Showing 24001 words to 27000 words out of 61846 words
Chapter 9 - Nakasa B Kasawaba Book 2 Complete Hausa Novel
tunani yazo masa, take yafasa shiga tada'ita da yayi niyya, sai ya ƙonƙasa mata ƙofar, kana ya juya ya tafi,
kai tsaye yawuce masallaci.
Zaleeha kuwa dama gaba ɗaya batayi wani ishashshen bacci ba, dan sanyine awajen sosai, jin motsi alaman cewa yatafi masallaci yasata tashi zaune, cikin sauri ta ɗau bargon haɗi da pillow'n ta, ahanzarce tanufi ƙofar falon nata, dai-dai lokacin Ahmad yafito daga ɓangarensu dan zuwa masallaci, idanunsa ne suka gane masa Zaleeha, fuskarsa ɗauke da ɗan mamaki yabita da kallo, ganin fitowarta daga cikin garden gashi hannunta riƙe da bargo da kuma pillow alamun nan ta kwana kenan yasanyashi girgiza kansa, cikin ransa yace.
"Allah Ya shirya ki, ae dama mai hali baya taɓa fasa halinsa, saidai in ba'a zauna ba kuma dai duk tsaurin wayon amarya to wlh sai ansha manta anci sadaki an suɗe ki dai gama ɓoye-ɓoyenki."
Nan yawuce masallaci.
Itakuwa Zaleeha sam-sam ma bataga Ahmad ɗin ba, kaitsaye ɗakinta ta wuce, cikin hanzari tasoma rage kayan jikinta, ruwan ɗumi ta haɗa inda tayi wanka, tana fitowa daga wankan ta zura wata farar jallabiya mai kyau, hijab tasanya tare da ta da sallah, koda ta idar da sallan bata tashi akan sallayan ba saida tayi azkar, nan ta ɗauko ɗan ƙaramin Qur'aninta tasoma karatu, ba'ita ta rufe Qur'anin ba saida taga gari yaɗan somayin haske,
wasu bedroom slippers masu kyau ta zura aƙafafunta, inda tasake feshe jikinta da turare me daɗin ƙamshi.
Koda tafito daga ɓangaren nasu kai tsaye part ɗin Ummi ta nufa, bakinta ɗauke da sallama haka ta kutsa cikin falon, wanda ke cike da jama'a, Raihana ne da Saminu waƴanda zasu koma Kaduna asafiyar ta yau, saikuma Goggo Dada da Aunty Meena wanda zasu koma Dukku, Aunty Rahama ma yau zata koma, don tunjiya Dr.Adnan keyi mata waya, kan cewar yayi kewarta gashi weekend yana gida shiyasa yace zaizo da safen ya ɗauketa.
Cikin yin ƙasa da kai haɗi da nuna tsantsar ladabi taƙaraso cikin falon, har ƙasa ta durƙusa inda ta gaishe da Ummi, cikin fara'a haɗi da sakin fuska Ummi ta amsa mata gaisuwan nata, tare da miƙo mata hannu ta kamo nata, cikin kulawa Ummi tace.
"Taso kizonan kusa da Umminki yarinyar kirki, kema ai ɗiyatace, tunda kika shigo cikin mu kuwa kinzama jininmu."
Tasowa tayi daga inda take tare da ƙarasowa kusa da Ummi,
Ummi ne tajawota inda ta zaunar da ita agefenta, sadda kai ƙasa Zaleeha tayi tana murmushi, hakanan itakam Allah ya samata son matan aranta, sosai take ganin ƙima da kuma darajan Ummi'n, su Raihana ne suka gaishe da Zaleehan, amatsayinsu na ƙannen Saifuddeen, haka ta amsa musu fuska asake, ɗan zamowa ƙasa tayi inda tagaishe da Goggo Dada dakuma Aunty Meena, sai kuma babbar yaya wato Adda Rahama, da kuma Saminu wanda ke zaune gefen Saifuddeen, da fara'a akan fuskarsu duka suka amsa gaisuwar nata, komawa gefen Ummi tayi ta zauna a ƙasan carpet dan tana matuƙar ji da ganin darajar Ummi, shiru tayi yayinda ko kallon inda Saifuddeen yake batayi ba, shikuwa har acikin ransa mamakin irin tsantsar ladabinta ga ƴan uwansa yake, tanason kowa acikin ahalinsa tana mutuntasu da girmamasu, amma wato shine marainin wayonta sam bata ganinsa da gashin ido, murmushi yayi wanda shi kaɗaine yasan ma'anonin murmushin ransa yace.
tabbas kuwa zanyi maganinta ne, very soon zankashe bakin tsiwan, badai ni ta raina ba?."
hmmm yasha alwashin duk randa ya kamata kuwa zataji ajikinta.
Saminu ne yace da Raihana su hanzarta sutafi, bayason tafiyar da bata safiya ba, saboda alokacinne yakejin karsashi ajikinsa, nan kowa yatashi don yi musu rakiya zuwa compound ɗin gidan, ciki kuwa harda Zaleeha wanda ta kamo hannun Daddy yaron Bappa Ali wato Junior mai sunan Abbandu Saifuddeen kenan, kasancewar yaron kyakkyawane yasanya sosai yashiga ranta, gashi nan da wayonsa irin yaran nanne masu shiga zuciya, haka suka fito compound ɗin gidan inda yaketa zuba mata surutu, itakuwa murmushi kawai take tayi masa, har bakin mota suka rako su Raihanan, nan sukayi sallama da juna, cikin yanayi na tsokana Raihana ta dubeta, tare da cewa.
"Kikulamin da Hammana da kyau da kyau, dan ko ƙuda bama son ya taɓa manashi."
Dariya sukayi gaba ɗayansu,
itakuwa Zaleeha ɗan guntun murmushi tayi, yayinda taji wani malolon abu ya tokare maƙoshinta, cikin zuciyarta tace.
"Lallai kuwa zai mutu, indai nice zan kula dashi!.
Yo ni me haɗina dashi kunamai ma su sauƙa ajikinsa mana ba ƙuda ba ni me yadameni."
Motar su Raihana baigama fita daga gidan ba saiga Dr.Adnan nan shima yazo ɗaukar matarsa, nanfa suka gaisa, inda Zaleeha tagaishesa cikin mutuntawa, Farouq da Adam kuwa sai tsalle suke dan sunga babansu, duk girmansu baigani ba haka yasasu ajikinsa, babu yanda basuyi ba akan cewa Daddy yazo su tafi ba amma yaƙi, waishi ala dole yasamu sabuwar Aunty yace shi Dukkunma bazai komaba, kusan saida yabawa kowa dariya haka suka tafi anata raha.
Daddy kuwa da ƙyar suka iyayi masa wayo yabi iyayen nasa da karatunshi, Ahmad ne yazo da motarsa wanda dama shine zai mayar dasu Goggo Dada gida, lokaci ɗaya fa gaba ɗaya jama'an baƙin biki suka watse gida yayi shiru.
Ummi Raliya da kuma Zaleehan kawai aka bari, dama Saifuddeen yana part ɗin Ummi, kasancewar shi baifito rakiyan ba, shikuwa Hayatudden sarkin bacci, yanacan tun dawowansa daga sallan asuba daya koma bacci shine haryanzun baitashi ba.
Direct Zaleeha part ɗinta ta koma, inda su Ummi da Raliya suka koma wajen Saifuddeen.
Tana shiga cikin ɗakin nata ta cire hijabin dake jikinta, kan gado ta faɗa tare da ɗan lumshe idanunta, sosai takejin wani sabon bacci naƙoƙarin ɗaukarta.
Can ɓangaren Ummi kuwa, Saifuddeen naganin dawowansu, ya sakawa Ummin nasa shagwaɓa, sanin halinsa na sakalci kaman wani ƙaramin yaro yasanya Ummi da kanta tashiga kitchine inda ta haɗa masa coffee, sosai yaji daɗin haɗin coffee ɗin da Ummin tayi masa, ɗaukan mug ɗin yayi tare da bar musu falon, kai tsaye yanufi sashinsu.
Saifuddeen nafita, Ummi tayi murmushi cikin jin daɗi tace.
"Allah kenan maiyin yadda yaso a lokacin da yaso, kafun auren nan kowa yasan cewa yarinyar nan bason auren nan take ba, amma yanzu cikin ƙuduran Allah gashi suna zaune lafiya, kinga ta saki ranta."
Murmushin gefen baki Raliya tayi tare daɗan muskutowa, cikin jimamin abun dake damun zuciyarta tun daren jiya tace.
"Hmmmm hakane kam Ummi, amma nikuwa jiya naga abun daya ɗauremin kai ya bani mmki, dan nima da fari da naga ta saki ranta naji daɗi."
Dubanta Ummi tayi tare da cewa.
"Mene kuma yafaru?."
Gyara zama Raliya tayi tare da cewa.
"Ummi kinsan kuwa cewa jiya awaje cikin garden ta kwana? wallahi Ummi abun yabani mamaki sosai, inata tunanin dalilin da zaisa ta kwana cikin garden, idan har zatana gudunsa haka, meyasa ta amince da aurensa?."
Cikin matsananci mamakin jin maganan da Raliyan ta faɗa Ummi ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya, jiki amace tace.
"Raliya kin tabbatar da abun da kike faɗa kuwa?."
Kai Raliya tajinjina tare da cewa.
"Wallahi Ummi da idanuna naganta jiya a garden ta kwana, kuma koda natashi sallan asuba dana leƙa naganta, alokacin tana ƙoƙarin barin wajen, kuma tabbas nasan babu makawa itace dan Abban Farida ma ya ganta dayazo tafiya masallaci."
Ɗan jim Ummi tayi tare dajinjina kanta, take taji zuciyarta tayi mata wani irin ba daɗi, hankali ya tashi fargaba ya cika mata zuciya wato har ƙiyayyar ta kai haka, jiki a mace tace.
"To Allah dai ya kyauta."
Amin Amin Raliya ta amsa jiki a mace.
Haka dai zaman yaci gaba da gudana har tsawon kwanaki, Kullum in gari ya waye Zaleeha na idar da salla zataje ta gaida Ummi a mutunce, lokuta da dam takan samu Saifuddeen a wurin Ummi, amman tsakaninta dashi sai harara da murguɗa baki,
tana son kowa na gidan yayinda suma duk suke matuƙar sonta musamman Raliya da takanje har ɗakin Zaleeha su ɗanyi hira,
dan itacema ta tayata shirya tarin akwatunan kayan aurenta da kimtsa mata duk abinda zata buƙata a durowa, sauran akwatunan suka kaisu ɗaya ɗakin,
Hayatuddeen kuwa dama akwai sabo a tsakaninta haushinta da yaji kan cewa da tayi bata son Hammanshi yanzu babushi tunda yanaga har ta yarda da auren ta zauna lafiya dashi.
tana matuƙar girmama Ummi wanda hakan yasama mata soyayya a idanunsu,
tana mutunta Ahmad a cewanta mai sunan yayanta ne dan Yaya ma take kiranshi tun tana gaidashi yana amsawa a yatsine har dai ya fara ɗan sasaautawa.
Har yau kuma a woje take kwana cikin gardin,
wannan abun shine yasa Ahmad yake matuƙar jin baƙin cikinta,
shi kuwa Saifuddeen da fari baisan bata kwana a ɗakintaba dan baya shiga kuma da safe yana ganinta a wurin Umminshi,
To tun shekaran jiya daya dare ya ankara da bata ɗakin, ya dudduba ko ina na cikin part ɗin nata babu ita ba dalilinta, falonshi ya koma wayarshi ya ɗauka tare da yin mgnar zuciya,
"To ina take zuwa ta kwana yau kwana biyu kenan bata kwana a nan."
Kanshi ya ɗan jingina da jikin kujerarsa tare daci gaba da mgnar zuci.
"To waya sanima ko ta daɗe da barin kwana a nan."
sai kuma yayi ajiyan zuciya tare da cewa.
"ko dai part ɗin Ummi take kwana? kai Anya kuwa Ummi zata barta ta kwana a side ɗinta,
to ko dai part ɗin Raliya take kwana."
Text ya rubutawa Ahmad,
"Kayi bacci ne?."
Ahmad da ke zaune a falo shida Raliyya suna mgnar Zaleeha dan hango wucewarta da sukayi,
murya a sanyaye Raliya tace.
"To wai ko dai Hamma Saifuddeen bai san bata kwana a ɗakinba?."
Ajiyan zuciya Ahmad ya sauƙe tare da cewa,
"Ina zaton bai saniba, kinfa san shi da miskilanci, in kuwa yasan bata kwana a cikin to yasan inda take kwanan shiyasa bai kulataba ai jiki magayi."
da sauri ya ɗago wayarshi ganin saƙon Saifuddeen ne ya sashi cewa.
"To ina ga dai bai san bata kwana cikiba sai yanzu dan ga text ɗinshi wai nayi bacci ne."
ido Raliya ta zuba fuskar wayarshi tana ganin amsar da yake rubuta mishi.
"A a banyi bacci ba, lfy dai ko?."
jim kaɗan sai ga wani saƙon.
"To lafiya dai zance,amman Zaleeha na wurinku ne?."
murmushi Ahmad yayi tare da cewa Raliya,
"Hmmm zanyi mgnin yarinyar nan."
sai kuma ya rubuta mishi amsa.
"A a Zaleeha kuwa, bata nan."
a take sai ga wani saƙon.
"Kasa Raliya ta dudduba nan wurinku, taje Side ɗin Ummi ma ta duba ko tana can."
yana gama karan tawa yace.
"Lafiya dai kam ko?."
tsaki Saifuddeen ya ɗan ja kana ya rubuta mishi,
"Nima ban saniba lafiya ko ba lfy ba, ina dai zargin yarinyar bata kwana a gidan nan, dan tun shekaran jiya na lura babu motsinta, sannan yanzu na dudduba ko ina bata ciki side ɗin."
cikin nuna fargaba Ahmad yace.
"Innalillahi, to ina take zuwa ta kwana, gani nan fitowa."
sai ya kuma miƙe ya kalli Raliya tare da cewa,
"Maza kije side ɗin Ummi ki gaya mata, ana neman Zaleeha ki kuma ce karta nuna tasan inda take kwana zanyi mgninta."
to tace tare da juyawa ta nufi side ɗin Ummi,
kana shi kuma Ahmad ya nufi ƙofar falon Zaleehan nan yayi kicibis da Saifuddeen daya fito,
"To wai ina ta shigane, mufa mun dudduba wurinmu babu ita."
kai ya jujjuya mishi alamun shimafa ya dudduba wurinsu babu ita.
dai-dai lokacin kuma Ummi da Raliya suka iso, nan fa suka haɗu suka nuna basu san inda takeba.
ita kuwa Zaleeha tun fitowan su Ahmad ta buɗe ido,
jin ita ake nema yasa ta zame a hankali ta konta a ƙasan kujerar fulawi ke zagaye da ita.
Ahmad kuwa yana hangota hakan ya sashi cewa.
"Hmmmm zaki gane kurenki."
wayarshi ya zaro lallatsata yayi ya nemo number Ya Aminu,
ya kirashi kana ya kara wayar a kunnenshi.
Can cikin bacci Ya Ameenu yaji wayarshi nata suwa,
a hankali ya ɗan zare Maryam daga jikinshi,
hannu yasa ya ɗauki wayar time ya duba ƙarfe ɗaya na dare.
"Ahmad kuma a daren nan lfy kuwa?."
sosai yaji fargaba ,kar dai Zaleeha nacan na tarfa musu rashin ɗa'a, jiki na rawa ya amsa kiran cikin sauri yace.
"Salamu alaikum ,Ahmad lfy kuwa?."
cikin nuna tashin hankali yace.
"Ya Ameenu Zaleeha ce bamu ganiba mun nemata ko ina a gidan babu ita ba dalilinta,
kuma Saifuddeen yace tun shekaran jiya bata kwana a side ɗinsu,
to sai yayi tunanin wai ko side ɗinmu take shigowa ta ɓuya ko na Ummi,
to shine yanzu ya sanarmana zatonsho tana wurinmu,mun duba kab gidan bata, nan shine nace bari in kiraka ko ta dawo gidane?."
cikin kaɗuwa Ya Ameenu ya miƙe tare da cewa.
"Zaleehan to ina take zuwa?."
a taƙaice Ahmad yace.
"To ko tana gida ne?." rai a ɓace Ameenu yace.
"Kai anya kuwa sam bata gida, to ina take zuwa ta kwana, yi haƙuri bari in kira Baba malam."
to Ahmad yace kana ya katse kiran sannan ya gaya.musu yadda sukayi da Yayanta Ameenu,
kana yace su shiga ciki kafin Ameenun ya kirashi.
Shi kuwa Ya Ameenu wani irin tashin hankali ne da ɓacin raine mai tsanani ya rufeshi to ina Zaleeha take zuwa ta kwana ina take tafiya ta bar ɗakin mijinta me haka yake nufi?
kiran Baba Malam yayi bawan Allah yana zaune bisa sallaya yana karatun qur'an kiran Ameenu ya shigo wayarshi,
har wayar ta katse bai ɗaukaba duk da yaga Aminune so yake yaje ƙarshen surar Arrahaman da yake karantawa,
yayinda wani fargaba ya rufeshi lfy kuwa kira da tsakiyar daren nan.
Yana zuwa ƙarshen surar kira na uku na shiga wayar, da hamzari ya amsa kiran,
"Barka da dare Baba Malam kayi haƙuri na tada kai daga bacci."
Ameenu ya faɗa a ladabce,
murya a ɗan harɗe Baba Malam yace.
"Ameenu lfy kuwa meke faruwa?."
cikin sanyi Ya Ameenu yayi mishi bayanin da Ahmaɗ yayi mishi, ya ƙara da cewa.
"Ko dai ta taho gida ne?."
lumshe ido Baba Malam yayi yana jin wani irin suya da zuciyarshi keyi me Zaleeha ke nufi zubda mishi mutunci da kima a idanun mutane ko?
a hankali ya cewa Ameenu.
"Ameenu bana zaton tana cikin gidana ,bazata zo nanba, amman dai bari in bincika."
to Aminun yace kana y katse kiran.
shi kuwa Baba Malam fitowa yayi da kanshi yayi tabin luggu da saƙo na gidan ya duba ko ina kab babu ita, koda ya titse Mama da tambayar ina Zaleeha ke zuwa ta kwana,
rantse-rantse tayi ta mishi akan ita bata san ina Zaleeha ke zuwa ta kwanaba.
a daren Ameenu ya kira goggonsu Maryama da duk inda suke zaton zataje ko ina sai ace musu bata zoba.
Wannan abu yayi matuƙar tada hankalin Baba Malam ya Ameenu kuwa ji yake in yaga Zaleeha zai kusan karta,
dole ya kira Ahmad yace,
wlh bata wurinsu amman tunda da safe tana dawowa zai zo ya sameta, har ɗakinta.
Da wannan kowa ya koma ɗakinshi, Ahmad kuwa ranshi ƙal yasan Zaleeha zata gane kurenta.
Washe gari kamar yadda ta saba, suna tafiya masallaci ta koma ɗakinta wonka tayi da ruwan ɗumi wai ko tsamin cizon sauro da jikinta keyi zai ragu, wanka da al'wala tayi,
kana ta fito tazo tayi salla koda ta idar azkar tayi sanan ta miƙe ta kimtsa jikinta cikin wata doguwar rigar mai ɗan karen.kyau wanda duk na kayan aurene, da mayafinshi ta yane kanta ,kana ta nufi sashin Ummi.
a falo ta samesu, dukansu, cikin nitsuwa ta isa gaban Ummi dake mata murmushi tare da cewa.
"Gari ya waye ko ɗiyata?."
murmushi tayi tare da rusunawa gaban Ummi cikin ladabi da sanyin lafazi tace.
"Ummi Ina kwana?."
cikin kula Ummi tace.
"Lafiya lau ya baƙunta?."
kai a sunkuye tace,
"Alhamdulillahi."
"Masha Allah." cewar Ummi kenan
Hayatuddeen ne ya gaidata ta amsa fuska a sake, kana ta kalli,
Ahmad dake zaune kusa da Saifuddeen bisa alamu lissafi sukeyi,
cikin sanyin sauti tace.
"Yaya ina kwana?."
a taƙaice yace.
"Lafiya lau." daga nan kuma sai ta miƙe tare da cewa Ummi .
"Raliya na kitchen ko?."
cikin jin daɗi Ummi tace.
"A a tana sashinta yau wai kanta ke ciwo."
a hankali tace,
"Ayyah ban saniba Allah ya bata lfy."
Amin Amin Ummi tace,
Kana sai ta ɗan rusuno tare da cewa,
"To Ummi bari in shiga kitchen, me zan haɗa mana breakfast?."
sosai Ummi take jin daɗin yadda take sakewa da Raliya su shiga kitchen tare, gashi yanzu har tana shiga ita ɗaya ma tayi musu girki.
cikin kula Ummi tace.
"Bari inzo mushiga tare to."
da sauri tace .
"A a Ummi ki bari zan iya ki huta."
sai kuma ta kalli Hayatuddeen daketa murmushi tace,
"Zo muje kitchen ka tayani hira."
da sauri ya miƙe yabi bayanta, yana cewa.
"Yauwa muje ki min dege-dege."
da ido Ummi ta bisu har suka shiga kitchen ɗin.
koda suka ƙarasa cikin kitchine ɗin, hayewa kan wata kujera Hayatuddeen yayi ya zauna, wayarsa ya fiddo daga aljihunsa tare da soma latsawa, ita kuwa Zaleeha, direct wajen fridge ta nufa, buɗe cikin firjin dake shaƙe da kayayyakin abinci tayi, nan ta zaɓo manya manyan kaji guda biyu, sake wankesu tayi sannan ta ɗaura akan wuta tare dasa kayayyakin ƙamshi dana danɗano.
nan ta ɗibo irish patatoe tasoma ƙoƙarin ferewa, Hayatuddeen ne ya taso tare da soma taya ta, haka suka cigaba da firan, yana ta zuba mata surutu, mayafin dake jikinta ta ajiye, tare da soma yin aikinta cikin nutsuwa, yayinda Hayatuddeen gaba ɗaya ya sakota gaba da surutunsa, cikin abun da bai wuce awa ɗaya da rabi ba, ta kammala haɗa barbecued chicken da kuma patotoe balls, sai kuma bread Pizza, wanda gaba ɗaya ƙamshinsa ya cika kitchine ɗin, Hayatuddeen dake zaune agefe sai haɗiye miyau yake, dan har ya tsara irin cin da zaiyiwa bread pizza ɗin, da ƙamshinsa ya cika masa hanci, spearmint tea ta haɗa, sannan ta juyesa acikin flask, nan ta kimtsa gaba ɗaya kayan akan wani babban tray, duban Hayatuddeen tayi tare dayi masa alama akan yazo ya tayata ɗauka, aikuwa shi ya kwashe komai inda ya jere musu break fast ɗin akan dinning table, ita kuwa Zaleeha har yanzu tana kitchine, fruit salad ta haɗa, inda ta zubashi cikin wani babban glass bowl, tunanin haɗa chocolate fudge cake ne yazo mata, nan ta duba taga akwai komai na buƙata, kanta ta jinjina, sannan tashiga ƙoƙarin haɗawa, cikin mintuna ƙalilan kuwa ta kammala, ita kanta saida tayaba da ƙamshin chocolate fudge cake ɗin, Hayatuddeen dake falo kuwa koda ƙamshin yaje masa, saida yakasa haƙuri ya biyota zuwa kitchine ɗin, ganin, fudge cake ɗin yasan yashi cewa.
"Wow fantastic, Aunty Zalee dama wai kin iga girki har haka ne?, na ɗauka a faɗa da masifa chart da zuwa wurin aiki kawai kika iya."
Hannu tasa takai masa bugu, da sauri ya kauce yanayi mata dariya, hararan wasa ta watsa mai, tare da cewa. "Kaɗauka yanda kuke sakarkaru kaida Zakariyya haka kowa ma yake ne baku da aikin sai yawo a gari dama tsokana da ci."
Taƙare maganar tana me miƙo masa, wani haɗaɗɗen