Showing 6001 words to 9000 words out of 61846 words

Chapter 3 - Nakasa B Kasawaba Book 2 Complete Hausa Novel

cikin garin na Dukku me al'barka.
Kaitsaye gidan Bappa Ali suka sauƙa.
Sosai Aunty Mina tayi murnar ganin Ummin, nanfa lokaci ɗaya tacika mata gabanta da kayan ciye ciye, hadda dangin su fura da nono,
Sosai Ummi da Auntyn ke shan hiransu, kasancewar Bappa Alin bayanan, sunje gaisuwan wani abokinsu wanda bashida lafiya, shida Malam Ashiru.
Cikin ikon Allah Kuwa Ummi na idar da sallan azahar saiga Baffa Alin ya shigo, koda yaga Ummin yaji daɗi, saidai kuma zuciyarsa ta basa kan cewa ba lafiya ba, domin lafiya ƙalau babu abun da zaikawo Ummi Dukku ana tsaka da shirye shiryen bikin Saifuddeen kana kuma jiya-jiya nan sukaje amsa kiran nata.
Bayan sun gaisa da Bappa Alin ne Ummi ta gyara zama, lokaci ɗaya damuwa ya bayyana akan fuskarta, dubanta Baffa Ali yayi cikin sanyin murya yace.
"Lafiya kuwa? badai wanine bashida lafiya acikin gidan ba?."
Kai Ummi ta girgiza cikin ƙunan zuciya tace.
"Akan maganan auren Saifuddeen da yarinyar nanne, kamar yanda na faɗa muku kaida Malam Ashiru jiya cewa yarinyar nan batason Saifuddeen, tana masa barazanar matuƙar ya aureta zata kasheshi, to fa yanzu abin k'aruwa yakeyi dan bata daina ba, awancan karon kun tausasheni ta hanyar cewa nayi haƙuri nabari ayi auren, na haƙura badon raina yana soba, saidai ayanzu bazan iya haƙura ba, inamatuƙar jin tsoron abun da zai faru anan gaba, inatsoron rasa Saifuddeen, Bappa Ali kasan yanda Saifuddeen yake awojenmu dan Allah Kayi wani abu!."
Nan ta kwashe duk kan abun daya faru da kuma text message ɗin da ta karanta wanda Zaleehan ta turowa Saifuddeen ta faɗa masa.
Ajiyar zuciya maiƙarfi Bappa Ali yayi, tare da sanya hannu ya ɗan dafe kansa, tabbas zuwa yanzu yakamata yabita maganan Ummi, don kuwa tabbas ayanda Zaleehan ke faɗa da kuma bayyana tsanar Saifuddeen afili tabbas zata iya aikata koma miyene don ganin ta cutar dashi, tabbas shima zuwa yanzu kam yafara tsorata da al'amarin.
Ɗan jim yayi tare da gyara zamansa, cikin kulawa yace.
"Insha Allahu Ayau yau ɗinnan zan ɗauki Malam Ashiru mu tafi Gombe tun lokaci bai ƙure mana ba, haƙiƙa wannan lamari yayi tsaurin da dole sai manya sun shiga cikinsa, ki kwantar da hankalinki, Insha Allah zamuje mu samu shi Malam ɗin, zamuyi magana ta fahimta dashi, bakuma zamu ɓoye masa komai dake faruwa ba, tabbas nasan zai fahimce mu, shi kuma Saifuddeen Allah yabasa wata mace tagari wacce ke ƙaunarsa!."
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ummi ta sauƙe tare da cewa "Ameen!."
Har cikin ranta taɗanji sanyi, haka dai suka ɗan taɓa hira kaɗan kafun daga bisani tace zata koma.
Haka suka rakota har wajen mota inda Sule driver ke jiranta.
Haka Ummi suka kama hanyar shigowa cikin garin Gombe zuciyarta wasai, tanajin kamar ta raba Saifuddeen da ƙaya.
Tafiyar 1 hour ne kacal ya kawosu Gombe, inda ta koma gida zuciyarta cike da salama, saidai kuma ta wani ɓangare, cike take da tausayin Saifuddeen, domin kuwa koda sau goma zata kalleshi, to akowani kallo ɗaya, saita hango zazzafar ƙaunar da yakeyiwa Zaleeha acikin ƙwayan idanunsa.
Amma addu'a bata bar komai ba. Zata tayi masa addu'a akan Allah Ya musanya masa da mafi alkhairi.

Su Bappa Ali kuwa ƙarfe biyar dai-dai suka kamo hanyan zuwa garin Gombe shida Malam Ashiru, daga cikin abun da Ummi ta faɗa masa, ko ɗaya bai rage ba, haka ya labartawa Malam Ashiru komai, shikansa Malam Ashiru saida yaji zuciyarsa tayi masa ba daɗi, tabbas yasan sharrin ƙiyayya, ƙiyayya bata da daɗi sam, kuma takan rufewa mutum ido, yayi duk abun dayaga dama, musamman ma ga mace da auren mijin da bata so dan haka shima ya yarda baza'ayi wannan aurenba.

Ƙiran sallan Magriba acikin garin Gombe tayi musu, nan suka tsaya sukayi sallah, inda suna idarwa suka nufi gidan Dirankaɗi, wato Baban Ishaq kenan, kasancewar tunkan su taso sunyi masa bayanin komai sun kuma sanar dashi zuwansu, inda shikuma ya ƙira Baba Malam ya shaida masa cewa da anyi sallan Isha za su zo.
Koda suka ƙarasa gidan na Dirankaɗi, anan sukayi sallan Isha, daganan suka wuce zuwa G.R.A wato unguwar su Zaleeha.
Tarba me kyau suka samu daga Baba Malam, inda ya sauƙesu acikin babban falonsa, nan yasa aka cika musu gabansu da kayan ciye ciye,
hira kaɗan suka ɗan taɓa, kafun Dirankaɗi ya gyara zama inda ya fuskanci Baba Malam, cikin nutsuwa haɗi da halin dattako yashiga labartawa Baba Malam abun dake faruwa, da irin saƙon text message din da Zaleehan ke turawa Saifuddeen wanda suke ɗauke da barazana haɗi da baƙaƙen maganganu, inda ya ɗora da cewa.
"Kayi haƙuri Malam, amatsayinmu na manya masu hankali, baikamata ace mun zuba ido hakan na faruwa ba, haƙiƙa duk auren da akace akwai ƙiyayya acikinsa to mafi al'khairi shine barinsa, tabbas babu wani uba dazai so ɗansa ya rasa iri awannan gida naka mai cike da kamala haɗi da tarbiya, saidai kuma babu yanda zamuyi ɗaukan ƙaddara ya zame mana dole, saboda hakane mukazo baka haƙuri, kayi haƙuri Malam bisa dole munjanye nemawa Saifuddeen auren Zaleeha da mukayi, fatanmu shine Allah ya bawa kowannensu abokan zama nagari!."
Ajiyar zuciya Baba Malam ya sauƙe tare da ɗanyin jigum, tabbas Zaleeha nason dasa masa ciwon zuciya, sannan tanason zubar masa da ƙima da kuma mutumcinsa a idanun jama'a, saidai kuma yayi al'ƙawarin bazai taɓa bari hakan ya faru ba, gyara zamansa yayi tare da duban su Baffa Ali, cikin dattako haɗi da tausasa zance yace.
"Babu wani abu dazan faɗa muku face haƙuri, kuyi haƙuri, haƙiƙa nine nan mahaifin Zaleeha, sannan nike da ikon bada aurenta ga koma waye, tuntuni nakuma bada aurenta ga Saifuddeen, kamar yanda Zaleeha take ƴa awajena, hakama Saifuddeen, shi ba iya ɗalibina bane kaɗai, inajinsa kamar jinina, saboda haka kuyi haƙuri, kujanye batunkun fasa auren, Zaleeha ƴatace kuma inada ikon tanƙwarata duk yanda naga dama, kuyi haƙuri ku ɗauka cewa duk waƴannan abubuwan da takeyi yarinta ne kuma zata daina watarana, tabbas nasan yanzu giyar ƙuruciya ne ke ɗibanta, nan gaba kaɗan bazatayi abun da tayi yanzu ba."
Ɗan jim yayi tare da cigaba da cewa.
"Kuyi haƙuri dan Allah, Amatsayina na Uba agareta na baku haƙuri, kuma kamar yanda kuke sha'awar haɗa zuri'a dani, haka nima nake sha'awar haɗa zuri'a daku, musamman Saifuddeen daba kowani uba bane zaiƙi son zamowarsa suruki agaresa, kamar yanda na faɗa muku tun daga farko babu abun da zan faɗa daya wuce nace kuyi haƙuri insha Allah aurennan ba fashi."
Da sauri Malam Ashiru ya fara jujjuya kai a hankali tare da cewa.
"A a Malam kayi hak'uri abar batun auren nan mu kam mun janye.....!







BY
*GARKUWAR FULANI*
[9/9, 9:05 PM] +234 806 222 4030: Ahankali ta murɗa ƙofar toilet ɗin ta fito,  sanye take da wani pink ɗin bathrube yayinda gaba ɗaya gashin kanta ke jiƙe da ruwa, da dukkan alama dai, daga wanka take,  fuskarnan tata akwaɓe take sam babu alaman fara'a asamanta, sosai abunda Saifuddeen ɗin yayi mata safiyar jiya yake cinnta tare da ƙara sosa ranta, inda yake ƙara motsa duk wani ɓacin ranta,    ƙarasawa gaban dressing mirror tayi ta zauna, dai-dai lokacin aka turo ƙofar ɗakin aka shigo,  azabure ta juyo don ganin kowaye yayi gangancin shigo mata ɗaki babu sallama.
Idanunta ne sukayi mata tozali da Balkeesu, ganin Balkeesu yasa ta sauƙe ajiyar zuciya, tare da juyawa tasoma ƙoƙarin shafa mai ajikinta, don acikin yanayin ɓacin ran da take ciki batajin zata wani iya nunawa Balkeesun cewa tayi farinciki da zuwanta.
Cikin yanayi na tsantsar mamaki Balkeesu ke kallon Zalihan, ba abun daya ɗaga hankalinta kamar ganin gashin Zaleehan ajiƙe da tayi, cikin mamaki haɗi da tsantsar gulma dake cinta tace.
"Zaleeha badai barinsa kikayi yayi ba?."
Juyowa Zaleeha tayi tare da ɗan dubanta, cikin rashin fahimtan maganan Balkeesun fuska a haɗe tace.
"Yayi me?."
Hararanta Balkeesu tayi tare da cewa.
"Meyasamu gashinki naganshi ajiƙe? inafatan ba kanki kika mallaka masa ba dai ko?."
Wani irin harara Zaleeha ta bankawa Balkeesu, tare dayi mata kallo, irin na baki da hankali ɗinnan.
Cikin hasala ta furzar da iskan bakinta, inda tace "Allah ya sauwaƙe ni Zaleeha nabawa wani wanda ba zaɓin raina ba jikina,  ke koda ma zan iya mallakawa wani kaina, to kidaina tunanin zan mallakawa wannan mugun virginty ɗina.
To wai ma kina tunanin ayanda yake always akan wheelchair zai iya amsan virgin ɗin macene, chab shirme ma kenan, mutumin da kullum yake bisa kujera kamar wani sarki." 
taƙare maganan tana me taɓe bakinta.
Murmushin jin daɗi Balkeesu tayi tare da cewa.
"Nasani ko zai iya karɓa abu a duhu."
Tsuka Zaleeha tayi tare da cigaba da shafa body lotion ɗinta.
Tana kammalawa taɗan murza powder akan baby face ɗinta,  tashi tayi tare da ƙarasawa gaban makeken drawer ɗinta,  wani yadi mai laushi wanda yaji ɗinkin riga da sket ta ciro tare da sanyawa, sosai kayan yayi masifar amsar jikinta, sosai surar jikinta ya bayyana, musamman ma hips ɗinta, dogon gashinta ya kama atsakiyar kanta, inda tayiwa kanta wanka da wani turaren oud mai ƙamshin gaske.
Duk abun nan da takeyi idanun Balkeesu na kanta, sosai Zaleehan tayi mata kyau,  tarasa meyasa hakanan Zaleeha kowani kaya tasa sai sunyi mata kyau, wannan yana ɗaya daga cikin abun da yasa, akullum kishin Zaleehan ke ƙara ruruwa acikin ranta, akusa da ita Zaleeha ta zauna tare da dubanta, cikin takaicin abun daya faru jiya tsakaninsu da Saifuddeen ɗin tace.
"Bazan zauna ba Balkeesu, inajin kamar ana huramin wuta aƙasan zuciyata, sam bazan iya cigaba da zama agidannan ba, wlh ji nake kamar ana korata daga ɗakin, akullum tsanarsa ƙara yawa take acikin zuciyata, banajin zan zauna har zuwa lokacin da muka tsara in sashi ya sakenin, idan ban gudu yauba to tabbas zan gudu gobe."
Murmshin gefen baki Balkeesu tayi, take zuciyarta tayi haske, dajin maganganun Zaleehan saitaji kaman an ɗauke mata wani nauyi dake kan ƙahon zuciyarta ne.
Gyara zama tayi tare da duban Zaleehan cikin ƙara ƙarfafa mata taurin zuciya tace.
"Bazan ce kada ki gudu yau ko gobe ba Zaleeha, saidai kuma guduwarki da gaggawa, zai iya haifar da rugujewar plant ɗinmu, tunda ai in guduwa kikayi da aurensa a kanki zaki gudu ko, ni kuma nafi son ki sashi ya sakeki inma zaki gudun kinga kin fita rayuwarsa salim alim,
sannan kadafa ki manta da cewar shekaran jiyannan aka kawoki, kibar maganan guduwan nan har sai lokacin da muka tsara ya cika please ki tsurfa musu rashi mitunci gidan gaba ɗaya ta yadda dole ya sakeki."
Kai Zaleeha ta rinƙa jujjuya mata cikin sanyin sauti tace.
"Bazan iyaba, me mutanen gidan sukayi min da zan musu rashin ɗa'a? Ina son Umminshi dan tanada kirki hakama ƙannenshi suna sona, kuma nima ina sonsu musamman Ummi da autanta,
Kuma shima ɗin ya za'ayi in mishi rashin kunyar bayan tsoronshi nakeji yanada kwarjini da yawa, ko idanunshi bana iya jurar gani, kuma dai ko yaya zanyi yanzu yana matsayin mijina ne, ya zanyi mishi tijara Allah yayi fushi dani in tarawa kaina zunubi. Gwara kawai in gudu yafi min al'khairi, bazan iya zaman ɗakin nanba da gidan Allah ji nake kamar korata akeyi."
Wani irin mugun harara Bilkeesu ta watsa mata kana tace.
"To mai imani da miji da tsoron Allah ai sai ki gudun kifi ruwa gudu in kinga dama ki dai sani in kin gudun nema tofa da aurenshi a kanki."
Shiru Zaleeha tayi tare da kawar da kanta gefe, tarantse bazata zauna da Saifuddeen ba, tagwanmace ta tabbata babu aure datai ta zauna dashi, tana ji a jikinta da zuciyarta cewa zata jira abun sonta, koda nan da shekara ɗari ne,  sam zama da Saifudden banata bane.

Saifuddeen kuwa, hakanan yakejin zuciyarsa wasai tun jiyan,   sosai murmushi ke bayyana akan kyakkyawar fuskarsa, musamman ma idan ya tuna da mood ɗin Zaleehan na jiyan tsantsar tsoronshi ne da fargaba ya hango acikin ƙwayan idanunta can ƙasan tsiwar da take mishi,  kaitsaye banɗakinsa ya wuce,  wanka yayi sannan yafito inda ya kimtsa kansa cikin wata ɗanyar purpule ɗin shadda mai masifar kyau, sosai yayi kyau, yayinda farar fatarsa taƙara bayyana acikin kayan,  shaddan irin ɗinkin nan na half jumper akayi mata,kasancewar haka nan shiyake bayason full jumper yafison half, duba da yanayinsa wanda ko yaushe azaune yake, so bayason duk wani abu dazai takurasa.
turarensa mai daɗin ƙamshi ya fesa, tare da sanya Cumb yaƙara taje kwantacciyar suman dake kansa, ƙarasawa gaban mirror yayi tare da ɗan duban kansa, shikansa yasan cewa yayi kyau, cikin nutsuwa ya danna madannin kekensa, wayoyinsa kawai ya ɗauka, inda ya fice daga cikin ɗakin, koda yazo falon na Zaleeha bai iske kowa cikinsa ba, hakan yasa kaitsaye yafice daga sashin nasu.
Direct ɓangaren Umminsa ya nufa, tundaga bakin ƙofar falon na Ummi yakejin hayaniya na tashi, koda ya shiga nan ya iske su, Ahmad, Ishaq, Wareesu, Saminu da kuma Saleesu, Mudassir harma da Hisham da Jabeer, Aziz gaba ɗayansu sun baje, yayinda aka cika musu gabansu da kayan ciye ciye, Ahmad da Salisu ba kunya haka suke lodawa cikinsu abinci, sam baruwansu da wani surkuntaka, saboda sunaganin duk suɗin ƴan uwan junane, haka kuma Ummi mahaifiyace agaresu, saboda haka babu wani batun noƙe-noƙe, duk da cewar ansan fulani da kunya, saidai sabo da kuma zumuncin dake tsakaninsu ya goge wannan kunyan.
Cikin mamaki yake kallonsu don sam basu sanar dashi zuwansu ba.
Ƙarasowa cikin falon yayi,  inda yakai hannu ya zunguri Ishaq wanda ke  ta faman suɗe hannunsa wanda yaci masa dashi, bakomai yasashi suɗe hannunba kuwa face daɗin miyar masan, shikam har yau baiga macen da takai Ummin Saifuddeen iya girki ba.
Ishaq kuwa cikin gane wanda ya zungureshi yace. "Banason wulaƙanci fa Saifuddeen, wato wulaƙanci zaka mana saboda mun riga mun damƙa maka amaryarka a hannunka ko?."
Gaba ɗayansu sukayi murmushi inda Saminu yace.
"Manta dashi da Allah, nasan bazai wuce haushinmu yakeji ba, kasan dai Saifuddeen sakaline baison wani ya raɓi masa Umminsa, kuma mumadai Ummin nan nasonmu."
Saminu yaƙare maganar yana me kai loman gandar fatan saniya, wanda yaji haɗi sosai, sai ƙamshin su kanumfari yake.
Kai Ahmad ya girgiza tare da duban Saminu cikin yanayi na tsokana yace.
"Surkinka nefa Yayan matarka."
Hararansa Saminu yayi tare da cewa.
"Kamanta tare mukai wasan ƙasa."
Dukansu suka saka dariya, banda Saifuddeen wanda shi kullum murmushine aikinsa, da haka yasaba kuma hakan yafi yi masa kyau, aduk sanda yayi murmushi idan kumatunsa da tsakiyar gemunshi da goshinsa suka lotsa, sai yayi wani irin fitinannen kyau.
Dai-dai lokacin Ummi da Goggo Dada suka fito daga cikin kitchine, bayansu kuwa Raliya ce riƙe da plate, wanda samansa ke shaƙe da yankakkun kayan fruits, agabansu ta dire musu plate ɗin, duban Ummi Saifuddeen yayi tare da shagwaɓe fuskarsa, cikin body language ɗinsa yayi mata alama da cewa.
"Shine kika wahalar da kanki wajen haɗawa waƴannan ƙattin abun karin kumallo ko bayan ga matansu!."
Gane abunda yake nufi yasanya Ummi sakin murmushi,  ƙarasowa cikin falon tayi tare da sanya hannu ta shafi lallausan suman kansa, cikin kulawa tace.
"Ae duk al'barkacin aurenka sukeci."
Jin abun da Ummin nasa tafaɗa yasanyashi sakin murmushi, idanunsa ya ɗan lumshe, ahankali ya dubi Goggo Dada nan yayi mata alamun gaisuwa, da fara'a ɗauke akan fuskarta ta amsa, tare da ƙarayi masa murnar biki.
Nan suka zauna inda suka shiga ɗan taɓa hira kaɗan, su Hisham na gama kammala cin abincin Goggo Dada tasanar dasu cewa zasu buɗe kan ango da amarya tunda dai jiya bata samu taje wajen diner ɗinba,  nan dukansu sukayi na'am, inda Aunty Meenat ma da fitowarta daga ɗakin Ummi kenan tace itama zata yiwa ango nasa liƙin,  su Adda Rahama da Raihana ne suka firfito falon, nan fa Ummi tace da Raihana taje ta ƙirawo amarya.

Zaleeha kuwa har zuwa yanzu suna tare da Balkeesu, inda Balkeesu ke ƙara fomfata tana kuma kunnata akan kada ta gudu ta tsaya ta fetsarewa mutanen gidan ta yadda uwarshi da kanta zatasa ya saketa shi kuma ta nuna kasheshi zatayi,  ita dai Zaleeha abun daya dameta ne ya isheta don wannan karon dai zugar bilkeesu ba abar ɗaukar mai hankali bane, to bare kuma asirin Mama ya riga zugar tasiri.
Ƙoƙarin kwanciya take, sukajiyo knocking door,  azaton Zaleeha Zaheera dake kallo afalo ne hakan yasa tace.
"Yes come in."
Ahankali Raihana tatura ƙofar ɗakin tashiga, ganin Raihana yasa Zaleeha ɗan sakin fuskanta, duk da batasan wacece ita ba, amma kallo ɗaya tayi mata ta hango matsanancin kaman da sukeyi da Aljanin gurgun da tsanarsa tayi mata tsaye acikin rai sosai ta yaba da kyan Raihana kuma har ranta taji tana sonta.

Balkeesu kuwa baki tasake tana ƙarewa Raihanan kallo, gaba ɗayama hankalinta yatafi ga tsadadden zanin dake jikin Raihana'n, domin kuwa babban Chiganvy ne ɗan ubansu.
Murmushi Raihana tayi tare da duban Zaleeha cikin kulawa tace.
"Idan babu damuwa muna buƙatarki afalo, za'a ɗanyi muku buɗan kai ne!."
Dammm haka Zaleeha taji ƙirjinta ya doka, sam batason abun dazai ƙara haɗata dashi, musamman idan ta tuna da abun daya shiga tsakaninsu jiya saitaji kanta kamar zai buga gaba ɗaya tsoro lamarinshi ke bata.
Cikin baƙinciki da takaici Balkeesu tace.
"Mezai hanamu zuwa kuwa, ai zamuzo yanzun nan." tafaɗa tana me miƙewa tsaye dan samawa Zaleeha mayafi, ɗan murmushi Raihana tayi tare da cewa.
"Badamuwa, ai bama sai kunzo ku dukanku ba, itaɗin dai kawai muke buƙata!."
ta ƙarishe mgnar cikin yatsina fuska dan sam ita da Bilkeesu bata konta mataba, Zaleehan kanta a fakaice take sonta tunda ance bata son Hammanta ita kuwa duk wanda yace baison Hamma Saifuddeen ɗinta itama bazata sotaba.
Ƙasake Balkeesu tayi tare da watsawa Raihana harara ƙasa-ƙasa, tabbas maganace afakaice Raihanan ta faɗa mata, amma dai koma menene ta rantse saitaje anyi buɗan kan da'ita.
Wani tsantsareren mayafi laffaya Zaleeha ta yafa aduka jikinta inda ya sauƙo ya rufe har fuskarta, wani flat shoe kalan yadin jikinta ta sanya aƙafafunta,  Raihana da kanta taƙara fesa mata turare nan Balkeesu uwar gulma tariƙe Zaleehan, Raihana na gaba sukuma suna biye da ita abaya haka suka nufi cikin gidan.

Sunanan zaune afalo suna ɗan taɓa hira, daddaɗan ƙamshin daya ziyarci hancinsa shiyafara sanar masa da zuwanta, juyawan dazaiyi kuwa ya hangota cikin wani light orrange ɗin mayafin laffaya mai tsananin kyaun gaske, sai walwali da sheƙi yake, Raihana da kanta ta kamo Zaleehan, inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login