kekensa ya hau inda ahankali ya buɗe ƙofar ɗakin ya fice.
Cikin nutsuwa yake tafiya da keken nasa har yakawo cikin falon na Zaleehan, ɗan shiru yayi ganin wutan ɗakin a kunne da kuma alamun motsi acikin ɗakin nata yasa kansa tsaye yafice daga cikin falon, don ya tabbatar da cewa tatashi sallan asuba ne.

Direct masallacin dake gefen gidannasu ya nufa.
Zaleeha kuwa fitsarine ya tasheta koda taga lokacin sallan asuba yayi kuwa shine taɗauro alwala, nan tazo tayiwa Zaheera dake kwance akan doguwar kujeran dake cikin ɗakin tashin duniya amma Zaheera taki tashi, sabida gajiyan hidimr daren jiyan hakan yasa dole Zaleeha ta ƙyaleta, nan ta shumfuɗa sallaya inda ta tayar da sallah,  tana idarwa ta soma gabatar da azkar ɗinta, koda ta gama, wayarta ta jawo inda ta shiga Qur'an app nan ta buɗe suratul baƙara ahankali cikin zuciyarya take karatun sai dai tana farawa kasala da wani gyangyaɗi mara tushe ya rufeta ta rasa meyasa haka cikin kwanakin nan duk sanda zatayi niyar yin karatu sai taji wannan yanayi da kyar take iya farawa dai.

Ɓangaren Saifuddeen ma kuwa tunda yayi sallan Asuba yana nan zaune acikin masallacin, karatun Al'Qur'ani yayi sai 7 dai-dai yabar cikin masallacin, kaitsaye ɓangaren Umminsa ya nufa, dan zuwa gaisheta, kamar yanda ya sabar mata kowacce ranan duniya.
Yana shiga yasameta tana zaune afalo, yayinda gidan yayi shiru duk ana maida baccin da ba'ayiba Daren jiyan shiyasa ita da kanta ta shiga kitchin,
hannunta riƙe da carbi tana ja,  rusunawa yayi agabanta cikin girmamawa yagaisheta cikin body language kamar yanda ya saba.

Ko gama dai-daita zamansa baiyiba fitinannen ƙamshinta yayi masa sallama a hanci, lokaci guda kuma saigata tashigo cikin falon, sanye take da hijab wanda takawo har zuwa ƙasa, sosai hijab ɗin yayi mata kyau, cikin nutsuwa taƙaraso cikin falon Ummi naganinta tasaki murmushi tare da miƙo mata hannu, gefenta ta zauna, har ƙasa ta durƙusa cikin tsananin ladabi da girmamawa tace da Ummi
"Ina kwana?."
da "Lafiya Ummi ta amsa tare da tambayarta ya kwanan baƙunta? ɗan murmushin daya ƙara bayyana zallan kyawunta tayi cikin nutsuwa tace.
"Alhamdulillah!."
Da "Masha Allah!!." Ummin ta amsa, still fuskarta ɗauke da murmushi, hakanan taji wani irin daɗi ya ratsa zuciyarta don kwata-kwata bataiyi zaton haka yarinyar keda ladabi ba, shiru tayi tana kallon yatsun ƙafan Ummi haka nan taji son Ummi cikin ranta,
cikin kula da sonta Ummi ta ɗan sunkuyo ta kalleta cikin sanyi tace.
"Ngd ɗiya Allah ya muku al'barka ya bamu zaman lfya."
cikin tsunkuyar ds kai da alamun jin kunya murya can ƙasa tace.
"Amin Ummi."
cikin kula Ummi tai murmushin jin daɗi tare da cewa.
"Tashi kije ki kwanta kiyi bacci ki huta gajiyan biki."
Cikin jin daɗi ta gyaɗa kai kana ta miƙe hankali tare da ficewa daga cikin falon, ko kallon inda Saifuddeen yake batayi ba, hasalima yi tayi kamar batasan da wani abu waishi mutum awajen ba, ita kuwa Ummi bataji wani abu akan rashin kula Saifuddeen ɗin da Zaleehan tayi ba, domin azotonta sunyi nasu gaisuwar a ɗaki, domin duk atunanin Ummin Saifuddeen ɗin aɗakin Zaleehan ya kwana.
Zaleeha na tafiya Saifuddeen yaɗan zubawa Ummi shagwaɓansa sannan ya nufo part ɗin nasu.

Koda ya shigo cikin falon zaune ya iske ƙanwarta Zaheera ta ƙurawa tv ido, inda take kallon wani series film a mbc bollywood wato (حب خادع) nasu tara da deep, kasancewar sosai dukansu ita da Zaleeha keson series film ɗin.
Tana ganin Saifuddeen taɗan zamo daga kan kujeran gaishesa tayi, yayinda shi kuma ya amsa mata cikin jinjina mata kai, fuskarsa ɗauke da ɗan murmushi, kai tsaye ɗakin Zaleehan ya nufa, don rashin ganinta afalo da yayi ya tabbatar masa cewa tana cikin ɗakin, ahankali yakai hannunsa inda ya murɗa handle ɗin ƙofar, kana ya shiga, tsaye take agaban gado tana ƙoƙarin zuge zip ɗin rigarta dake a wawage, yayinda white skin ɗin bayanta keta shinning, jin motsin anshigo ɗakin yasanya batare da ta juya ba tace.
"Zaheera zoki zuge min zip ɗin nan please."
taƙare maganar tana me watsa dogon gashin kanta akan wuyanta.
Ahankali ya danna madannin wheelchair ɗinsa, take keken tasoma tafiyu as slowly, yana ƙarasawa gab bayanta ya tsaya cak, hannunsa yakai kan lallausan skin ɗinta, jin sauƙan wani lallausan hannu abayanta wanda sam baiyi kama dana ƙanwarta Zaheera ba yasan yata juyowa da sauri.
Idanunsune suka faɗa cikin na juna take kuma losing balance ya kamata nanfa ta faɗo kansa, hannayensa duka biyu yasa inda ya rungumota jikinsa, azabure cikin matsanancin tsoro ta turesa tare da tashi tsaye, cikin fushi tace.
"Waya baka izinin shigomin ɗakina, har takai ka gayin azarɓaɓin taɓa mini jiki? ko an faɗa maka cewa na nemeka ne."
tura baki tayi tare da dubansa cikin shakkarsa da takaicin aurensa da tayi tace.
"Ni jikina na mutum ɗaya ne, kuma zan cigaba da adana masa kaina, sannan jikina bana musaki bane, jikina na cikakken namiji mai lafiya ne, halan ko kamanta cewa kai Nak...."
Batare daya bari ta gama magananba ya wani irin fusgota ta faɗa jikinsa, hannunsa yasa inda yayi mata wani irin tsastsauran riƙo, cikin tsoro da fargabar zuciya ta ɗan kalato tsiwa tace.
"Da Allah ni kasakeni, na tsani haɗa jiki da kai!."
Ahankali yaɗan lumshe idanunsa wanda suka ɗan sanja launi, laɓɓan bakinsa yaɗan cije,
"wato shi nakasashshe ne saboda haka bazai iyayi mata komai ba ko? hmmm zaiyi maganinta ne."
yafaɗi maganar acikin zuciyarsa.
hannunsa ɗaya yasanya ya tallafo fuskarta, ganin haka yasa Zaleeha waro idanunta, cikin mamaki ta ɓuɗe baki tare da da cewa.
"Kai Malam da Allah miye haka zaka...."
Kamar amafarki haka taji sauƙan bakinsa acikin nata, yayinda yasa hannunsa ya riƙe kanta da ƙarfi, tayanda bata iya ƙwacewa ba, idanu Saifuddeen ya lumshe tare da kamo sweet lips ɗinta yana tsotsa, cikin son ladabtar da ita ya shiga tsotsan bakinnata da ƙarfi ƙarfi, inda har teeth ɗinsa yake sanyawa akan lips ɗinta yana ɗan cizonsu, harshensa yasa ya naɗo nata harshen tare da kanainaye mata harshen take yashiga musanya yawunsu, firgici da takaici haɗi da tashin hankali Zaleeha kam tashigesu, sosai take son ƙwace kanta daga azabar tsotsar lips ɗinta dayakeyi amma takasa.
Idanuntane suka ciko da ƙwalla, take tasoma dukan ƙirjinsa da duka ƙarfinta amma ina Saifuddeen ko gizau, saima ƙara zafafan tsotse laɓɓanta da yakeyi da ƙarfi.
Azaba kuwa da zafi har cikin kanta, dan kansa ya janye bakinsa daga nata tare da hankaɗata kan gado, baya yayi da kekensa tare da dubanta giransa ɗaya ya ɗage mata tare dayi mata alaman to ya?
Kuka mai cin rai tafashe dashi cikin matsanancin takaici haɗi da sabuwar tsanarsa tace.
"Allah Ya isa na bazan taɓa yafe makaba mugun mugaye kawai, wanda babu abun daya sani sai son kai dana zuciya."
hannu tasa tana goge harshenta data ɗan zaro kana idonta na zubda siraran hawaye tace.
"Allah ya isana kuma Allah zai saka min"
Murmushin daya bayyana tsantsar kyawunsa yayi ahankali ya ɗage kafaɗunsa alaman ko oho, madannin kekensa ya danna tare da juyawa ya fice daga cikin ɗakin, tana ganin fitarsa ta silalo daga kan gadon zama tayi aƙasa tare da sakin kuka, cikin matsanancin takaici tashiga harba ƙafafunta tamkar ƙaramar yarinya ƴar shekara 6, ji take kaman tayita zabga ihu na baƙin cikin abunda yayi mata, ga kuma bakinta dake masifar yi mata raɗaɗi harshenta kuwa har jinsa take kaman baya cikin bakinta, laɓɓɓanta sai wani zut-zut sukeyi, kuka takeyi tsakananinta da Allah tana harba ƙafafunta, cikin kukan tace.
"Bazan taɓa yafe maka ba, mugu nakasashshe mai zubin ƴaƴan ruwa, wallahi ayau plant ɗina zai fara aiki bama sai gobe ba, don in na zauna da kai zalina zakayi taci."

A garin Doho kuwa Mamace da yayarta Ruda ke zaune gaban wani shirgegen kasurgumin bokansu na arnan kan dutse bayan ya gama jin baya nansu sun gama tattaunawa, zuru-zuru yayi da ida nunshi tare washe wawakeken bakinshi cikin amo mara daɗin ji yace.
"Kada ku damu, bazata zaunaba dan sihirin ya kamata, munyi sa'a lokacin da mukayi aikin bata salla, sihirin yana ƙarƙashin gadonta bazata iya zama cikin ɗakinba dole, zata gudu zata bar gidan babu zama da wannan gurgun, dan tuni mun gama aikinmu babu wanda zatayiwa biyayya akan zama a gidan, dan ji zatayi kamar cikin kushewarta take, mutanenmu zasu sa mata tsanan gidan da mijin sosai."
cikin jin daɗi Ruda tace,
"Yauwa boka bashallu mun gode."
Mama kuwa kai ta jinjina tare da cewa.
"To amman ya batun aurenta da Abdussalam?."
kai ya jujjuya mata tare da zaro idonshi yace.
"Ki bari kiga mun samu mun raba wannan aurenma tukun, dan shi yaron da wuya mu sameshi."
jin haka Ruda tace.
"Mun gode a gama wannan ɗin kafin a fara wani."
itama Mama godiya tayi kana suka ajiye mishi kuɗin aikinshi suka tafi.


~Wasa farin girki~




By
*GARKUWAN FULANI*[9/9, 9:05 PM] +234 806 222 4030: Cikin bedroom ɗin ta da nufin zataje ta sanarwa Ahmad,
ko meye ta tuna kuma, oho sai ta koma ta zauna tana nazari.
Sosai abun yayiwa Raliya ciwo, koda Ahmad ya fito ganin meya tsareta,  kamar zata faɗa masa saikuma tayi shiru, shi kuwa da bai san meke faruwaba sai janta yayi suka koma bedroom ɗinta dan yana tare da begenta.

Ɓangaren Saifuddeen kuwa kwata-kwata ma bai nemi Zaleehan ba, yana fitowa daga wanka kwanciya kawai yayi,  sam bayaso yaje gareta, harma yaga abun da zai rabasa da nutsuwarsa, dan shikaɗai yasan irin azaban dayasha jiya, saboda haka baya sake fatan shan wani azaban kalan wannan, kasancewar agajiye yake hakan yasa yana kwanciya bacci ya ɗaukesa.
Zaleeha kuwa gaba ɗaya tatakura akan kujeran da take kwance, sam kujeran bata da daɗin kwanciya bare daɗin bacci, cikin mintuna ƙalilan har jikinta yasomayi mata ciwo, gawani irin masifaffen sanyi dake busawa acikin garden ɗin, mutsutstsuka jikinta kawai takeyi, sosai takejin wuyanta ya ƙage amma kuma bata da wani zaɓi, wanda ya wuce yin haƙurin kwana awajen.
Atakure haka bacci ɓarawo yasamu nasarar ɗaukarta.

Ƙiran sallan asuban fari da akeyine ya ratsa jikinshi ya bashi lokacin salla yayi, ahankali ya buɗe idanunsa,  ɗan miƙa yayi tare da haɗawa da salati a zuciyarsa, nan yatashi zaune, kekensa ya jawo tare da hawa kanta, cikin nutsuwa da ɗan sauran kasalan bacci yakai kansa banɗaki, wanka yayi tare da ɗauro alwala, kaitsaye yafice daga ɓangaren nasa.
Har yaƙarasa jikin ƙofar na Zaleehan saikuma wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login